← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 144

Sashe 48

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga chan bangaran Iya tace"Ina ga daga nan ne ya huto nan cl jiya ma muna tare dasahi da Safe."
Sai alokacin ya Fahimci dawa Ummi ke waya sai yaji hankalinsa ya tashi kada Iya ta ballomai ruwa fa.

Yana ji Ummi na fadin"Bai fadamin ba iya..!."
Sai gabansa ya fadi Ras..Nan take Ummi ta Dago wayar ta saka a speaker sanda Iya ke fadin"Ai jiya mun so mu koma wajen mai mgani yace shi ya warke sai hamdala muke yi.."
Dayake ai Iya ta kira Ummi tamata bayanin mganin data ke nemama Saifudden din kan Aljanna ta auresa,Itama Ummi Dayake ba ruwanta da wannan Shigen shigen bata Dauki mganar da Muhimmanci ba tunda shi kanshi Yaro ai bai gayamata komai ba basu taba mgana ba.

Amsa mata tayi da "Alhamdullah to anyi barka tunda waraka ya samu."
Iya tace"Wlh ai shine har na taso da mganar maida auran Sa da majeeda sati mai zuwan nan ma yake fadamana yana neman aure a zaria ma.."
Ummi Cikin mamaki ta kai kallonta kan Saifudden wanda yayi kasake jikinsa ya saki ya kasa mgana duk da Sanyin A.c sai zufa yake yi Ummi ta kasa Hankalinta wajen Iya tana Fadin"Topah ni bansani ba Iya."
Iya tace"Wani irin baki sani ba..Yace ma kin santa.."
Ummi ta kallesa cikin mamaki shi kuma sai ya sadda kai gabansa na fadi shima ya fadi hakane saboda mafitansa ba Domin yana nufin hakan ba.

Ummi tace"Gaskiya iya ban santa ba..Kai yaro wacece domin ni dai bamu taba mganar dakai ba..?.

Tafada tana kallon Saifudden daya kasa mgana Iya da Baffa Hashimu dagachan bangaran suna jinsu.

Ummi ranta ya fara baci ta dakamai Tsawa tana Fadin"Nace wacece har da zakayi karyan na santa alhalin ban santa ba.."
Kamar wanda aka kwaci bakinsa kawai yaji ya furta"MUHIBBA ce Ummi..!

Muhibba..!"
Gaban Ummi ya fadi ta Bude baki Tana Fadin"Wata Muhibba din?

Domin sai taji bata wani ji dadai ba Sanin su iya na jinsu yasa yace"wacce kika sani yarinyar nan ta zaria."
Ummi ta saki baki ta rufe yafi sau Biyar Iya Dagachan bangaran Tace"Kin ganeta kenan zaliha.!?

Ummi ta Hadiye miyau mai zafi kafin tace"Eh na ganeta iya..Muna da zumunci ma dasu..."
Iya ta tabe baki daman ai tasan za"a rina a karkace tace"Zumunci ta ina..?

Ummi tace"Mahaifinta Aminin yaya Sunusi ne kafin rasuwarsa."
Iya tace"Uhm Daman ai Danginsa ne Ki kasa yake kin su Zaliha ammh naki Dangin ke kike sakashi ya so su..To ni ban Damu da ya aurenta ba ammh ya sani itama majeeda ba fashi Rana ita jiya sati mai zuwa za"a maida auransu in an shirya mganar ita wanchan baffanin sa sai suje su nema masa ai mijin mace hudu ne shi bazamu hanasa abunda yake so ba sai dai kamar yadda zai auri naki zabin muma namu kamar yayi ya gama."
Ummi zata yi mgana Iya ta katse wayarta Dagachan bangaran tana ta masifan Zaliha da Danginta sun rainata Baffa Hashimu na zugata.

Ummi kuwa tafi minti goma rike da waya tana ma Saifudden dayaki Dagowa ya kalleta kallon mamaki Tana maimaita sunan Muhibba acikin ranta.

Cikin Fusata tace"Kai dago ka kalleni bana son rainin wayau..!"
Da sauri ya dago yana kallonta Daman Ummi ai bata da wasa wani Lokaci..

Nunasa tayi da yatsa tana Fadin"Ka fadamin gaskiya mganar da ka fadama su iya ko A"a raina mu daka saba ne yau ka fara ta kansu..?

Saifudeen ya sosa kansa yana Fadin"Am Serious Ummi."
Da karfi tace"Karya kake yi..ai na sani ba sonta kake yi ba kayi amfani da sunanta ne ka Rugaza mganar Majeeda sai dai bakaci nasara ba..Maimakon haka sai ka jamin zargi da Zagi wajen dangin Ubanka.

Tafada Ranta na Tafasa Saifudeen ya marairaice kafin yace"To ya zan yi Ummi..!,?Har ga Allah bana son yarinyar nan tayi karama da yawa gata kazama rayuwarmu ba Daya ni fa bansan sadda bakina ma ya Furta wannan yarinyar ba Ummi kiyi hakuri kada kice komai yanzu har Satin yazo ina da yakinin bazasu maida aurena da yarinyar nan."
Ummi tana Hararansa tace"Bazan taba baka goyon baya ba wannan karon..Kaje kabi dangin Ubanka na daina yarda ka kara jazamin Damuwa kan aikin daka ke aikatawa"
Rarrafawa yayi ya kama kafarta yana Fadin"Plz Ummi."
Ummi tace"In Iya ta matsa sai an je Zarian neman auran fa me zan ce mata..?.

Saifudden yace"Sai aje Ummi..Gwara ita MUHI din sau dubu kan na kara auran wannan yarinyar plz Ummi."
Sai da ya fada sannan ya tuna ma ga abunda yace to ya iya..?

Yana ji aransa Zai iya zama da Muhibba sau dubu bai zauna da majeeda ba sannan akaai wani abu mai girma game da yarinyar wanda kemai nauyi a kirji da bai san komiye ba.

Ummi tayi dariyan Takaici kafin tace"Ni yaro ai kagama shani masilla..In je in shige maka gaba Daran Farko ka sako musu y"a..?

Muhibba kamar su Laala nake Daukanta bazan yi sonkai saboda kana D'ana ba..Nasan baka sonta so kake yi ka cimma manufarka mu ka barmu da jin kunyar Iyayenta masu karamci."
Saifuddeen ya kara rike kafafun Ummi yana fadin"Ummi ba haka bane Bazai taba faruwa ba.."
Ummi ta kallesa rai bace tace"bazai faruwa daman ai bazai Faru ba..Bana son mganar banza kada na karajin mganaar muhibba abakin ka kaje ka auri wacce Dangin Ubanka suka Zaba maka kada ka kara min wannan mganar sannan ka koma ka fada musu karya kake yi ba wannan mganar ayanzu na samu kwanciyar Hankali bana son damuwa"
Ta fada rai bace tana kokarin mikewa yana kara riketa Hannu ta Daga tana Fadin"Sakarni ko na Duma maka Dundu wlh."
Kin Sakinta yayi aiko ta shiga Duma masa Dundun son ranta har ta gaji bai Saketa ba sai ta koma ta zauna tana Fadin"Nima ka maida ni su iya kenan ko...?

Jin haka yasa ya saketa ya koma gefe ya Dafe kansa mikewa tayi Dauke da wayarta tana Fadin"Ka koma ka warware wannan mganar domin bazan amince da ita ba..Da sauran kimata bazan bari ka yayemin ita ba"
Daga haka ta shige Dakinta ta barsa nan zaune kai dafe ya rasa mafita Wata zuciyar tace to kai sonta kake yi da zaka damu da mganar Ummi..?

Ba kana da tabbacin in Majeeda tace bata son auran nan baza"a daura ba..?

To meyasa ka Damu..?.

Sai kuma ya rasa Dalili haka ya shiga Dakinsa duk yadda yaso ya zauna yayi Tunanin Damuwarsa sai ya kasa yana kwanciya kamar an dannesa sai barci bai iya Tuna komai bama.
*Janafty*
*SFD0018*
*Amnaf_sudanese _collection*
*Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401*
*Ki biya ki karanta cikin salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba, kada ki karanta min littafi sannan kada ki yada'min shi don Allah pay N500 via jamila umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*
Saboda ba su yi gudu sosai ba yasa basu isa akan Lokaci ba sai wajen biyar da rabi na yammah gidansu Amaryan mai suna Sa'adatu suka fara zuwa dake nan cikin garin bauchi su Ummi kadai suka sauke Dangin ita Sa"adatun suka fito suka taryesu Daman Tuni sun san da zuwansu da kuma suka taso Dattin ya kira ita Amaryan nasa ya sanar da ita tasowarsu anyi anyi su tsaya su ci abinci suka ce sai sun dawo cikin gari suka shiga Saifudden ya kama musu Dakunan Hotel Guda hudu daya nashi daya nasu bama guda biyun nsu Datti ne.

Daman duk yana jinsa a takure ne,kamar mara Lafiya bai saba dogon Tafiya ba sannan tafiya cikin Taro haka bai saba shi ba sai dai in zasu raka gwamna wani taro mai muhimmamci tare da sauran kwamishinoni shima duk a Takure yake balle yanzu.

Wanka suka farayi suka sauya kaya sannan suka fito domin komawa gidan Amarya su ci abinci su kuma gaida surukai Saifudden yace su je kawai shi ba inda zai je sanin Halinsa yasa ba wanda ya Damu dashi nan suka tafi suka barsa Dakyar ya iya Rama Sallolin dake kansa sama sama Daganan ya kira Handline din Otel din yace a kawo mai Tea da kwai soyayye su bama ma yace su karbi abunda suke da bukata Lokaci kadan sai gashi an kawomai ya karba ya shiga dashi Ciki yasha Tea din da yawa Saboda yana jin yunwa kwan ne yaji salaf sai karni ya Turesa kyamkyami ya rufess bai ci sa ba,Daganan gado ya haye barci nacin idonsa yana kwanciya bai kara sanin inda kansa yake ba,balle yasan Lokacin da su Muhajeed suka Dawo sai da Safe suka Hadu dasu bayan Mujaheed ya shigo inda yake nan yake Fadamai jiya sai afer ten suka Dawo.

Saifudeen na zaune gefen gado yana Danna Tab dinsa daya kunnata bada Dadewa ba yace"Duk kuna menene har Tsawon wannan lokacin baku dawo ba..?
Chapter 48 · 0% Book details