← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 144

Sashe 84

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da Sauri Sani yace"As u wish Sir.."
Saifuddeen ya kara murmusawa kafin yayi mgana Sani ya rigasa da fadin"Wato ranka ya Dade ayi hakuri na Dauka wayar tata bata tayi ko an Sace ne..To dayake kasan Ita din Auta ne yar gatace in akaji Labarin nayi mgana da wanda ya Dauke wayar nan har ta Salwanta to Inna ma sai ta Daina min mgana Ballatana Ya Habibu mugun ji da ita yake kamar ita Kadai suka Haifa ga Anty Habiba ma agefe ina fada maka in na tafi makaranta mantawa ma dani suke su dai Burinsu ya Cika ga Auta a gefensu Yallabai in fada maka gaskiya ni kaina Ina ji da ita duk da wani zubin kana ganinta shuru shuru ba Mutumci gareta ba haka nayi ta Hakuri da ita har yan Dauke Dauke yarinyar ta sha yi min ammh bayan tayi auran sai na yafe mata a baya dai naso na cire Lissafin cikin kudin da zan bama Inna na Gummuwar Bikinta sai kuma na yafe mata tunda ina gaba da ita."
Sani ya karishe Fada Hankalinsa kwance me Saifudeeen zai yi in ba Dariya ba tun balle ma daya Dago ya kalli Muhibba yadda take kallonsa Ido duk a waje cikin Nishadin daya Dade bai yi ba yace ma Sani"Nice to meet u Barrister..Zan so kwarai watarana ka kawo mana Ziyara ina nan."
Sani yace"In sha Allahu Ran ka ya Dade..Zan dawo nan da 2weeks zan shigo mu gaisa"
Saifudden yace"Da naji Dadin haka Barrister"
Sani kansa girma yake yi in Saifudden ya kirasa da Barrister ai Muhibba bata ji jiri jiri na shirin kayar da ita Sai da taji Saifuddeen na Fadin"Bani Labari wani irin yan Dauke Dauke AUTA ta taba yi maka..?

Yafada yana kallonta Muhibba da ta zaro ido tana kallonsa cikin mamaki Sai kawai ya Daga mata gira Sani kuma an Samu Dama ai sai ya Bude baki ya fara Zuba duk wani kalan Fadan su da Muhibba sai da ya Zayyano mai Muhibba kuka ne kadai batayi ba Sani ya gama da ita ganin haka yasa ta yi yunkurin barin Falon da Hannun ya Dakatar da ita Lokaci daya ya nuna mata Kujera alamun ta koma ta zauna jikinta a sanyaye ta koma ta zauna kamar kankara haka ta Daskare balle da taga Saifuddeen na kallonta yana yi yana Dariya Lokaci bayan Lokaci Sai taji yace"Gaskiya Auta bata kyauta ba.."
Sani yace"Ai ta yi rashin mutumci yarinyar nan ina gaya maka yallabai gashi ni tafi sakama ido duk abunda nayi idonta na kaina ni dai nace duk kushen mai kushe wlh sai ya ganni ya barni"
Saifudden na shafa kansa yace"Kwarai Barrister..Naga tana ta Hararan mu zan karbi lambar wayarki barrister i will call u In sha Allah."
Sani yaji kamar an bashi kujeran makka ya fara kirari yana Fadin"Allah ya kara girma yallabai Godiya nake yi"
Saifuddeen yace"My pleasure..Gata ku yi sallama"
Da Sauri Sani yace"A"a kyaleta mun yi Tsiya ko ka bata Baram baram zamu rabu ka gaisheta sosai"
Saifuddeen ya jinjina kai kafin yace"Ok..Thank you so much Barrister U make my Night sai na kira ka din"
Da ga haka sukayi sallama Saifuddeen ya Sauke wayar sa daga kunne yana kallon Muhibba da kanta ke kasa Tana wasa da yatsun hannunta Miko mata wayar yayi yana Fadin"Ur phone..!

Jikinta ba kwari ta mike taje zata karba ta rike sai yaki sakin mata ta Dago tsuka Hada ido cikin son ya Tsokane ta yace"Fatan nima bakya min Halin yan Dauke Dauken da kike ma Barrister ko..?

Muhibba taji ina kasa ta shige kunya ya kamata ta Runtse ido kafin tace"Wlh sharrin Sani ne Sau daya ne..Na taba Daukan masa wani Turare"
Da sauri yace"Ashe gaskiya ne."
Da Sauri itama tace"Ban yi amfani dashi ba Inna na ba mawa ita kuma tayi kyauta dashi"
Iya gaskiyanta ta fada shiyasa sai ta basa Dariya wayar ya mika mata yana Fadin"Ki Turomin Lambar Barrister i like Him.. na tunasa na gansa sau biyu ko uku ne har ranar Daurin auran mu ma He is so Friendly ina taya ki murna da kika Samu Brother kamar sa he is so Nice"
Sai taji sanyi aranta ta saka Hannu ta karbi wayarta Lokaci daya tana Fadin"Nagode..!

Kai tsaye yace mata"Must wlcm"shirin juyawa take ta bar Falon ya Kira sunanta"Muhi..."
Ta fahimci haka yake kiranta shiyasa ta waigo tana kallonsa kujera ya nuna mata ta zauna tana Fadin"Have a sit please..'
Ba musu ta koma ta zauna kanta na kasa tana matse kafafunta kai tsaye taji yace"Bani Labarin ki naji MUHIBBA.

Ina so na san komai a kanki..Kema if u like zaki san komai a kaina."
Sai ta Dago tana kallonsa sai ya Daga mata kai lokaci daya yana lumshe idanu
wansa kanta ta maida kasa sannan ta shiga bashi Tarihinta Tunda farko har zuwa Sanda Mahaifinsu ya rasu da gatan da Inna da yan"uwanta suka nuna mata duk yana sauraranta sai kawai taji yace"Lalle Baba na sonki..Allah ya jikan sa da Rahma"
Kanta na kasa ta amsa da Ameen ta cigaba da basa Labarin karatun ta har matakin B.ED da yadda ta Samu aiki a makarantarsa inda suka Fara Haduwa.

Katseta yayi da Fadin"Baki bani Labarin Sani ba..?Sannan Samarin ki nawa..?Friends fa..?

Dagowa tayi tana kallonsa Cikin mamaki shi kuma sai ya jinjina mata kai yana Fadin"Yes duka ina so naji"
Mirmishi tayi ta maida kanta kasa Kafin tace"Sani ya fada maka komai..Samari kuma ni duka bana son su Friend bani da ko daya sai wadanda muke Huldar arziki dasu..Har gobe bani da wata kawa..Kawata Daya ce INNA TA sai Anty Habiba in kuma amaza ne Ya Habibu da Sani"
Mirmishi ya sakar mata kafin yace"Happy Family..Nice a labarin ki kin Tauye abu daya mai matukar muhimmanci."
Da mamaki ta kallesa shi kuma sai ya Gyara zama yana Fadin"yes..Kin manta baki Bani Labarin Waye SAIFUDDEEN BA..?
muhibba ta Dago kanta da Sauri Cikin Razana da mamaki kafin ta Bude baki Cikin wani yanayi tace"Wa..Wani Saifuddeeen din kai..?"
Ta fada tana nunasa kai ya girgiza mats kafin yace"Ni ai Mutum ne Muhi..ALJANIN da kike gani mai suna SAIFUDEEN da irin suffata da komai nawa."
Muhibba sai ta kasa Dagowa jikinta ya fara rawa aranta tana Tunanin daman yasan wannan Labarin Ita a Tunaninta bai sani ba sai taji ya cigaba da fadin"Ummi ta fadamin kadan daga ciki hakama Mujaheed Sai dai ina so naji daga bakin ki ne."
Kanta na kasa ta fara bashi Labarin Saifudden da wayonta da Sanin da tayi mai har zuwa neman mganin da Inna da su ya Habibu suka yi tayi akanta da yadda akayi ta Daina ganinsa.

Saifuddeen ya Dade yana kallonta abun kamar almara cikin karin mamaki yace"Kuma da suffa irin tawa..?

Muhibba ta Dago kanta tana kallonsa Idanuwanta sun ciko da kwallah ta Dagamai kai tana Fadin"Komai iri daya har da kamshin Turaran ka"
Saifuddeen ya waro ido yana Fadin"Is das Serious.."?

Kai ta gyada mai sai ga Hawaye sharr Jinjina kai yayi kafin yace"Is ok..ba sai kin yi kuka ai ya wuce tunda yanzu is no more"
Hawayenta ta share shi kuma mamaki ya kamasa ammh bai maida Lamarin abun Serious ba,Saboda ba komai ya sani game da Labarin Aljanu ba.

Kallon Muhibba yayi kafin yace"Kina so ki cigaba da aikin ki ne..?

Ki kina son ki huta?

Da Sauri Muhibba tace"Ina ina so..Don Allah ka barni na cigaba da yi."
Saifuddeen ya gyada,kai kafin yace"Is ok ni bani da wata Damuwa a hakan.U are free zaki iya tambayata abunda kike son sani a kaina."
Muhibba kanta na kasa tace"SAIFUDDEEN ACADEMY na waye..?

Naka ne.. da gaske..?

Dariya tambayar ta ya bshi sai da ya Dara kafin yace"Yes..Ni na Budeta da Gumina duk da gadon da na gwada wajen Mahaifina na Lere na saida da wasu kadarorina Tunda ina da Ra"ayin haka Tun kafin na fita waje karatu Sosai nake son Teaching Muhi shi yasa matsyina na kwamishina bai sa na Daina koyarwa a Department din da nafi kwarewa ba wato B.A ENGLISH a ABU zaria ba"
Da Dauri ta Dago tana kallonsa kai ya Daga mata kafin yace"5,yrs back..Kafin na Bude ma wannan makaranta a baya akwai kudin Adda ta acikin makarantar Buh na cire mata share dinta na bata kayanta By now Makarantar da komai nata duka mallakina ne"
Muhibba sai ta samu kanta da mirmishi kafin tace"Congratulation Sir..Makarantar mai kyau ce daga malaman har Daliban They are Unique and Brilliant Kamar yadda mai makaranta yake shima na musamman ne"
Mirmishi yayi kafin yace"Derector din ku ya Dade yana bani Labarin Hazikar Teacher din primary 4a MUHIBBAT nasan kokarin ki Tun kafin na fara ganinki Ba tun yau ba am so proud of u da duka malaman dake makaranta saboda da kokarin su ne makarantar ta kai matsayinta da take a yau"
Muhibba tayi mirmishi kanta na kasa kafin tace"Wlh duka mun Dauka Makarantar tana da alaqa da D.Musa"
Saifuddden yace"Ba kowa yasan ina da makaranta tawa ta kaina ba..Saboda ina Boye haka daga yan"uwana sai dangina..Shiyasa amanar komai na Damkama Musa in kuma wani abu ne ya taso ta waya muke mgana
ko zuwan da nayi muka Hadu mujaheed ne ya hadani da Ummi tace in ban je ba zata min Rashin Mutumci"
Yanayin yadda ya Fadi mganar sai da Muhibba tayi dariya yana kallonta yace"Karshen bacin ran Ummi kenan bazata zagi sai dai tace zata yi maka rashin mutumci."
Mirmishi yake yi itama tana tayasa Ya kalleta yana Fadin"any Question?
Chapter 84 · 0% Book details