← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 144

Sashe 72

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aranar da yammah mai shara ya fara zuwa bata dawo da wuri ba saboda Daga makaranta kasuwa ta shiga ta siyo ma kanta Cornflaks da Goldenmorn sai Vanila na Costard,Saboda makaranta in ta makara tana wahala kafin ta gama Hada abun karin ita kuma Tea bai cika Damunta ba tayi sallar la"asar kenan ta zauna tana karatun Qur'ani taji sallaman Junaidu sai da ta kai karshen Ayan sannan ta mike da Hijabinta ta fita falo suka gaisa Ta ganshi Tare da wani matashi Tsab dashi.

Junaidu ya rankwafa yana Fadin"Hajiya Mai yi ma yallabai Share share ne."
Aranta sai da ta maimaita Share share kuma..?Sai dai bata nuna wani abu ta basu izini Tunda bata san ina zai share ba abun da ya bata mamaki a jikin Tv Stand din dake falo ya Dauki keys da yawa ita data ke gidan bata taba Lura da wajen ba ko da yake bata cika zaman falon nan ba ta fi shiga Ciki tayi uzurorinta.

A gaban i don ta ya bude Dakin ya shiga mamaki ya kara kamata abunda bata sani ba Junaidu ya nema masa Abbas da yake mai share share yaron kawunsa ne yana karatu a Nan Poly ne dake zaria haduwarsa da Yallabai ne ma yasa ya koma karatu kuma ya Dauki nauyinsa shi yake masa sharan gida da goge goge duk sati a wata kuma kudi yake Biyansa ko wani babban ma"aikaci albarka nan gidan kawai yake ma sharan shiyasa in ba iyayensa ba ba wanda yasan Abbas na aikin shara Ko ma an sani aikin sharan nasa mai aji ne ba irin na sauram mutane ba..

Ita dai tana cikin Dakin bata san ma ya tafi ba sai dai taji ba Dadi da har sai ya kira daga waje an share mai Daki wata zuciya tace ai ya san dake bai sakaki ba sai kuma ta ba kanta amsa da cewa Hakkinta ne a matsayinta na mace ta tsbtace gidanta Har da dakin nasa.

Da kamar zata share sai kuma ta kasa ta Dauki wayarta ta Tura masa sako.

"Kada mai shara ya kara zuwa zan rika sharewa ina gyara maka Dakin."
Da haka ta turamai bata da masaniyar ya gani bai gani ba shi dai bai bata amsa ba kuma bai kirata ba,Aranta tace mai mugun Hali kawai,To Ranar jumma"a sai ga mai kwasan kayan wanki sai dai Yana gidan ya dawo da Safe ko da ta dawo makaranta taga motarsa da su Bama daya tabbatar mata da ya dawo gidan basu hadu ba sai sanda mai wankin yazo ita bata san dasu ba ta fito daga Kitchen kenan suka kusa cin karo da yaron Shi Saifudden din yana daga bakin kofar Dakinsa yaron yayi saurin Dukawa yana gaisheta bata amsa ba kawai sai ta juya ta koma Kitchen din bata Fito ba sai da ya tafi sannan ta fito ta koma Dakinta.

Sai kuma washegari da Safe suka hadu a falo yana zaune yana shan Tea rankwafa tayi ta gaishesa ya amsa sama sama Hankalinsa na wajen Tv yana kallon Labarai da taso tayi girki ne sai kuma ganinsa a falon yasa ta Fasa daman tana da ruwan zafi sai kawai ta Dama Goldenmorn ta fito ta koma Dakinta basu kara haduwa ba kuma Sai Dare gaishe shi tayi ya amsa ya bita da kallo.

Ta dafa Shinkafa jalop da Kifi da Dankalin Turawa da Rana ta dibar ma su Junaidu cikinta ya chuse shiyasa bata ciba sai da tayi sallar mangariba a cikin Kitchen din taci komai ta wanke Hannunta sannan ta fito har zata shige Dakinta taji yace"Zo nan..!"
Mamaki ya kamata kamar ta share sai taga bai kamata ba sai ta Dawo chan gefe ta samu ta tsaya kawai batare data zauna ba Bai dago ya kalleta ba yace"Meyasa baki zuwa makaranta ko da yaushe..?

Gabanta ya fadi ya akayi ya sani..?

Wata zuciyar tace kema kina da kokari ta ya za"ayi bazai sani ba kina aiki a makarantarsa.

Sai ta kasa mgana kanta na kasa tana wasa da yatsun hannunta Sanye take da Riga da wando irin na yadin nan Cikin wanda Anty Habiba ta dinka mata sai karamin Hijabi data saka saman kayan ta kasan ido yake kare mata kallo Shurunta ya tabbatar mai da gaskiyan mganar Musa,Lokacin daya ga Sakon sa bai maida Hankali ba Shi dai bansan komai game da ita ba tana zuwa ko bata zuwa duka bai da Masaniya.

Yanzu din ma ya tambayeta ne saboda ya san me zai gayama Musa in har wahala take sha ta bar shi sai a dauki wani malami Saboda Students.

Sai da ya kara maimaita mata Tambayarsa sannan cikin Sanyin murya tace"Wani Lokacin ina ina na makara ne..!"
Ya dade bai yi mgana ba har ta fara gajiya da tsayuwa kawai taji yace Ok,daganan bai kara mgana ba Haka taja Kafafunta da suka mata sanyi ta shige ciki shi kuma sai ya saka aransa kila bata samun abun hawa ne sun yi mganar Direba da Ummi sam ya manta ne kamata yayi ya samu dan gari da zai rika zuwa yana kaita duk inda zataje.

Zai yi mgana da Mujaheed yaji ko ta barayin sa yasan wani mai Amana ko kuma zai yi ma Junaidu mgana mai Hankali yake so tunda Amanace ta iyalinsa.

Sai da ya fadi haka kuma abun sai ya basa Dariya wai iyalinsa.

Wannan satin kwana uku yayi mata ko basa mgana suna jin motsin juna Ranar Litini da Safe da zai tafi afalo suka Hadu dukkansu cikin Shirin fita kudi ya bata kamar yadda ya saba har zai fita ya juyo yana Fadin"Tunda kin korar min mai shara..Ina bukatar sharan kafin na dawo".

Daga haka ya juya ita kuma sai ya bata Dariya ta Murmusa ta bisa da Allah ya kiyaye kafin su wuce sai da yayi mganar da Junaidu na samun Direba yace zai bincikamai in Allah ya yarda bata fito ba sai da suka yi nisa sannan ta fito ta tafi makaranta..

Aranar taji Labarin Vacancy Daukan wani ma'aikaci wani yazo D.Musa yayi mai Interviue bata san dalilin Daukansa ba sai da Uncle Hafiz ya Fadamata ba parmanent bane Ranar da bata zo ba ne zai rika rike ajin nata.

Aranta tasan kwanan zencen Saboda ai ya mata mgana sai kuma taji Dadin haka ko bakomai karatun yaran bazai Tawaya ba shi daman D.Musa bai da Damuwa nasa Umarni kawai yake bi,Sako Saifudden ya Turomai da cewa ya Dauki Temporary din malamin da zai rika rike ajin in Muhibba bata zo ba su Anty Usaina suna ta mganganu,na hassada dai da kyashi su a ganinsu Muhibba ma ta kusa barin makarantar tunda tana wasa da aikinta.

Muhibba ta samu Lafiya kwanciyar Hankali ya zauna mata Tunda ta daina wannan barcin da mugun mafarkin nan,kamar an yi ruwa an Dauke Sai ta danganta haka a Sakaci da ta ke yi da addu"a ne yasa yanzu kuma data dake Allah ya yaye mata koma Menene.

Abunda bata sani ba wani Salo kuma zai kara juyawa da ita,kila ma wanda zai kara D'aure rayuwarta wannan karon yafi na farko Dimuwa....

Kamar ta sani wannan Satin bazai zo ba Shiyasa bata yi karambanin shiga Dakinsa ta gyara ba sai Ranar Lahadi da yammah bayan su Ya Zeenatu da yan gidansu sun tafi nan suka mata yini suna tafiya sai ga mai wanki ya Dawo dasu,Dole ita ta karba ba manya kaya ko daya sai suit kawai har kuma da aka wanke basu daina kamshin Turaransa ba ita ma kayanta sun Taru sai dai Anty zeenatu da su ka zo Dazu ta kulle ta bata a kusa da gidansu Yalwa nayi tace in an wanke an goge a fada mata zata aiko a karban mata.

Dalilin da yasa ta bude Dakin nasa ta shiga kenan tayi mamakin ganin komai Fari ne da baki a Dakin Daga Ranar ta kara Tabbatar ma kanta Best Clours dinsa Blank and White ne.

Bata yi gyaran Dakin a ranar ba ta bari sai ranar friday balle ba Datti Sosai sai dai ba Kintsi ne komai a wargatse duk inda ya samu watsar da kaya yake yi.

Satin da ya kara zagayowa bai yi niyyar zuwa Zaria ba Sai yayi sati uku haka sai dai Iya ta saka Baffa Hayatu ya Kirasa tana mai tsiyan shuru har yanzu bai kawo musu Amarya ta gaishe su ba.

Saifudden ya kasa ma mgana kuma Ummi sai da ta fadamai Iya kuma ta karkakace baki tana Fadin"Nace ko ka manta damu ne..?Nasan ai ka Zagaya ka kaita wajen uwarka Zaliha da Danginta ko..?

Saifudeen ya matse baki kafin yace"A"a Iya ko ina bamu je ba..Daman ina ta so na saka rana sai mun zo nan ta gaisheku kafin mu tafi wajen Ummi."
Jin haka yasa Iya taji Dadi ta kama saka albarka kafin suyi sallama nan take ya Kira Ummi tana wajen aiki Sama sama sukayi mgana Cikin Kasala yace"Ummi inaga wannan satin zamu shiga Lere ta gaida iya..Daganan zamu zo mu gaisheki."
Ummi ta washe baki tana Fadin"Kace ina da babban bakuwa..Allah ya kawo ku lafiya ammh kwana zaku yi ko..?

Baki ya Tura kafin yace"Ummi ni bakya marmarin ganina..?

Ummi na Dariya tace"Ja chan..Ni d'iyata nake marmarin gani."
Cikin Fushi yace"Ummi ni kuma ba D'amki bane..?

Ummi cikin nishadi tace"Ni Uwar Muhibba ce nemi uwarka chan Zuwaira.

"
Da sauri yace"a"a Ummi gwara na zabi Umma babba..Mama zuwaira ta cika masifa."
Kamar yana ganinta sai da tamai Dakuwa kafin tace"Kaci gidan ku yaro..Kanwar tawa ce masifaffiya.?

Yana Dariyan daya Dade bai yi ba kafin yace"Na Tuba Ummi."
Kai ta kada kafin tace"Ai sai na Fada mata..!"
Da sauri yace"Kiyi hakuri Ummi in kika Fadamata na shiga uku da ita..Allah sai tazo mussmantan Saboda taci Min uwa."
Daga shi har Ummin Dariya suke yi Ummi tace"Kadan daga aikin zuwaira kenan..ammh zaku kwana a Lere ko..?
Chapter 72 · 0% Book details