← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 144

Sashe 112

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai Lokacin ya juya yana kallonta cikin yar Dariya yace"Af ni fa nace naji muryanta..Ta shige cikin baki ban shaidata ba Baki sannunku da zuwa"
Suka amsa da Yauwa kawu ya karisa zai gaida Baba mallam sai yaki amsa gaisawar sa ya mika masa Hannu yana Fadin"Kyakyawan gaisuwa itace mu yi juna musabaha"
Kai tsaye suka yi musabaha Baba Surajo ma ya kariso shima suka gaisa sai Mujaheed da Ya habibu Saifudden kan jikin Ummi ya Sauke Muhibba ya karisa suka gaisa da Baba mallam ya Sarke Hannunsa yana kallonsa cikin wani yanayi haka Kurum yaji sa kamar UMARu Haka suke acikin Idanuwansu zaka ga wani Dakewa da Haiba ta Jaruman maza.

Cikin Dattakon sa yace"Ya sunan ka..?

Saifuddeen yace"Saifuddeen..!

Jinjina kai Baba mallam yayi kafin yace"Allah ya yi maka albarka"
Saifudden ya amsa da Ameem Ya Mujaheed na gefe yace"Allah gafarta mallam Ban damu nshi kadai..?

Sai akayi Dariya gabadaya Kawu ne yace"Kasan Tare suka taso Mallam.."
Baba Mallam ya yar Dariyan su na Manya kafin yace"To nayi kuskure dukkan ku Allah ya albarkaci Raywarku"
Gabadaya suka amsa da Ameen Ameen har sun ji Salama da Sakewa da Fatan kila Muhibba zata samu Lafiya ta Hannun wannan Dattaijon arzikin.

Alhaji Sa"idu ya kalli Kafafun mallam yana fadin"Baba mallan ya kafafun suka dan tasa yau..?

Baba mallam yace"To Sa"idu ba na fama ta ba..Duk da ma Tafiyar Jirgi ce bata Mota ba ai da tafi haka tasawa ammh an gode Allah Hajiya ta Shafamin mganin nan da Umaru ya taho min dashi Daga Madina kuma naji Dadin sa sosai"
Alhaji Sa'idu yace"Gaskiya kam Shiyasa naso ka hakura da zuwan nan Baba kaki jin mganarmu ni da Hajiya"
Baba mallam yace"To ba gashi mun je mun Dawo ba..?

Ba naki jin mganarku ba ne nan Duniya ai kune kadai ke sakani abun ba ban yi niya ba..Kawai dai nayi ma Magajina alkwarin zan rakasa wajen gasar Fidda gwani nan ne ba gashi kuma munje yaji Dadi ba kuma mun Dawo da Nasara ba"
Hajiya Babba tace"Hakane..Da yake ma Magajin mallam din dan gaban goshinka ne"
Baba Mallam na yar Dariya yace"A"a wlh dukkansu yan gaban goshina ne..Daga mai sunan Sa"idu har Takwara na duka ina ji da su..Ya'yan da Uwata da Umaru suka fara Haifamin ne kin ga kuwa kowa a bayan su yake"
Alhaji Sa"idu yace"Ka manta da Amaryan ka Imam ne..?

Mai sunan Hajiya..?

Baba mallam yace"Ai ita Amarya ce..Ba na biyunta"
Hajiya tace"A haka..?

Yarinya sai Tsiwa da rashin kunya mallam?

Yana Mirmishi yace"Haka kuma ta Ture gwammatin ki Hajiya sai Hakuri"
Wannan karon har su Ummi sai da sukayi Dariya Saifudden na gefe abun ya fara bashi Haushi sun zo da Matsalarsu ammh sai yaga kuma an shiga wata Hira nadabam.

Hajiya tace"Ai bata isa ta iya Ture gwammati na ba..ai ni Kujera ce Dole a zauna dani..an buga dani an barni.

Baba Sa"idu na Dariya yace"Kwarai Hajiya ina bayanki."
Baba Mallam yace"Ai daman ina zaka kware ma uwarka baya..?Sai ni da ka Fifita Hajiya a kaina..Ba komai Amaryata ta kusa zuwa Mamana ta fadamin jiya da mukayi mgana suna nan suna Shiri dukkansu su da yaran Tunda sun samu Hutun makaranta nan zasu yi Azumi sai bayan Sallah zasu koma"
Hajiya da Alhaji Sa'idu suka amsa da Allah ya kawo su Lafiya,Lokaci Daya Hajiya na fadin"Nima mun yi mgana da Sakinar ta fadamin suna tafe,Nasara ma ta nakira jiya ta bani yayarta na mata murna sai da tamin mganar naji su Danmallam zasu zo nan suyi azumi..? nace mata mun yi mgana da Sakina Mamah ne da shi Danmallam din bamu yi mgana dasu ba Kila sai daga baya."
Baba mallam yace"Ni dai mamana ta kirani ta fadamin."
Hajiya tace"Nima Di'yata ce..Zata kirani. na sani.."
Anty Hadiza na gefe tace"Wannan azumin muna da manyan baki kenan Hajiya."
Kafin Hajiya ta samu bakin mgana Kuka na da ihun da na Farka dashi ya cika Falon da yasa kowa ya maida Hankalinsa kaina,Tashi nayi Daga jikin Ummi ina kokarim Fizge jikina, Ina kuka wanda dashi na Farka Cikin yanayin da na saba Farkawa Saifuddeen duk da yana son zuwa ya Rikeni ammh yana tsoron na kara Rikicewa
Kokarin kwace kaina nake yi da karfin Tsiya ina fadin"Ku sakeni..Zasu kasheni..Zasu kasheni!

Ummi tace"Mganin ya saketa..Ko a kara bata wani ne..?

Anty Habiba tace"Gashi a jakata baria sake bata ta koma barcin."
Kiciniya nake yi Ummi da Adda Sadiya sun Danne ni Anty Habiba ta Dauki mganin acikin Jakarta Lokaci daya tana kallon su Hajiya tace"Don Allah muna son Ruwa..!

Daga Hajiya Har Baba mallam sun kasa motsi Anty Hadiza ne ta Ruga Karamin Frigde din dake Falon ta Dauko Ruwan gora guda daya ta kawo Anty Habiba ta ballo mganin zasu min Dorensa kamar Daga sama Suka ji Muryan Hajiya tana Fadin"Ku kyaleta kada ku bata mganin nan"
Gabadaya suka Dago suna kallonta ciki Hardani Ummi ce tace cikin Wani yanayi"Hajiya in ba"a bata ba..To ba zaman lafiya fa"
Hajiya tace"To meye amfanin mganin nan da zaku bata..?

Ummi tace"Na barci ne A asibiti suka Rubuta mana"
Hajiya ta kariso gaban su Ummi tana Fadin"A"a ku bar bata don Allah..Kuna kara rikita mata Tunaninta da wannan mganin ne bakusan mganin barci na da illah ga Lafiyar Dan"adam ba..?

Sai aka rasa wanda zai yi ma Hajiya Gaddamma Saifuddeen ya kalleta aransa yana ayyana matar nan Jajirtacciya ce cikin bada Umarni tace"Ku sake ta"
Adda Sadiya tace"Hajiya muna sakinta zata ce zata fita ne fa"
Hajiya tace"Ku saketa da yardan Allah ba Inda zata je"
Jikinsu a sanyaye suka sakeni ni kuma Idona da duka zuciya na kan Hajiya ita nake kallo in na kalleta sai na koma na kalli Baba mallam shi ma ni yake yana Nazarina sai na koma ina bin Mutanen Dake falon da kallo duk ina natse sai da na ci karo da Saifuddeen sannan Hauka na ya fara tashi da wani irin ihu na mike har sun Razana sun zata fita zan yi sai suka ga na nufi Hajiya ita kuma ta Tarbeni har doguwar rigar abayan da Anty Habiba ta sakamin da Safe kafin mu taho na neman Hardeni in Fadi sai Hajiya ta tallafeni na Fado jikinta kamkameta nayi ina Fadin"Ki boyeni don Allah..Zai kasheni..Wyyo Allah zai kasheni zai kasheni."
Nake fada jikina na kyarma ina kuka kamar raina zai fita Zuciyata na Bugawa da Sauri Sauri Rumgumeni Hajiya tayi tana Buga bayana cikin Sigar Lallashi tace"Shi..Kwantar da Hankali gani nan ba wanda ya isa ya kasheku in dai ina raye.."
Ban san Dalili ba kamar muryan ta nada wani Salama sai na natsu nadai Riketa gam ina kara fadin"To.to.."
Cikin Fitan Hayyaci ga wanda yaga wani abu mai Cutarwa Saifudden na inda yake zaune kansa na kasa bai Tashi ba Hajiya ta jani gaban Baba mallam zata zaunar dani nace ban san wannan ba sai dai muka zauna Tare ina rike da ita sai leko mutane nake yi ta jikinna kyarma yake yi in na Hangi Saifudden mugun Tsoron sa nake ji.domin ina ganin sa a matsayin wanda ke son kasheni.

Baba mallam ya Sauke Numfashi kafin ya kalli Baba Sa'idu yana fadin"Wannan ce mara Lafiya da ka fadamim..?

Cikin Ladabi ya gyada kai Lokaci daya yana Fadin"Itace Baba..Ga Alhaji Sunusi kana jin sunansa a bakina baku dai taba Haduwa ba ne..Mun Dade muna Tare yana daga cikin Costumers din mu na Dabobbi."
Baba Mallam ya jinjina kai yana Fadin"Masha Allah ai duk kamin bayani..tana da miji..?

Da Sauri kawu yace"Eh mallam tana da miji shekara daya da wani abu da auran su"
Baba mallam na kallon Saifudden yace"Wan chan ne mijin nata..?

Kawu yace"kwarai shi ne mijin nata"
Baba mallam yace"Meyasa ya ke zaune Daga baya..ya matso kusa nan gabana"
Wannan karom Mujaheed ne yace"Ai akwai matsala ne..Tana jin tsoron sa wannan gudum ma nashi ne in ya matso akwai Damuwa."
Baba mallam yace"Na Fahimci haka wani taimako kuka nema..?

Sannan daman tana da wannan luluran ne ko daga baya ta same ta..?

Anty Habiba itace duk tayi ma Baba Mallam Jawabin yadda abun ya fara Harda Labarin Saifudden na bakin Muhibba din.

Baba mallam ya jinjina kai kafin yace"Mu iyaye muna da Sakaci mu rika barin yaranmu saka saka ba Kula Duk da wani abun Kaddara ne ammh Harda namu Sakaci kun ga irin matsalan yarinyar nan ana samunta dadama Daganan in aljanu suka Dafe Mutum har Sai sun rabasa da Numfashin sa"
Shuru yayi na wani Lokaci kafin ya Cigaba da fadin"Da Tuntuni da kuka Fahimci tana wasa a kangon da ba Mutane da kun Hanata..duk da ba na Duba na tabbata shima hakan ya Zame mata matsala..Ni bana
bada mganin Aljanu Shi Sa"idu ya sani Ina da Diyata har ta koma ga Allah matsalan junnu tayi fama dashi na karbo mata Taimako duk inda nasan ana zuwa kuma a karbo na karbo mata ammh ba'a dace ba har sai da ta koma ga Allah da wannan Laluran."
Cikin jimami aka ce Allah ya jikanta Baba mallam ya amsa da Ameen kafin ya Dora da Fadin"Bamu da karfin da Allah ya bama Aljanu suna iya shiga Har Cikin jininmu bamu sani ba..Saboda Haka zasu aikata komai ba abun mamaki ba ne..a Fahimtata Dai auran yaran nan ne basa so shi ne suke so su Rabashi da karfin Tsiya"
Kowa sai jinjina kai yake alamun gamsuwa Baba mallam ya kalleni ina ta Kifta ido Cikin Dattakon sa yace"Ya sunanki Diyata..?

Kallon sa nake yi ina gyada kaina Hajiya tace"Sunanki ya ke tambaya.."
Nima sai na maida mata ina Fadin"Sunanki yake tambaya"
Ummi ce tace"Muhibba sunanta.."Baba mallam yace"Yawan Firgitata da aka rika yi shi ya fara Taba Kwakwalwarta..Sannan mgangunar da aka rika bata asibiti da allurai da jininta bai karba ba sun kara taimakawa wajen kara Rikita ta ammh Tana da Hankalinta bata HAUKACE ba kamat yadda kuke Zato ba"
Kawu ne ya gyada kai kafin yace"A hakan Mallam kana ganin da Sauran Hankalinta..?
Chapter 112 · 0% Book details