← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 144

Sashe 106

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kusa dani ya kwanta bayan ya Jawoni jikinsa ya tofamin addu"a ya kamkame ni mukayi barcin mu cikin Salama da asuba shi ya Tasheni ya Rakani Tiolet nayi alwala,Shima yayi muka Dawo dakin shi ya Tunasar dani Sallar Isha"in da ta kubucemin jiya sai da nayi ta sannan ya jamu jam"i sallar asuba bayan mun idar yana azkar nima na fara sama sama naji yaji a idona kafin ya juyo na Fadi gefe ina barci sai kawai ya jawoni ya Dora kaina saman cinyarsa ya cigaba da azkar bayan ya gama ya Fara Karatun Qur'ani acikin wayarsa sai bakwai na Safe ya gama ya kwasheni muka koma kan gado muka kamkame juna kamar zasu koma Abu daya.

Ni ina ta barci ammh shi ba barci yake yi ba gabadaya komai ya Tsayamai ya kasa Fahimtar abunda ke faruwa duk da ya gama tabbatar ma kansa shima yana da nasa matsalan Sai dai shima yana so ya gano meke Faruwa,Kuma gano hakan sai ya kara Jaraba kusarta Muhi duk da zata sha wahala yana so ya kara jarabawa ya gani,ko zai iya ganin abunda ke faruwa.

Abunda ya faru tsakaninsa da Janet zai iya Fassarasa da wannan yanayin sanda bai taba jin wata mace aransa ba ko sha'awarta a Fili ba sai akan Muhi ita kadai ce a zahirinsa Sannan hadda Mafarkinsa,Duk macen da ta Rabe sa da sunan so basa kareta ta Dadi,shiyasa ma baya ma farawa muhi ce ta shiga Rayuwarsa da Duniyarsa shigar da bazai Fidda ta ba ya Dauki alkwarin sai ya Gano bakin zare zasu zama Daya da Muhi ko ana so ko ba'a so sannan ya yi Alkawarin ba zai rabu da Muhi ba har gaban Abada.

Barci ne ya kwashe shi bai sani ba cike da wani irin Mafarki mara Dadi Muhi ya gani tana kiran sunansa cikin Wani irin Daji mai duhu yana kokarin mika mata hannunsa kamar almara yaga an Dagata sama kafafunta na Lilo a sama kukan jarirai ne yaji ya Karade mafarkinsa kafin kiran wayarsa ya tada shi a Firgice ya mike yana Share zufa Tun bayan auran sa da Muhi ya daina mafarkai ya Daina mafarkin yana Saduwa da macen da bai sani ba karo na Farko da ya yi mafarkin Muhi wanda ya kara bayyana mai koma meke Faruwa da ita yana da babban alaqa da abunda ke Faruwa dashi shekaru masu yawa a baya.

Wayar tana gefen sa,juyawa yayi ya Dauko Muhi na jikinsa bai cireta ba Saboda kada ta farka Ummi yaga ta Kirasa guda biyu,Sai yabi bayan kiran gabansa na fadi tana fara ringing Ummi ta Daga yayi saurin cewa"Gud Mrning Ummi"
Ummi ta amsa mai dagachan da cewa"Mrnin yaro kana Lafiya..?

Ya amsa mata yana sosa kansa Cikin Tausayinsa Ummi tace"Ya Muhibba da jiki kuma..?na kira Innar Habibu ban same ta ba"
Saifudden yace"Taji sauki Ummi"
Ummi tace"Allah ya kara Lafiya yanzu zan taso na taho hankalina yaki kwanciya"
Cikin wani irin Sauti yace"Ummi da baki zo ba kaduna zan kai muhi kawai na asibiti zan jaraba na gani"
Ummi tace"Ikon Allah ciwon ta ai bana asibiti ba ne yaro..Matsalan Junnu kasan suna da wahalan sha'ani"
Saifudden ya sauke ajiyar rai kafin yace"Ummi hayakin nan da wannan Rukiyan ne bana so..Suna kokarin kara Hautsina kwakwalwar Muhi..Asibiti zan kaita Likita ya Dubata ya Dora ta kan mgani kuma in sha Allahu za'a dace"
Ummi tace"A ina ka taba jin irin haka ya faru kuma an je asibiti an dace..?

Saifudden ya Gyara ma wayarsa a zama a kunnensa na Hagu hannunsa Daya yana Rumgume dani yace"Ummi akwai fa sashen Masu matsalan kwakwalwa chan zan kaita a duba ta a Dorata kan mganani muna kaduna tare da ita zan taimaka mata da Lafiyata da aljihu na domin naga ta samu Lafiya"
Ummi tayi shuru kafin tace"Ban ki mganar ka ba..Ammh sai an zauna an Tattauna in iyayenta sun amince shikenan"
Cikin Ladabin sa yace"Shikenan Ummu in sha Allah."
Cikin Tausayinsa gabadaya tace"Sai nazo din sai asan abunda za"ayi ammu kam baza'a bar yarinya cikin mawuyacin Hali ba"
Saifudden yace"Ummi direba ne zai kawo ki..?

Ummi tace"Motar haya zan shigo"
Cikin wani yanayi yace"A"a Ummi kinsan bana so fa"
Ummi tayi karamin Tsaki kafin tace"Kar ka so..Tun ubanka na raye na saba shiga motar haya bana so Fi'ili da iyayi"
Daga haka ta katse wayar sai ta bashi Dariya wato Ummi mgana ta gayamai tun ubansa na raye tana hawa motar Haya kuma bai matsa mata ba,ballatana shi yaron data haifa acikinta Mirmishi yayi yana Shafa kansa Sauke wayar yayi a gefe daya kafin ya juya yana kara Rumgume Muhibba kamkam acikin jikinsa Lokaci daya yana Lumshe idanuwansa Domin shima barcin yaji yana son Fizgansa sama sama ammh Mafarkin nan bai bar ransa ba afili ya Furta"Allah ka bayyana min sirrin da ke Boye"
Tabbas Allah ya amshi addu"arsu Sirrin da ya Dade yana Boye ya kusa bayyana.
******
Da wuri Ummi ta taso domin suna gama wayar nan da Yaro ta kamo Hanya gidan Barrister ta Tura su Laala har sai ta Dawo daman bata barin su sukadai agida mata ne sannan ba wani namiji makusanci acikin gidan shiyasa bata aminta da kowa.

Tun tana Mota suka yi waya da Adda Sadiya take fadamata Halin da ake ciki Daman sun yi mgana jiya da Daddare,Sai jajanta Lamarin suke yi sun yi sallama akan sai gobe Mujaheed yace zasu shigo zarian gabda zata sauka Kiran Kawu ya shigo mata sai tace ya bari sai ta isa Sai dai Su Inna suka ga Ummi kwatsan duk daman jiyan tace musu tana tafe Inna ta Rika ina zata saka ta Saboda karramawa ita da Anty Habiba da daman gidan ta kwana har aka gama cika gabanta da kayan karya domin karfe 11 am da wani abu na rana ta shigo Zaria.

Ruwa kadai Ummi ta sha ta kalli Inna Tana fadin"Innar Habibu ya muka ji da wannan Firgicin kuma..?

Inna tace"Umh bari kawai Zaliha..Mun gode Allah"
Ummi tayi Tagumi kafin tace"Ina Diyar tawa ko barci take yi ne..?

Inna ta kasa mgana sai Anty Habiba ce tace"Tana tare da mijinta ba nan ta kwana ba"
Ummi ta sauke Tagumi tana fadin"Ban gane ba..?

Wani mijinta nata..?

Badai yaro ba..?

Anty Habiba tace mata Eh sannan ta gayamata abunda ya faru jiyan da abunda Mallam Haruna yace Ummi tayi kasake kafin tace"Meyasa kuka Biye musu..?in ita bata da Lafiya shi yaro ai lafiyarsa kalau bai kamata ku barsa ya tafi da ita ba,in ya maida ta gidan fa..?

Inna tace"To nayi mgana Mallam Haruna yace na kyaleta.

Ummi ta fito da wayarta Daga cikin Jaka tana Fadin"A"a rashin Tunani ne bata da Lafiya bai kamata ya tafi da ita ba bari na kirasa."
Ba wanda ya kara mgana har ta Kira Saifudden bai dauka ba ta kara kiransa bai Daga ba cikin wani yanayi tace"Bai dauki wayata ba"
Inna tace"Ki kyalesu kawai Zaliha..Muna nan muna gayama Allah duk abunda ya zartar daidai ne."
Sai Ummi ta kasa mgana Sun dan taba Hira duk akan Laluran Muhibba din ne sai ga Ya Habibu ya shigo suka gaisa da Ummi har ta sako mai mganar asibitin da yaro yayi mata ta kara da ceewa"Kuna ganin ayi na asibitin ba matsala..?

Ya Habibu yace"To ba zamu cea"a ba Ummi ammh sai dai a hada Biyu ayi na Musulunci ayi na asibitin shima Duk yanayi."
Anty Habiba tace"Sai dai fa ayi Daya ba'a so ana hada mgani biyu alokaci daya sai dai in za"a gwada na asibitin ne sai a bar na mallam Haruna din zuwa wani lokaci a gani"
Inna ce tace"ammh ai zukata da bakuna bazasu daina ambaton Allah ba Habiba"
Ummi tace"Tabbas..Mganin Ubangiji shine kan gaba Innar Habiba agwada na asibitin gefe daya muna gayama Allah in sha Allahu komai zai warware."
Sun cigaba da Tattaunawa In da Ya Habibu yace"ina so ya bari a kaita nan ABU chika ne domin akwai matar abokina Nura itama kamar irin hakane an yi na gargarjiyan duk ba'a dace ba ammh suna zuwa nan Chika a ka kai su shashen Sacatiring aka dorata kan mgani na wata shida gashi ta samu Lafiya kamar ba ita ba"
Ummi tace"Sai ya bar mganar Kadunan Habibu a kaita Chika a jaraba agani Allah yasa a dace."
Suna cikin mganar Kawu ya kara kiranta ta Dauka suka gaisa nan yake ce mata"Ashe kuma jikin matar Saifu ya kara tashi ko..?

Yanzu Umma babba ke cemim zuwaira take shaida mata"
Ummi tace"Eh wlh gani ma azarian nazo dubata"
Kawu yace"Abu dai ba Dadi ya jikin nata..?

Yanzu me ake ciki..?

Ummi ta shiga yimai bayanin yadda ake ciki da mganar zuwa asibiti Kawu yayi shuru kafin yace"To ni ma ba na Damkafar da Niyarsa ba..Aje a Jaraba in ba"a dace ba akawai malamin da nake hashashen in akaje wajensa Da ikon Allah za'a dace.'
Ummi tace"Shikenan in yaron sun Dawo sai muje asibitin mu gani.

Kawu yace"Allah yayi jagora bani Innar Habibun mu gaisa.

Nan ta mika ma Inna suka gaisa yayi mata kaico kaico tare da jan Hankalinta na kada ta Damu Cikin Sigar Lallashi kafin suyi sallama.

Taruwa suka yi suna ta Tattauna abunda ya faru ya Habiba ya fita ya kira Nura abokinsa shi ya ce zai hadasa da Likitan da ya rika Duba matarsa Dr.Anandi yana da kirki ya Turomai Lambarsa sannan yace ya Fadamai suna tafe yace su yi sauri Zai bar asibitin da La'asar zai tafi Abuja sai nan da sati biyu zai Dawo.

Jin haka yasa Ummi ta kara kiran Saifudden sai alokacin muka tashi Daga barci,Saif na Daga kiran tace muyi sauri muzo ana jiran mu barci bai wani isheni ba ya Tattarani yayi min wanka shima yayi muka yi sallah na Saka Dayan Sabuwar Doguwar rigar shi kuma ya saka Farar Jallabiyansa da Dogon wando.

Breakfast mukayi sannan ya biya kudin Dakin su bama na Haraban Hotel suna jiran mu muna fitowa suka Bude mana kofar mota muka shige sai Dogarawa.
Chapter 106 · 0% Book details