← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 144

Sashe 87

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsam ta mike ta fice zuwa Dakinta yana ganin ta fita sai yaji jikinsa ya karayin sanyi ya gyara zama ya rasa Tunanin da zai yi har Tunanin shiga makarantar maza yayi sai kuma mganar ta shiriraance yasan har da Sakacinsa Lokacin suna BUK mujaheed baya yarda karatttukan Addini na wucesa in yace yazo su je sai yace karatu zai yi gashi yayi karatun a Boko bamai kadashi ammh a bangaran karatun da zai amfane sa Duniya da Lahira bai iya komai ba bai Taba jin kunya irin na yau ba ace matar ka ta Fahimci baka iya komai ba..yana wannan Tunanin ta Dawo Dakin Dauke da Qur"ani Izifi Sittin gabansa ta zauna sannan ta mikamai Ita kuma sai ta Dauki wayar ta ta kunna App din ta na Qur"ani karba yayi jikinsa a sanyaye ba wasa a mganarta tace"Bude Sabbin ka karanta naji"
Ya kasa Dagowa ya kalleta sannan ita kanta Sabbin ya kasa kamo ta sai da ta amsa ta bude mai sannan ta bashi Cikin Tsausayinsa tace"Kada ka damu ka karanta yadda ka iya zam maka gyara"
Gwarin gwiwa sai ta shigesa yayi Bismillah ya fara karantawa sai gashi bai bata ba Saboda da Qur"ani sai ta Fahimci ya iya bakin karatu zai iya karanta komai indai ta Littafi ahannunsa,Har ya Kai karshen ayan tana Sauraransa sai kuma tace ya kara maimaita mata haka ya nanata Har sau uku tana zaune tana kallonsa shi kuma kansa na kasa ko Sau daya bai Dago ya kalleta ba ta Fahimci yana jin Nauyinta"
Bismillah tayi sannan ta fara karantawa Cikin zakin muryan ta da Kira"arta mai Dadi cikon Fidda Tajweed sosai sai da ta karanta sau Biyu sannan ta kallesa tana Fadin"Ka Fahimci bambamcin dake Tsakanin nawa da naka karatun..?

Kai ya gyada mata ya kasa Dagowa Mirmishi tayi kafin tace"Izifi nawa ka Haddace..?

Sai Lokacin ya Dago ya kalleta sai ta Gyada mai kai Cikin yanayinsa yace"Na manta na dai san nayi karatu wajem Ummi sannan nayi makaranta Islamiya ta barikin jaji har na kaduna sai dai komawata Lere ne ban kara zuwa wata makarantar Islamiya ba"
Muhibba ta gyada kai kafin tace"Na Fahimta kayi bakin karatu sannan kayi karatun sai dai rashin Bita yasa ka Fara mantawa..Ka sani shi karatu yana son Bita ko duka Qur"ani ka Haddace in baka Bibiyarsa kamar Ruwa haka yake zubewa in kana so karatu ya zauna maka sai kana yawan Bibiyansa Ma"ana ka rika Karatun Qur"ani kowani Lokacin hakan zai taimaka maka wajen kara gyara Karatunta sannan kuma karatun bazai Zube daga kwalkwalwarka ba"
Tabbas mganarta haka yake haka ya Fada a ransa kafin ya Dago ya kalleta Cikin wani yanayi yace"Thank you so much MUHIBBATU"
mirmishi tayi mai kafin ta mike tana Fadin"Daga yau in dai kana gida duk bayan sallar asubahi zamu rika yin karatu in sha Allahu"
Batayi Tsammami ba taji ya riko Hannunta sai ta Dago tana kallonsa Nakarkaun idanuwansa da suka Tara ruwa ya sakar mata mikewa yayi yana Rike da Hannunta Qur"anin hannun sa ya sauke saman madubin Dakin ba Zato ba Tsammani kawai taji ta acikin jikinsa ya Rumgumota ta baya da sai taji wani irin Yim ya shiga Jikinta kafin taji wani Dimi ya shiga jikinta Cikin kunnenta taji yana Fadin"Thank you so much For coming into my Life Muhi.Allah yayi miki albarka da baki yi ma Rayuwata Dariya ba"
Sai taji ta kara jin tsausayinsa da Sauri ta kwace jikinta shima kokarim Sakinta yake yi domin yaji Wani irin al"amarin da akanta kadai yake ji bata tsaya ba ta fice da Gudu shi kuma ya Bita da kallo Sajensa ya shafa a Fili ya furta"Son yarinyar nan nake yi fa"Da kansa kuma yayi ma kansa Dariya Komawa yayi ya zauna ya sake Dauko qur",nin ya bude ya kara karantawa tun daga Fatiha,Haka kurum yaji karsashi da son abun na kamasa ashe dai ya iya rashin Bita sai gashi har sai da ya karanta Izi Biyu sannan ya Ijiye ya koma ya kwanta Yana jinsa kamar bashi da wata damuwa natsuwa na shigarsa da bai taba ji ba.

Ranar bakin juna suka zama shi da Muhibba haka suka yi brekfast bakin kowa shuru kamar kurmaye sai chan ajuma da Sani yazo suka Saki jikinsu Saboda Sani dai kowa ya san san dan Shafta ne in yaje waje ko bakwa so sai kun Saki jiki dashi.

Muhibba dai kitchen ta tafi ta barsu suna ta Hira tana jin Dararrakin su har abun na bata mamaki bata taba ganin Saifudden na Dariya haka ba Daga Mujaheed sai Sani Fanten Dakalin turawa tayi musu mai Hanta sai Ferfesun naman kai Da Safe Su bama suka yo cefane sai Fruit salt data Hada musu sai da sukayo sallar Isha"i suka Dawo sannan suka zauna zaman cin abincim
Itama Sallar taje tayi sannan ta Fito Falon bayan tayi wanka ta Sanya wani jan Lees dinta Dinkin Riga da Sikat tana shigowa duka suka Dago suna kallonta Saifudden kadan ya Rage bai kware ba Sani kuwa Sai da ya cinye na bakinsa sannan ya kalleta yana Fadin"Muhibba wai bayan auran ku hala kin shiga Makarantar girke girke ne..?

Me Muhibba zatayi in ba Dariya Cussion din kujera ta Dauka tayi ma Sani waigi tana Fadin"Bari na agaza maka kada ka sha kasa."
Saifudden dariya kawai yayi bai ce komai ba Sani yace"Ke ba Santi bane..tsakanimki da Allah kin Taba mana irin wannan Dahuwar agida..!?

Mugunta ce ashe kin iya azababen girki haka..?

Muhibba ta hararesa kafin ta wuce Kitchen tana Fadin"Ko anyi zaka sani ne kai dai baka zaman gida kana makaranta"
Tafada tana shigewa kitchen sai da ta shige ya karkata yana cema Saifuddeen"Yallabai ta taba yi ma su Snaks kuwa..?

Saifudden na shan Fruit salat yace"Me ye hakan..?

Sani yace"Su cake,Donut,Meatpie da su Cookies da su Samosa mana kayan Fulawa"
Saifuddeen yace"Bata taba yi min ba gaskiya Barrister"
Sani yace"Tab ta kware fa yasin..ba abunda bata iya ba,Anty Habiba sana"arta kenan kuma tare suke yi tama ta iya wlh kada ka yarda yallabai kace kana so zatayi maka"
Bai gama mganar ba ta dawo Falon sani na ganinta ya gyara zama yana Fadin"Wato yallabai ina fada maka akwai albarka acikin Dankalin nan"
Muhibba tayi Dariya tana Dauke da Filet ta zubo abinci ta wuce Dakinta Tana Fadin"Daman ai sunan ka Barrister ne"
Sai da ta shige Sani yayi Dariya Saifudden ya taya sa da Mirmishi bayan sun gama cin abincin suka Dasa wata hirar kuma sai dai ta yanzu ta karatu ne da kuma yadda aiki ya Zama ga ya"yan talakawa a Nageria.

Muhibba ita ta fito ta kwashe abunda suka bata takai kitchen ta Tsaya ta wanke komsi gobe tana so taje makaranta shima Tunda goben zai koma Kaduna.

Har ta gama suna hiran su ita dai barci take ji sallama tayi ma Sani bayan ta Dauko mai Sakon Inna yace mata shima yanzu zai tafi aiko sai goma sannan Saifudden ya saka su Bama suka kaisa gida Inna sai Fada take yi mai yaje ya zauna yana Sosa kansa yace"Haba inna ki gane mana..Barrister ne fa ya hadu da kwamishina ki hasaso yadda Hirar tasu zata kasance mana"
Inna ta buga mai mafici a bayansa tana Fadin"Barosu ne ba Barrister ba"
Yana sosa wajen lokaci Daya yana Dariya yace"Inna Barrister dai don Allah"Kyalesa tayi ta Bude sakon Ummi Atamfa guda biyu da Turaren jiki da na Daki Inna nata saka albarka Sani ya Dauki Turaran yana Fadin"Inna mai Tsada ne fa ni dai ki bani na bama Budurwata kafin ki aika ma wannan Tsohuwar ta bakori"kwace Turaranta Inna tayi ta saka aleda Tana Fadin"Ni uwata ce kai ma in kaji Haushi ka siyar ma taka uwar mana"
Sani ya Rike baki yana Fadin"Inna Har da gori..?

Inna tace"Eh an yi maka gorin"
Sani ya mike yana Fadin"Inna sai da Safe an kusa Lokaci kadan ne da na zama Lauyan gwamnti zan gina mana Gida a abuja mu koma sai kin zama Saurauniya yan aiki ne zasu yi ta miki Hidima ko wanka kike so zasu yi miki"
Inna ta wurgamai Mafici ya fice yana Dariya ta girgiza kai kafin ta Daga Hannu Sama tana Fadin"Allah ka cika ma Sani wannan Burin nasa Ameen'"
*****
Washegari basu makara ba kamar Jiya bayan ya Dawo sallar asuba a Dakin sa suka zauna sukayi karatu kowa ya karanta abunda ya Sauwaka ita ta shiga Kitchen shi kuma ya shiga wanka,Saboda yana so 8 ya shiga Kaduna,Kafin 7:30am ta kamallah Hada mai Breakfast Doya ta soya mai da kwai sai plantai sai Ferfesun jiya Data Dumamai,Daki ta koma ta shirya Ko da ta Fito yana jiranta Saboda ta makara shima Taga yana Sauri bata Tsayawa karyawa ba da yayi mata mgana Sai tace Zata saka a cooler haka ko akayi wata Doguwar cooler karama ta saka Doyar da kwai da plantain sai Maltina data Dauka Shi Tunda yaga tana Sauri yasan makaranta take so taje bai hanata ba Daman ya bata zabi.

Ta shirya cikin wata atamfarta ma kalan Maroun,sai ta yi amfani da mayafi maroun da takalminta mai Saukakken Tudu ta rataya jakarta da Kuma Littafinta na leeson Note da Farko adaidaita taso ta shiga sai yace bari su ijiyeta su bama daman yace ta Daina wahalar da kanta yana basu kudin abinci ammh takan Dibar musu in ta Dafa da yawa.

Suna tafiya ne yake ce mata zata koyi Tuki zai siya mata mota Muhibba taji abun kamar daga sama cikin wani yanayi tace"Ina da tsoro fa"
Yana Duba Tab dinsa yace"Zaki iya ne Tunda Addata ta iya mota bala"in tsoro gareta"
Muhibba tace"Tab nagani kuma ta kware sosai"
Bai amsa mata har suka isa makarantaa ta Dauka bakin get zasu ijiyeta sai ta ga har ciki suka shiga Security suna ganin su bama suka Wangale get suna shiga ya kalleta yana Fadin"ina ne Class din ki"
Da Hannu ta nuna mai primary section umarni ya bama Tim akan su sauketa a kofar ajinta alokacin kuma ana Assambely ne both primary and Secondary din kowanne nayin nashi.

Kunya duk sai ya kamata har Bakin ajinta suka je malamai da Dalibai suka bi mota da kallo Sabuwar Corolla dinsa ba kowa ya shan shi da ita ba.
Chapter 87 · 0% Book details