Sashe 56
Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abbati kuma awaya ya Kira Muhibba yayi mata Fatan alheri dama tun abunda ya faru yace ya Hakura da ita sai a alokacin Muhibba tayi nadama taji Dama dama ace shi ta bama dama da wannan Kaddaran bata Fada mata ba.abunda bata sani ba shi Allah ba"a yi masa Dubara..Allah ya riga ya kaddara Haduwar kaddaran dake jiranta a kan auran Saifudeen.
*****
*Abuja..*
Lahadi 10:30am
Tun goma da rabi na Safiyar Ranar Lahadi kawu na falon gidan Ummi bata nan tana asibiti Zeeha na gidan Barrister mu"az wajen karatu Laala kadai ya samu agida bata jin Dadi itama kwatsan ta gansa Sai da ranta ya bata akwai wani abu Domin zasu iya Kirga zuwan kawu gidan nasu in ma wani abu ne sai dai ya kira Ummi taje Laala daman akwai son jin Gulma da Bin kwakwaf.
Ita ta cika gabansa da kayan karyawan da Zeeha tayi musu kafin ta tafi gidan Baba Barrister Ummi kuma Tun asuba ta fita an kirata an kawo masu Haihuwa har guda hudu a lokaci daya.
Lokacin da Laala ke jeramai kayan karyawan saman center table sai da ya kalleta yana sanye da shadda da Babban riga da Hula cikin Dattakonsa yace"Kayya Zainabu da baki wahalar da kanki ba..Sai da na sha koko da kosai na kafim na fito kune yan gayu sai goma kuke saka wani abu a cikin ku sannan kuke daukan Shayi abun rike ciki."
Laala tayi dariya ta zauna gefensa suka kara gaisawa cikin Dattakonsa ya kalleta yana fadin"Ke kadai ne a gidan ina mahaifiyarku da yar"uwanki..?
Laala tace"Ummi an kirata a asibiti Zeeha tana gidan Baba Barrister muna da Karatu yau ni bana jin Dadi ne yasa ban je ba."
Cikin Tausayawa yace"Dakyau..Sannu Allah ya sauwake bari na kirata ba jimawa zan yi ba na taso yaron makota shi ya Tukoni Tunda yaran duk basa gida."
Batace komai ba agabanta ya Fito da wayarsa ya kira Ummi har ta katse bata Dauka ba sai da ya kara kira ta Dauka suka gaisa sama sama yace yana gida yana jiranta tazo yanzu.
Ummi mamakin zuwan kawun ya kamata matuka sai dai bata tsaya ba ta bar ma su Maman Nana sauran aiki,dayake duk masu labour sun Haihu ita ta tuko motar ta daman da kantactaje tayi sallama da ma"aikatan wajen Gabanta na Faduwa ta Nufo gida..
Aharaban gidan taga Isiya yaron makocin kawu ne Alhaji Buhari wani Lokaci ke shi ke tuka kawu in isma"il na makaranta shima ya gama karatu sai dai aikin bai samu ba har yanzu suka gaisa da Ummi cikin Sakewa kafin ta shiga cikin Gida kawu kadai a afalo Laala ta koma Ciki sai Tibi dake babatu shi kadai direct gabansa ta Zube tana gaisheshi ya amsa cikin Sakewarsa Lokaci daya yana Fadin"Zaliha ku aikin naku ba hutu ne naga yau Lahadi..?
Kan Ummi na kasa tace"Yaya ai kasan aikin asibiti..Ko wani Lokaci ana samun marasa Lafiya shiyasa aikin ne ba Hutu."
Kawu ya jinjina kai yana Fadin"Hakane Allah ya taimaka duk suna gaisheki."
Ummi ta amsa da tana amsawa,Ta kallesa kafin tace"Yaya baka ci komai ba..?.
Kai Tsaye yace"A koshe nake Zaliha."
Cikin Taushinta tace"Ammh yaya kafin ka tafi sai na dafa maka wani abu.
Ko.?
Kawu yayi yar dariya kafin yace"Duk nagode Zaliha zauna
mu yi mgana Daman ita ta kawoni."
Ummi ta gyara zama gaban kawu kanta na kasa taji yace"Kin yi mgana da Saifuddeen cikin Satin nan..?
Ummi tace"Ko jiya mun yi mgana..!"
Kawu yace"Masha Allah Daman ni nace kada ayi miki mganar har su chan gida din da kaina nace zan zo na sameki mu yi mgana..Abun da ke faruwa shine kwanaki bayan auran shi Datti na samu wayar Hajiya iya kakar ita yaro nan tamin mgana akan Saifudeen yazo ya same su da mganar Yaga yarinya yana so da suka miki mgana sai kikace kin santa ammh kuma Su bar mganar..!?
Ummi ta dago a Razane kafin tace"Yanzu Iya sai da ta kiraka kan wannan mganar..?
Allah yasa baka yi wani abu akai ba..?
Kawu yace"To ai aikin gama ma ya riga ya gama bakin Alkalami ya riga daya bushe mganar da nike ma yanzu haka mun nemi auran kuma an bamu Biki nan da wata biyu masu zuwa".
Ummi ta zaro ido cikin mamaki kafin tace"Auran shi yaro da Muhibba yaya..?
Ya gyara zama yana fadin"Kwarai ma kuwa..nan ya shiga bata Labarin abunda ya faru tun daga farko ya karishe da Fadin"Ni bani na nema masa auran nan ba Iyayensa ne na Lere su kuma suka Biyamai kudin Sadaki da gaisuwan iyaye ni nawa kawai na shige gaba ne kan al"amarin"
Ummi sai hawaye tuni ta fara kuka Kawu yace"Daman Dalilin zuwana kenan Tunda shi Saifudeen ya Fadamin ya sanar dake kika nuna mai ya bar mganar yanzu kuma wannan kukan naki ya Tabbatar min da baki son wannan auran ni a zato na zaki fi kowa Murna sanin yarinyar mai hankali ce da natsuwa sannan da zumunci a tsakaninmu."
Ummi na sharan kwallah tace"Wlh bana kin Muhibba yaya kamar Sadiya na Dauketa shiyasa naki bama yaro Fuska kan mganarta..Nasan karya yake yi wlh ba sonta yake yi ba wannan auran nasa yana da manufa ko nace kamar sauran ne sai an yi kafin a watse taro ya sako yar mutane Yaya ina zamu da wannan abun kunyar..?
Kallonta yake yi cikin Nazarinta kafin yace"Me yasa kika ce baya sonta..?ni na tambayesa ya tabbatar min da zai zauna da ita."
Ummi tayi yaken takaici kafin tace"Yaushe ya santa..?sau nawa ya ganta..?ya taba mgana da ita..?
Yaya haka ake so da aure banda yaro da son yawo da hankalin mu Yaya'"
Kawu yace"kada ma kiyi duba da wannan. in sun zauna waje Daya duk wannam mai sauki ne..A baya Lokacin iyayanmu ba sanin mazajen sukayi ba sai dai a kaisu kuma su zauna Ballatana su yaran zamani."
Ummi tace"Yaya kace fa yaran zamani..Ni ina tsoron wannan yaron."
Kawu yace"Insha Allahu bazamu ga komai ba sai Alheri..Ina Umurtanki ki Saka masa albarka a wannan auran kada na kara jin wata mgana mai kama da wannan.'"
Ummi tace to Kawu ya mike yana Fadin"Kin ji ni ko baki ji ba..?
Ummi a sanyaye tace"Naji yaya..!
Babbar Rigarsa ya saba yana Fadin"To ba Laifi Allah yayi albarka.Ni zan koma."
Ummi ta mike tana fadin"Yaya da wuri haka..?.
Kawu yace"Insha Allahu."
Tasan tunda ya mike bazai zauna ba sai tace mai tana zuwa jiya su Laala suka yi dambun kaza shi ta Dibar musu mai yawa ta bama kawi tace ya kai ma yara ya karba yana saka mata albarka tana Bakin motar su har suka fice Daga haraban gidan sannan ta koma Cikin gida tare da Fatan Allah ya Saukesu Lafiya..
Ummi ta wani Fanni tafi kowa murna ammh kuma tana jin Tsoron yaro kada ya kunyatasu ta Kira Sadiya sun yi mgana ta kara kwantar mata da Hankali barin ma datace Hamma fa da Saninsa acikin wannan auran ba kamar na baya bane sai hankalinta ya kwanta da kawu ya isa ta Kira sa ta mai barka da sauka sannan Umma babba ma ta kirata da godiyan Dambun Nama da kuma Murnan saka Rana tana tana yabon Muhibba da Innarta Sai Ummi taji hankalinta ya kwanta Mama zuwaira ma da sukayi mgana hankalin ta kwantar mata da Fadin In Allah ya yarda wannan auran an yi shi kenan na Har Abada.
Sai washegari ta Kira wayar Baffa Hayatu suka gaisa ta tambayi Iya yace yana gona in ya koma zai kira ya hadasu sau dare ya kirata ya ba mata Iya da Farko Ciki ciki ta dinga amsa mata sai da Ummi ta sadda kai ta rika bama Iya Hakuri sannan ta Hakura Fadi take"Ko ke fa Zaliha..Ai sai ki saka albarka kawai ni raina yayi fari Domin su hayatu sun yabi karamcin Dangin yarinya Tunda suma ai Haifaffun garin Gaya ne duk Dan juma ne dan jummai Zaliha bai bar gida ba yaron nan.."
Ummi tace"Hakane Allah ya saka albarka Allah ya sa ace gwara da akayi."
Iya ta amsa da Ameen cikin jin Dadi Ummi ta karishe da yi musu godiya Iya tace hakkinsu ne sun rabu Cikin Aminci kan Ummi zata shigo nan lere kafin sha"anin.
Sai da kawu ya kwana Biyu da zuwa Sannan Saifudden ya Kira Ummi bayan sun gaisa tace"Sannu da aiki naji abun da ka aikata.."
Kansa ya sosa kafin yace'Ummi ne nayi..?
Kamar yana gabanta tace"Bansani ba..Yaushe zaka shigo ina son ganinka."?
Da zumudi yace mata wannan satin tace sai yazo daman Sadiya ta kirasa ta Fadamai kawu yaje ya samu Ummi kuma da alama taa sauko.
Rannar Alhamis yaje lere saboda iya taji dadi yasa ya kwana agarin ammh a Hotel,Sai da safe ne yayi ma Iya mganar Majeeda da kudirinsa iya bata ce komai ba tace sai ta fadama Baffa Hashimu abun da yace shikenan to basu samu zama ba suna Gona har ya tafi sun rabu dai iya zata kirasa in sun yi mgana ya zube musu kudi kamar yadda ya saba mutanen gidan ma haka har da makota Majida ma da tazo suka gaisa ya bata nata kudin yace kuma ta kara jiransa zai zo ya tafi da ita ta kwashi gudu zuwa shashensu tana ta murna..
Ranar jumma"a ya isa Abuja sosai ya samu Tarba wajen Ummi su Laala sai murna suke yi zasu sha Biki Tunda Ummi ta sanar dasu.
Bata yi mai mgana ba sai washegari da yaran basa gidam sannan ta same shi tayi mai fada kaca kaca kamar zata ari baki da kakkusan murya cewa in ya Cutar da Muhibba bazata yafe mai ba..saifudeen yaji kamar Ummi ta gama Dauresa da jijiyon jikinsa ammh bai nuna zai gaza ba Cikin Biyayya yace"Insha Allahu Ummi wannan karon bazan baki kunya ba..."
Baki ta tabe kafin tace"Kai dai ka sani ni dai nagama mganata..In har ka sakar musu yar mutane ka nemi wasu Dangin bamu ba..!
Kansa na kasa yace"Bazai faru ba Insha Allahu Ummi."
Sai taji sanyi cikin Salama ta koma tana yi mai nasiha daga karshe tace"Ka je zarian kuwa..?
Kai Tsaye yace"Eh..!
Ummi tace"Ba aikin ka ba Wajen muhibba nake mgana..
Kai ya sosa kafin yace"Ummi..!