Sashe 39
Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sadiya tace"Ya fita neman Hamma Tun dazu na kirasa yace min bashi a gidansa na kaduna kila bai baro zaria ba sai dai ya kashe duka wayoyinsa."
Ummi tayi wani mirmishin dayafi kuka ciwo kafin tace"Gobe zan shigo kadunar Sadiya zaku rakani zaria gidansu yarinyar nan na basu hakuri da kaina.
Daga haka ta katse wayar saboda kada su Laala dake dakinsu su jita sai ta koma ta Rufe kofar Dakinta ta zauna gefen gado ta fara kuka tana Faman sharan kwallah fadi take"Ko wata kaddara ce wannan mun karbeta Hannun Bibbiyu Ubangiji.
Take fada tana kuka kiran kawu ya katseta sai da ta Daidaita kanta sannan ta Daga wayar Tambayar ta ya farayi da Fadin"Ya ake ciki Zaliha.?.
Nanta warware mai duka yadda sukayi da Sadiya Kawu yayi shuru kafin ya sauke Numfashi yana Fadin"Wannan lamari akwai sarkakiya acikinsa to shi Saifudden din yana ina ne..?
Ummi tace"Ba wanda ya sani..Sadiya tace mujaheed yace yaje gidansa na kaduna baya nan.
Kawu yace"Allah yafi mu sanin abunda ke faruwa da rayuwar wannan yaron..Koma wani al'amari ne Allah ya kawo mai da sauki..ki daina kuka Zaliha komai zai wuce insha Allahu.
Ummi ta ja hanci kafin tace"Bakomai kawu..Ammh na yanke shawaran Gobe zan je kaduna Sadiya ta Fadamin mujaheed ya karbi lambar yayan yarinyar da haka ta Faru Tsskaninta da yaro..Zan je na bata hakuri ita da iyayenta Kawu na Fada musu an samu rashin Fahinta ne ammh Yaro bazai taba Tozarta wata mace ba koda bai santa ba."
Kawu yace"Eh hakan nada kyau..Kije din ya kamata zan yi ma Zuwaira mgana gasu nan suma hankula duk a tashe sai ku hadu agidan Sadiya kuje gabadaya Allah ya kyauta na gaba.!"
Ummi ta amsa da Ameen suka rabu da kawu akan zai kira Mujaheed su yi mgana Ummi tayi ta amsa wayoyi har da abokan aikinta saboda ai sun san yaronta ne sai jaje ake mata,suma Daga chan kwamishinono yan"uwan Saifuddeen sun gani suna ta kiransa basu samu ba har Gwamna yaga Abunda ke faruwa sai dai bai wani Damu ba ya Dauka siyasa ce,Kuma indai Siyasa ce babu abunda bazai gani ba Kuma zai zo ya wuce kamar ba"ayi ba.
Agidan su Muhibba Inna tafi kowa Rudewa sai kuka take tana fadin"Wannan kaddara dake tunkaro ki Auta..Allah ya baki ikon Cinyeta..!
Saboda Rudewa Inna ko tunawa data Kira Mallan Haruna batayi ba Lamarin gabadaya ya rikitasu Ya Habibu kuwa fadi yake"Siyasa ce kawai sun yi amfani da wannan damar sun batamai suna.
Sani yace"Ni Bacin raina sunan muhibba da Hotonta duk da Fuskarta bai bayyana sosai ba Allah kadai yasan inda wannan Abun zai tsaya.
Anty Habiba dake gidan domin ba Zencen tafiya tace"Ni haushina Daya basai su saka shi kadai ba ina ruwan Auta da wannan abun kuma..?
Inna kai kawai take jinjinawa tana Fadin"Ku dai kuyi fatan Wannan kaddaran tazo mana da sauki.
Gabadaya sun yi jugum jugum,Ko abinci ba wanda yaci Ranar sai yara da Zeenatu tayi mawa har Siyama ranar bata wani sake ba ganin muhibba sai kuka take yi balle ma dataji Abunda ke yaduwa a kafar Sada Zumumta shikenan sunanta ya gama baci a duniya.
********
Washegari Ummi tun Safe ta baro Abuja,Su Laala gidan Barrister ta Turasu bata ma bari sun san wani abu na faruwa ba tunda basa da waya sai dai Ipad ta games,Tadai ce musu zataje Kaduna wani taro ne,Ummi motar Haya ta shiga Direban ta yayi tafiya kuma banda Asibiti bata zuwa ko"ina da Motar,Sai ko cikin gari kamar kasuwa ko ziyara.
Sun yi waya da Mama Zuwaira da Umma Babba da Kawu yace itama suje tare yadda iyayan yarinyar zasu san an samu akasi ne.
Kusan kamar tare suka isa gidan Sadiya Su sun riga ummi sauka Saboda Isma"il ya tukosu a motar kawu 306,Sai dai tsakaninsu ba Nisa duka hankali ba"a kwance ammh dai da Sauki ba kamar jiya ba Tunda Mujaheed dasu Datti kowanensu yayi dogon bayani a page dinsa na wanke Saifudden daga batancin da ake yimai sai abun yad'an Sarara.
Dayake da wuri suka fito gida basu tsaya sun karya ba Sadiya ta shirya Breakfast suka tsaya suka karya Sama Sama Daman Mujaheed ya Kira Abban walid sun yi mgana ya bashi Full address na Gidan su Muhibba bayan ya sanar dashi gasu nan zuwa.
Abban walid shi ya kira Yaya Habiba ya sanar dashi zuwan su Ummi shi kuma ya sanar ma su Inna mamaki ya kamasu duk da sun tsammanci zuwan nasu ammh basu zata nan kusa ba.
Anty Habiba tatashi ta kara gyara gidan aka shimfida Tabarmu anan Tsakar gida Mintina arba"in da wayar su da Abban Walid suka shigo Layin Mujaheed shi ya Dauko Ummi da Sadiya Mama zuwaira da Umma babba suna motar Isma"il.
Suna shigowa anguwan Mujaheed ya kara kira Abban walid ya kara mai kwatance suna tafe dai Har kusa da Gidan Mujaheed ya fito ya tambayi gidan Habibu Bello mai rago.
Nan da nan aka nuna musu suna shiga Layin gabansu gida na uku nan ne ai Umma babba mamaki bai Saketa ba tun sanda suka tsaya a kofar gidansu Innar Habibu batayi mgana ba sai da suka Firto firto ta kalli mujaheed tana Fadin"Nan ne gidan..?
Yace mata"Eh haka yamin kwantance kuma da nayi tambaya achan nan suka Tabbatarmin.
Umma babba ta kara kallon gidan duk da d'an kwana biyu rabonta da zuwa tun Haihuwar Fari na matar Habibu baisa ta manta gidan ba cikin mamaki tace"To in nan ne kuwa ai du gida ne muka zo.."
Da mamaki suka kalleta kafin Ummi tace"Bamu gane ba..?
Umma babba tace"Nan gidan ai gidan Marigayi Aminin kawun ku ne da kuke ji yana fadin sa Bello mai rago..Nan gidan Innar Habibu ne"
Sai dukkansu suka kasa mgana Mujaheed ya jinjina kai yana Fadin"In hakane abun yazo da sauki.
Abban walid ya sake kira shi ya kira Yaya Habibu yace mai bakin sun iso sai Sani da Ya Habibu suka fara fitowa shi Ya Habibu bai gane Umma babba ba ita kuma ta ganesa suka yi musabaha da Mujaheed da Sani,wanda sai alokacin yaga Isma"il cikin mamaki yace"Islma'il Sunusi Gaya.."
Isma"il ya kallesa yana fadin"Muhammed Sani Bello mai rago.
Ya Habibu cikin mamaki yace"Ka san shi ne..?
Sani na dariya yace"To ai isma'il ne dan wajen Baba sunusi da muke karatu a bayero tare.
Sai ya Habibu ya kasa mgana Umma babba tace"Ai baka shaidani bane Habibu ina ta kallon ka..Umma babba ce matar Baban naku."
Wlh sai alokacin ya shaidata Cikin mamaki da jin kunya yace"Wlh Umma hankalina baya wajen ne sannun ku da zuwa ku shigo."
Yayi gaba da sauri suka rufamai baya sani da isma"il ne karshen shiga mamaki duk ya kama sani ana nufin wadanan sune iyayan Kwamishina din.?
Suna shiga Tsakar gidan Anty Habiba ne da Zeenatu ke musu maraba dayake ita ba wani sanin Umma tayi ba ko gaya taje sai ta kama ne takan je su gaisa rabonta kuma ko da zuwa gaya tun wani rasuwa da akayi ta jima.
Su Ummi suka zazzauna cikin mamaki ita da Mama zuwaira,Sai ga Inna ta fito da Hijabinta ta zauna suna gaisawa Mazan kuma suna gefe suma Inna ta Dago kanta sai suka hada ido da Umma Babba cikin mamaki tace"Umma Babba."
Umma tayi dariya kafin tace"Na"am Innar Habibu.
Sai Inna ta kasa mgana ta dago tana kallon Habibu kafin ta kara kallon Umma tana fadin"Tare kuke dasu..?
Ta nuna su Ummi Umma tayi Dariyan Farinciki kafin tace"To Innar Habibu ai duk yan gida ne nan..Wanchan ba Habibarki bace.?
Ta fada tana nuna Habiba Inna ta Daga mata kai cikin mamaki kafin tace"Eh itace.
Umma tace"Ba shakka Habiba bata da zumunci sai dai muji ta shigo garin bama ganinta..
Habiba dai batace komai ba itama ta shiga Rudu.
Umma babba tace"To ita yarinyar da suka Hadu da Yaron mu ba diyar ki bace..?
Inna da take neman karin bayani tace"Auta ce MUHIBBA..!
UMMA ta juya tana kallon Ummi ta nuna ta Tana fadin"Wannan fa Zaliha ce kanwar Alhaji,ga Zuwaira baki gane su ba ko..?
Inna ta saka salati ta Dire kafin tace"Ina zan gane su Umma babba rabo na dasu da shekaru fa..Sannunku da zuwa maraba.
Umma tace"To Zaliha ce mahaifiyar SAIFUDEEN da rashin Fahimta ya Hadasu da Autar taki kuma shine mai makarantar nan sannan kuma kwamishinan ilimi ta kaduna.
Sai kowa yayi shuru ana kallon Umma ,Ita kuma sai mirmishi take yi Inna ta kalli Ummi tace"Yaron wajen Zaliha fa kikace..?
Ikon Allah."
Ummi ta Dago tana kallon Inna kafin ta maida kanta kasa tana Fadin"Inna kuyi hakuri don Allah kan abunda ya Faru ba Halin YARO bane Tozarta dan adam bama mace ba don Allah ku yafe masa..!
Sai kuka Mama zuwaira na lallashinta Sadiya ta juya ta kalli mijinta shima ya kalleta Cikin mamaki.
Inna ta rike Hannun Ummi tana Fadin"Ko ba danganta Tsakanimu bamu rike wannan abun da wata manufa ba sai rashin Fahimta Zaliha..Bakomai kaddara ce Allah ya sa ta zo mana da sauki ki daina kuka.
Ta fada tana goge mata hawaye sai zuciyar kowa tayi sanyi Mama zuwaira Tace"Ina Diyar tamu take ne..?
Inna ta nuna Dakinta tana Fadin"Tana ciki kwance tun jiya da lamarin ya faru take kuka an samu sabani ne..Muhibba tana da wata kaddara daman..tana karama wani aljani ya Bude mata ido tana ganinsa Daga baya da muka Dage da addu"a da mgani sai ta daina ganinsa har min Dauka komai ya tafi tofa tana ganin dan wajen naku ta rikice tace shine SAIFUDDEEN dinta shi kuma yace bai santa ba..Sai kuka take in mukayi mgana tace ataufau shine Saifudden dinta shi ta gani Mutum ne ba ALJANI BA.."
Sai kallon kallo kawai su Ummi ke ma juna da jin wannan labari mai cike da Alja"abi da abun mamaki,Ummi da bata gane komai ba tace"Aljani kuma Sunansa SAIFUDDEEN Inna..Kuma irin Suffar YARO garesa..?
Inna tace"To waya sani ma Zaliha..?