← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 144

Sashe 25

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tare suka fara karatu da Mujaheed a Jami"ar Bayero Dake kano,ammh ba Course dinsu daya ba shi mujaheed shi Computer ya karanta yayinda Saifudeeen yake karantar B.A English Saboda Ra"ayinsa ne wannan tun fara karatunsu ana ma bai yi Laushi ba kaf Department dinsu ba wanda ya kama kafarsa a kokari da naci kan abunda ya sama gaba mujaheed ma na da kokari sai dai bai kai Saifuddeen ba,Lokacin da suka gama Degree dinsu na Farko Saifudden yaje yayi Jarabawar Scolarship,da Jahar kaduna ke tallafama matansa masu kokari irinsa kuma yaci yana gama Service dinsa aka turasa Standford University inda ya Hada Master dinsa akan B.A English again,kafin Tafiyarsa ne Ummi ta Haifa Zainab suna kiranta Laala sannan yana chan bai Dawo ba ta kara haihuwan zeeha Samina,Domin Daga Mastes dinsa gwannati ta basa Damar Hado Phd dinsa Akan Literature,Tsatsan Turanci kenan Allah sarki Yana chan yaji Rasuwar Baba Barisster ba ciwo ba komai Daga Dare zuwa Safe daman Ya samar ma Ummi aiki a asibitin gwannati dake Unity Hopital and maternity Dake garin na Abuja.Iyayansa masu karamci ne basu kwace su Laala ba,sai suka bar mata ganin ta fara aiki sannan tana da Rufin asiri sannan wajen rabon gado su Laala sun ci gidan data ke ciki yasa ya Sunusi yace tayi zamanta anan ta cigaba da aikinta.

Mama zuwaira ma babansu mujaheed ya rasu bayan ta kara haihuwan Saudat Sai ta barta chan hannun Wan babanta ita kuma ta dawo gidan ya Sunusi daya kara aure matansa biyu sannan yasamu rufin asiri sosai fiye da baya.

Mujaheed daman Saifudeen na Tafiya kasar Turai yayi joining din Airforce,Saifudden kuma sai da ya shafe wajen shekaru Takwas sannan ya Dawo alokacin yana da shekaru ashirin da tara aduniya ya iske Sadiya ta kusa gama karatunta a nile Universty a Abuja sannan mganar Soyayyar su da Mujaheed kowa ya sani Sannan su Laala duk sun girma har sun kusa gama primary dinsu.

Bayan dawowarsa bai zauna ba ya koma Hardvard University ya kara yin Kwas na wata goma akan Literature,Daya dawo ne yafara Koyarwa a Abu zaria a Deparment din B.A Englishi kamar yadda yafi kwarewa akan haka shi kuma Mujaheed har ya gama karatunsa anyi posting dinsa anan kaduna ana ma shirin auran su ne shi da Sadiya.

Gadonsa shi da Sadiya Su Baffa Hashimu suka damka musu Saifudeen yayi shawara da Ummi akan gudurinsa ita da kawu ko su Iya basu sani ba ya saida duka kaddaransa,ummi ta hadamai da kudadenta alokacin sannan ta saida gidan da suke ciki ya siya mata wani babba wanda yafi girma anguwan Apo dake Abuja,Na sadiya kuma Gonakinta suna chan lere tana bada Haya Shanayenta kuma sun zama garke.

Saifudeen ya Dade yana Tsari da Tunani kafin ya fara gudurinsa,ba karamin Wahala yasha ba,Sai dai duka kudinsa ya kare Allah ya taimakesa albashinsa na aiki Sannan kuma da al"amarin ya cushemai sai ya nemi Tallafin Sadiya take matsayin matar Mujaheed alokacin ta Saida gonakinta guda Biyu ta basa kudin ya hada dasu,bayan Ummi da kawu sai mujaheed ba wanda yasan gudarinsa bai kamallah aikin nasa ba sauyin Gwannati Gwamna Abdulhadi shitu ya zama sunansa amatsayin kwashinan ilimi wannan itace silar Daukakansa bai Rufe shekara ba ya gama Hada gudurinsa sai Lokacin su iya suka sani Domin sun hallaci walimar Bude wajen sannan bai samu matsala da Hukumar ilimi ba Tunda ai sune Hukumar alokacin.

Ganin wannan Daukakar ne yasa Iya ta hada sa aure da Amirar da ita ta rike ta adakinta,Aikuwa a washegarin Ranar da aka Daura aure ya Dankara mata Saki akayi ta rigima domin Har alokacin Iya bata Daina jin Haushin Ummi ba barin ma ga auran data kara sannan ga kuma mganar auran Sadiya da taso tayi hadin zumunci da yaron wajen Baffa Hayatu Sadiya tace Mujaheed take so sai ya kara Wutar kiyayyan ballatana da Saifudeen ya Girma yasan matsayin uwarsa.

Iya ta dinga zagin Ummi ita da goggo Atika kan ita ta zuga Saifuden yayi musu ewannan aikin ita kuma sai kuka Mama zuwaira ne ma ke kare mata Dayake ita ai sun santa Tuni.

Dakyar Ya Sunusi ya kashe mganar Sannan shima Saifuddeen din yama zuwa sai kaji mgana ta kwanta Har Amira ta sake aure shine kuma su iya suka sake shirya na Majeeda basu dandara ba.

Ummi azuwa lokacin Dadewarta aiki yasa ta kai matsayin Metron,Sannan tana jin dadin zamanta anan Abuja Inda su Laala ke makarantar Intetnationl Community School Abuja,Ita kuma Saudat tana chan kano Hutu ke kawota gaya ko Abuja Hamma Saifudeen kuma awata sau Daya yakan zo Abuja ya gansu ya koma kaduna inda yake aiki.

Akwai kyakyawan alaqa da abota mai karfi Tsaninsa da Sadiya kanwarsa yana sakin jiki yayi hira da ita bayan Ummi wacce indai su kadai ne zata saki jiki dashi in kuma taga idon mutane kunya take ji Saifudden tun yana jin haushin rashin kiran sunansa da Ummi batayi har gaji ya Daina ya cigaba da amsa sunan Yaro da riga ya saba dashi.

Lere ma yana zuwa ya Dubasu Lokaci bayan Lokaci sannan Alheri kan kamar mahaifinsa hatta da mutanen garin Lere sun shaida haka Chan Gaya ne dai bai cika zuwa ba sai dai suna waya da kawun sannan suna taba juna da Datti Babban yaron Kawu Sunusi.

Saifudden mutum ne Nagari mai kirki da sanin Darajan manya,Sannan yana da naci kan abunda ya sama gaba,Bai da hayaniya ammh kuma bai cika Miskili ba,Saifudden shi yafi kaunar karatu fiye da komai yana son karatu koma na wane bangare ne Dalilin haka ya jone da Unites States University(USU)San_Diegoi California Dayake suna karatunsu ta online yana son samun kwarewa kan harkan Na"ura sannan takardan Degrree garesa kan harkan siyasan cikin gida Saboda ai yana cikinta tsumdum Dole yan kwarewa akan hakan yafi maida Hankalinsa akan aikinsa baya neman mata baya shaye shaye,sai dai ba"a ce baya kallon matan ba yana kallonsu tunda Hulda na Hadasu ammh bai taba jin ya kalli mace yaji wani sauyi atare dashi ba tun yana ganin wasa ne har dai ya amince bashi da Lafiya har Bff yasha daukowa ya kallah ko zai ji wani abu bai taba jiba indai akan mace ne,Sannan mace ya tabbata ko Tsirara zatayi agabansa bazai ji komai ba ammh kuma abun mamaki yasha yin mafarkin yana Saduwa da mace har in ya tashi ya gansa cikin yanayin yin wanka,Saboda wannam matsalan har India yaje yaga Likitan Daya shafi wannan bangaran Dr Mathew,an yi mai gwaje gwaje an kuma Tabbatar mai da cewa komai lafiya ba inda yayi Rauni ajikinsa amatsayinsa na da namiji Jin haka yasa sai ya gasgata sai ya saka aransa in ya aurin mace dayake so komai zai Daidaita shiyasa bai yarda ya zauna da Amira ko Majeeda ba domin yana ganin zai cutar dasu Saifudeen yana da rauni ta bangaran addini matuka domin zaman a lere ba wanda ya kula da wannan bangaran karatun bokon ma shi ya jajirce.

Sai dai shi mutum ne
Mai Tsantsane wajen sabama Allah,in dai yasan wannan abun in ya aikata Allah zai kamasa da Laifi to gwara ya sabama koma waye da ya sabama Allah,shiyasa batare da sanin kowa ba yake sakin su gwara ran su Iya ya baci da Allah ya kama sa da Laifin Danne musu hakki yasan dai baya sonsu kuma in ya zauna dasu zai kwaresu,Kuma aransa yake jin bazai iya zama da su ba in yace zai iya kuma sai yaci aransa kamar ana zare mai wani abu acikin jikinsa.
*Littafin Saifuddeen na kudi ne pay N500 via 0552179550 Jamila umar Gt bank,sai a turo evidence of payment ta wannan Lambar 09069067488 ko kuma katin waya na Mtn sai adauki Hoton katin a tura ta wannan Layin kai Tsaye 09069067488 mutanen mu na Niger kuma zasu tuntubi Kausar aglan Nissa ta wannan lambar domin karin bayani +22796562223 Ina maraba da masoya n
a a duk inda suke*
*Janafty*
*SAIFUDDEEN*
_(Ba mutum ba ne)_
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Amnaf_sudanese _collection*
*Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401*
Bama da Tim Amintattun Excort d'insa ne da gwamnati ta bashi domin kula da lafiyansa a matsayinsa na kwamishinar ilimi mai ci alokacin,abaya yana da Direba mai suna Nura,sai dai Allah yayi mai rasuwa yaso ya kara daukan wani sai kuma ya sha"afa ganin su Bama na tukasa duk inda zai je shiyasa bai damu da Daukan Direban ba.
Chapter 25 · 0% Book details