Sashe 73
Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kai Tsaye yace"Eh friday zamu tafi Mu kwana Saturday mu zo Abuja Monday mu baro ku mu sauka gidan Addata mu yini yammah in tayi sai Su bama su maidata zaria."
Ummi tace"Zata rasa makaranta har kwana Biyu.."
Kai tsaye yace"Ba matsala akwai malamin da suka Dauka zai rika rike mata ajinta in bata nan.."
Ummi taji Dadi cikin Fara'a tace"Kaga yaro Tunda hakane ssi tayi maka ko Sati ne anan kaduna kafin ta koma.."
Sai yaji Tunanin Ummi ya zauna mai cikin Halin ko in kula yace"Shikensn Ummi in ta amince."
Kamar yana ganinta ta kara mai Dakuwa kafin tace"Kaniyar ka..!
Yana Dariya ya katse kiran ba kamar Ummi a wajensa ko yana cikin Damuwa da zarar sun yi mgana da ita sai yaji kansa cikin Farinciki.
Ranar yana tashi Office gidan Mujaheed ya sauka dashi da Adda suka Hada kai suna mai tsiyan yayi kiba Tunda yayi aure sannan ya fara Dauke musu kafa shi dai bai Sauraresu ba ballatana ya tankasu sai da yaci ya koshi.
Adda Sadiya ta kallesa tana Fadin"Hamna naga kana ta tabe baki ne Test dina ba irin na Muhibba bane ko..?
Yana goge bakinsa da Tissue yace"Ai ban san nata Test din ba Addata."
Mujaheed saboda mamaki sai da ya Dakata da cin abincin sa ya kallesa yana fadin"ko bata fara girki bane..?
Dukkansu ukun suna kan Dining ne suna cin abinci cikin Halin ko in kula ya Zakuda kafada kafin yace"Ta fara tun satin bikin."
Adda sadiya ta kalli mijinta shima ya kalleta kafin su taru su kalle shi tare Shi kuma kokarin mikewa yake yi ko ajikinsa.
Mujaheed ya saka hannu ya maida sa zaune yana fadin"To uban me kake ci in kaje zarian..?
Ko itama baka yarda da Tsaftarta bane..?
Saifudeen ya koma ya zauna yana Fadin"What ever..!
Adda Sadiya tace"Muhibba kuma mai Tsatace Hamma kuma ta iya girki matuka nasan in ka gwadata zaka ji Dadinta."
Mujaheed ya karbe da Fadin"Kuma kada ya manta matarsa ce..Shi yayi aure bazai sauya ba..Ina wani kyakyami aciki matarka ce fa Saif..!"
Saifudden ya Dago yana kallonsa kafin yace"To bata taba bani ba zan roketa ne..?ni ai ban raina tsaftar taba Infact ma gidana ne ai na aminta da komai na gida na da ita kanta mai Girki sai dai ta girka ita da Maigadi ko in su bama na nan ta basu.."
Ya karishe mgana cikin wani yanayi me Mujaheed zai yi ba Dariya ba Saifudeen yayi tsaki ya bar wajen ya koma Falo ya zauna.
Sadiya ta kallesa cikin wani yanayi bai Daina Dariyar ba yace"Ki bar ni nayi dariya..Kin ga yadda yake fadan bata basa abinci sai dai megadi da Garadan sa.?
Kinga yadda abun yayi masa ciwo..?
Ai da ciwo kayi aure ammh masu gadi ne ke amfana da auran naka."
Duk yana jinsa sai kuma kawai yaji Ransa na baci ko sallama bai musu ba ya fice daga gidan Adda Sadiya na binsa tana kira yayi mata banza.
Mujaheed na tsagaita dariyarsa yace"Muhibba tamin daidai yanzu haka bakin Halinsa ya jamasa."
Sadiya bata ji dadi ba cikin Tsausayin Hamman nata tace"Ni ko sai naga bata kyauta ba ai mijinta ne Cinsa da shansa yana Hannunta."
Mujaheed yayi shuru kafin yace"Da wannan kuma.
Da wannan"
Sadiya ta sauke Numfashi kafin tace"zan yi wani abu akai in sha Allahu."
Mujaheed yayi saurin Fadin"Kada fa ki kirata kice yace bata bashi abinci ki kwafsamai."
Sadiya tace"Nasan abunda nake yi.
Tafada Lokaci daya tana Hararansa shi kuma yana mata Dariya.
Sadiya abun na ranta ta rasa yadda zatayi ma Muhibba mgana ta gane sa
i ta kira Saifudden yana Dauka bayan sun gaisa tace"Hamma jiya ka tafi ko sallama.?
Karamin Tsaki yaja kafin yace"Ki fara Kula da mahaukacin mijin ki mana.."
Baki ta bude kafin tace"Haba hamma.
Da Sauri yace"Karya nayi..?
Sai ta kssa mgana ta koma tana Dariya ganin ransa ya baci Cikin Lallashi tace"Hamma a gida zakayi weekend din nan.?
Kai tsaye yace"Gida..?nan a Daji naake..?.
Kai ta Dafe kafin tace"Kai Hamma kayi hakuri mana.
Sai alokacin ya Sausauta yana Fadin"Eh A"a.
Sadiya tace"Bangane ba."
Kai Tsaye yace mata"Lere zamu tafi mu kwana daya daganan wajen Ummi zamu wuce ammh zata zo ku gaisa ranar monday din."
Sadiya murna ta kamata cikin fara"a tace"Hamma ban da kai..?
Tsaki yaja kafin yace"Zan zo ne gabanta mijin ki ya tasani yana min Dariya yarinya ta rai na ni..?
Sadiya ta Danne Dariyanta kafin tace"A"a Hamma."
Cikin Basarwa yace"Zan shiga meeting zamu yi mgana wani Lokaci.."
Da haka sukayi sallama murna duk ta cikata da Mujaheed ya Dawo ta Fadamai Bude bakinsa sai cewa yayi"Nima ki Fadamai in na gansa a gidana Hukuma ce zata shiga Tsakanina dashi."
Dariya tayi kafin tace"Ka manta sune Gwamnati.?
Baki ya Datse kafin yace"Hakane fa..Nima ai gwamnatin ne Shege ka fasa.."
Sadiya sai Dariya take musu in dai Fadan Hamma da Ya Mujaheed ne har gajiya take yi Sanda zasu shirya ma bata sani ba aranta ta kuduri niyar sai Muhibba tazo cikin hikima zata sa ta gyara zamantakewar auran ta kamar kuma har yanzu ba wani sauyi.
Ranar Alhamis da yammah tana Falonta tana Fitar da Lesson plan wayarta dake karatun Qur"ani cikin Suratul Yusuf ta fara kidan larabawa da ta ke kamawa in an kirata data dakata ta Dauka taga bakuwar Lamba ce, bata taba kawo ma ranta shi bane,Sai da ta Dauka da Sallama Duk da muryan ta Dakesa karo na Farko daya fara kiranta Tun kafin auransu da bayan auransu.
Cikin Amon Sautinsa yace"Gobe kada ki shiga makaranta ki shirya akan Lokaci zamu tafi Lere."
Daga haka bai jira cewartaba ya katse wayarsa mamaki ya kamata Ina ne kuma Lere..?Sai daga baya ta Tuna cewa garin su ne Tunda sunansa akwai lere aciki kuma in bata manta ba Inna ta taba Fadamata Mahaifinsa daga chan yake duka Dangin mahaifinsa suna chann.
Jin haka yasa ta ijiye abunda take yi Dakinsa ta fara Budewa ta gyara mai daman ta Dade da jeramai kayansa Cikin Makeken wadrobe dinsa,Ta wanke Tiolet din tas sannan ta Fesa Air Freshener sai kuma ta Dauko Burnee ta saka Turaran wuta bata da tabbacin yau din zai shigo ko sai goben..?
Ita dai ta kulle masa Dakin aranta tana fadin shi ya sani.
Sai kuma ta fara Tunanin bazata tafi Hannun Rabbana ba sai ta kira Inna ta Fadamata Inna tace"Gaskiya ya kamata kije musu da wani abun..Ki kira dai yayar taki ki gayamata mu ji me zata ce."
Da sauri ta katse wayar ta kira Anty Habiba ta fada mata Cikin jin Haushi tace"Shine baki Fadamin da wuri ba Auta.?
Muhibba ta tura baki kafin tace"Nima yanzu yake fadamin to."
Anty Habiba tace"Cake kadai gareni shima bai da wani yawa sosai sai dai zuwa gobe kina da kaji ne ko Nama..?
Muhibba tace"Akwai duka satin chan daya koma ya bada an karo cefane."
Anty Habiba tace"Yauwa ki Sarrafa Dambun nama ko na kazan wanda dai zai fi miki Sauki ni kuma zan san abunda zan yi a wajena..Ki Hada musu da Turaran wuta kwalba Biyu da na Fesawa da Turmin zani cikin kayan Lefenki sai in kun je ki bama ita kakar tasa."
Muhibba ta gyada kai cikin gamsuwa kafin su yanke kiran daganan bata zauna ba Kitchen ta fada tana Bin karatun ta Cikin waya tana aikinta Duka tayi Dambun Nama da Dambun kaza aikin da bata gama shi ba sai wajen goman Dare duk da ta tsaya yin Ibadarta.
Bayan ta gama ta kira Anty Habiba ta fadamata tace ta barri zuwa gobe man jikinsu ya tsane zata aiko mata da Robobin da zata saka su aciki da haka suka rabu akan Sai da Safe Alarm ta saka karfe Hudu ta tashi ta Fara shirinta Tunda bai shigo Jiya ba tasan yau yana tafe da wuri.
Ta Fiddo da Turarukan da Turmin zani Holland ce babba ta Dauko mata Cikin kayan lefenta,koda Takwas tayi ta shirya cikin wani Swice less mai Baki da pick sai tayi amfani da bakin Mayafi da jaka da Takalmi.
Takwas da Rabi Abban Walid ya kawo mata sakon ta Filet guda Biyu duk tayi Rapping dinsu da foul paper Sai kuma wasu Robobi masu kyau Farare tana ganinsu tasan na zuba Dambun Nama ne Dakyar Muhibba ta sa ya shiga Ciki ya sha ruwan kafin yayi mata Sallama yana sauri wajen aiki zai wuce.
Muhibba da kanta ta Kira Inna ta Fadamata shawaran Anty Habiba da abunda ta aiko mata dashi Inna nata saka albarka da sakon gaisuwa kafin Taji Innar na Fadin"Wajen su Zaliha kuma yaushe zaku je..?
Muhibba tace"Inna kina gani ko gida ban taba zuwa ba.in ba makaranta ba ban taba zuwa ko"ina ba."
Inna tayi Dariya kafin tace"Haba Auta..Yaushe duka duka kikayi auran..?
Zaki zo insha Allahu ai yana sane.."
Muhibba dai baki ta Tura batayi mgana ba sukayi sallama da Inna.
Cikin roba daya ta juye Duka Dambun Nama dayan kuma na kaza yau batayi abun kari ba Tea ta sha shi kuma ta kaima Junaidu tayi aiki jiya ta gaji matuka.
Ta gama shirya komai bata san cewa zasu kwana ba shiyasa bata dauki kaya ko Kala daya ba Bai shigo gidan ba sai Sha daya na Safe ashe cikin makaranta ya shiga yana da Lacra da Dalibai da Safe.
Yana shigowa gidan ko Dakin sa bai Nufa ba domin ba abunda zai Dauka kayansa yazo dasu daga kaduna kala Daya ne yana da kaya achan Abuja.
Tana zaune gefen gado da Ledojinta a gabanta waya take dannawa Chart suke sa sani yana faman tsokananta tana Dariya bata ji motsin sa ba sai mganarsa Daga saama.
"Kin gama shiryawa..?
Sai da ta tsorata kuma yaga Tsoron a Cikin idanuwanta shiyasa yace mata"Sorry..!
Kai ta jinjina kafin ta gaishe shi ya amsa yana kallon ledojin gabanta Cikin mamaki yace"Kayan ki ne a leda ina Trolley din ki..?
Kara kallonsa tayi kafin tace"Kaya..?.kwana zamu yi..?
Juyawa yayi yana kallon agogon azurfan dake hannunsa kafin yace"Eh ki Dauko kamar Set uku haka kada ki zo kina ce min baki Dauko wani abu ba, so better for u ki Dauko abunda zaki Bukata ko da mun isa chan din."
Daga haka ya fice bayan yace mata ta Same sa a mota.