Sashe 132
Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ina Dariya nace"To mu dawo mana ai bakomai naji ina son zaman garin nan"
Dariya kawai yayi bai yi mgana ba ko shi yana son garin lere saboda nan ne asalinsa,Bamu fara shiga masaukin mu ba sai da muka sauke gajiyarmu a Dakin Iya,Ummi da Inna Talatu muka iske sai Iya suna ta Hira nan muka zauna ni ce ma ke basu Labarin karramawar da Sarki yayi mana Iya na Dariyan jin dadi tace"in dai maimartaba Sarkin Lere ne karamci kadan kuka gani..Yana da kirki da Sanin Darajan na kasa dashi"
Na jinjina kai ina fadin"Na ko gani Iya kowa ya tambaya har da ke"
Iya tace"Lokacin ina da karfin jikina Duk Ranar juma"a sai naje Fada mun gaisa akwai kyakyawan alaqa tsakanin gidan nan da Sarautar wannan garin"
Nan fa itama Iya ta karkace tana ta bani labarai Saif dai na gefe yana faman Latsa wayarsa Sama sama Ummi da Inna talatu kan sako mana baki ana haka sai ga Baffa Hayatu da Baffa Hashimu sun shigo nan fa aka Hadu ana Hira sai wajen goma Saura Iya tace na fara gajiya Saifu ya Daukeni mu koma masaukin mu na kwanta ba Musu ya mike daman ya gaji da zama nima kuma na fara jin barci har mun yi musu sallama Ummi ta kira sunana na juyo ina Fadin"Na"am Ummi.'
Ummi ta karkace zama tana Fadin"Kin ga na manta dazu na kira Hajiya Babba muka gaisa tace tana gaisheki da kyau da kyau"
Nayi mata jim ina so na Tuna waye Hajiya Babba har ga Allah na manta Saboda ba komai nake tunashi Lokacin da nayi wannan jinyar ba.
Sai da Ummi takara min bayani da cewa"Hajiya Babba ta gumel..Gidan da muka fara kaiki kafin ta Dalilin su kika samu waraka"
Na fara kokarin tunata ammh ba Duka ba Cikin jin dadi nce"Allah Sarki ina amawa Ummi zan karbi Lambarta na kira ta mu gaisa"
Ummi tace"Ai ba ma mganar waya sai dai na zuwa domin damam akwai mganar zuwa ayi musu godiya To muna mgana ma tace min duka yaran sun zo gida sallah har da babban yaron Mallam din dake Madina yanzu ma mun gama mgana da kawu yace yana Tunanin jibi sai mu je ayi musu godiya"
Kafin na samu zarafin mgana Iya ta Rigani da Fadin"Gaskiya kam ya kamata abun aje ne ayi musu godiya ne ni ba domin kafa da ta matsamin ba ai da ni za"aje mutane masu karamci haka Jibi yaran nan kamar wata kaddara bata taba Fada musu ba"
Ummi tace"Wlh kuwa Iya..Yayan yace Bazanga zamu fara zuwa wajen shi ainihin malamin da ya warware mana komai daganan sai mu wuce Gumel din"
Baffa Hashimu yace"ya kamata gaskiya..Allah ya bada iko ko ni in ba inda zani sai na bisu iya"
Iya ta washe baki tana jin Dadi Ummi ta kalli Saifuddeen da Hankalinsa ke kan wayarsa tace"yayan yace kun yi mgana ko..?.
Kai ya gyada mata kafin yace"Eh mun yi mgana dazu da gobe yace ni nace sai jibi Saboda ina da Taron old Student na makarantarmu ta Federal Science And Tecnical collage(FSTC) Kafachan so ina so na Hallarta sannan mun yi mgana da Mujaheed yace sai goben zasu baro kano zuwa nan din"
Ummi ta jinjina kai tana fadin"Bakomai hakan yayi Allah ya nuna mana"
Aka amsa da Ameen gabadaya Daganan muka kara yi musu sallama muka koma gidanmu jikina duk ya Mutu nayi aiki duk na gaji yau Tuwon Shinkafa muka yi da miyar gyada ni da su Laala don ma suna tayani ai da na raina kaina wanka ma Saifu yayi min ya sakamin kayan barci ni sai da asuba najini na fara Dawowa daidai.
Da Safen ya kara gayamin Taron tsoffin Daliban da zai hallata nayi mai Fatan alheri na kuma tayasa ya shirya Cikin Riga da wando na wani Bakin yadi yana Sheki dinkin zamani har da Babbar Riga da farko ma kin sawa yayi wai sun mai nauyi na Dauko mai na Shadda yace baya so na kallesa ina bata rai kafin nace"Haba Saif kai fa babban Mutun ne shigar manyan mutane ya kamata kayi ko ba a matsayin tdohon Dalibin Makarantar nan a baya ba,akai yanzu Wakilin al"umma ne da an kanga kamar fa an ga ruwan ilimin ne da kansa"
Na karishe Fada ina kashe mai ido kiss yayi min a saman kaina kafin yace"Antything for u my Muhi"
Ni na shiryasa ciki da bai na saka mai Farin agogo na Fata da Farin Takalmi Budadde na fata sai Hula mai zanen baki baki ya fito yayi kyau kamar Zara cikin wata na dinga mai barin Turare yana ta kare Hancinsa yana Fadin"Muhi yayi yawa kada ya fara hawa min kai"
Nace"Na lura kamshi bai Dame ka ba Saif dina"
Cikin yamutsa Fuska yace"Ina so ammh ba mai hayaniya da yawa ba..Kinsan bana son Damuwa"
Duk nacin sa ban kyalesa ba sai da nasan har ya baro wajen kamshin sa bazai bar inda ya baro ba sannan na kyalesa.
Har cikin gida tare muka shiga yayi ma su iya da Ummi Sallama sannan suka Dauki Hanya shi da su Bama ya tafi ba jimawa sai ga su Adda sun Sauka Ita da Nihad da Mujaheed,Cikinta har ya fito yana wata na Bakwai ne Iya bakinta yaki Rufuwa ta rike Nihad yarinyar Sai ta saka kuka sai ta saketa tana Fadin"Tafi chan jar banza Daman Dangin Zaliha Kadai kika sani ba kinsan Tushen uwarki ba"
Duk da cikin wasa ta fada ammh mganace Mujaheed yayi mirmishi kafin yace"Iya ta sani mana..nan zamu bar miki ita ta tayaki zama"
Iya ta tabe baki tana fadin"A"a ku tafi kayan ku..Kuka bar min ita in yi yaya da ita ina fama da kaina wannan yarinyar naku da ke kyamar Mutane ba yadda zatayi kowa ya taba ta ba..kuje da ita nagode"
Adda Sadiya tace"Iya da gaske muke yi nan zamu bar miki ita"
Iya tayi Dariya kafin tace"To nagode ammh ku tafi da ita bata saba damu ba bazata zauna ba..Nagode kwarai da ziyartamu da kuke yi akai akai ba abunda zan ce ma Zaliha sai Fatan alheri da Farkobnayi Tunanin zata Rabamu da ku sai gashi bama ku da kuke namun ba Gabadaya zuru"arta basu manta damu Allah ya jikan Salahudden da Inuwa suna kasa ammh nasan suna alhafari da ke Zaliha"
Iya sai kuka Adda Sadiya da Ummi suka koma bata baki Mujaheed na gefe dai yana kallon Diraman iya,Daganan shi ficewa yayi ya shiga gari Tunda shi ma ai ba bako ba ne balle ya Samu dan gari Da Gaddafi suka Dinga yawon gari sai yammah suka Dawo suka iske Saifudeen ya Dawo shima ba Jimawa basu samu zama ba sai da suka fito sallar Isha"i lokacin mutane sun ragu suna zaune saman Tabarma a waje a kofar gidan su Saifudden na garin lere iskar Farkon Damuna na kada su.
Mujaheed ya kalli Saifudeen yana Fadin"Ya taron man..?
Saifudden ya muskuta yana Fadin"Lafiya lau..Sosai naga Mate din mu wasu sun yi karatu sun zama wani abu wasu kuma sai a Hankali..Sannan wasu kuma sun rigamu gidan gaskiya sun bar iyalai Wasu kuma kafin ma su tara suka rasu,sannan ita kanta makarantar tana bukatar gyara sun nemi in kai bukatar hakan gabam gwamna na muna musu makarantar tana karkashin Fedreal Goverment ne Dole sai ta sama ne gwammati zata iya yin wani abu"
Mujaheed ya jinjina kai yana fadin"Wlh hakane abun nima ai mun yi namu ta chan kano..Duk sai a hankali Cikin mu masu aiki mai kyau bamu da yawa yawanci duk watsar da karatun sukayi wasu fa Man babu ce kuma babu kasan bazatayi ma Dan Talaka Karatu ba"
Saifudden yace"Sosai wlh..Abun gwanin ban Tsausayi..Na bada Tallatin 200k ayi gyaran makaranta sannan na yi alkwarin zan yi ma gwamna mgana ya shigar da korafin makarantar wajen shugaban kasa in an dace shikenan"
Mujaheed yace"Madallah da Madaran Ilimi da kanta Muna godiya"
Saifuddeen yace"Nayi bayanin zamu Bude Asusun tallafa ma marasa karfin mu Cikim mu nayi alkwari ni da kaina Duk wata zan saka 50k sauran kuma duk abunda ya sauwaka nan take aka samu masu 30k,20k da 10k duk wata sauran marasa karfin ma sun ce baza a barsu a baya zasu rika saka duk abunda Allah ya Hore musu"
Mujaheed yajinjina kai kafin ya Daga Hannu alamun jinjina yana Fadin"Allah ya kara Nasibi ranka ya Dade.."
Dariya Saifudeen yayi kawai bai ce komai ba sun dade suna Tattaunawa kafin su watse cikin gida suka shiga Dakin Iya suka gaisa da su,nima ina Dakin iya mun jima anan kafin mu koma Masaukin mu Adda ma nan suka Sauka Bangaran su Ummi ni ina bangaran Saif inda aka taba yima Majeeda Jere dukkanmu mun kwanta da Shirin tafiya gobe tun da har adaran kawu ya sake kira ya kara Jadadda mganar tafiyar yace ya kira Alhaji Sa'idu ya fadamai Sannan ya kira Mallan Surajo ya shaidamai yace yana maraba da wannan ziyaran Ummi ma adaran ta Kira Hajiya Babba ta fadamata ta dinga Murna tana Fadin"Madallah da mutanen arziki..Muna nan muna jiran ku Allah ya kawo ku lafiya"
Daga zaria ma Ya Habibu yace suna tafe Har da Inna tace zataje da Sani da yazo gida Sallah,Anty zeenatu dai da yara gidan su zataje ammh Anty Habiba zataje ita da Siyama da mai sunan Baba karami su khalipa suna gidan kakaninsu duk a ijiye a Bazanga Gidan Mallam Surajo zamu hadu dasu kafin mu wuce Gumel din
Tun Safe da muka tashi bamu koma ba muka yi wanka muka shirya kayanmu Saboda Dagachan kowa gida zai koma,ko kafin karfe goma na Safe mun gama shirin mu duk an saka kayanmu a mota kayan abinci bamu koma da su mabukata aka rabamawa,Baffa Hashimu ya samu zuwa Har da shi zamu tafi Ummi daman tazo da Direba wanda Saifudeen ya kara Daukan mata ne Cikin Sabuwar Motarta Vibe baka,Sai mujaheed suma da tasu motar sai namu Tafiyar gabadaya ce har da su Laala suma Dagachan Abuja zasu wuce.
Gabadaya an taru a kofar gida ana ta yi mana fatan isa Lafiya Har da iya Goggo Atika taso zuwa to Sailuba ba Lafiya Ummi ta bata kudi tace ta kaita asibiti a Dubata karfe sha Daya na Safe muka bar Lere muka Dauki Hanyar Bazanga.