Sashe 70
Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Anty Habiba tayi Tunanin kiran sai kuma taji ta kasa Daga aure sai korafi Saifudden kuma Sako kawai ya Turo mata wanchan Satin ya fadamata bazai Dawo wannan Satin ba ta kula da kanta,cikin ikon Allah kuma washegari asabar datake da sati uku agidan ta kwanta taa tashi Lafiya lau da Kuzarinta ta gama gyara gidan kenan Tunda satin chan bata samu zama ba ga makaranta ga Rashin Sukuni,Tayi wanka kenan ta saka kaya taji Hayaniya afalo tana Fita taci karo da Anty Habiba da siyama da Walid har da Khalifa bata san sadda ta kwashi gudu ta rike Anty Habiba tana Murna ba yaran kuma suka makaleta.
Anty Habiba na Dariya take fadin"Sakeni Abban walid na waje shi ya kawo mu nace ya tsaya ku gaisa."
Muhibba tace"Eh Wlh..Khalifa je kace ya shigo..Wayyo ni Auta..!"
Tafada cikin murna kafin ta kwashi Gudu zuwa Dakinta ta Dauko mayafi ta saka Abban walid ya shigo Shida Khalifa Falon Muhibba Anty Habiba ta kaisa yaran kuma suna Falon Farko Muhibba kuma ta shiga bare baren jiki a kansu ta cika gabansa da Lemuka da ruwa sai Ferfesun kifin datayi yau da Safe Abban walid Maltina kadai ya sha sai ya Dauki Coke bai jima ba yayi musu sallama ya tafi bayan ya yaba da tsarin gidan ya tambayi Muhibba megidan tace yana Kaduna.
Yaran suna Falon Farko ta zuba musu Ferfesun kifi ta basu Buredi tace suci kafin anjuma Ita kuma suna Falon ta ita da Anty Habiba da sai kallonta take yi sai da ta zauna gefenta sannan tace"Auta kin rame..Sai dai Fatar ki tayi haske Amarya.."
Dariya kawai tayi batayi mgana ba Domin in bata manta ba Inna kullum sukayi mgana sai ta mata Fadan rike Sirrin auranta sannan bata da Burin Tada ma iyayenta Hankali.
Muhibba ta kauda mganar da Fadin"Anty Habiba shine baki Fadamin ba..?
Jiya fa mun yi waya dake..?
Anty Habiba tace"Suprise Siyama tace mu baki."
Muhibba tace"Naji Dadi sosai Tunda ya tafi ni kadai agidan nan Inna ko tace zata zo.. ba Ya Habibu ba Anty Zeenatu wani fa bai kara zuwa ba sai yau.."
Ta karishe Fada kamar zatayi kuka Anty Habiba na Dariya tace"Aure kenan yakin Mata Auta..Ya Megidan..?Zaman ku dai Lafiya ko..?
Muhibba ta gyada kai kafin tace"Eh Lafiya lau tunda yayi sati daya ya koma bai Dawo ba yadai cemin wannan satin ban dai sani ba.."
Muhibba ta sharara karya ita yaushe sukayi mgana yadai ce wanchan bazai samu zuwa ba,daganan sakon nasa ya Tsaya nan suka cigaba da Hira da Anty Habiba sai bayan azahar bayan sun yi ssllah suka shiga Kitchen Tare Anty Habiba ta taka ta Bude Drowers din dake saman kitchen din tana nuna ma muhibba kayan su Toster na yin Cake da Oven tana fadin"Tun da kin iya ki rika yima mijinki Auta..."
Muhibba ta gyada kai bata ce komai ba aranta tace ina naga mijin..?ko yana nan ai abinci na ma bai ishesa kallo ba.
Jalop din shimkafa da wake suka Dafa da Kaza suka Taru afalo sukaci a Faranti Daya kamar yadda suka Saba in kaga bakin Muhibba har kunne Farinciki ya cikata,Khalifa ta aika ya mikama Junaidu nasa Anty Habiba data gani tace"Mijin ki ya san kina bashi abinci..?
Muhibba tayi shuru domin bata da ta cewa Don bai sani din ba.
Anty Habiba tace"Bai kamata ba Duk da abu ne mai kyau in ya Dawo ki Nemi Izininsa."
Kai ta gyada mata kafin tace"In sha Allahu.
Daganan suka cigaba Hirar su ta yan"uwa masu kaunar juna kafin su koma Bedroom din Muhibba Anty Habiba nata Fadan mgungunata na mata Tunda aka kawo mata ta daina shan su ita dai Hakuri ta bata ina zata Fadamata bata gaban mijin aikin banza suke yi.
La"asar ta wuce Lokacin da Siyama ta shigo tana fadin ga wani yazo suna Fita taga Bama ne ya shigo da wayoyin Ogan nasa da Tap dinsa kafin shima ya biyo bayansa Yaran daya gani da ita kanta Muhibba din da Anty Habiba da kallo daya yayi mata yasan yar"uwanta ce shi ya hanasa shiga Dakinsa Direct ya tsaya suka gaisa Anty Habiba nata jin kunya Sanye yake cikin Suit Fari da baki a dan zaman datayi dashi yasa ta fara Fahimtar fari da baki sune kalansa Domin bata taba ganin sa da wani kalan ba bayan su.
Hannu ya bama khalifa sukayi musabaha Lokaci daya yana Fadin"What is ur Name.
Khalifa yace"My Name is Khalifa Abubakar Bammalli."
Saifudden ya shafa kansa yana fadin Good Boy ,walid ya tambaya shima ya Fadamai ai Siyama ce kafin a Tambayeta ta fadi nata sunan sai ta bashi Dariya ya rike hannunta suka kama Hanyar Dakinsa Muhibba ta saki baki tana kallonshi Dama yana Dariya haka..?
Suna shigewa Anty Habiba tace"Hadamai ruwa ki kaima kafin kizo ki Dora abinci tunda mun cinye wanda muka Dafa."
Bata isa tayi musu da Anty Habiba ba ta koma Kitchen ta saka mai Maltina da Coke sai Kofi guda daya Allah yasa bakar Riga ce ajikinta da Mayafin Rigar haka ta nufi Dakinsa ita kuma Anty Habiba tace su Walid su shirya yanzu zasu tafi.
Yana chan yana Jin hirar Siyama yana Mirmushi,Zaune suke gefen gado dukkansu ya cire Coat din sama ya bar Farar rigar ya cire tektie da takalmin kafarsa sanda ta shigo da Sallama ya amsa mata Lokaci Daya Yana kallonta kanta na kasa ta shigo har Kan side drower ta sauke Farantin hannunta kafin tace"Sannu da zuwa."
Murya a sanyaye ya amsa mata da"Yauwa..!"
Zata gota shi yace"Ruwa..!
Daganan ya duka yana Sabule Safar kafarsa Jikinta a sanyaye ta juya ta Dauko Ruwan ta Bude ta Tsiyayamai a kofin daidai Lokacin da Siyama ta mike zata fita da Sauri yace"Hey Siyama where are going..?
Kai Tsaye siyama tace"Mommy tace in manya na waje we shall get out..!"
Sai yaji yarinyar ta Burgesa har sai da ya Murmusa da Hannu ya Kirata tazo Walet dinsa ya Dauko kudi masu yawa Sabbin yan Dari biyar biyar ya bata sai taki karba daya ware mata ido sai ta dago tana kallon Muhibba dake rike da Ruwa cikin yarinta tace"Anty In karba mommy bazata yi Fada ba ko..?
Kau da kai Muhibba tayi kafin tace"A"a mommy zata zaneki.."
Jin haka yasa Siyama ta noke Hannu kafin tace"Sorry Uncle..!
Daga haka ta fice a gaje ya bita kallo,Bai Dauka yana son yara ba sai yau da Siyama ta shiga ransa agefensa ya Sauke kudin hannunsa ya Juya yana kallon Muhibba kanta na kasa da Ruwa a Hannunta yana kallonta ya saka Hannu ya karba ita kuma kanta na kallon kasa bai san ya akayi ba yaji ya Hada da Hannunta ba, dukkansu sai da suka yi saurin sakin juna shi har Ruwan na saukan mai saman kafarsa sanyin yasa yayi saurin janye kafarsa yana Dakuna Fuska Muhibba taja baya tana Fadin"Sorry..!
Da haka tayi saurin Ficewa Daga Dakin kamar zata kifa sai ta bashi Dariya har sai da ya murmusa,Yaga mata kala kala kyawawa Larabawa da Indiya da Turawa ya kuma yi cudayan acikin su ammh bai taba jin wani abu na Fizgansa kan mace kamar yadda yake jin yana Fizgansa kan Muhibba ba akwai abu tattare da yarinyar dake Burgesa san yin ta da Natsuwarta uwa uba tana ta wata irin Haiba da kamewar da baya iya Dauke ido a kanta sannan yana jin wani irin yanayi in ya kalleta Faduwar gaba da Sanyi jiki ya rasa me yasa ita kadai yake jin haka tare da ita..?
Saboda mikakkiyar Kaddaran ku tana da kamaceceni ya da juna.
Ruwan kadai ya sha bada yawa ba ya maida kofin ya ijiye Mganganun Ummi kawai yake tunawa duk sanda ya Kirata mgana Daya ce har ya gaji da Haddanta Fadi take"Yaro ka rike Muhibba da gaskiya ka sani Amana ce gareka kuma in kaci Amanarta Allah na ganinka ni kaina bazan taba yafe maka..ko wannan Satin yaso yayi zamansa ne wayar su da Safe da mganganunta yasa jikinsa ya mutu tunda ya barta bai kirata yaji Halin datake ciki ba shifa waya bata Damunsa in ba Lalura ba bai cika son mgana ta waya ba.
Wanka ya fara yi kafin yayi sallar La"asar din da ake binsa Yana zaune kan Darduma Siyama ta shigo da gudu Tana Fadin"Uncle we are going..!
Sai kuma ta sake Fita mikewa yayi yana saka Silafas dinsa Dake gefen gado Dakin nasa yayi kura Saboda mai masa shara daya kirasa haka kurum yace kada yazo satin nan Ko saboda Muhibba tana gidan ne..?
Baisan Dalili ba,Kudin daya bata taki karba ya Dauka ya fita Falo Su Walid har sun Fita Haraban gidan Muhibban ya gani ta rike Hannun yar"uwanta tana ta mgana kamar zatayi kuka kamshin Turaransa yasa tasan yana Falon da sauri ta saki Anty Habiba ta Juyo suka kalli juna Jallabiya bakace yar Saudi ajikinsa.
Daga nesa ya tsaya yana fadin"Ba sai Dare zaku tafi ba..?
Domin bai san sunan Anty Habibar ba ita kuma cikin Kamewa tace"Ai mun yi kokari tun safe muna gidan nan..."
Kai ya jinjina kafin ya mikama Muhibba kudin hannunsa lokacin da Anty Habiba tayi gaba tana kiran Siyama.
Kamar bazata karba ba ya kalleta Fuskarsa ba Annuri kafin yace"Bana son gaddama."
Dole ta matso ta karba Tana godiya juyawa yayi yana Fadin"Bama zai kai su gida."
Mamaki yake bata wani Lokacin in yayi abu kamar bashi ba Daman da hijabinta ajikinta ta fita haraban gidan ta bama Anty Habiba kudin taki karba Tana Fadin"Bangane ba..?
Muhibba ta tabe baki kafin tace"Nima dai shi nagani."
Dariya Anty Habiba tayi ta karbi kudin Tana godiya aahe har ya Kira Baman sai gashi ya yi kwana da Motar yazo gabansu Tim ya Bude musu bayan Mota Anty Habiba ta kalli Muhibba ita kuma ta gyada mata kai Tana Fadin"Shi yace su kai ku gida."
Anty Habiba tayi godiya ita da ya"yanta suka shige mota tana Daga musu hannu har suka Fice daga gidan Hawaye suka ciko idanuwanta.