Sashe 109
Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fada su Baba surajo suka dinga yi da suka zo suka ga Halin da nike ciki balle da akace na Dade cikin Laluran nan suna ta fadan meyasa ba'a kira su an Fada musu ba su Inna dai sai ban Hakuri,Kaf yan gidan nan namu sai da suka zo,Har ta da su Goggo Fa"iza da Goggo Barira,Yara da manya sai da suka zo Dubani duk wanda yazo ya tafi sai yayi min kuka ace Muhibba mai natsuwa ga Hankali da zati itace kwance a shashen masu Tabin kwal
kwakwalwa kai muji Tsoron Rayuwa Domin bawa bai gama shiga Iftila"i ba sai Ranar da ya koma ga Ubangijinsa.
Haka ma Mutanen Lere Iya kamar zata ari baki wajen fadan ba"a gaya musu akan Lokaci ba Duk Fadan Goggo Atika da kyashinta wannan karon batayi ba sai da ta Tausayamin duk wanda yazo ya ganni ya tafi sai yace ciwo na kaza ne mganganu dai kowa da irin nasa Tunanin wasu ma suna cewa wai sihiri ne wasu kuma suce Jifa ne su inna dai sun toshe kunnensu basu saurari kowa ba Saboda Zama na asibiti yafi Safe akan na koma gida domin La shakka za'a neme ni watarana su rasa sannan shi Kanshi Saifun ya Dage a bar ni a asibitin Karkashin kulawar Likitoci tun ballatana da Likitocin ke Yawan Fada musu kada su damu da zaar na jikina da kwakwalwata ya fara karban Treatment din su zan warke kunsan Likitici ko kana gangaran mutuwa ne basu cika Sarewa ba.
Mgana ta fita ta zaga gari gabadaya Matar kwamishinar ilimi Dr.Saifudden Conel.Salahudden Lere tana fama da ciwon Hauka Shi dai bai kira kowa ba ammh haka yake ta samun kira na Jaje Har da Gwamna sai da ya kira sa yayi ma sa Jaje sannan Daga gidan gwamnatin mota guda doguwar nan suka ciko da Kwamishinoni,suka zo har asibitin Chika Dubani sannan Gwamna ya aiko mataimakinsa da wasu Daga cikin Amintattun sa,Saboda Kowa yasan Saifudden wajen kwarewa akan aikinsa sannan yana zaune da kowa Lafiya ba ma haka ba gwamna na ji da shi sosai.
Malaman makarantar mu ma sun zo kwansu da kwakwartar su sun Dubani duk yadda Anty Usaina da Anty Khadija ke nuna min Tsana da Hassada sai da suka Sare ganina cikin wannan Halin masu Saurin kuka cikin su sai da suka koka irin su Uncle Hafiz da Anty Khadija Director musa Ya tausayama Saifudden matuka ganin yadda ya rame kamar ba shi ba,Sai da na kwana goma sannan Sani ya Dawo Saboda suna Jarabawa yasa ya Habibu ya hana a fada masa ammh abokinsa Abbati sai da ya kirasa ya fadamai Paper karshen ma ya dai Rubuta ne kadai ba wai domin yasan me ya Rubuta ba,Da akwatin sa yaje Hall din Jarabawar ana gamawa sai Tasha Daman kuma sun yi mgana da Isma"il shima ya fadamai Halin da ake ciki gabadaya hankalinsa a tashe ko gida bai isa ba asibitin ya fara yada Zango Sai dai kawai ya Kira ya Habibu ya tambayesa in da suke yace suna Shashen Psychiatric.
Sani yayi kuka da har sai da ya gaji ganin Halin da nake ciki Yana kallon Inna da ita ke kwana dani Su Ummi da Anty Habiba sai da Safe suke zuwa kowa yayi firgai firgai abun gwanin ban Tsausayi kafadan Anty Habiba ya fada yana fadin"Anty haka Auta ta koma..?
Innalillahi wa'inna ilaihirraju"un.
Anty Habiba na matsan kwallah tace"Haka Auta ta koma Sani..Auta ta Haukace Sani."
Kawai sai ya Rumgumeta suka Taru suna Dirzan kuka Inna na zaune gefe tana jan carbi Ummi ce ke basu baki Saifudden tun faruwar Lamarin hotel ya koma yana kwana ya bar gidan Gabadaya,Har ta Junaidu sai da ya Sallama Gabadaya gidan ya ficemai acikin kansa.
Su kawu duk sun zo shi da su Mama zuwaira sai dai basa kwana in suka zo suka Dubani sai su koma Mama zuwaira dai ta kwana Biyu ta koma Haka Adda Sadiya kullum suna Hanya ita da Mujaheed wajen zuwa Dubani jiki kam sai godiya in ina barci na samu Salama in kuma na Farka ba zaman Lafiya duk cikin masu zuwa Dubani ni ban san ma suna zuwa ba Saboda yawanci Daga waje suke lekeni in ba su Inna da ya zama Dole ba bamai shiga inda nake.
Ranar da na cika kwana goma sha uku a gadon asibitin gabadaya asibitin ya cika da baki,Mutanen gaya duk suna nan ga su Iya ma sun Dawo Dubani Saiff na nan shi da Mujaheed ga Adda Sadiya,da su kawu da Mama zuwaira da Umma babba Har da Datti da matarsa da Mudansir da suka iso garin ajiya shine yau suka ciko mota suka nufo zaria kowa kagani zuciya da Jiki babu Dadi sai dai kawai Takwalli da kuma Musulunci.
Iya ce ke ta fada tana fadin a maida ni gida ayi na gargajiya mana Tunda na asibitin yaki hannu har yanzu.
Goggo Atika ce tace"Iya an ce miki Saifu ne ya hana a maida ta gida."
Iya ta kallesa tana fadin"Kai kalle ni nan mara kunya"
Kallonta yayi cikin Gajiya shi fa yanzu wlh baya son hayaniya cikin Fada Iya tace"Yarinyar nan Muhirba ciwon ta ba na nan ba ne a maidata gida a bazama nema mata mgani wajen malamai jifarta akayi da junnu"
Ido ya Lumshe kafin ya shafa sumar kansa da ta kara yawa sannan ba gyara yace"Iya bazan kaita ko'ina ba..Likitoci suna iya bakin kokorin su kuma sun ce za"a dace"
Iya na Hararansa ta sakarmai Dakuwa tana Fadin"Kaga naka nan ba kokari ba kaniyarka da kokarin..su har sun fi malaman mu sanin abunda ya Dace ne..?
Ka bar yarinya sai zaluntar ta suke yi suna mata allurai suna kara Haukatata yarinyar nan Muhirba ga Ladabi mai hankali an haukata ta abanza"
Sai kawai ta saka kuka ta bar su kawu da aikin Lallashinta ammh taki yin Shuru ganin asibiti ne kada ta tara musu mutane don ma ba kusa da Dakin suke ba suna barandar shiga Shashen ne.
Iya fadi take"In dai ana so na Daina kuka sai an taimaki wannan yarinyar an Dauketa daga asibitin nan ni wlh gabadaya ma ban aminta da asibitin nan ba bana son asibiti a rayuwata"
Kawu ya Kalli Saifudden kafin yace"To kai kaji abun da kakar ka tace"?
Kai Tsaye yace"Nifa kawu bazan bari a maida Muhi gida ba..Bana son azo ana kiran malamai daganan har a kira Bokaye suzo suna karya suna Hayakin banza wanda daga karshe maimakon Lafiya sai suka kara mata wata cutar"
Iya ta saka Salati taja ta Dire tana Fadin"Mun shige su Malaman kake Zagi Saifu?
Lalle wannan yaron an yi ja"iri"
Ganin zata Damesa ma sai ya Daga waya kamar an kirasa ya Sauka daga wajen suka bisa da kallon Tausaya har aka gama mganar nan Inna ko su ya Habiba ba wanda ya saka baki sai su Baba Surajo da sukace mganar Iya tana kan Hanya Iya na jan Hanci tace"Ku gaya musu dai kila ku zasu saurare ku tunda suna ganin ku da kima"
Sai alokacin Inna ta muskuta tayi mgana tana Fadin"Ba haka ba ne Iya..Auta tana karkashin mijinta ne Duk abunda yace dashi zamu yi amfani.
Baba Surajo ne yace"Hakane ammh ai muna gaba da su in suka kauce zamu karkato su.
Kawu yace"Kwarai kuwa a bari a bi komai a sannu sai an san mafita in sha Allahu"
Da haka aka kashe bakin Iya,Kawu Gefe ya koma ya na ta waya ba wanda yasan da wanda yake mgana ammh Daga gani mgana ce mai Muhimmanci.
Lokacin da aka sarke da Diramar Iya Sani Sulalewa yayi ya tafi Dakin da nake ciki ya zauna yana kallona yana sharan kwallah afili yake furta"Allah ya baki Lafiya Auta"
Kamar a mafarki yaga na bude ido ina kallonsa da Sauri ya matso kusa dani yana Kiran sunana Sama sama nake jinsa sai dai na Kuresa da Ido nuna kansa ya dinga yi yana Fadin"Auta nine..Kin gane ni..?Sani ne"
Bakina naji ya Furta"Sani..'
Kawai sai ya Rumgumeni yana kuka Daya ke Raunina ya warke har na saman Nono ya fara kamewa,Nima sai kawai na kamkame sa na Fashe da kuka,farko kukan masu Hankali nake yi Daga baya kuma sai na koma na Mahaukata na fara ihu da karuruwa ina Fadin"Ka boyeni zasu kasheni..Zata kasheni tace shima Zai kasheni."
Sani jijjigani yake yi yana Fadin"Waye zai kashe ki..?
Nace waye zai kashe ki..?
Cikin Fitan Hayyaci jikina na kyarma nace"SAI...SAI...!
sai na kasa karisawa Saboda yadda zuciyata ke rawa ashe sun jiyo Hayaniyarmu da Ihu sai gashi an cika Dakin Kawu ke fadin"Sani me yasa ka shigo..?
Nurses ne su biyu suka shigo suna Koran su waje su na ke kallo ina ganinsu suna komamin wasu Hallitu ban gama fita Daga Hayyacina ba sai da naga Saifudden ya shigo Dakin Tsalle na Daga nayi gefe jikina ba inda baya kyarma Gashin kaina Duk ya Tsufa wahala yasa ya fara warware kansa shi nake nunawa ina Fadin"Shii.Shiii...!
Neee..!
Sani yana kokarin rikoni yana Fadin"Shi ne wa Muhibba..?
Chakume masa wuya nayi ina Fadin"Nace maka kashe ni zasu yi bakaji ba ne..?
SAIFUDDEEN ba mutum ba ne Kasheni zai yi nace makaa..'"
Na karishe da wani tsawa Lokaci Daya ina wancakar da Sani ya yi gefe Zai Fadi Datti ya Tallabesa ni kuma na Fara zagaye Dakin ina watsi da kayan Dakin ina jifan duk wanda na gani a gabana kokarin fita nake Nurses sun fi goma adaki
sai ga Likita ya shigo yana Fada duk ya kori kowa ni kuwa Fadi nake yi"Ku kyaleni bakwa ganin sun zo zasu kasheni ne."
Dr.Isa yayi min mugun riko yana Fadin"Nasan zasu kashe ki ne..Ammh gani nazo ba wamda ya isa ya tabaki Duk na koresu duba ki gani"
Da wannam Dubaran nasa na Daina Fizge fizge ina bin sa da kallo da Haka wata Nurse ta Min allura Daganan nayi week suka kwasheni suka maida kan gado Dr.Isa ya Dafe kansa Cases din nan na neman fin karfin su Gabadaya ba na karban ko wani Treatment abun sai kara gaba kawai yake anyi har Hoton kwakwalwata tabbas ta fara Tabuwa kuma in ban fara Karban Treatment ba To in na kai wani Stage ba kuma zan iya karban kowani Treatment aka Dorani akai ba.