← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 144

Sashe 122

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Laala kuwa tana zuwa Dakin da suka sauka ta iske majeeda na kuka,ita kanta ta rasa kukan me take yi sai dai mganar gaskiya tana kukan mganar Laala ta auna ta ga kuma gaskiya ta Fadamata She ia a Loser ta rasa gwarzo miji irin Hamma tabbas batayi karya ba itama data fara Sanin Ciwon kamta da yadda maza suke sai ta Fara ganin wautanta na kin bari a maida auran su ta tabbata da bazai hanata Karatu da yanzu Laala bata isa ta fada mata mganar banza ba.

Ganin ta tana kuka sai Laala taji jikinta yayi sanyi ta haura kan gadon tana Fadin"Maji am sorry wlh ban yi din na bata miki rai ba"
Majeeda ta Dago idanuwanta Jajir tana kallon Laala kafin tayi wani munafukin mirmishi tace"No need to say Sorry Laala..Gaskiya kika Fada am a Loser"
Daga haka ta mike ta fada Tiolet ta bar laala da bin ta da kallo Tun daga Ranar Majeeda ta Daina walawala ko ni da ba Lafiya gareni ba sai da nasan Majeeda ta sauya na tambayi su Laala sun ce basu sani ba sai na Tambayi Saif bai ce min komai ba sai ya bani amsata da aikinsa da ya saba acikin jikina Daganan nima na manta da mganar.

Satin su daya da zuwa Saudat tazo tare da Mama zuwaira da Umma babba da karama suka zuka Dubani ammh a gidan Adda Sadiya suka kwana Har da ni na matsa ma Saifuddeen mukaje kai su Mama zuwaira,Mun iske ta duk ta rame Bata jin Dadi sosai ammh taji Sauki Ta na dai kan Dokar Likita ne ganin haka yasa sai Mama zuwaira tace Saudat ita ta zauna nan ta rika taimaka ma Adda Su Laala nata Tura baki basu so haka ba Saboda Majeeda ta daina Hira da su sai dai kullum tana Daki tana Faman Tunani ita kadai har Zeeha sai ta mata mgana tace mata bakomai Shiyasa suka fita batunta.

Bayan sun kebe agidan Adda mu kuma muna Falo ne ita kuma Majeeda da Wasila suna Tare da Nihad a Dakin Adda Saudat ne da Zeeha da Laala Adakin baki na gidan Adda Sadiya suna Hira.

Cikin Hirar ne Saudat ke fadin"Naga Maji sukuku hala me aka yi mata..?

Laala ta tabe baki kafin tace"Wahala ce ke Dawainiya da ita ba wani abu ba"
Saudat tace"Ban ga ne ba"
Zeeha tace"wulakancin Laala ne ita ta Fara ci mata mutumci"
Daganan ta gayama Saudat abunda ya Faru ta karishe da Fadin"Kin ga ko ke ne sai kin ji ba dadi daga ranar sai ta sauyamana Fuska"
Laala tace'"Kada ki ga Laifina Zeeha..Ai wasa ne itama ta sani in ba tana da Intension kan haka ba meyasa ta saka ma ranta?

Saudat tayi wata Dariya kafin tace"Son Hamma take yi fa har yanzu"
Baki suka saki suna kallonta Zeeha tace"So kuma..?

Saudar tace"Banzaye ku kuna zaune da ita ammh baku gane ba..?

Wlh ba Tun yau ba ni nasan
Majeeda na sam Hamma"
Laala tace"Exterlly Saudat..Nima na Fahimci hakan..In ba so ba,meyasa zata Damu da mganata'?

Saudat tace"ammh bata da Hankali Wlh Hamma bazai so ta ba"
Laala tace"Bata da Hankali ne"
Saudat tace"Kila tana ganin domin ta fara wayewa kila ya so ta yanzu..Bata san Hamma ba ne shiyasa"
Zeeha tace"Tab..In dai ko Hakane tana da wahala Hamma yana son matarsa bazai iya mata kishiya ba"
Laala tace"Ga ta ga Hamma din in zataci Riba"
Nan suka cigaba da Tattauna mganar suna ganin Majeeda ta Dauko ma kanta Wahala sai wajen goma na Dare muka koma gida da su Laala Majeeda abun mamaki tace nan zata kwana taki bin mu,Su Laala sun san Dalili ni kuma ban sani ba Saifudden ma bai nemi sanin Ba'asi ba
Ashe Haushina take ji in ta ganni gefen Saifidden da gaske ne bata Daina son
sa ba,Ya suma ne Saboda Rashin wayewa ammh kuma yanzu Soyayyar ta Farfado tana ganin kamar
ita ta Saki Damar ta har Muhibba ta kama shi su basu san badakalan da aka rika yi ba sun dai san Muhibba bata da Lafiyan aljanu har aranta tana Fadin ga ta mai Lafiya ammh ya auro ma kansa Wahala.

Shiyasa ta zabi tayi zamanta a gidan Adda Har su tafi data koma ta Rika ganin mu muna shigewa Daki muna Soyewa Allah sarki ni ina na Sani Rabi Hankali Rabi Tabuwa gashi Dogon Hotu ne in suka koma zasu shiga SS3 kiri kiri Majeeda taki dawowa tayi zamanta agidan Adda Sadiya su Laala kuma suma sun ji Haushi sai suka Rabu da ita.

Ina da Sati Hudu da Dawowa Kaduna Anty Habiba tazo dubani ita da Anty Zeenatu da yara gabadaya,naji Dadin zuwan su matuka Barin ma da naga Siyama da su Walid haka nake ina son yara matuka kwana Biyu sukamin suka koma bayan tazomin da Snaks Har da Cookies,su Laala sai murna suke yi da shi muke shan Tea har sai da yayi ma sati sannan ya kare su Samosa tun ranar muka soye sauran kuma na aika ma Adda Sadiya har da Cinci da Cake din itama ta shaida.

Sati Hudu cur su Laala suka yi min suka yi shirin komawa sai ana Gobe Tafiyar su Majeeda ta Dawo Sauda ta koma Gaya tun kwanakin baya,Aranar ya kai su Shop suka zabi dukkan abunda suke so washegari kuma Tun Safe Bama ya Dauke su sai Abuja,wasila nata kewa ni kaina ai nayi kewarsu gidan sai ya zamana Dabam ni ma ma basu kayan kwalliya da Hijabai na Sabbi da ban taba Sakawa ba.

Ummi ta kira ta na ta godiya Duk da yayan su ne ammh taji Dadin siyayyar da aka yi musu,Ashe har suka koma Abuja Majeeda bata saki ranta ba Har Ummi sai da tayi mgana Zeeha ta fada mata abunda ya faru,Ummi ranta ya baci ta Kira Laala ta mata Fata fata fata har sai da tayi kuka ammh batayi ma Majeeda mgana ba sai dai ta mata Fadan kada ta bari tunani ya shafi karatunta sai dai ta Lura Majeedan na son zuwa gida lere sai Ummi tace ta bari zata je kafin karatu ya kamkama ko Weekend sai tayi achan,kamar bazata barta taje ba sai kuma tayi wani Tunani sai ta ce bari ta kyaleta taje taga iya gudun ruwan yarinyar.

Asatin ta saka ta amota zuwa Lere Laala da Zeeha daman basu ce zasu ba Ummi kuma bata matsa musu ba Tana asibiti Majeedan ta kirata da Wayar Talatu tace ta isa lafiya Ummi tayi Hamdala.

Majeeda taje Lere jumma"a Ni kuma Ranar Monady muka Dawo asibitin Abu shika a shashen Masu fama da lalurar kwakwalwa,In da aka taba kawo ni wajen Dr.Anandi, Saifudden ya Kirasa shi ya bamu Apportment yace mu same sa Ranar Monday zai ganni.

Ni da Saifudden munaa rike da Hannun juna muka shiga Office din Dr.Anandi muka zauna saman kujerun Office din bayan sun gaisa da Dr.Anandi sai yace Saif ya bamu Waje da ni kadai zai yi mgana sai na fara kwakwal kamar zan yi kuka sai ya kalleni yana fadin"Don"t worry bazai yi nisa ba.."
Sai na gyada kaina ammh ina ta waige waige,sa sai da ya shafa kaina yamin Rada a kunme sannan ya fita ina Zaune cikin natsuwata Sanye da Less mai ruwan kasa da mayafina jakata tana Hannun Saifudden Dr.Anandi ya Dade yana kallo na lokaci daya yana Rubuce Rubuce saman Fayel din dake gabansa sai zuwa chan sannan ya Sauke Biron Hannunsa ya Fuaskance ni.

Cikin Harshen Turanci yace"What is ur Name?

Cikin Dakiya duk da ina jin Tsoro Tsoro sai da nace"My Name is Muhibba..Muhibba Bello Mairago"
*Janafty*
*SFD0044*
*Amnaf_sudanese _collection*
*Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401*
*Ki biya ki karanta cikin salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba, kada ki karanta min littafi sannan kada ki yada'min shi don Allah pay N500 via jamila umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*
Sai da yayi Rubuce rubucen sa kan fayel din dake gabansa sannan ya dago ya sake kallona cikin nazari na ni kuma sai gabana ya fara fadi haka kurum sai naji tsoro tsoro ya fara shigana.

Gilshin sa ya gyara zama akan Fuskarsa kafin ya sake jefomin wata tambayar"Kina da aure..?

Cikin harshen Turanci sai mamakinsa ya kamani bai ga nazo tare da mijina na ba ne..?

Ganin yadda na bayyana mamaki na shiyasa ya dan yi mirmishi kafin yace"Kada ki damu duk tambayar da zan yi miki ki bani amsata kai tsaye saboda ya Shafi lafiyarki ni kuma ya shafi aikina"
Jin haka yasa na jinjina kai ya sake jefomin tambayan dazu cikin Sanyin murya nace"Eh ina da aure"
Cikin gamsuwa yace"Good kin Taba Haihuwa..?

In kin taba ya"yan ki nawa..?

Kai tsaye nace"Ban taba Haihuwa ba"
"Shekarar ki nawa da aure..?

Auran soyayya kika yi ko auran Dole ne..?

Ya jefomin tambayan kai Tsaye batare daya kalleni ba sai da nayi shuru na wani Lokaci kafin nace"Na fi shekara da aure..Sannan auren biyayya ne Daga Farko ammh yanzu ya koma na Soyayya"
Dr.Anandi ya Dago ya kalleni da Mirmishi kafin yace"Good"
Mirmishi nayi ina wasa da Gefen mayafina kaina na kasa ya Dauki kusan mintina goma yana Rubuce Rubuce kafin ya Dago yana Fadin"Matakin farko na tambayoyi na sun kare zamu shiga mataki na biyu"
Kai na gyada mai alamun na shirya kai Tsaye yace"Me kike jin Tsoro yanzu..?
Chapter 122 · 0% Book details