Sashe 75
Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Iya ta tsinke da Labari fadi take yi"Ai itama Saifu din ya aureta kafin ya aureki"
gabadayansu suka Dago suna kallon Iya ita bata damu ba ta cigaba da Fadin"Ai mun auna arziki yaron nan fa da kike gani jikokina Biyu na wanke na basa yana sakin su washegarin auran a baya zargin Zaliha nake yi sai daga baya muka Fahimci ba Laifinsa bane wata Muguwar aljanna ce ta auresa."
Gyaran murya yayi yana kallon Iya kafin yace"Iya me ya kawo wannan mganar..?
Iya ta Hararesa kafin tace"Bansani ba Don kaniyarka gwara a Fadamata aure da gaskiya ai yafi karko."
Muhibba na Danne Dariyanta ganin yadda yayi tace"Gaskiya ne Iya ni bai taba Fadamin ba"
Iya tace"Kaji ko.?ai ina Fada miki Ashe muguwar aljannar nan auran min jika tayi sai da muka yi da agaske muka Rabasu har ya samu ya futar zai aureki da kafin ayi mganinta ne da kema Daran auranki zai sakeki."
Muhibba ta kallesa cikin mamaki da Dariya ganin yadda ya kara Daure Fuska kafin ta kalli iya tana Fadin"Iya Ita ke saka shi Sakin matam kenan..?
Iya ta gyara zama tana Fadin"sosai ma an ce in suka auri Mutum shi da aure har gaban Abada da muka Fahimci haka ko uwarsa bata sani ba kin ganni da Tsufana nake zuwa karbo mai mgani ina aika mai dashi da Taimakon malamin nan da Taimakon Allah ta rabu dashi shine fa yazo da kansa yace ya samu mata a zaria zai aura."
Iya na cikin mgana ya mike ya fita iya ta bisa da kallo tana nuna sa da baki kafin tace"Haka yake da an fara mganar sai ya hade rai ya tashi."
Me Muhibba zatayi ba Dariya ba har da kayatawa duk da Lokacin da Sabanin nan ya faru Tsakaninsu an yad'a ya taba aure sau biyu ya rabu dasu bata Dauka da gaske bane ashe ya Faru kuma duka acikin Danginsa abu daya ya bata Dariya wai Aljanna ta auresa ashe shima kallon da ake rika yi mata shi ma haka ake yi mai nan dai ta kasa kunni tana shan Labari wajen Iya hatta yadda auran Ummi da Conel ya wakana sai da iya ta Fadama Muhibba suna cikin Hirar ne sai ga Goggo Atika iya ta gabatar da ita a matsayin Goggon Saifudeen ta gaisheta cike da Ladabi ta amsa Sama Sama tana kare ma Muhibba kallo cikin yatsina tace"ai ban ga in da tafi Majeeda ba da ya ki ta ya auro ta ba"
Iya ta Daka mata tsawa tana Fadin"Atika zam sabama miki na karajin wannan mganar a bakinki._
Goggo Atika ta mike tana Fadin"Allah ya baki Hakuri Iya..Daga Fadin gaakiya sai Laifi,nan ta fice tana Mganganu Iya na ce mata ta Tsaya ta karbi Tsarabanta ko tanka ta ma batayi ba.
Sai da Ta fice ne Iya ke fadin"Sai hakuri haka take da zafi.."
Muhibba ta gyada kai bata ce komai ba Tunda ai Iya ta fadamata kuma ta fahimci inda mganarta ya Dosa Tuna Majeeda tayi sai kuma taji Dariya in ba ma iyayen mu ba, ina Majeeda ta Dace da Mutum irin Saifudden ai hadin ma bai yi Tsari ba.
Ita dai Muhibba bata kara ganin Saifudden ba sai dare yini sukayi baki na shigo musu barka da zuwa matan makota sai Dare suka samu kafa ta Dauke sai wajen tara na Dare ya shigo Lokacin Baffa Hayatu ya Dawo suka shigo Falon Iya tare ita tana Uwar Dakin Iya ta gyara mata Gadon karfenta har ta sauya kayan barci ta kwanta Waya suka yi da Inna suka gaisa har ta bama iya itama suka gaisa tana saka albarka.
Daga cikin Dakin taji Baffa Hashimu na tambayanta sai Iya ta kwalama kira Da Muhirba tun dazu Iya ke kiranta da Haka ita Dariya ma sunan ke bata.
Hijabinta da tayi sallah ta Saka sannan ta fito har kasa ta duka ta gaida Baffa Hayatu cikin Sakewa ya amsa yana Fadin"Masha Allahu..Iya ta gwadamin abun arziki sannan yara nata murma da Tsaraba Allah ya alheri."
Sai Lokacin ta Dago kanta ta amsa da Ameen idonta ya fada kansa yana zaune gefe ya sauya kaya zuwa Farar Riga mai gajeron hannu da bakin wando waya ce a Hannunsa yana matsawa bai ko Dago ya kalleta ba itama sai ta mike tana Cema"Iya bari na koma na kwanta sai da Safen mu."
Iya ta amsa da Allah ya tashemu Lafiya ita da Baffa Hashimu shi kuma Gogan sai Lokacin ya Dago ta riga ta juya baya bata gansa ba sai da ta shige ya maida kansa Wajen iya yana Fadin"Ummi tana son mgama dake."
Iya ta gyara zama tana Fadin"To kiramin ita mana."
Daman ita yake kira bata Dauka ba sai daga baya tana Dauka ya mika ma Iya ta karba ta saka a kunni tare da Sallama cikin Fara"a fiye da ko yaushe
Suka gaisa da Iya sannan ta gayamata abun arzikin da Muhibba tayi musu Ummi taji Dadi matuka aranta tana godema Allah tana godema Muhibba Ummi tace"Allah ya bada Lada iya..Yaro ya ce min gobe zasu taho wajena shi ne nace a Fadama majeeda ta hada kayanta su taho min da ita..Daman wanda zan aiko ne ban samu ba shiyasa kuka jini shuru."
Iya tace"Ai kayan Majeeda sun Dade a hade Daman ta kosa ta tafi yanzu zan aikama Talatun angode Allah ya bada Lada."
Ummi na mirmishi tace"Bakomai iya an zama daya agaida kowa da kowa
Da haka sukayi sallama ta mika masa wayarsa tana Fadin"Majeeda tace ku tafin mata da ita"
Kamar zai yi mgana sai kuma ya Fasa ya Mike yana rike da wayarsa yace"Sai da Safe."
Iya tace"Allah ya tashe mu Lafiya..Gidan naku zaka kwana..?
Cikin Basarwa yace"A"a Hotel na kama.."
Iya tace"Me ye Osel kuma..?
Baffa Hayatu na Dariya yace"Iya Hotel wajen saukan baki ne ka biya kudi ka kama Daki har na Tsawon kwanakin da zakayi."
Iya tayi tsaki kafin tace"aikin banza banda asaran kudi ga gidan nan in ma ba zaka kwana ba gidan ku fa..?Miye amfaninsa..?
Saifudden ya fice yana fadin"Yayi kura iya."
Wani tsakin ta kara saki kafin tace"Kashe kudi dai kuran me ko ni Da kace min zaka kwana ciki da naje na gyara maka ballatana ga yara cike da gida ko matarka in kayi niyya sai ka Dauketa kuje ta gyara makaa inda zaka kwamta kafin gobe."
Shi dai yana jinta bai ce komai ba yayi Saurin ficewa kada Iya ta kara jawo mai wata mgana,a Shashen su Ummi bai da key din su sai nashi barayin kuma Katifa ce kadai a Dakinsa in ya Dauko Muhibba ina zai sakata Domin bai shirya fara kwana waje Daya da ita ba shiyssa ya zillema al"amarin shima yaje ya kama Daki daya na su Bama Daya nashi baya son Damuwa abinci ma duk nan yayi Oder baya iya cin wani abu in ya zo Lere ba domin wani abu ba kyamkyamimsa yayi yawa Tun yana yaro ko Hutu ya Dawo da yunwa wani Lokacin yake zama sai iya tayi Fada me yakan Tura hakanan Yaci dai yana yaro ammh yanzu kam ya yafe.
Muhibba dai barcinta tasha Hankalinta kwance sai asuba ta tashi Iya a Falo ta kwana saman Cafet ita tama tasheta suka mike suka yi alwala sukayi sallar Asuba Muhibba nan ta zauna tana azkar har Gari ya waye ta duka har kasa ta gaida iya tana saka albarka da majeeda ta shigo kawo mata Ruwan zafim wanka Iya tace in ta shirya tazo ta rakata shashen su su gaisa da iyayen nata
Muhibba tayi wanka ta shirya cikin Doguwar rigar atamfa da Hijabinta kalan Oniom Colour,iyakarsa gwiwanta ko kafin ta fito an sauke mata ruwam zafi da kayan Tea har da Soyayyan Dankali da kwai Iya ta tasata sai da ta karya Ta sha dai Tea din da Dankalin kwan kuma karni ya hanata ci Tana gamawa sai ga Majeeda ta dawo tana ta murnaa yau zata koma Habuja tun Safe har taje tayi sallama da kawayenta ita ta rakata Shashen inna Talatuwa suka gaisa da ita da Baffa Hashimu ta dan jima anan Majeeda nata mata Hira Farat Daya taji yarinyar ta shiga ranta itama ta saki jiki suna Hira Baffa Hashimu da Talatuwa na jinsu sai abun yayi musu Dadi.
Daganan sai Shashem gaje nan ma su dan jima Saboda Baffa Hayatu ne ke ta janta da Hira,Dagaman suna Fitowa Muhibba ta kalli Majeeda tana Fadiin"Majida kaini gidan Goggon ku mana.."
Majeeda tace"Wai Goggo Atika..?
Muhibba ta Daga mataa kai Majeeda tace"Iya tace kije..?ni bana son zuwa gidanta ta cika fada."
Muhibba tayi Dariya kafin tace"Muje ki rakani Daga nan sai ki muna min gari."
Jin haka yasa da Murna Majeeda ta amince suka fice daga gidan a kofar gidan sun ga maza da yawa sai da suka wuce me Majeeda tace"Duk fa Ya Saifu suke jira"
Muhibba ta kalleta da mamaki kafin tace"To me zai yi musu..?
Majeeda tace"Tab kudi zai raba musu haka yake yi in dai yazo sai yayi ta Raba kudi."
Muhibba ta jinjina kai bata ce komai ba Suna cikin Tafiya Majeeda ta nuna mata wani gida mai kyau tace"Ga gidan su ya Saifu..!"
Muhibba ta kalli gidan Iya ta fadamata gadon su shi da Sadiya ne suka kara siyan Filin kusa da wajen suka yi gida.
Cikin Yar dariya tace"Kice min inda aka kawo ki dai ko..?
Majeeda ta zaro ido kafin tace"Laala..Hala iya ta fada miki..?
Muhibba tace"Ita ta fadamin..Ni da zaki aminta da kinzo mun zauna Tare.
Majeeda ta zabura kafin tace"Ni bana so wlh..Karatu zani Habuja nayi abuna."
Mahibba tayi Dariya batace komai ba Har suka karisa gidan Goggo Atika sun Sameta tana ta wanki bata wani karbe su ba sama sama dai Majeeda ke fadamata zata bi su ya Saifu Habuja sai alokacin muhibba ta san da tafiyarsu ma Abuja.