← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 144

Sashe 95

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kaina na Dafe da Dubara na share hawayena kafin nace"Lafiya lau Headteacher kaina na ke min ciwo kad'an"
Headteacher tace"To ba sai ki sha mgani ba"
Da Sauri nace"Nasha kafin na fito"
Wajen zamanta ta koma tana fadin"Ai da baki zo ba tunda baki da Lafiya"
Ni dai ban iya ce mata komai ba Daga karshe ma Fita tayi ta barni Saboda bashin barcin jiya yasa na kifa kaina jikin Desk na fara barci Ban farka ba har a ka koma Break ina tashi Naga Uncle Hafiz ne a Office din yana rubutu Idanuwana Luhu luhu na Dago ina kallonsa shima kallona yake yi Cikin Damuwar ganin yanayi yace"Anty Muhibba are u ok..?

Ido na na Mitsike kafin nace"Karfe nawa..?

Agogon Hannunsa ya Duba kafin yace"10:56am'
Ido na zaro kafin nayi mgana ya Rigani da Fadin"Anya kina Lafiya..?

In baki da Lafiya ki koma gida mana"
Ban ce komai ba naja Lesson Note dina ina Fadin"Naji sauki zan iya Uncle"
Rubutu na fara yi da gaggawa kamar wacce aka tsare da Bindiga,Shi dai sai kallo na yake yi Saboda yaga abubuwa da dama a wajena wadanda bai sanni dashi ba.

Ranar dai ba abunda na Tsinana a makarantar nan karshenta ma kafin a tashi na tafi gida Headteacher ta matsa min na tafi gida Saboda ko Lesson Note din da nayi ba Cikin natsuwa ba ne.

Adaidaita na hau zuwa gidan Inna ko da naje bata nan ta shiga makota an yi haihuwa gadonta na haye na kwanta ina jin kamar na samu salama.

Daganan kuma sai barci sai jin mganar Inna nayi sama sama tana Sababinta Ina bude ido naganta tsaye a kaina tana fadin"Wannan wani irin barci ne..?,Tun shigowata fa kina barci to ki tashi kiyi sallah biyu ta wuce na rana"
Mitsike ido nayi na sauko Daga kan gadon ina Fadin"Ina na gaji ne jiya ban yi barci ba"
Cikin mamaki Inna take kallona har na mike ina Tangadi na fice,Buta na Dauka na shiga makewayi na Kama ruwa na fito nayi alwala,na koma Dakin Inna na zaune tana gyaran gyada ta Dago ta kara kallo na batayi mgana ba sai da na Idar da Sallah sannan tace"Jawo cooler din chan abinci ne aciki"
Ba musu na jawo cooler din Na Bude Shinkafa da wake ne Jallop,Yadda Inna taga inaci ne hannu baka hannu kwarya ya bata tsoro sai kawai na koma mata abar kallo Tas na Tada abincin na Kora da ruwa ina Haki na koma na Jingina da gado kamar Daga sama naji Inna tace"Meke Damun ki Auta..?

Cikin gajiyar data sakkomin na kalleta kafin nace"Inna gajiya ce kawai"
Inna tace"Ban da ita fa..?,Me ya hanaki barci jiya"?

Sai anan na gane na kusa nayi barna cikin gyara mganata nayi saurin cewa"Aikin makaranta ne ya Daukeni Lokaci kafin na gama sannan na dade kafin barcin ya Daukeni."
Inna bata aminta da mganata ba ammh kuma bata kara cemin komai ba Mikewa nayi ina Fadin"Anty Zenatu na nan..?

Inna ta Daga min kai Fita nayi zuwa Shashen ya Habibu achan ne na Sake sosai muna ta Hira sai da aka kira La"asar na koma bangaran Inna Salla kawai nayi Inna taga na share kafa naki Tafiya har Biyar tayi ana neman shidda Sai Inna ta kalleni tana Fadin"Auta baki ga yamma tayi ba ne..?

Hankalina sai ya tashi jin zan koma wannan gidan cikin bata rai nace"Inna ni fa bana son zama agidan nan ni kadai ina yarinyar da kikace zaki samar min?

Inna tace"Ana kan bincikawa ne.."
Shuru nayi na kasa mgana Sanin Inna bazata Saurareni ba Hakanan na mike na shirya Naso na jira ya Habibu ya Dawo Inna ta Fattake ni,Dole na koma gidan da nake jinsa kamar Mutuwa ne wlh Sanda na koma sai Firgici ya Dawo min bani da Natsuwa kwata kwata.

Adaran na kwana Lafiya Domin kusan Raba Dare mukayi muna Hira Da Saif ya taimaka wajen Debemin kewa matuka.

Washegari cikin Hayyacina naje makaranta ba kamar jiya ba,Wauta ta farko ban yi wayaun gayama Inna ko wani nawa Halin da nake ciki ba shima Saif sai ya Biyemin bai fadama kowa ba,Laraba da alhamis Lafiya lau na kwana acikin gidan nan,Ranar Jumma"a ni na rike Ajina Uncle Idris yazo yana Staff Room,Na gama yi musu Math kenan na koma na zauna kan kujera,Akwai Homework da na basu jiya shi ne suka yi Submitting,ina Marking kamar an ce na Dago kaina ina Dagowa kawai ajikin Farar rigar Uniform din dake jikin Isma"il Bala wani Dalibin ajina sai na Hango Jini Duk ya bata gaban rigansa Gabana sai ya Fadi na Sauke Biron Hannuna ina Fadin"Isma"il Bala."
Na kira sunansa Da sauri ya mike yana Fadin"Yes Mah"
Cikin Harshen Hausa nace"Meyasa baka wanke Uniform din ka ba?

Cikin mamaki ya Duba kansa kafin yace"Anty Mom dina ta wankemin ta Gogemin jiya"
Ni fa Jini nake gani agaban Rigansa Yasa na taso naje gabansa ina Dubawa Stil kuma jinin nake gani Cikin bacin rai nace"An wanke kuma wannan jinin fa..?

Na fada ina kallon Gaban Rigansa Cikin mamaki shi da sauran Daliban Ajin sukace"Jini.."?

Suka fada cikin mamaki kai na Daga musu cikin Fitan hayyaci ina nuna gaban rigan Isma"il ina Fadin"Jini fa baku gani ne hala..?

Na dake ina Bala'in naga jini har sai da na Rudar dasu Anty Debora ce ta shigo Saboda tazo wucewa taji Hayaniyata Ina ganinta naja Hannunta Ina fadin"Anty Duba ki gani Ba jini ba ne anan..?

Na fada ina Nuna mata inda naga Jinin Sai dai ina juyawa sai naga Kusan Duka kayan yaran jini yayi faca faca Sai na kara Razana cikin Firgici na Fara nuna mata yaran bakina na rawa nace"Ji...Jjjjjji...JiNiii..."
Na Fada a rarrabe cikin tashin Hankali,Lokaci daya Firgici ya bayyana awajena Rawan da jikina ke yi ina nuna yaran duk sai suka Firgita Anty Debora ganin haka yasa ta rikeni Tana Fadin"Anty what Happend..?

Itama sai kawai naga Mayafinta mai Ruwan Madara ya koma Kalan jini Ihu na Fasa ina Fadin"Jini"
Jini"
"Jini"
Cikin wata irin murya kamar wacce aka saka ma karfin mutane goma,Haka na Fizge jikina na Ture Anty Debora da ita ta fara Rudewa tana Fadin"Blood"
What wrong..?

Ba ta da mai bata amsa Suna gani Muhibba ta Rumtuma aguje Daman mayafi na saka Tuni yayi barayinsa haka na Fita har haraban makaranta Ina Ihu da kuka Ina Fadin"Jini"
Gabadaya malamai da Dalibai suka yo Waje cikin Tashin Hankali neman nake yi na bar cikin makarantar D.Musa da yaji hayaniya ya fito Tuni Kallabina ya Sabe ya fadi kalabar da nayi sun watse kamar mahaukaciya ina Ihu ina waige ina Fadin"Jini"
Garin gudun ceton rai naci Tuntube na Fadi kasa jikina da fuskata ya baci da kasa haka na mike na kara Gudu zan Fita Daga cikin makaramta su Uncle Hafiz sun shiga tashin Hankalin da basu taba gani ba Cikin mamaki da al"ajabin me ya faru.

D.Musa ne ya bada Umarnin kar a barni na Fita a Rufe get din makaranta.

Ina zuwa na Rika Jijjiga get din kamar zan Balla ina Fadin"Jini..jini ku budemin"
In na juya kuma yaran nake gani har da Anty Debora suna nufoni jikinsu na Digar jini Gabadaya sai na Firgice Su Headteacher ne da su Anty Jidda har da su Anty Usaina suka Nufeni suka Rirrikeni suna Kiran sunana ina bana jinsu suma sama sama nake ganin su jini na malala ajikinsu. ganin haka yasa na Fara Fizge Fizge kamar almara haka na watsar da su Na nufe get zan fice kawai naga wata mata Doguwa a gabana Ta saka Fararan kaya Tunda ga sama har kasa Bakin gashi ya Rufe Fuskarta Sai dai Jikinta gabadaya Fararan kayan nan suna Digan jini Tana mikomin Hannayenta da Zararan kumbunanta suna Dingan jini,Ido na Zaro jikina na mazari Hannu na Daga ina nuna ta na kasa mgana Kawai sai naji ta saki wata irin Gigitattaciyar Dariyar da ake yi min irinta agida Kaina yayi wani Dum Dam!

Kawai sai na Sulale a sume ban Fadi ba naji Hannuwa sun Tareni Daganan ban kara sanin inda kaina yake ba Sai da na Farka na ganin a Dakin Inna,Da Daddare ga Ya Habibu na rikeni dani ina kan kafafunsa Sai Anty Habiba da Abban walid sai mallam Haruna da wasu almajiran sa guda Biyu Sama sama naji yana Fadin"Masha Allah ta farfado"
Gabadayan su suka tallafoni kowa kiran sunana yake yi yana tambayata yadda nake ji inna kawai na amsa mawa data rikeni tana Fadin"Sannu Auta Sannu kin ji"
Kallonta nayi ina Daga mata kai Cikin wani yanayi nace"Inna wa ya kawo ni nan..?

Inna na sharan kwallah tace"Malamam makarantar ku suka kawo ki a sume Auta bakya cikin Hayyacimki sun ce kina ta Ihu kina Kiran Jini Tun Safe mallam Haruna ke kanki Sai yanzu kika Farfado"
Kamar a majigi haka al"amarin ya Fadomin sai na Fashe da kuka ina Fadin"Inna sai da na Fada muku bazan iya zama acikin gidan nan ba Inna a na Firgitani ne wlh akwai aljanu agidan"
Anty Habiba tace"Nima dai haka nace Gidan ne ke da matsala"
Ya Habibu yace"Ni dai ban san ko Auta ta taba Fuskanta wata matsala agidan ta ba ko Inna tasani s bata gayamim ba"
Inna tace"Nima ban sani ba Habibu sai yanzu kuma kaji mallam yace an Dade ana Firgitata"
Mallam Haruna yayi gyaran murya yana Fadin"Ku barta tayi bayani da kanta Muhibba ki fadamin tun yaushe kika fara samun wannan matsalar..?

Muhibba na kuka ta makale jikin Ya Habibu kamar an saki bakinta ta fara Bada Labarin abunda ta fara Fuskarta Tun ranar da aka Daura mata aure da Saifudden da Duka abubuwan data Fuskata har zuwa yau din ta karishe da Fadin"Na ganta..Wlh na ganta tana min Dariya tana mikomin hannu jikinta duk jini"
Mganar ma da take yi jikinta na rawa,Inna da Ya Habibu suka riketa mallam Haruna yayi shuru bai yi mgana ba Inna t
a fara kuka Tana Fadin"Innalillahi wa"inna illaihirraju"un ka gani ko mallam Daman ni nasan wannan aljanin bazai Rabu da Auta tayi zaman aure ba,Sai da ta fara samun natsuwa agidan auranta sannan zai Dawo ya kara Ruguza mata rayuwa..?wannan Rayuwa da me yayi kama..?
Chapter 95 · 0% Book details