← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 144

Sashe 3

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai ta juya ta kalli na kusa da ita kawai sai tayi luu ta Fado jikinsa a Sume.
_Madallah da mutanen kirki Madallah da mutanen da suka san karamci, madallah da mutane masu kima da Daraja ina mgana ne kan Al"ummar da alherin su ya Zagaye Rayuwata gabadaya,wato masoya na da sune Silar Mirmishi na da Nasara ta nagode kwarai bisa soyayyarku da kaunarku kan duka Littafaina Ina godiya bisa yadda kuke tare dani a koda yaushe Allah ya saka muku da alheri ya bar zumunci Allah ya Ribanya arzikin ku Allah ya kara Wadata da kwanciyar Hankali Janafty ta gode matuka kuma Godiyarta bazata taba karewa ba, Allah ya Hada Fuskokin mu a gidan aljannah gabadaya Nagode Nagode_
*Assalamu alaikun Masoya na,Gashi na dawo muku da Sabon Labari kamar yadda na fada,Basai na wasa kaina ba ko kuma na yaba kaina ba abu mai kyau da inganci baya bukatar Tallah shi yake tallata kansa,Nasan D'an Adam tara yake cika goma ba, kuma Koda yaushe shi mai kuskure ne To nima ina kuskure wani Lokaci,Sai dai ina kokarin ganin na Faranta muku,Kowani Labari da nashi Salon karo na Farko da alkalami na zai Rubuta Labarin da ya faru a gaske tare da Labarin yadda aljanu suke shiga Rayuwarmu su gurbata mana bamu sani ba Labarin Ta fita zakka da Sauran Labaraina daban suke da kowanne bangare da nashi,Abu daya na sani zaku ji Dadin sa Fiye da na baya kuma Insha Allahu bazan baku kunya ba Wannan Labarin Na kudi
ne akwai Free page goma zuwa sha uku,Idan kina Bukatar ayi wannan Tafiyar Dake zaki biya kudin Karatunki akan N500 ta wannan acct Number din 0552179550,sai a turo Shaidar Biya ta wannan Lambar 09069067488 in kuma katin waya ne, zaku Dauki Hoton Katin ki Tura kai Tsaye ta wannan Lambar 09069067488 in kuma yan Niger ne ku Tuntubi wannan Lambar +22796562223 Kausar aglan Nissa,Zan Fara Sakin Free page ranar 26 na wannan watan zaku iya fara payment kafin Mufara,Zamu kamallah shi da yardan Allah kafin watan azumi ya kama Allah yasa mu dace Ameen.*
*SAIFUDDEEN*
_(Ba mutum ba ne)_
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
_*Bismillahir Rahamanir Rahim*_
*Sadaukarwa ga iyayena*
*Malam Umar muhammad mailoki(Babana)*
*Malama Khadija muhammad Ba'are(Mamana)*
*Ina rokon Allah ya kare ku daga dukkan sharri Allah ya kara muku Lafiya da nisan kwana*
*Tukwici ne na musamman ga Masoya na,a duk in da kuke,wad'anda suke goyamin baya a ko wani Lokaci wad'an da alherin su suka Lullebi ni gaba na da baya na, Ina matukar godiya Allah ya saka muku da alheri Allah ya bar mana zumuncin mu har agidan Aljannah Ameen*
*KADUNA STATE.*
_Lere local goverment_
*Area:Abadawa.*
Monday:6:40am.

Zaune take kan wata katuwar Darduma,tayi zaman tankwashe Kafafunta jikinta sanye da Hijabi mai yalwa mai ruwan kasa kanta na Duke da Casbaha a hannunta lokaci Daya bakinta na motsi sai dai baka iya Hango Fuskarta saboda yadda tayi kasa da kanta sosai.

Kamar wacce aka biyo haka ta fado cikin bedroom din da Ummi take ciki ita da k'anwarta Hajiya zuwaira ,cikin wata irin murya mai cike da kuka ta d'aga takardan hannunta tana fadin" YA SAKE NI..YA SAKE NI..Yaya Saifuddeen ya sakeni na shiga uku na."
Take fada kafin tayi zaman yan bori saman cafet din daya malale bedroom din Ummi dake saman Darduma tana lazimi ta mike a Firgice gabanta na fadi Hajiya zuwaira data fara barci sama sama kan wani makeken Royal bed din Dake Dakin sai da ta tashi a Firgice gabadayansu suka yi kan Majeeda suna tambayanta me ya faru..?.

Ta kara Daga farar takardan dake hannunta tana fadin"Ya sake ni..yace ya sake ni.."
Sai Ummi ta Dafe kanta tayi baya kamar zata fadi hannayen k'anwarta Zuwaira suka taro ta lokaci d'aya tana fadin"Yaya zulai ki yi a hankali fa."
Ummi ta kalleta cikin wani yanayi kafin tace"Na shiga uku zuwaira YARO zai kasheni kwana na bai kare ba..?Jiya fa aka daura masa aure da Majeeda itama ya sake ta kamar yadda ya saki Amira..?

Anya yaro na da lafiya kuwa..?

Hajiya zuwaira ta kalli yayarta cikin yanayin Tsausayi da jin kai kafin tace"Kiyi hakuri ya zulai mu bi komai a sannu.."
Tafada Lokaci Daya tana taimaka mata ta zauna gefen gado ammh har Hawaye sun fara wanke mata Farar Fuskarta da girma da shekaru bai sa ta sauya ba.

Majeeda kuwa kuka take bilhaqqi da gaskiya har tana kwanciya kasan Cafet bedroom din tana Hadawa da ihu kalaman na shiga uku na lalace ya Sakeni bai bar Bakinta ba..

Mami ta kura mata ido tana kallonta cikin Tsananin Tausayinta Zanen kunshin da akayi mata baki da ja take kallo tare da Dishi dishin kwalliyan Amarcin da aka gama Tsantsara ma ita Majeedan ajiya duk domin Daranta na Farko Ammh Lokaci Daya yaron nan ya aikata abunda ya bata komai..!

Kawai sai taji Rauninta ya karu in akwai abunda ke sa jininta na yawan Hawa yaro ne shi ne kadai Damuwarta data rage mata a nan duniya ta tabbata yadda yake saka ta kuka ko Laala da Zeeha basa saka kuka haka.

Kawai sai ta Rufe fuskarta da Tafukan Hannayenta har Lokacin bata saki Casbahan hannunta ba ta fara Rera kuka ahankali Cikin kuna da Takaici Sabanin na Majeeda dake take da ihu Har da kururuwa.

Zuwaira ta kasa jure kukan yayarta yasa ta matsa kusa da ita ta Rumgumota tana faman lallashinta Lokaci D'aya tana Fadin"Haba ya zulai ki daina wannan kukan don Allah kin fa san baki da cikakkiyar Lafiya sannan kuma kukan da kike yi kamar karin Fushi ne ga SAIFF a wajen Ubangijinsa mubi komai a sannu don Allah..!

Ummi ta Dago kanta cikin wani yanayi tana kallon kanwar tata kafin tace"Haba zuwaira ya bazan yi kuka ba..?

Kin manta Jiyan nan aka Daura ma yaro aure da yarinyar nan Majeeda yar wajen Babansa Hashimu..?

Ko kin manta yadda jiyan nan da Daddare Hashimu ya tashi Daganan bayan ya gama Fadamin yanzu ma na kara nuna iko na akan Yaro na kara sakawa ya saki Majeeda kamar yadda ya Sako Amira..?

Ashe ko Saboda Yaro ya kaucemin wannan Zargin bai isa ya rike auran wannan yarinyar ba..?

Bata ba ta Damar mgana ba ta cigaba da Fadin"Yasan ai kukana bala"i ne ga Rayuwarsa ammh bai taba Nadamar abunda yake aikatawa ba...Daman Zagin Dangin Ubansu yake so ya kara jamin ai shikenan Zuwaira Burin Yaro ya cika yau gani a lere agidan Ubansa ban tafi ba. duk abunda Hashimu da iya suka ga Dama yau sai sun Fadamin acikin gidan nan bani da ikon kare kaina bani dashi Zuwaira..!

Ta karishe Fada cikin matsanancin kuka mai tafe da cin rai da bakinciki..

Zuwaira ta sauke ajiyar zuciya cikin wani yanayi tace"Baki da iko kam ya zulai..Saboda ke Uwa ce..Ita kuma uwa a koda yaushe D'anta in ya aikata wani abu mara kyau sai a Danganta ta dashi in kuma ya aikata akasasin haka sai kaji ana Kuranta Mahaifinsa da Danginsa ita uwa ai sha kudum ce duk kwaramiyan Duniya kanta yake karewa ya zulai Shiyasa nace ki bar wannan kukan mu bi abun a sannu"
Ummi bata kara mgana ba illah Hawayenta datake sharewa tana kallon Majeeda dake kukanta har na yanzu yafi na Dazu karfi dagunji.

Hajiya Zuwaira ce ta kalleta cikin Takaicin yadda take kuka agogon bangon Bedroom din ta kalla taga Bakwai saura na Safe cikin Haushi ta Dawo da kallonta kanta tana Fadin"Ke miye haka..?

Ki bar mana wannan kukan don Allah kalli Halin da kika jefa ya Zulai aciki da wannan Hayaniyar taki..?

Tafada ranta na kuna Saboda ita har ga Allah bata ga Dalilin matsana Saif da auran yarinyar nan ba Tun an basa Na farko ya saki miye kuma na kara Cusa mai wata kuma..?

Majeeda da ko Nuna ta jita ma batayi ba illah kara dora hannu asaman gyalen Dake kanta datayi ta kara sakin wani kukan tana Fadin"Na shiga uku ni Majeeda ya sakeni.."
Mama Zuwaira ta saki wani Dogon Tsaki ta mike afusace Mami ta Dakatar da ita Lokaci Daya da Fadin"ki kyaleta Zuwaira tayi kukanta ai abun kuka ne ya sameta Kada ki manta tana da karancin shekara ta zama bazawa sakin wawa ko ke babbar mace ki auna abunda ya Faru da ita akan ki,ki gani ko zaki iya Sarrafa kanki..?

Tafada Tana sakar mata Jajayen idanuwanta wadanda suke kamar na Zuwaira kana ganinsu zaka san Yan"uwan juna ne saboda suna kama sosai sai dai ita Mami ta fi kanwarta Zuwaira Tsawo ayayinda Zuwaira Ta fi Mami kiba da Kuma Fadin Fuska ammh Farare ne Tas Fulanin da suka Fito Daga Bungudun ta jahar zamfara.

Nan da nan mama Zuwaira taji jikinta yayi sanyi ta koma gefen yayarta ta zauna,ta rasa mafita gabadayansu sun tasa Majeeda agaba suna kallon yadda take Dirzan kuka...

Zuwaira ta sauke Tagumin da tayi Lokaci Daya tace"Ya zulai ya zamu yi da yarinyar nan ne..?

Ummi ta kyaci majina kafin tace"Uhm..Bansani ba Zuwaira..Bansani ba..!

Zuwaira sai ta mike ta isa bakin Madubin Dakin ta Dauko wayarta Tana latsawa Ummi ta Dago tana kallonta kafin tace"Wa zaki kira kuma..?

Zuwaira tace"Su Sadiya zan kira.".

Kamar zatayi mgana sai kuma ta fasa ta koma ta Sadda kanta kasa Lokaci Bayan Lokaci tana Faman sharan kwallah Ga Majeeda da kuka ya Sarke muryanta ta Daina Fita sosai.

Wayarta ta Kanga a kunnenta Lokaci Daya Tana Fadin"Sadiya kun tashi..?

Ku taho Dakin Ummi muna jiran ku..!

Daga haka ta Datse wayar ta Fara Tunanin Laluban Saif sai dai kuma Duka Layukan nasa guda Biyu suna kashene Daman tana da yakinin bazai aikata wannan Danyen aikin ba kuma ya tsaya nan kusa ba..!

Kamar wadanda suma aka Jeho haka suka shigo Dakin Fuskokinsu a Matse Da alamun Daga barci suka taso,Adda Sadiya ce kan gaba Sabe da Karamar D'iyar ta Nihad sai Laala da Zeeha da suke bin bayanta kowannensu sanye da kayan barci Riga da wando masu ruwan kasa yara ne yan mata Laala bazata wuce Shekara sha Shidda ba yayinda Zeeha iyakarta shekaru sha takwas ita kuma Anty Sadiya ta kai matakin matashiya Domin zata Haura ashirin da Biyar ita dai Ta yo Lullube ta Rufe Doguwar Rigar Barcin Dake jikinta.
Chapter 3 · 0% Book details