← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 144

Sashe 66

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana Daga kiran kafin tayi mgana Adda Sadiya ta rigata da Fadin"Muhibba kuna Lafiya kuwa..?tun dazu muna ta kiran wayoyin ku daga ke har Hamma baku dauka ba sannan Sani da isma"il sun kawo muku Breakfast baku tashi ba sun dai barma masu Tsron Hamma Sallahu daman mu yi muku sallama ne mun shirya zamu wuce su Mama tun dazu suka kama Hanyar Gaya..!"
Muhibba bata gane mganarta sosai ba cikin mamaki tace"Da asuban nan Adda Sadiya..?

Adda tayi yar dariya kafin tace"Wani asuba yanzu karfe goma..Ku dayake Amaree ne shiyasa baku san gari ya waye ba.."
Gaban Muhibba ya fadi Dam!

Ta kasa gasgasta abunda taji,Sauke wayar tayi Daga kunnuwanta tana duba Lokaci sai da ta zaro ido ganin 10:16am na Safe ko Sallar asuba batayi ba ai bata san sanda ta kife wayar nan saman gado ba tana ji Sadiya na mgana bata Tsaya Sauraranta ba ta mike da karfi wannan karon kafarta ce ta amsa mata ammh bata bi ta kai ba ta Bude kofar Tiolet din dake bedroom din ta shige Tunaninta me ya makarar da ita haka..? ita da kiran sallat Farko a kunnenta abun ma ya zame mata jiki ko bata sallah tana tashi tayi azkar ta koma barci ammh barcin jiya wani barci ne da bai taba kamata ba,babu sukuni ko kadan acikinsa ammh sai da danganta haka da gajiya da Rashin Addu"a yasa har tayi mugun mafarki mara Dadi ganin ta riga ta makara yasa ta Tube kaya tace bari tayi wanka aranta tana mamakin irin zaman da zasu yi da Saifudden acikin gidan nan ace sallar ma bazai iya tashinta ba ai tana da Tabbacin har masallaci yaje tana wannan Tunanin Madubin Tiolet din ya hango mata Fuskarta sai da ta tsorata kamar wacce tayi Dambe Goshinta ya kumbura kumatunta duk yayi wani ja alamun ya tabu haka ma jikinta gaba daya ke mata Tsami ta Daga hannunta shima ya bugu Sai muhibba ta rasa wani Tunani zatayi ne sai Tunaninta ya bata mabugin Dare ta Hadu dashi Tun da ta kwanta batayi addu"a ba Tana wanka tana Fadin"Astagarullah acikin Ranta har ta gama ta Dauro alwala babban Towel dinta da su Anty Habiba suka shiryamata da sauran kayan wanka jiya a Tiolet din ta Dauka ta Rufe jikinta ta Fito Sauri Sauri haka ta sha fa mai ta Bude wardrpe dinta da Anty Zeenatu ta gama shiryamata kayanta sabbi dana gida wata Doguwar riga baka ta Dauka ta zira da Sabon Hijabinta Akwai Sabuwar Darduma Saman Side Drower ta dauka ta shimfida bata san gabans ba kintata tayi ta tada Sallah har ta idar ta zauna tana Istigafari kunyar kanta bai saketa ba Tasan Allah bazai kamata da Laifi ba domin bata sani bane sai Alokacin ta samu tayi azkar dinta sannan ta mike Tana da man zafi Domin Inna na yawan siyan mata Saboda tana yawan tashi da ciwon wuya Cikin kayan ta na gida ta Duba sai ko ta gansa cikin karamin akwatinta tayi Hamdala shi ta mulkama Kafafunta da Hannayenta ko zasu saki sannan ta kwashe kayan data cire ta kakkabe ta Ninki Tunda ba Datti sukayi ba ta maida cikin Wardrope.

Ko zama bata kai ga yi ba aka sake kiran wayarta tana Dauka ta Duba Taga Adda Sadiya da Hanzari ta Dauka tana Fadin"Yi hakuri Adda yanzu nake shirin kiran ki."
Dagacham bangaran Sadiya tace"Ba komai Amarya..Taimako zaki mini.Hamma zaki kaima wayar ki wayarsa muna ta kiransa ni da Ya Mujaheed bai Daga ba gamu har mun dau hanya.."
Muhibba tace"Adda har zaku tafi..?Ina su Laala dasu zaku wuce..?

Sadiya tace"Su ai sun kusa isa Gaya ma..Kinsan gobe zasu koma Abuja da Ummi Saboda makaranta ni da ya Mujaheed ne da Nihad Ya Datti ma Tun Safe sun Dauki hanya shi da Sa"adatu."
Muhibba tace"Allah ya tsare..Basu zo mun yi sallama ba.."
Sadiya na Dariya tace"sai wani jikon Muhibba yanzu dai ki taimaka ki Sadani Hamma na."
Ba musu ta mike ta fita sanye da Farin Hijabin datayi sallah sai yau ta ga yanayin falon domin shekaran jiya idanuwanta suna Rufe cikin Hijabi Yanayin Falon da kalan kujerun yasa tasan ba nata bane tun da ita nata Red ne
Ta gansu a waya sannan ta tuna su Asma"u sun fadamata falo biyu ne Daya sun gansa yana da komai Dayan ne aka saka mata nata kayan na ciki kenan,Kan center Table ta Hangi wayoyi Guda uku da bakar leda asaman wajen sai tayi Tunanin nan ya bar wayar nasa kenan bata karisa cikin Falon ba ta nufi Dakin dake kusa da nata sai dai tana Budewa taga wani Tsararan Falo mai kyau da yarari har sai da ta shiga ta kara ganin komai Mirmishi ya Subuce mata afili ta Furta"Allah ya saka ma Ya Habibu,Inna da Anty Habiba da alherinsa.."
Dakin dake gabansa kuma D'ayan bedroom dinta ne shima mai Dauke da Gado mai kyau kalan ash colour ne Gadon da wardrpe din sai Italiyan Cafet din mai kalan Ash shima.

Wanchan bedroom din nata ja ne gadin so harta Labulan Dakin jajaye ne Sabanin wannan da duka komai Ash ne haka ta fito tana mai jin Dadi da alfahari,bata taba kawo ma ranta Dakin sa bane kanta tsaye ta Bude ta shigo sai dai tayi turus ganinsa zaune kan Darduma sanye da Jallabiya Fara kal da ita yana kallon gabas yasa Keyarsa da bayansa kawai take gani gabanta ya fadi jikinta ya fara rawa Tayi saurin juyawa zata fita sai wayar hannunta ta fara kara da yayi sanadiyar
tsayawarta da kuma Juyowarsa daga inda yake zaune.

Shima bayanta ya ke gani cikin Farim Hijabi sai ya samu kansa da kasa Daina kallonta Kusan daman Farin abu Best colour dinsa ne duk da Hijabi ta saka kuma ta juya baya sai yanayinta yayi mai kyau matuka har yaji kamar ta Burgesa.

Bakinsa nauyi yayi masa ya kasa mata mgana ita kuma jikinta sai rawa yake yi ta kasa juyowa sai da taji Adda Sadiya ta kara kira sannan ta juyo Cikin Sanyin jiki kanta na kasa daga inda take kawai ta duka bakinta suna Rawa tace"Ina..ina kwaana..!"
Karaf kuma ta mike bata jira amswarsa ba ta kariso Cikin Tsakiyar Dakin Saman farin madubin dake Dakin ta Sauke mai wayar Lokaci daya ta juya tana fadin"Adda..Adda Sadiya na mgana..!"
Kamar wacce wani abu ke ja haka ta fice da gaggawa ya rakata da kallon mamaki da wani abu a kasan ransa da baisan ko na miye ba bai bama Tunaninsa Dama ba wayar ta sake Daukam kira Dole ya karisa ya Dauka ya kara a kunne Sadiya Dagachan bangaran tace"Hamma..!

Cikin murya shake ya amsa mata"Na"am Addata.."
Ajiyar rai ta sauke kafin tace"Hamma duk amarcin ne muna ta kiran wayar ka baka Dagawa..?

Kansa ya shafa kafin yace"Bata tare dani ne..!"
Gaisheshi tayi ya amsa mata kafin ta Dora da fadin"Hamma breakfast din ku na waje fa da su isms'il suka kawo muku baku tashi ba sai su ka bama masu Tsaron ka ka fita ka amsar muku..Dama na Fada maka ne saboda kaci Sosai nasan kana Tare da yunwa da Hannuna nayi muku shi Hamma.."
Dan mirmishi yayi kafin yace"Mungode.."
Adda Sadiya tace"Hamma asha Amarci lafiya mu mun kusa isa kaduna."
Cikin mamaki yace"Har da mujaheed..?

Sadiya tace"Yes..Su mama zuwaira ma yanzu muka gama mgana suma sun sauka Gida yan zu nan.."
Saifudeen ya shafa kansa kafin yace"Har da Datti..?

Sadiya tace"Dukkan mun mun tafi..Shima suna Hanya sun riga kowa tafiya Tunda suna da nisa."
Saifudeen yace"Allah ya kiyaye hanya zan kira su in sha Allahu."
Da haka sukayi sallama bayan ta tayasa da Fatan alheri bai amsa mata ba ya katse kiran,,Wayar Muhibba yake kallo Infinix ce ammh daya ke baya rike irin wayoyin sai yaga kamar ba waya bace,Cikin aljihun Jallabiyansa ya zurata yasako Silafas dinsa na yawon Cikin gida ya fita Har Haraban gidan su Bama na ganinsa suka Mike suka kame hannu kawai ya Daga musu kafin yayi Mgana Tim ya Bude bayan mota ya Dauko mai Kwando shake da food flks,Junaidu ya shiga Bayi shiyasa har ya shiga gida baisan ya fito ba daya tsaida shi da mganarsa.

Tsakiyar Falon ya Dire komai Domin yunwa yake ji kamar zai fadi ya kuma san Tunda Sadiya tace ita ta girka da gaske take yi,Kan kujera ya zauna sai Lokacin yaga inda ya watsar da Wayoyinsa da Ledan kajin jiya da su Mujaheed suka siyamai shaf ya ma manta dasu,Acikin kwando har ta Filet da Cokula akwai kuma Daga ganin su Sabbi ne na Muhibba ne da Niyar basai ta Dawo dasu ba zama ya gyara ya Zuna Doya dafaffiya da miyar kwai yaci sosai ya Kora da kunun gyada yau ko Tea din bai sha ba Saboda ya Samu abunda yafi Tea din dad'i Sai da ya gama ya mike yana gyatsa ya kwashe Wayoyinsa ya nufi Dakinsa domin ya shiga wanka sai alokacin yaji wayar Muhibba cikin aljihunsa bai bukatar Fitowa kuma in dai ya kimtsa Saboda yana da Hutun Sati daya sai Next Monday zai koma Office dinsa yau kuma yana da Lecture ne ta Online bai san adadin Kwanaki nawa yayi baya samun karatu ba sai dai ya bibiyi abunda aka yi musu ta Internet.

Tauttausan Silifas dinsa ya zura ya sake Ficewa shima duka Dakunan sai da ya Bude ya leka bai san inda take ba ammh fa shima ya yaba da yadda duka Tsara komai sai yaga Falon nata yafi na farko nasa ma Tsaruwa da kyau matuka.

Bedroom din karshe ya yi knooking Domin yana da tabbacin tana ciki Ita kuma tana zaune gefen gado ta Zabga Tagumi ga yunwa ga mamaki ga Tunani a yanayin data iske Saifudeen shima ya nuna mata bai Samu tashi kan Lokaci ba in lissafinta yayi daidai dukkansu sun makara kenan tana wannan Tunanin taji knooking gabanta ya fadi ta mike a Sanyaye taje ta Bude kofar duk da bata Rufe ta da key ba.
Chapter 66 · 0% Book details