← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 144

Sashe 128

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tafamin Dr.Anandi ya farayi Saifudden shima ya bi bayansa Kafin ya fara Takowa gabana cikin jin Dadi yace"Congratulation Mrs Lere kin Tsallake mataki na Biyu na Treatment din mu da ke"
Ina jin haka sai na Sauke ajiyar zuciya na Ruga muka Rumgume juna da Saif Cikin Dariya hade da kuka nake fadin"Na kusa warkewa Saif..Na kusa warkewa"
Shima cikin jin dadi yake fadin"Sure Muhi dita ta kusa samun lafiya"
Dr.Anadi har ya koma wajen zamansa yana kallon mu cikin Farinciki yana jinjina Tsananin son da muke yi ma juna.

Kafin ya sallame mu sai da ya kara Rubuta mana wasu mganguna Sannan Saifu ya yi complain din yawan barcina da cin abincin da nake yi sosai Dr.Anandi yace"Is ok..Saboda mgangunar da take sha ne..Ta fara samun ma jikinta da kwakwalwarta hutun samuwar haka ne zai sa treatment din mu ya tafi yadda muke so"
Ya bamu Sati hadu mu Dawo muka Rabu Cikin karramawa.

Mun biya gidan Inna sai dai bamu Dade ba Ya Habibu baya gida yana kassuwa Anty Zeenatu kuma na Gidan su bamu wani Dade ba muka koma Kaduna Tunda yau agida muka bar Wasila ita kadai
Tun da na fara shan Sabbin mgunguna kamar an kara Budemin jiki na gabadaya nake Kiba Daga sama na Har kasa na ni kaina nasan ma fara Sauyawa,Sannan barci na bai Ragu ba,da uban cin abincina Wasila ne da shi suke wahala dani,Sai Adda Sadiya da kusan yawanci Daga gidanta ake kawo abinci itama taji Sauki cikin nata ya zauna sosai,Da Farko Saifiddeen yaso ya nema ma Wasila Leeson Teecher domin yana so ya inganta Rayuwarta da ilimi ammh ganin Halin da nike ciki sai ya Saurara sai na kara samuwa Tukunnah.

Cikin haka ne na cinye Satin hudun da Dr.Anandi ya bamu muka koma asibiti wannan karon ya sakani adakin Duhu an samu nasara na Sarrafa Tsoro na sai dai rawan jiki da Firgita akwai kadan,ba mai yawa ba Dr.Anandi nata jinjina min ya kuma Tabbatar mana kafin wata Shidda zan iya warkewa sai jin Dadi nake yi Saifuddeen kuma ai yafi ni jin Dadi da duka yan"uwana na kusa damu.

Ya sake Rubuta mana Sabbin mganguna muka sake siya,Muka koma gida,ni kaina ina ji ajikina na Fara samun Lafiya kuma kowa ya ganni zai shaida haka Saboda walwalata ya fara Dawo duk da ba Duka ba.

Ina cikin wata na uku da Fara shan mgani da zuwa ziyaran asibiti,Na fara Samuwa sai dai na narka uban Kiba kamar wata Jaka na ninka kibana sau Uku wuyana ya na neman ya Hade da Gangar Jikina mazauna na sun kara girma Har da Timbi,Sannan fata ta ta kara gogewa nayi fresh nayi fari Saboda bana komai sai dai naci na kwanta,Duk wanda ya ganni sai ya kara kallo na yana mamakin Muhibba ce ta koma haka..?

Ni kaina ina jin nauyin jikina Saifudden kuma fadi yake yi"Muhi dina ta zama giwar mata"
Sai na fara mai kukan shagwaba yana zagina ne yanzu ya daina sona saboda nayi kiba sai yayi Dariya ya jawoni jikinsa yana fadin"Har abada bazan Daina sonki ba..Ni Muhibba nake so Autar Inna ba wata ba"
Ni kaina ai nasan yana sona Saboda ba kowani namiji ba me zai zauna dani ya Wahala dani kamar yadda yayi ba.

Harta Sani da ya dawo yazo ya ganni Sai da ya Zabura yana kallona Dariya nayi ina Fadin"Miye haka abun tsoro na zama..?

Sani ya dafe kirji yana Fadin"Uhm..wai sannu Baba..Tab ai ko Inna albarka ke kin ga yadda kika koma kuwa..?

Kamar nayi kuka nace"Mganin da nike sha ne ni kaina kibar ta isheni"
Jin haka yasa yace"Masha Allah ai mganin yana amfani muma son haka"
Kowa haka yake fadi na samu lafiya na samu Hutu.

Ganin haka yasa Saifudden ya Dauko ma Wasila Lesson Teacher Both boko da Islamiya wani mallam Idirs ne matashi ne dan Corpars ne,Shi yake zuwa har gida Daga karfe biyu na rana zuwa Biyar na yammah,Awa Biyu su yi karatun boko awa daya kuma su yi Na addini.

Kafin Lokacin ta gama duka ayyukanta Wasila akwai kokari matuka Shiyasa kyautatawa ba wanda Saifudden ba yayi mata ita da iyayenta.

Zuwa Lokacin ya siyamin Sabuwar waya Samsumg mai Tsada na cigaba da waya da yan'uwa da Dangi kamar bani ba Dole sai dai Welcome back akayi min na layina Domin an je har Gra gidanmu na zaria ba"a ga wayata ba sai kawai Saifudden ya Dauke ni mukaje mukayi welcame back.

Nayi mgana da Uncle Hafiz da su Anty Jidda suna ta fadin suna ta nema na basu samu na sun ji Hankalin su ya kwanta Tunda ina nan lafiya.

Asatin da zamu koma asibiti bamu samu komawa ba Saboda Zazzabi da Ciwon kai da amai ya kwantar dani Litinin din da zamu je Zaria sai ya kaini asibitin Barau dikko aka Dubani aka Dauki jinina Da Fitsarina sai washegari muka koma muka amso Result Ciki gareni na wata Biyu da kwanaki Murna wajen Saifudden kamar zai lasheni nima sai da nayi hawaye ashe zan ga kwai na nima a Duniya,ashe ashe kibar nan har da ciii ajikina Da wannan hasken da nayi ashe Ciki ne Dani Labarin cikina ya kai Zaria da Gaya da Lere Iya ta kira tana ta Murna da saka albarka baki kuwa suna ta zuwa Dubani Saboda Laulayi ya kwantar dani Satin kaf bamu samu komawa asibiti ba Saifidden dai ya shiga makaranta ya biya yayi ma Dr.Anandi bayani shima ya tayamu murna.

Inna ce kadai bata zo ta Dubani ba ammh har ta Lami mahaifiyar wasila su Anty Habiba da zasu zo sun taho da ita,Daga Lere kuma Inna Talatu da Goggo Atika sun zo sun Dubani sai matan kawu dukansu,Daga gidan mu ma Gogo Naja da Inna Firdausi sun zo Bakori dai babani jiki yayi zafi,Ummi dai bata zo ba ammh Mama zuwaira tazo da tawagan su Laala da su Saudar har da Majeeda wannan zuwan naga ta sauya ta Dawo majeedar da na sani ashe gaya suka yi Hutu kwana Biyu suka yi agidana Kwana Daya gidan Adda Daganan Mama zuwaira ta koma ita da Saudat su kuma Daga nan suka koma Abuja.

Sai da muka kara sati biyu Sati Shidda kenan sannan na koma muka kara ganin Dr.Anandi ya sauya min mgani Saboda Cikin jikina yace in na sha mgani mai karfi akwai matsala,Gabadaya yanzu na Daina jin tsoro ko wani firgita na riga na saka ma raina duk abunda ya faru ba Zahiri ba ne.
*Janafty*
*SFD0046*
*Amnaf_sudanese _collection*
*Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401*
*Ki biya ki karanta cikin salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba, kada ki karanta min littafi sannan kada ki yada'min shi don Allah pay N500 via jamila umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*
Sakamakon gabatowar watan Ramadan na wata mai albarka da Falala yasa Saifudeen ya yi tunani Dauko wacce zata taimaka ma Wasila Saboda aikin zai mata yawa ga lesson din ta bazai yuyu ta samu nakasu ta wannan bangaran ba Ni kuma har alokacin ban fara aiki ba bayan Lalurata ga Laulayin ciki ya karu komai naci sai ya Dawo min kwanciyata asibitin kudi na Kaduna har sau biyu ina shan karin Ruwa Saboda jikina ya Saki bani da karfin jiki.

Da ya fara Tuntuba ta da mganar sai ni kuma na kira Ummi na fadamata sai tace min na kira Inna sai a cigiya tamin wata Dattijuwa anan zaria haka kuwa akayi da kaina na Kira nayi mata zencen sai tace min zata bincikamin ta gani kwana uku tsakani ta kirani tace duk wadanda take Tunani sun samu aiki azumi gidan masu kudi na yin koko da kosan Sadaka ammh Ga shawara mai zai hana mu Dauki Lami mahaifiyar Wasila Tunda daga ita sai kannen Wasila yara guda biyu zata iya yin komai Sannan hakan ma taimako ne ta bangaran ita wasilan.

Ban yanke shawara ni kadai ba sai da na Shawarci mijina shi kuma nan take ya amince ya kuma ce hakan ne ya kamata,ba tare da Sanin ita Wasilan ba ana saura Sati daya a fara azumi muka tafi zaria naje naga Dr.Anandi daganan muka Sauka gidan Inna.

Inna ita kanta sai da ta rike baki data ganni fadi take"Auta ke ce kika zama haka..?

Sai naji kunya Daga gani zan yi girman ciki Domin har ya fara nuna kansa balle ga uban kiban da na narka kamar giwa,Bamu jima ba saboda Saifu yace bazamu yi Dare ba ya Sauke ma su Inna kudi masu yawa yace na Hidiman azumi tana ta Godiya Daganan muka je gidan su Wasila Daman already Inna ta mata mgana ko da mukaje ta shirya kayanta sai godiya take yi mana Har da kuka Saifudeen ya kalleta kafin yace"Baba ki daina kuka Hakkina ne..Wasila kamar kanwata na Dauketa..Wahalan da take yi dani da Matata ban isa na iya saka mata ba"
Lami ta Share hawaye da haban zaninta tana fadin"Nagode Nagode..Allah ya saka da alheri Allah ya bama Hajiya Lafiya ya rabata da abunda ke cikinta Lafiya"
Da mirmishi ya amsa da Ameen Ameen Baba,Ni kuma kunya yasa na kasa mgna Gidan Rufesa tayi Saboda Daman karami ne mai ciki da Falo da Ciki daya sai bayi da Tsakar gida da shi ta tsira a gadon mahaifin su wasila ita da ya'yanta.
Chapter 128 · 0% Book details