Sashe 101
Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bai bashi amsa ba cikin gida ya Shiga da Sauri Inna na zaune ta idar da Sallah tana Lazimi Ya Habibu ya Fado Dakin yana Kiran sunanta itama sai da Gabanta ya fadi Cikin wani yanayi ta mike a firgice tana fadin"Habibu lafiya meke faruwa ne..?
Cikin wani yanayi yace"Inna mijin Auta ne yazo yace jiya basu yi barci ba Auta ta Rufe kanta adaki tana ta kuka"
Sai Inna ta Sulale ta koma ta zauna Dabas tana fadin"Innalillahi wa'inna alaihirra"jun."
Ya Habibu ya Duka gaban Inna yana Fadin"Inna ya zamu yi yanzu..?
Kamar an tsikari Inna haka ta mike tana Fadin"Kuje chan gidan Habibu kuga lamarin ni kuma yanzu gidan Maallam Haruna zani na Shaidamai abunda ke faruwa"
Ya Habibu yace"Inna da son samu ne kibimu muje ki gani"
Inna tace"a"a basai naje ba ga Sani nan kuje dashi in Lamarin bai Saukaka ba ka kira yar'uwarku Habiba kaji ko?
Da kai ya amsa mata kafin ya Fice da Sauri Hawayenta ta Share tana Fadin"Ya Allah duk wani Al"amarin daka Lallube kan wannan baiwar taka Allah ka warware mana shi"
Ya Habibu Shashen sa ya koma ya mika mai sunan Baba Anty Zeenatu ganinsa a Firgice tana tambayansa Lafiya Dakyar yace mata Auta ce bata kwana cikin sukuni ba.
Salati ta saka da Sallami tana Fadin"Kuma dai..?kai wannan baiwar Allah tana ganin jarabawa"
Yadda Ya Habibu ya fito hankalin shi tashe haka ya samu Saifudden da Sani Cikin wannan yanayin har suka isa gidan nan ba wanda ya iya ma wani mgana gabadaya kan Saifudden ya kulle ya fara Shinshino wani abu,Ya fara Tunanin abubuwan da suke Faruwa sun Tsallake muhibba in yayi Duba da wanan al'amarin daya faru a Daran jiya.
Har suka isa gidan ba mai umh acikin su har kofar Dakin da Muhibba ke Ciki wasila na zaune tana ta kuka Tana ganin Saifudden ta nufesa tana Fadin"Tana ta kuka Unlce kace Anty ta Daina kuka"
Kanta ya shafa shima kamar ya Fashe da kukan yake ji Cikin Dauriya yace"Ki daina kuka Anty ma zata Daina"
Kai ta gyada mai da kansa ya share mata Hawaye wasila ai tare suka wahala daran jiya,domin Tunda ta Farka bata koma barci ba kamar yadda ya kwana shima bai Runtsa ba.
Ya Habibu ne ya karisa jikin kofar ya fara Knooking yana kiran sunan Muhibba ni kuma Hannayena na saka na toshe kunnenna bata kaunar wani karan Sauti ammh suna jin Yadda muryanta ta Dishe Saboda kuka..
Sani ya shiga tashin Hankali sannan gashi bai san farkon bayanin ba Daga ganin yadda Ya Habibu yayi yasan akwai wani abun da bai sani ba.
Kallon Saifudden yayi wanda ya Harde Hannuwa akirji shima kamar kayi mai kuka yana Fadin"Ranka ya Dade babu Spare key ne?
Saifuddeen yace"Na duba ban gani ba Ina Tunanin suna kaduna.
Kai ya jijjiga kafin ya matsa yana Fadin"Ya Habibu bari nayi mata mgana"
Ba musu ya matsa ya bashi wuri jikin kofar ya saka kansa yana Fadin"Auta..Ki bude kofar nan kin ji..Auta..Autar inna yar gatan Ya Habibu da Anty Habiba yar Gatan Sani..Haba Auta ki bude ki Fadamin waye yayi miki Laifi ko waye sai na Kullesa har igiya tayi Rarara"
Kamar daga Sama naji kamar muryan sani Sakin kunnena nayi na kara kasa kunne kamar muryan sani Rarrafawa nayi zuwa Bakin kofar Dakin bakin na na rawa nace"Saniii.."
Da Sauri yace"Nine Auta Bude kofar nan gani ga Ya Habibu ma"
Ya fada yana Dafasa da Sauri Hannuna na rawa na Murza key din ina Budewa dukkansu suka Shigo Dakin da Sauri ina Daga ido na Hango Saifudden ban san Lokacin da na Fasa wata gigittaciyar kara ba na Fada jikin sani na Makalkalesa ina kuka ina Nuna Saifudeen fadi nake yi"Gata nan ita ce..Wlh itace kasheni zata yi"
Alokacin Yanayin da na gansa jiya kawai nake hasasowa balle Jallabiyan jiya fara ce ajikinsa tashin Hankali baisa ya sauya ba.
Hankalinsu ya tashi shima nashi ya tashi sai ya fara ja da baya cikin Tsoro da Firgici karo na farko da ya fara Gasgata tabbas wani abu na Faruwa Ya Habibu ne ke rike ni yana Fadin"Ke Auta wata mgana kike yi haka..?
Mijin ki ne fa?
Ihu na fasa ina Fadin"Wlh ba mijina bane itace..Itace tazo zata kasheni jiya ku Duba jikina duk ta Cakeni da kumbunanta"
Na fada kamar mahaukaciya ina bude musu jikina ni ina ganin Shatin farcen ammh su basa gani Sani ne yaji kuka yazo mai ya kamani ya kamkame yana fadin"Yallabai ka fita Tunda bata son ganinka don Allah"
Juyawa yayi ina kallonsa kamar zai yi kuka yana fadin"To to zan fita..Na fita shikenan ko..?
Yana fita ya jawo mana kofa bai koma Daki ba haraban gidan ya fita bama na ganinsa ya Bude mota ya shiga kansa ya jinginar saman cussion din Motar gabansa na faduwa Cikin Harshen Turanci Tim ke tambayansa ina zasu je..?
Bakinsa na wani daci da Nauyi yace"Kaduna"
A wannan Lokacin ya Dauki Hanyar Kaduna cikin wannan yanayin,sun isa gidan Mujaheed bakwai ne da wani abu ya same ko Tashi ma basu yi ba gashi bai zo da wayoyinsa ba sai ma da ya zo ya Fahimci a yanayin da ya shigo yana Haraban gidan zaune cikin mota sai ga Mujaheed ya Dawo daga Jogging da matukar mamaki ya ke kallon motar Saifudden da Excort dinsa bai gama mamaki ba sai da Saifudden ya fito daga Cikin motar ya kallesa Daga sama har kasa ai sai ya Nufesa yana Fadin"Saif me ya faru ne..?an yi ankwatsa mutuwa ne..?
Kawai sai yaji Saifudden ya Fado jikinsa Cikin rawan jiki yake fadin"Mujaheed na aikata kuskure ni na ja mata..Ni naja ma muhi..Meyasa nasan matsalata itama ban saketa ba tun farko..?
Meyasa itama ban saketa kamar yadda na saki su majeeda ba..?
Duk ni naja wannan matsalan."
Ya karishe fada cikin wani irin yanayi Hankalin Mujaheed ya yi bala'in tashi da Sauri ya Bude motar Saifudden din ya tusa sa ciki shima ya shiga ya Rufe Motar cikin Rawan jiki da Alhini yace"Kagani gayamin abunda ke faruwa..?
Wani abu ne ya faru da Muhibban..?
Hannayen Mujaheed ya riko ya rufe Fuskarsa dashi yana sakin ajiyar zuciya kawai sai mujaheed yaji Dashin Hawayen saif a Hannunsa da Sauri ya Zare hannayensa yana Fadin"Saif kuka kake yi..?
Kai ya kauda yana Dauke Hawayensa kafin yace"Duk nine silar komai sai yanzu na Fahimci wani abu..Ka aminta dani Mujaheed bansan cewa Har da Muhibba ma zan rika samun yanayin haka tare da ita ba..Da nasan haka zata faru jiya na rantse maka har ga Allah bazan ce zan kusanceta ba"
Mujaheed ransa ya fara baci cikin Tsawa da masifa yace"Haba don Allah..Zaka gayamin abunda ke faruwa ne ko sai naci Ubanka tukunnah"
Saifudden ya kauda kansa sannan ya Fara gayamaa mujaheed duk abunda ya faru daran jiya har zuwa cewar da Muhibba tayi bata son ganinsa da Tahowarsa nan wajensa Mujaheed ya jinjina kai yafi sau goma ya kasa mgana Dakyar yace"Meyasa ka Danganta haka da kanka kuma..?kowa yasan matarka ba ita Kadai bce Kila aljanunta ne basa sonka"
Saifudden yayi shuru bai yi mgana ba Muhajeed ya kara tambayansa kawai sai ya runtse idanuwansa kafin yace"Ni naji ajikina Ba daga muhi bane ne daga ni ne"
Mujaheed yace"To ka fadamin Dalilin ka mana"
Saifudden ya kallesa da Zurmamun Idanuwansa kafin yace"Lokaci zai fada maka komai.."
Kamar ya makesa haka yaji ammh ganin yanayinsa yasa ya sausauta yana Fadin"Bai kamata ka taho ba Saif"
Cikin wani irin murya yace"Ya zan yi Mujaheed tace bata son ganina"
Mujaheed ya kallesa yana Fadin"Dole ka koma fito muje ciki kayi wanka ka karya sai mu tafi gabadayanmu"
Kin fitowa yayi bayan yace ma Mujaheed ya shiga ya fito mujaheed ya Leko yana Fadin"Wlh ko yanayinka kadai ya isa yasa ta Firgita kagan ka kuwa..?kamar wani mahaukaci Sabon kamu"
Ajiyar zuciya ya sauke duk da akwai Sharrin Mujaheed ammh yasan ai baya cikin yanayi mai kyau Cikin gida suka shiga Dakin mujaheed Adda Sadiya na Dakinta bata san Hamma dinta yazo gidan ba har yayi wanka Mujaheed ya basa kayansa riga da wando na shadda mai ruwan kasa ya saka Adda Sadiya na Kitchen ta Dora Ruwan zafi taga mijinta cikin Shirin Fita Cikin mamaki tace"Ina zuwa haka..?
Yana leka abunda take yi yace"Zaria"
Cikin mamaki tace"Zaria kuma..?
Wani abu ne ya faru..?
Kai Tsaye yace mata"Eh muhibba ce bata da Lafiya hada mana ko Tea ne mu sha kafin mu wuce"
Cikin Wani yanayi tace"Mun shige su ba dai Laluranta ne ya tashi ba..?
Kuma kai da waye..?
Yana fita daga kitchen din yace"Saifuddeen Lere"
Ido ta zaro kafin ta biyosa sai ko ga Saif din Tsaye afalo wajensa ta Nufa tana Fadin"Hamma"
Ganin yadda ya Rame kamar bashi ba,Cikin karfin Hali yace"Adda Sadiya"
Kallonta yake yi bai san tana da Ciki ba yasa yace"Ke lafiya cikin ki naga ya kumbura ne"sai taji kunya ta juyaa ta koma Kitchen mujaheed ne yayi Tsaki kafin yace"To don ubanka wake na bata taci tunda kai hamman yan iska ne"
Baya cikin mood din yasa bai tankamai ba sai ya kyalesa Tea kadai suka sha sai buredi da soyayyan kwai Adda Sadiya ma tace zataje mijinta yace ta shirya su tafi sai su dawo tare Dayake Nihad na Gaya Mama zuwaira Daga yaye ta riketa.
A mota hanyar su ta zuwa zaria,Adda ce da mujaheed ke ta jajanta Lamarin ban da Saifudden da yayi Dif Shi kadai yasan Zullimin dayake ciki sai Sha daya na Safe suka isa sun iske gidan Cike sai da Inna tazo ga Anty Habiba ga Mallam Haruna da almajiransa guda Biyu.
Muhibba taki sauraran kowa ashe bayan Tafiyar Saifudden har kwacewa tayi zata fita suka Damkota Da farko tace bazata zo ba da Mallam Haruna yazo yaga yanayin Muhibba din sai yace Inna tazo,Ya Habibu yaje ya Taho da ita Zuwan ta ne ma yasa Muhibban ta Daina Fizge Fizge sai dai kuka An yi mata Rukiya basu yi mgana ba sai dai tayi Ladab jikinta ya saki Sannan sai aka shaka mata wani mganin daya Bugar da ita sai barci.