← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 144

Sashe 1

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Root Entry
WordDocument
0Table
Data
Normal
Default Paragraph Font
Normal Table
No List
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K6EydMUVPIdJ2cJCvx7jHT
*SAIFUDDEEN..!*
_(Ba Mutum ba ne)_
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
_A TRUE LIFE STORY- 50% Fiction_
_*Da sunan Allah mai Rahma mai jinkai Salati tare da Aminci su tabbata ga Annabin Rahma Annabi muhammad salallahu alaihi wassalam tare da iyalansa da Sahabbansa gabadaya*_
*SHIMFID'A...*
Meyasa Inna da Ya Habibu suka ki yarda da ni ne..?Meyasa suke ikarari da cewa SAIFUDDEEN Ba mutum bane..?

Wata zuciya ta bani amsa da cewa"To in Mutum ne a ina yake MUHIBBA..?Rabon ki da ganin Saifuddeen shekaru wajen goma kenan ammh Tunaninsa bai fita daga ranki ba,in kuma mganar su Inna ba gaskiya ba ne meyasa baki kara ganinsa ba..?Baki san komai a kan sa ba..?baki san kowa na shi ba ballatana abunda ya Danganceshi..?Kai ina nima na
fara jin tsoro ko dai ko dai..Saifuddeen da Gaske ba MUTUM BA NE"
Kamar wacce aka biyo haka ta fado cikin bedroom din da Mami take ciki ita da kanwarta Hajiya zuwaira cikin wata irin murya mai cike da kuka ta daga takardan hannunta tana fadin" YA SAKE NI..YA SAKE NI..Yaya Saifuddeen ya sakeni na shiga uku na.

Take fada kafin tayi zaman yan bori saman cafet din daya malale bedroom din, Mami dake saman Darduma tana lazimi ta mike a Firgice gabanta na faduwa Hajiya zuwaira data fara barci sama sama kan wani makeken Royal bed din Dake Dakin sai da ta tashi a Firgice gabadayansu suka yi kan Majeeda suna tambayanta me ya faru..?

Ta kara Daga farar takardan dake hannunta tana fadin"Ya sake ni..yace ya sake ni..!

Sai mami ta Dafe kanta tayi baya kamar zata fadi hannayen kanwarta Zuwaira ya tare ta tana fadin"Yaya zulai ki yi a hankali fa"
Mami ta kalleta kafin tace"Na shiga uku zuwaira YARO zai kasheni kwana na bai kare ba..?Jiya fa aka daura masa aure da Majeeda itama ya sake ta kamar yadda ya saki Amira..?

Anya yaro na da lafiya kuwa..?

Zaliha..!

Ina zalihar take."
Ummi ta Dago Jajayen Idanuwanta ta Sauke kan Adda Sadiya wacce itama ta Kalleta Cikin wani yanayi kafin ta samu Zarafin mgana Ummin ta mike tana Fadin"Ga su chan sun iso..Abunda nake jira ne bari naje na same su"
Mama zuwaira na sallah tana ta umh uhm da gyaran Murya Ummi bata Saurareta ba kafin Adda Sadiya tayi wani yunkuri Ummi ta Fice da Dogon Hijabinta Dauke da Carbi a Hannunta Fuskarta har ta kumbura Saboda kuka.

Sadiya ta Dafe kanta daya fara sara mata,Daman tasan ai hakan zai Faru,Iya bazata yi shuru ba koda kuwa wannan karon Baffa Hashimu bai yi mgana Majeeda wajenta ta girma duk cikin jikokinta tafi sonta kamar yadda Baffa Hashimun yake Dan lele awajenta.

Bata yi kasa a gwiwa ba ta bi bayan Ummi Mama zuwaira kuma sai Allah Allah take ta idar da Salla ta je Falo saboda tasan Yayar nata nachan duke Dangin Uban Saifuddeen suna kare mata Tanadin da suka saba.

Koda Adda Sadiya ta fito Falon karaf Daidai Lokacin da Inna Atika ke nuna Ummi Tana fadin"Karya take yi iya..Wlh ko Rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba Tasan inda Dan iskan yaron nan yake..Tasani ai itace uwarsa sannan in akwai wacce ke zuga Saifuddeen wajen Bijiremana ai itace
Kada ku yarda da Magiyarta da wannan kukan munafuncin data saba Rudar ku dashi."
Ta fada tana jin kamar ta kai ma Ummi Duka wacce ke duke a kasan Saman Cafet din Dake falon inda Iya ke zaune ranta bace tana Faman jijjiga Jiki Baffa Hashimu na gefe ya kasa mgana Baffa Hayatu na zaune kan Hannun Kujeran da Iya ke Zaume Goggo Atika da Daman bata bar komai na Tijaran iya ba,Tana tsaye ta kasa zama tana Faman auna ma Ummi Dake duke tana sharan kwallah gaban Iya harara.

Kafin Sadiya tace wani abu Laala Dasuke leke a Dakin da suke tayi Zaraf ta fito Tana Fadin"Iya mganar gaskiya Ummi fa batasan ina Hamma yake ba..Muma nemansa muke yi."
Tafada idonta kar domin bata da Tsoro.

Ran Iya ya baci ta Dago tana kallonta kafin tayi kyaci Lokaci Daya tana Fadin"Su cin Danko har da su kaza..?

Ke kuma miye naki aciki..?

Da zaki sakomin baki ina mgana.

Kaji min ja"irar yarinya mara kunya.?

Tafada tana kumfar baki ko Tsufanta bata Duba ba,Domin ta tsufa kawai jin Dadi ne ya lullubeta Ammh zata bama Saba"in baya sai dai ganin yanayinta zakasan tun tana matashiyarta ta iya tijara da bala"i.
****
"Shikenan Sunusi naji batunka kuma na amince..Sai dai abu Daya nake so..Wannam auran Saifudden ko yak'i ko ya so bai isa ya tada shi ba..ko wa"adinsa ya wuce sai an kara maida shi..Ko shekara nawa zai yi bai Dawo ba watarana zai zo kuma duk inda yaje ya Dawo Dangin Uwa basu ishesa ba, Dolensa ne mu bashi da yarda zai yi..Hashimu ku tashi mu tafi.."
*****
Goggo Atika ta kurama Saifuddeen ido tana kallonsa kafin tace"Ko dai gaskiya ne kai ma Aljanar ta aureka kamar yadda ta auri musan gidan Alhaji isuhu shekararsa Sitti bai yi aure ba..

Sai iya ta Rude ta fara Salati Tana Fadin"Saifuddeen kardai mganar Atika gaskiya ne..?

Kana da lafiya kuwa..?

Kansa na kasa bai yi mgana ba kadan ya Rage bai yi dariya ba wai Aljanna ta auresa ba bazai manta ba har Ummi tasha tambayansa bai da wannan amsar,amsar kuma da zai gayamusu bai shirya fad'inta ba bazai iya sanar dasu acikin mafarki ne kadai zai iya Saduwa da mace ba, ammh ba"a Zahiri ba mace ko Tsirara zata yi agabansa bazai taba jin komai akanta ba.

Gajiya sukayi da Tambayansu yayi musu shuru yaki mgana Iya ta Fashe da kuka tana Fadin"Allah Sarki muna ta Zargin baiwar Allah Zaliha ashe shi lafiya ce bai da ita..Mun shige su.

Baffa Hashimu yace"Iya to menene mafita..?zamu maida masa da auran majeedan ne yanzu..?

Iya tace"Wani aure Hashimu..?

Ana neman Lafiya ai in muka maida masa ita mun kwareta..Sannan yaron nan yafi mu hankali..Muna ta kokarin yi masa aure bamu taba tambayarsa yanayinsa ba, da sai aure yayi nisa ayi ta samun mtsala..Ai yanzu mganar maida aure ba ta Hashimu sai dai ayi mganar Lafiyarsa kawai.

Baffa Hashimu yayi shuru bai yi mgana ba goggo Atika tace"Tab Iya abun fa ba sauki Domin in suka aureka har Abada mutum bashi ba aure.

Iya ta zaro ido Kafin tace"Uban Aljana tayi kad'an ta auremin jika ta hanashi aure..Bata isa ba"
****
"SAI..FF...UUDEEEN....!

Ta fada kamar mai koyon mgana da Sauri ya Dago ya kalleta sai manyan idanuwansa suka shige cikin na Muhibba nan take gabansa ya yanke ya fadi Ras..Wani yar yabi jikinsa A karo na farko daya taba haduwa da macen da ya kalleta sau daya yaji yanayinsa ya sauya yaji bugawar zuciyarsa na kara gudu da Sauri da Sauri fat.Fat.Fat.

Meke shirin faruwa ne..?

Zanen kaddara ne..Haduwar Allah ne ya Tsarata daga wannan Rana Kaddaran Rayuwar Muhibba zata fara sannan Bayannar Boyayyen al"amarin dake tare da Saifuddeen zai bayyana
****
"Abu daya nake so ka tabbatar min kana sonta..Indai kana Sonta zan nema maka auranta"
Saifudeen yayi shuru ya kasa mgana a mganar kawu bai ji wani sauyi ba ko bakinciki ko Farinciki ba sai dai Tambayar ne tayi mai nauyi har sai da kawu ya kara maimaita mai sannan Cikin kasala yace"Eh zan iya zama da ita."
Kawu yace"Shiririta..Zaka iya zama da ita daman ai sai ana son mutum ake zama dashi..Kada ka damu gobe goben zam shiga zarian mu yi mgana da Innar Habibu
in sun bamu Dama zan Kira Baffaninka mu taru mu nema maka auranta.

Saifudeen yaji kansa ya sara da karfi Cikin karfin Hali yace"Kawu Ummi tace na bar mganar fa"
Kawu yace"Rabu da ita sai komai ya Daidaita zan je na sameta naji Dalilinta.

Daga haka sukayi sallama Saifudeen ya Sauke waya wani abu na basa mamaki Karo na uku zai sake aure sai dai ya sha bambam da sauran Tunda har gashi ana mganar auransa dashi yanayinsa bai Sauya ba,shi dai bai ji K'i ba bai ji So ba acikin Ransa sai dai yana jin Zumudin zai iya zama da Muhibba ba..Zai iya tabbas zai iya Zama da ita.
****
iska ce mai bala"in karfi
ta mamaye Dakin gabadaya Labulan window na kadawa tare da Bugawar glass din Windows din suna Gif Gif kamar zasu cire sannan kofar bedroom din yana Budewa yana Rufewa Bam!bam!

Da kunnuwanta take jin komai ammh kuma Idanuwanta kamar an saka Super glue an danne su ta kasa Budewa,Ballatana jikinta da Hannayenta dataji kamar an saka Dutse mai nauyi an danneta bakinta kuma shima kamar an saka mai zare da Allura an dinke mata ta kasa Bude bakinta ballatana ta iya addu"a Sama sama take jin abun sai ya zama na kamar mafarki a mafarki komai ke Faruwa ba a zahiri ba.

Kamar wasa taji kamar wani abu ya fado saman kirjinta Ya daketa da Mugun karfi kafin kuma taji kamar kafafun mage ne a saman kanta tana Takata tun daga samanta har kasanta Lokaci daya kuma ta sake jin wannan gigitattaciyar Dariya acikin kunnuwanta lokaci daya ba"a daina Takata ba Akan kirjinta koma wani irin Hallita ne yake daka Tsalle yana Fado mata Lokaci daya ana Sakin wata Dariya mara Dadin ji da Saurare tana ji jikinta na Faman rawa Zufa na keto mata ammh kuma ko yatsanta ta kasa motsi dashi kamar almara taji an yi sama da gadon da take
kai yana lilo a sama Lokaci daya iska taji tana kadawa da karfi har tana jin karan Gadon ta da kuma wardrope din Dake dakin Lokaci daya da madubin dake shake da kayan kwalliya Haka take jin karan Haduwar kwalabe suna bada Sauti Gif! gif!

Karan ya Kaure Dakin Tare da Dariyar da bata san daga ina take Fitowa ba sai ya bada wani Sauti na Dabam mara Dadin ji da Saurare
Dum!dum!

Gif!Gif!

Gwaram!Gwaram!

Hif!Hif!
Chapter 1 · 0% Book details