← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 144

Sashe 67

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna Hada ido kamar ko yaushe gabansu ya fadi kuma ya amsa Lokaci daya Muhibba ta janye idanuwanta ta kasa Dagowa bai damu ba, wayarta ya mika mata sai da ta saka Hannu zata karba Zararan yatsunta masu Dauke da jan kunshi suka bayyana ya shagala da Kallonsu bai san ma ta karbi Wayar nata ba sai ta juya zata koma cikin Dakin sannan ya Dawo Hayyacinsa shima juyawa yayi yana Fadin"Ga brekfast chan a falo..!"
Daga haka ya bace ma ganinsa Ita dai bata fita ba wayarta ta damke jin har ta gauraye da kamshin Turaransa Sai da ta bada tazaran minti Talatin sannan ta fita falon yunwa take ji matuka yasa sai da ta ci ta koshi Sannan ta kula da ledar dake Falon ta jawo ta Bude gasashiyar kaza guda Biyu sai youghort da Madaran Holladian mamaki ya kamata wato shi bazai iya bata ba sai dai ya bar shi anan taso itama tayi kamar bata gani ba sai taga bai kamata ba sai kwashesu zuwa Kitchen nan ma sai da ta saka ma Su Inna da albarka Frizer ta Bude ta saka su aciki Kayan basket dim kuma ta sauke su saman kanta din kitchen din tunda akwai waina basu taba tabama,Har Store sai da ta leka kanar tayi kwallah kayan abinci Damkam komai buhu hatta Fulawa Buhu ya Habiba ya siyamata ta Dade a kitchen din Tana gane gane kafin ta fito ta koma Bedroom dinta sai Lokacin ta Dawo natsuwarta ta zauna gefen gado ta Dauki wayarta Inna ta Fara Kira suka gaisa har ta bata su Babani da Inna tace sai gobe zasu koma ammh su Goggo Fa'iza yau zasu koma suna ta shirin su daga Inna sai Ya Habibu ta kira ta gaisheshi ya amsa tare da kara mata Nasiha ta Kira Anty Habiba suna Tare da sani ya karba yana mata Tsiya tana Binsa da Dariya..taso ku su siyama a Turo mata Anty Habiba tace itama gidanta zata koma an juma da yammah..

Ta kira Asma"u da Aisha ta musu ban gajiya da sauran kawayenta har da Anty Jidda da su Usaina Uncle Hafiz ma ta kirasa Saboda Sani ya Fadamata sun je har chan Gaya Sannan ta Turama D.Musa sakon godiya ta Text Masages ishashen kati Ya Habibu ya saka mata Daganan WhatApps ta Bude ta shiga tana ta ganin sakonin Mutane na Fatan alheri kiran Sallar azahar ya tada ita taje ta sake yin wanka ta Dauro alwala tazo tayi sallar Ta sauya kaya zuwa shigar atamfa riga da zani ta kashe Dauri duk da batayi kwalliya ba.

Gajiya tayi da danna waya ta koma gyaran kayanta da aka Chakula mata ya Dauketa har La"asar ta sake Dauro alwala tayi sallarta ta Hada da Nafila sai alokacin ta kira Sadiya ta matabya Hanya tace tun dazu tana gida ita ta Tura mata Layin Sa"adatu ta Kirata sukayi mgana tace mata Suna hanya basu isa ba ai Delta ba kusa ba.

Sai Dare ta samu ta kira Ummi ta tambayi saukar su Mama zuwaira Ummi tace sun sauka Lafiya nan ta kara mata Nasihan hakuri suka rabu Ummi na binsu da Fatan alheri Muhibba bata kara ko jin motsin megidan ba da Daddare kunun Gyadanta ta kara sha yana cikin Flaks bai Huce ba Waina kuma tace da Safe zata Dumama taci abunta kafin ta fara girki.

Kamar abunda ya faru a Daran jiya wannan Daran ma haka ya faru da ita shawaran Anty Habiba tabi na yin wanka sau uku arana ta fito wanka Dauro da alwalanta na sallar isha"i da Shafa"i da wutiri
ita dai ta san ta zauna gefen gado tana kokarin goge jikinta ta sha mai daganan bazata Dora komai ba sai kuma jin kwatankwacin abun da taji jiya da Daddare aka gama wujiga wujiga da ita daganan sai Dif bata kara sanin Inda kanta yake ba sai Tara na Safe ta iya tashi tayi sallar isha"in jiya da Asuba yau abun sai ya fara Damunta kuma yau ma din jikinta sai ciwo yake mata sai da ta shafa man zafi Da Safen ma Sani ya kawo musu abun kari Daga gidan Inna Muhibba ya kira yace ya bama Dagaron mijinta shi ya wuce Muhibba taji ba Dadi da bai shigo ba,Har falon Bama ya kawo kwando ya fita data Duba sai taga Sinasir ne da miya sai kayan Tea da Soyayyan Dankali ita dai bata ji motsin megidan ba ita kadai take Budirinta Ta Dumama Wainar jiya acikin injin Dumama abinci bata san albuzuranci shiyasa ta Lulluba mayafi ta Fita haraban gidan Junaidu taci karo dashi ya Duka har kasa ya gaisheta ta amsa cikin kulawa sannan ta bashi wainar bayan ta hada musu har da Sinasir tace su ci shi da su Bama da bata san sunayen su ba ya amsa yana ta godiya cikin jin Dadi aransa yana alfaharin ogansa ya zama Mutum yanzu kuma ga duk alamu yayi Dace da mace tagari.

Ita dai taci nata ta bar komai a kitchen din ta koma Daki kasa kwanciya tayi saboda tsoron abunda ke Faruwa da ita in ta kwanta azkar dinta ta Dauka ta fara karatunta cikin natsuwa sai da Rana data fita taga an Diba Dankali sannan ga Mug nan an sha Ruwan tea dashi sai tasan eh yana Gidan sannan ya fito Daddare ma Sani ya kawo musu Tuwon shinkafa Miyar Zogale ya shigo ammh ko zama bai yi ba yace mata zai tafi mashin din Abbati ya aro sannan ya Fadamata Ranar Friday zai koma makaranta.

Har shudewar kwana Hudu ana kawo musu abinci Daga gidan Inna sai taga Wahalar tayi yawa ga Sani zai koma makaranta dan sako ma aiki ne sai ta Kira Anty ZEENATU tayi mata godiya tace Wahalan ya isa zata fara girki da kanta Da haka sai ta fara Duba abubuwan da bata dashi ta Samu paper ta Rubuta duk da bai fi sau uku suka Hadu da Saifudden tun kawota gidan ba abunda ke bata mamaki ko masallaci baya fita komai acikin gida yake yi hana Rantsuwa ranar alhamis da Safe taji fitar mota data fita kaima Su junaodu abinci yace shi kadai ne Su Bama sun fita tare da Oga ita bai Dameta ba Ammh tana mamakin bai tsoron yunwa ta kamasa ba baya cin abinci daga Tea sai Dankali in an soya cikin kayan karin su ko Doya ita ko cin kayan take yi ya Ragu ta Dibar ma su Junaidu har su Bama suna yabama Matar Oga domin suna amfana da abincin nan kudinsu na abinci ya fara yi musu rara.

Ranar jumma"a da Daddare ta rasa Yadda zata mai mganar Kayan cefane jiya da Daddare itama Tea din tasha ta kwanta da Safe ma haka kuma ko Buredi babu kazanta na amarci kuwa Tun shekaranjiya ta kara Dafa ta suka cin ye ita dasu Junaidu madaran Holladian kuma tuni ta shanye abunda ko Ruwa fa babu agidan ya kare shima kamar katan Daya ne wanda Su Mujaheed suka shigo dashi Washegarin Bikin.

Ganin ba mafita yana Dakinsa bataji motsin sa yasa ta yanke shawaran Turamai sako ta waya bata da Layinsa sai ta Duba Massages dinta ta Lalubo lambarsa daya taba Tura mata Sako ta Rubutamai kamar haka.

"Ina so zan fara girki ina bukatar Cefane..!"
Haka kawai ta Turamai shiru shuru tana jiran amsar sa to ita Daga ma Lokacin bata kara sanin inda kanta yake ba sai cikin Daran da bata fahimtar abunda ke Faruwa da ita Tunda tazo gidan nan duk Dare sai tayi wannan mafarkin mara kyau tatashi da Safe a makare kuma jiki duk yana ciwo Fuskarta da Goshi ya Kumbura har kuma alokacin Tana ganin kamar abun mafarki ne abu Daya ke Damunta Raunin Ibadarta Bata samun Sallar asuba kan Lokaci Isha'i ma watarana sai da Safe take yi kada a sakama shafa"i da Wuturi aciki Tunda isha"in ma ba yin ta take yi ba watarana sannan bata azkar din kwanciya barci ba alwala ba komai batama sanin barcin ya Dauketa abu kamar almara ta sha saka alarm a wayarta ammh aikin banza ne ya gaji da Kira bata iya ko Daga Hannunta sai fa gari ya Dade da wayewa take tashi wannan al'amarin yasa gabadaya ta Rame daman ga Hidiman biki ga kuma wannan zullumin yasa muhibba duk tayi d'anWuya kuma ta kasa Fadama kowa Tana ganin Laifinta ne da bata azkar din kwamciya yasa wannan al'amarin ke Faruwa da ita.

Haka tatashi suku suku ranta ba dadi sai da tayi wanka tayi sallah Cikinta ya fara kukan yunwa ta Tuna da Sakon data Turamai a daran jiya da Sauri ta jawo Wayarta ta Duba sai ko Taga Sakon sa jiki na rawa ta Bude ga abunda yace..!

"ki rubuta duka abunda kike da Bukata"
Abunda kawai ya Rubuta mata kenan mamaki ya kamata na Halin wannan bawan Allah,Ammh bazatayi fushi ba in shi bai Damu da cikinsa ba ai ita bazata Zauna ta mutu ba ta Zauna ta Dauko paper data Rubuta ta kwafe masa ta text Massages ta aika mai dashi Sai Tura baki take yi ya bata Wahala shi kuma yana kwance ne ma sakon ta ya shigomai sai yau da Safe ma ya gani ya Dade yana tunanin menene Cefane bai sani ba sai da ya Kira Mujaheed ya tambayesa sannan yamai bayanin cefane kayan mahadin kayan Girki Shi ina yasan Hanyar kasuwa Daya ga sakonta bai ko Duba ba yayi ma Bama Forwding yace suje kasuwa su siya komai Atm dinsa na First bank na cikin Mota su dauka suyi amfani Dashi.
Chapter 67 · 0% Book details