← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 130 OF 144

Sashe 130

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai bazan fara ba ma "Dariya na saka shima yana Tayani Cikin Dariyan ne yace"Dole zan rika kiyaye miki watarana in kika Zaune ni ai sai dai Metro zaliha ta haifi wani"
Baki na rike kafin nace"A kunnen Ummi"
Baki ya tabe kafin yace"Da sauri kafin guda ya riga ki yarinya"
Ina sosa kunnensa nace"kasan ai bazan fada ba ne shiyasa"
Kwace kunnensa yayi yana Fadin"Bari ki bari muhi"
Naki ji har ina zura Harshena ina karkadawa Cikin Taushin murya yace"Nace ki bari ko"
Naki bari sai ya daga Murya yana Fadin"Nace ki bari meyasa bakya jin mgana ne Muhi..?.

Yanayin muryansa yasa sai na bari na koma ina kallonsa da haskem Dumlight,Ransa ya baci kadan sai na rumgumesa ina fadin"am sorry"
Shuru yayi ya kyaleni sai da na kara maimaitawa sannan ya sauke Numfashi yace"Muhi baki da lafiya ni kuma mai Tattalin lafiyan ki ne Saboda Rayuwarki da Lafiyar ki suna da matukar Tasiri a rayuwata..ni kaina i Need u ammh Dokar Likita zamu bi shi yace na bari sai cikin ki yayi kwari bana so kina Birkitani kada na kasa Tattala Lafiyarki data Bbynmu am sorry nima nayi miki Tsawa"
Idanuwana suka ciko da Hawaye Daman asibitin da na kwanta ne sukace na samu Bedrest ban da mu'alaman aure sai cikina yayi kwari.

Cikin wata muryan shagwaba na kamkamesa na kasa mgana shi kuma aai yaji Rikon yayi yawa yasa ya karkata Cikin kunnena yana fadin"Menene Muhi..?

Is Antything wrong..?

Cikin Muryan tausayi nace"Thank you for Everthing...inna ta kirani ta fadamin abun alherinka ga Yan"uwana Allah ya faranta maka Allah ya saka maka da alherin Duniya da Lahira"
Yaji dadin addu"ata haka maza suke jin Dadi in matar su ta yi musu addu"an alheri?

Nagani domin haka ya kamkame ni yana shinshinani ta ko"ina yana Fadin"Ni da ke mum zama Daya Muhi..Dangina dangin ki ne..Dangin ki nawa ne so ba godiya Tsakanimu Domin nayi musu wani abu ai ni suka yi ma karamci suka ba ni ke da Lafiyarki Karshe na kusa Haukatar mu da ya" ammh ko a Fuska basu nuna min ba kin zauna dani kin kusa Rasa Hankalnki Saboda ni Wlh in na zauna ina Tuna wahalan da kika sha a kaina Sai naga ko kaina na baki Duka ban Biya ki ba..Muhi ki fadamin wata kasa ki keson zuwa na kai ki..?

Makaranta zaki koma ki cigaba da Karatunki..?

Ko kuma wani abu kike so ma mallaka miki..?

Shuru nayi na kasa mgana to me zan ce komai ai ina da shi ya gama mallakamin ya siyamin sabuwar mota tsohuwar kuma yace tawa ce nasan yadda zan yi da ita sai na bama Yaya Habibu suturu kuwa sai ina Kyautarwa kudi kuwa ban san nawa gareni ba Duk watan duniya albashina na Saifuddeen acadamy bai taba yankewa ba bayan shima Kudin dayake Turamin nan duniya bayan Yardan iyayena na gama samun komai Tunda na samu Saifudeen Da Dangin sa masu kauna na tabbata na gama samun duk wata sa'ar Duniya Ta Lahira kuma indai ta sanadin sa ne nasan bani da Haufi.

Kaina na Bisa kirjinsa nace"Bana bukatar komai kai kadai kanka da Allah ya bani ya gamamin komai"
Yaji dadim mganata ya sakarmin kissa agoshi yana fadin"ya gama min komai dai Muhi ni da ya bani Lu'u lu'u kuma ya Hadamin da zinare mai Tsada ai ni ya kamata nace Allah ya gama bani komai a Duniya saura kuma Lahira"
Ban iya ce masa komai ba na Dago ina kallonsa kafin nace"Just a Kiss plz"
Mirmishi yayi kafin ya Turomin bakinsa yana fadin"Gashi ma ki cinye bakin Muhi dita"
Atare muka tarbi bakin juna cikin Muradi da zamudi mai girma mun Dade muna yamutsa juna Dakyar muka Hakura bayan mun samu natsuwa ya kara kamkameni muka shige Cikin Blanket sai asuba muka tashi yaje masallaci ni kuma nayi a gida bayan ya Dawo mukayi azkar Tare sannan mukayi karatun Qur"ani kafim mu kwanta sai 8 muka tashi ya makara a gurguje muka yi wanka muka shirya muka fita Wasila kadai muka gani tana goge goge afalo ta gaishemu muka amsa mata naja ma Saif kujeran Dining ya zauna yana Fadin"Wasila kina gane Karatun Lesson teacher dinki..?

Da sauri tace"Eh uncle sosai ya iya koyarwa"
Jinjina kai yayi kafin yace"Gud Ki maida Hankali so nake first tearm ki fara zuwa makaranta"
Bakinta yaki Rufuwa tana kokarin Dukawa tayi godiya da Sauri yace"Zan saba miki Wasila me na fada miki..?

Muka hada baki ni da wasila wajen Fadin"Kamar kanwata na Dauke ki babu godiya in dan yaya yayi ma kanwarsa wani abu"
Kallammu yayi yana Mirmishi kafin yace"Allah ya shirya Wasila da Antyn Wasila"
Na amsa mai da Ameen ina kokarin Hada masa tea shi kuma yana Tambayan Wasila Baba Lami tace ta dan kwanta ne Ina zubamai Soyayyar Doya na toshe Hanci ina fadin"Da Baba lami ta sani da manja ta soya Doyar nan"
Hararata yayi kafin yace"Shikenan kuma don kina son manja sai nima na fara ci da shi kenan..?

Bakina na Tura ina Fadin"To da fa".

Kai ya jijjiga kafin yace"Plz ki bani abun karyawa am late Muhi ki bari na isa office na natsa zan yi Lokacinki yarinya"
Ina Dariya na Turamai komai gabansa ni dankwake na saka Saboda Damam Baba Lami tasan da shi na ke karyawa muna breakfast muna Hira sama sama kamar wasa nace"Saifi dina..wai ina D.Musa ne..? allah sarki makarantarmu"
Yana kurban tea bai yi mgana ba sai da ya Dire kofin sannan yace"Ya nan in muka yi mgana sai ya tambayeki..Nauyi yayi mai yawa yanzu To kinsan Sangogina ba komai nake tsayawa na Duba yadda ya kamata ba suma suna kewarki yasha ce min shikenan ki bar koyarwa nace eh mana"
Na marairaice kafin nace"ko zan koma ne..?

Yana goge bakinsa da Tissue yace"Ina zaki koma?

Ina Lomar Danwake nace"Zaria mana"
Mikewa yayi yana fadin"Sai dai ki cigaba ba dai baya ba Muhi..Ki bari na kara zama mai kudi zan bude miki wata makaranta a kusa dake tunda da gaske kike yi Anty Muhibba"
Cikin jin Dadi nace"Da gaske?

Yace"In sha Allahu.."
Dadi ya isheni na tsame hannuna a Filet din danwanke naje Kitchen zan wanke hannu ya Daga Murya yana Fadin"Take care of ur self sai na Dawo"
Bai jirani na fito ba sai tashin Motarsa naji kawai nayi mirmishi murna duk ya Cikani da Daddare ma daya Dawo sai da na kara mai mganar yace"Nace in sha Allahu fa muhi"
Cikin jin Dadi nace"Allah ya baka iko Saif dina"
Ya amsa min da Ameen alokacin ne na Tambayesa a ina yasan D.Musa kai Tsaye yace min"Na koyar dashi yayi Masters dinsa a Abu shima ai B.A Englishi ya karanta D'alibi na ne mai kwazo da Rikon amana da Support dinsa Saifudeen Acadmay ta ginu shi yasa na Dankamai Ragamar komai a Hannunsa"
Ina jinjina kai nace"Gaskiya D.Musa akwai Amana sannan jajirtattace ne"
Har muka kwanta Hirar D.Musa muke yi adaran ranar aka Duba wata kuma aka gani Washegari da azumi aka tashi ni dai ban dani Ciyarwa Saifudeeen yace za"ayi Saboda bani da Lafiya daman kuma Baba Lami zata rika yin Abincin Sadaka za"a rika kai shi masallacin gaba damu Saboda mabukata
Tunda aka fara azumi sai komai ya natsa Domin wata ne na bautar ubangiji da Fatan dacewa,Naso na kwantata azumi ko sau daya ne Saifudeen ya Hanani da na matsa sai ya yi fushi Dani Shiyasa na Hakura ammh ina son Falalar azumin watan Ramadana bana aikin komai sai dai yanke yanke Daga zaune ba abunda bamu dashi ana gobe azumi su bama suka kawo Cefane sai da Store ya cika Wasila da Baba lami aiki ya karun musu abincin sadaka wani mutum ke zuwa yana karba kamar yana Daga cikin kwamitim masallaci,Na ciyarwa na kuma kamar Danye Saifudeen ya ba da shi,kullum aka sha ruwa sai na kira Inna da Ummi nayi musu barka da shan Ruwa haka ma Iya tayi ta sakamin albarka ni ana fadin Rigimar matar ni dai bana gani kaunata take yi Tsakanina da ita sai saka albarka.

Ranar da aka kai azumi goma na rika yima Saif kuka sai da ya barni aka Dauki na sha Daya dani cikin Ikon Allah na kaisa lafiya ina ta jin Dadi na Sha Biyu ma lafiya na kaisa har aka kai na sha Hudu yayi yayi dani na rika Hutawa naki ranar na sha Biyar ban iya kaiwa ba a sibiti na yini na kwana Fadan da Saifuddeen ya yi min ban sa iyakarsa ba yayi a asibiti a gida ma ban Tsira ba Fadi yake yi"baki jin mgana Muhi sai da nace kada ki yi baki da lafiya kika jin mgana ta yanzu look at ur self don Allah..?addinimu mai sauki ne Muhi shi yace in kuna da Lalura ku ciyar da Gajiyayyu sai ku rama in kun samu lafiya"
Ni dai da na san bani da gaskiya ko Uffan ban ce ba Tunda ga Ranar ban kara kwantatan azumi ba sai dai ban yi sanyi wajen Ibadu da karatun Qur"ani ba Tunda bam samu Falalar azumim ba sai na samu na Ibada Tunda aka fara ni da su Baba Lami muke asham agida abun mu shi kuma Saifudden masallaci ya ke zuwa sai wajen tara yake dawowa gida yayi Bude baki.

Tafe tafe kwana nesa sai ga azumi ya fara yi mana bankwana Satin karshe ya Shiga kudin kayan sallar su Laala Da su wasila Adda Sadiya ya bama kudi ta siya ma kowa ciki Hardani kala Biyar Wasila kala uku ita da kannenta da Baba lami su laala ma Haka Ummi ma kala shidda yayi mata har da Inna kala uku sai mutanen Lere suma sha tara na arziki Shadodin maza har da su baba Surajo sun samu da ya Habibu su siyama kuwa suma siyayya yasa aka yi musu sai wanda ya gani nayi godiya kamar zan ari baki daga karshe ma sai ya hau min Fada na daina mai haka baya so Dangina ai Danginsa ne..
Chapter 130 · 0% Book details