← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 144

Sashe 62

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anty Habiba ta ballaamin harara kafin tace"Bansani ba..Bazaki sakani nayo asara ba wlh sai kin sha kaya ne masu kyau da inganci na gwada kuma nagani.(Mai neman karin bayani zai iya Tuntubar wannan lambar 08069179244 Kayan suna da kyau da inganci ku nema ku gwada da izinin Lahi sai kun godemin babu abunda bata saidawa in dai abun da ya shafi gyaran jiki ne da gyara ma megida)
Nasan ni kaina ban isa nace bazan sha ba Sanin Halin Anty Habiba,Anty Zeenatu ta bar ma sallahu tace in ban sha ba ta kirata,ai ban ma yi gaddama ba na fara sha ina Ture turen baki Duka na Hada Saboda Lokaci ya tafi Na Infection Sauri nayi na gama dashi,Sannan na fara shan na gyaran ni kaina wasu gumbar sun min Dadi barin ma na zuma mai Hade da Dabino da ake curesu waje daya a sha da Madara da garin aya da sauran garrinkan basai ma an matsamin ba Saboda ina jin Dadin mganin ba Daci ba Bauri sai naman Zabo ne ke da Dacin mgani da kazar ina ci ina tura baki Ba Halin nace bazan ci ba Anty Zeenatu da Anty Habiba sun sakani gaba
Ban kara zuwa makaranta ba Saboda D.Musa ya turomin sakon sun bani Hutun Sati Biyu har a gama Biki nima sai naji Dadi na samu na natsu waje Daya,Mganar walima da abimci kawaye duk Anty Habiba da su Asma'u ke Tsara komai a makarantar islamiyarmu suka tambayo Walimar Inna ce da wannan aikin Mallam Haruna ta bama Ragamar komai Tun Ranat Tala
ta baki suka fara cika mana gida Mutanen Bakori har da Babani Tana Fama da kanta da duka matan ya'yanta da ya"yansu,Laraba sai ga Goggo Naja da Fatima da sauran mutanen gida su Inna Firdausi ita da su Goggo Barira, sai gobe alhamis zasu taho Aranar mukayi gyaran kai kunshi Daman Anty Zeenatubta iya shashenta na kwana ta Sakamin na Salatif kafin Safe yayi jawur da Safe ni da su Asma'u mukaje bayan gidan mu aka Zanamin Baki da Safe har da su suna ta shirin walima da yammah wanda chan gidan Anty Habiba akayi su Cake abun Rabo Hatta girkin Amaryan chan naji suna mganar zasu yi ni dai ko bakina bana saka musu ta kaina nake yi.

Karfe Hudu aka fara shirin Walima Anty Habiba tasa nayi wanka na Saka Doguwar riga baka cikin lefena da Hijabi milk wanda Inna ta Dinkamin ne Saboda ni na san cewa na amsa sunan Auta Inna tamin kayan fitar Biki kala uki less Daya atamfa Biyu Ya Habibu yamana shadda Mai ruwan kasa gabadayamu har da Inna sannan ya Dinkamin kala hudu Atamfofi masu kyau da mayafi har da Jaka Anty Habiba tamin materila da Dogayen Riguna na yadi na zaman gida Kawar ta Zahrajj ta zo tamin light makeup kafin a gama sai hawaye nake yi tana Dauke min da Tissue sai da Taga bazan daina kukan ba yasa ta bata Fuska tana Fadin"Haba kanwarmu so kike ki bata kwalliyar da Hawaye..!?

Jin haka yasa na Tsagaita kukana ammh in na Tuna gobe zan bar Gidanmu naje wata Sabuwar Rayuwa sai naji komai ya fita kaina Ina Tsakiyar Anty Habiba da Anty zeenatu har gaban mallam Haruna a Harabar makarantar aka shimfida Tabarmu an sha wa"azi mallam Haruna ya bani guzurin addu"o'i wadanda suka fi Lu"lu"un zinare a wajena sai shida saura aka tashi su Fati daman suka je suka taya Anty Habiba aiki su kuma sukayi Rabon su Har da kananun Five alive aka raba lemu.

Mun dawo mnaa kofar gida dan mashin ya Sauke Sani da jakar bayansa da akwatinsa ba san sanda na kwace hannuna cikin na Anty Zeematu ba na nufi sani ba Shima bai ganni ba sai da na Fadomai ina mai Fashewa da kuka sannan ya ganeni ya Dago ni yana kallona cikin mamaki yace"Wow...Wani abu sai aure..Ranki ya Dade!'
Jin haka yasa na Turesa ina fadin"Sai yau..?

Sani na rike hannuna yace"Yau muka gama Test fa..Ai bikin ki nada muhimmanci da Barrister Sani bai da Uzirin badawa.."
Yafada yana Sakalo hannunsa Saman kafadata nima sai ta sakalo munw Tafiya yana Fadin"Wani abun ma sai gobe Dani fa za"a je kai Amarya.!"
Ina jinsa na masa banza ina jan majina sai Dariya ake mana mun bama mutane Dadama sha"awa haka muka shiga cikin gida abokan wasa yan gaya suna ta yi mana Tsiya Sani na Shigar mana har Gaban Inna bamu Saki juna ba Inna ta kallemu ta kara kallanmu kawai sai ta kauda kai tana sharan kwallah Sani ya sakeni ya Nufi Inna yana Fadin"Oh Inna give me a Hug mana..Kinsan yadda nayi missing dinki kuwa..?.

Yadda Inna ta make hannunsa ne ya bama mutanen Dakin Dariya har dani ganin haka yasa ya nufi Babani ya Rumgumeta yana Fadin"matar Lauya ashe rai nan nan dai..?

Keyarsa ta make tana fadin"Kaniyarka..!

Sai Dariya yake yi nima ganinsa sai ya Sani Nishadi matuka,nan na bar su Asma'u na koma Dakin Sani muna ta Hira sai bani Labarin makaranta yake yi nan yake fadamin Abbati ya Turomai 5k ya ce ya bani gudumuwa sai naji Tsausayinsa cikin jimami nace"Allah Sarki nagode"
Sani yace"Ba wani Allah Sarki..Kin gujesa zaki zo kina wani nuna mana Allah ne bai yi ba.."
Baki na Tabe kafin ma mika hannu ina Fadin"Naji bani kudin daya baka yace ka bani..!?

Sani ya kalleni yana zaune ya gama cin abinci Ruwa ya sha yayi gyatsa kafin Yace"Kin cika azarbabi ni fa da nayi Tunani na cika na siya miki water Dispenser kin san gidan manyan mutanen nan ruwa a Fridge bai cika Burgesu ba sun fi gane su Tsaya su zura kofi su sha su wuce."
Muhibba tace"Ya Habibu ya siyamin."
Sani yace"Au to..Bari bayan Bikin nayi Tunanin wani abun da zan siya miki."
Yafada yana Hade rai sai ya bani Dariya sai da na Murmusa Sani bazai Sauya ba ajininsa yake,sai da naga zai sauya kaya na bar mai Dakin na koma Shashen Anty Zeenatu nan ma ya cika da mutane Ya Habibu tun kwana Biyu baya kwana ma agidan sai dai ya shigo da Safe da Daddare.

Gidan su Anty Zeenatu muka kwana Ni da su Aisha washegari tun Safe suka tafi gidan Anty Habiba zasu yi girki har da su Nusaiba da suka zo sukace suma zaje nace,sai sun dawo suna tafiya ni kuma
gida na Dawo na Shige Dakin Inna na kwanta a bayanta ina Hawaye Babani ta Fara Fadan na cika Sakarci Goggo Fa'iza tace"Ayi mata Hakuri babani Auta ce fa.."
Ita kanta Inna jikinta duk a sanyaye ina Dakin su Ya Habibu suka shigo sallama wajen karfe Tara na safe ya sha Farar shadda har da Babban riga shi da Sani,Sani sai iyayi yake yana ta Fama da Hankcif yana goge Rufaffan Takalminsa Muhibba na kuka sai da Tayi Dariya gira ya Daga mata yana Fadin"Yarinya taga wanka..!"
Muhibba sai hawaye ganin haka yasa ya fice yana Fadin"Mu dai mun tafi kada Tawagan Kwamishina su rigamu isa..!"
Aka bisa da Dariya sallama ya Habibu
yayi ma su Inna suka bisu da Fatan isa Lafiya da dawowa Lafiya Mota Biyu ce Siyana Ya Habibu ya Dau tasha da abokansa da yan anguwa mutanen arziki bawan Allah Abbati har da shi azuwa tara da Mintoci suka Dauki Hanyar Gaya Sani da Abbati motar Abban Walid suka shiga shi da su khalifa da Walid acikin gida kuma ana ta Binsu da Fatan isa lafiya cikin Salama.
*Janafty*
*SFD0023*
*Amnaf_sudanese _collection*
*Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401*
*Ki biya ki karanta cikin salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba, kada ki karanta min littafi sannan kada ki yada'min shi don Allah pay N500 via jamila umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*
*GAYA..*!

Sun isa Gaya da misalin sha d'aya da mintina na safe dayake basu yi gudu sosai ba saboda fadan su Inna da Babani kan su bi a sannu banda gudun ganganci ko da suka isa kofar baban gidan su na Gaya cike da al'umma Tunda daurin auran shad'aya da rabi na Safe ne har da Uncle Hafiz da wasu malaman su muhibba su biyu har da D.Musa yazo shima da Uncle James suka iske su achan har sun isa tunda akwai Address din wajen Daurin auran a jikin katin.

Tawagan ango bata iso ba ammh Baba Sunusi da tawagan sa suna wajen sannan su baba Surajo sun sha wanka da Fararan Shadodi da manyan Riguna wanda ya habibu ya Dinka musu da Huluna sun yi shar dasu bakin su kamar gonar auduga Haka bangaran Waliyan ango su Baffa Hashimu da Tawagan su Daga Lere Har da Hakimin lere acikin su Mota wajen Hudu suka ciko Tun goma da Rabi suna garin Gaya sai Hada hada ake yi gwanin ban sha"awa.

Acikin gidan kawu kuwa na cike da Mata ana ta Biki Ummi Tun shekaran jiya ta iso ita da su Laala Jiya kuma abokiyar aikinta Maman Nana ta iso taji Dadin wannan karan har da yan'uwan su Laala daga Suleja sun zo mata Biki Ummi sai Faman kai da kawo take ita da Mama zuwaira sun sha adon su cikin Leshi mai kyau suna ta walwali.

Sadiya ma tana garin tun jiya ta iso itama sai kai da kawo suke yi Tunda sun yi gayya taron Biki suke yi bani da Biki ba gida cike da yan"uwa da abokan arzuka har da Sauran dangin su na Bungudu sun zo wannan karon abinci kala kala sai wanda ka zaba.
Chapter 62 · 0% Book details