← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 144

Sashe 45

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mujaheed sun shiga kaduna kenan Saifudden ya kirasa yana tambayansa sun shigo kaduna ne..?Ya amsa mai a Dakile,Sai yace ya bashi address din inda yake,Bama zai zo ya kai Ummi Abuja shi ya shiga Office bai yi musu ba ya Turamai suna masallacin Sultan bello ba jimawa Bama yazo da Motar Saifudden din sukayi sallama da Ummi Ta shiga suka tafi su kuma suka Nufi gida ya Sauke Sadiya, ya wuce wajen aiki yana da Unform achan in yaje in bukatar hakan tataso sai ya Sauya.
******
Tun bayan abunda ya faru Muhibba sai dai ta shafe satin nan ko kofar gida bata leka ba,Ballatana mganar zuwa makaranta aka kuma ci sa"a Inna batace mata komai ba ita da Ya Habibu ganin yanayinta na tayi sanyi sosai yasa basu matsa mata ba,Suna waya da Ummi sosai saboda ta karbi Lambarta kafin su tafi Ita da Adda Sadiya suna kiranta su ji lafiyarta.
ranar jumma"a da Ummi ta kirata bayan sun gama gaisa ne tace"Diyata ina fatan kin warware kin koma bakin aikin ko..?.

Cikin sanyin Murya Muhibba tace"Ai ban koma ba Ummi..."
Cikin mamaki Ummi tace"Saboda Mene D'iyata..?

Muhibba tace"Bakomai Ummi.

Ummi tace"A"a zaman ai ba Dadi ki shirya Ranar Monday ki koma bakin aikin kin ji..?

Muhibba ta amsa ta mata basu Rabu sai da taga ta saki Ranta sannan Da Ta fadama Inna itama taa bata goyon bayan komawa Tunda abun ya fada ko masu yada sharrin sun daina kuma Labarin yadaina Tredding kamar baya,Sannan wanda akayi domin shi bai Damu ba shi dayake ma social Media bata Damesa ba sannan Da Rubutun da su Mujaheed sukayi ya Taimaka wajen lafar da al"amarin.

Ya Habibu daya dawo Inna ta Fadamai Shima yace ta koma Daman ya bari ta samu natsuwa ne Sani ko cewa yayi bai kamata ta koma ba,domin har yanzu bai ga alamun Saifudden ya Saduda ba yana wani cin mgani Sai da Inna ta bishi da Dakuwa sannan yayi shuru ita dai Muhibba duka a Tsorace take da Fargaba Ranar Litini da Safe Haka tatashi wani suku suku da ita tayi wanka Ko Tea din da Inna ta Hadamata kadan tasha ganin yanayinta yasa Inna ta saka Sani tace ya rakata.

Har sun fito tana rike da Jakarta ta saka Wani less da Hijabi dogo Sai Littafin lesson note dinta dake Hannunta,Ganin yanayinta yasa Inna ta Dafa kafadarta Tana fadin"Ki saki jikin ki Auta insha Allahu ba wata matsala komai ya wuce..kai ta gyada ma Inna Sani na gefe yace"Inna ni fa nagaji da tsayuwa ga barci a idona"
Inna ta hararesa kafin tace"Kai ai daman baka gajiya da barci..Kuje Auta Allah ya Tsare ya bada sa"a."
Haka suka fita ita da Sani,Shi kanshi ya fara tsokanarta ganin yanayinta yasa ya koma Lallashinta yana Fadin"Matsala fa in ta Tunkaromu Yakar ta fa muke yi muhibba..Allah shi ya tsara miki haka mu bamu isa mu kauce miki wannan kaddarar ba ki yi Fatam kin rabu da wannan matsalan kenan shi kuma wannan abun da ya Faru ki sakashi a bangaran Sabani ne,Shi wannan SAIFUDEEN din ki saka aranki ba ki sanshi ba kuma wanda kika sani a da ba shine wanda kika sani yanzu ba ki saka ranki ba Mutum bane sabani ne da Kaddaran Ubangiji ya Hadaku yanzu kuma ya Rabaku in kika saka haka aranki Lami lafiya zaki ga kin cigaba da Zama ayadda kike."
Tabbas mganar sani gaskiya ne sai ma da ya kara da ce mata"Kinga ni wannan Saifudden din ba ajin Rayuwar mu bane Muhibba Mai kudi ne sannan mai mukami ne kinga kuwa baki da wata alaqa dashi kada ki bari Wasi wasi da damuwa su rika Dangantaki dashi in wannan Sabani aka samu abunda zai faru agaba to ganganci ne Muhibba.."
Gabadaya kalamansa sun shigeta sannan sun gama kashe mata jiki kuma gaakiya ya fadamata Hawayenta ta share kafin tace"Insha Allahi zan cire komai araina Nagode matuka..

Sani yace"A madadin godiyar albashinki na wannan watan ki rantamin don Allah."
Hararansa tayi kafin tace"komai ba don Allah kake yi ba.

Sani yace"Kaji sharri aikin nawa Allah na taba miki..?

Wannan ma rakakin da zan yi ai shima Jihadi ne."
Sai ga Muhibba na Dariya daman Burinsa ya sakata farinciki kuma tayi har suka samu abun hawa suna ta hira abunsu har kofar makarantar su Muhibba duk da gabanta na Fadi haka ta Danne Ta Dauka sani zai koma ne sai taga ya Biyota cikin mamaki tace"Ina zuwa..?

Cikin basarwa yace"Ke nima shiga zan yi na gwada sa"a ko zasu Dauke ne koda Temporary ne.."
Muhibba tayi dariya kafin tace"Lauya da kansa da yace yafi karfin Teaching.

Sani yace"Ai na kare yawa ne..kafin na gama karatu na zama lauya mai zaman kansa Barrister Muhammad Sani Bellomairago."
Ya fada har yana sauya Tafiya Muhibba sai Dariya take yi haka suka jera Sani na gwada mata yadda zai koma da tafiya in ya zama cikakken Lauya,office din head teacher suka fara zuwa Uncle Hafiz na ciki shi da Anty Usaina da Anty Debora,Uncle Hafiz bakinsa yaki Rufuwa dayaga Muhibba cikin farimciki yace"Laala..Anty Sai yau..?

Mirmishi kawai tayi batace komai sani ya bashi hannu suka gaisa Muhibba ta gaida Head teacher suka gaisa da Anty Debora Anty Usaina kuma Dakyar ta amsa bakinciki ya cika ta domin ita da khadija sun gama Murnan Muhubba ta bar makaranta sai gashi ta dawo.

Uncle Hafiz ya kalli Sani yana Fadin"Yayanmu kai ne dan rakiya yau kenan..?

Sani yace"To ya na iya..?ina fa barcina Inna ta tasoni wai nazo na raka Auta makaranta don Allah ita yarinya ce..?ai wanda agidansu basu da Auta ya samu Freedom wanda kuma suke da Auta irin yarinyar nan sunan mutum Sorry"
Yafada yana nuna ta da baki Hararansa Tayi da sauri yace"Daga fadin gaskiya..?Allah baki hakuri Anty.!"
Yadda ya fadi Antyn ne harta Headteacher sai da tayi Dariya bai jima ba yace ma Muhibba zai tafi har da bata 200 da taki karba yace"Ke karbi abunki yar nan..Mu samu kudi haka muke hannayenmu a bude suke".

Karba tayi tana fadin"Hakane fa Alaji Sani."
Sani ya fice daga Office din yana Fadin"Ban cika son godiya ba in nayi ma mutum alheri."
Sai dariya Su Uncle Hafiz suke shi da Head techer wacce sai da tace"Wannan yayan naki dan chapter ne."
Muhibba tayi dariya batace komai ba,Lesson note dinta ta bata sannan ta Cike Attedencens ,Head teacher ba ta bata izinin tafiya aji ba sai da ta Kira D.Musa daman yakan kira yaji ko Muhibba tazo makaranta to tana Fadamai yace ta Tura masa ita.

Muhibba gabanta sai da ya fadi ammh haka ta Daure taje office din D.Musa Sakatariyarsa tasan da zuwanta kai tsaye ta shiga..

Cikin girmmawa ta gaisheshi ya amsa yana Kallonta Cikin mamaki yace"Meyasa satin chan baki zo makaranta ba..?

Kan Muhibba na kasa tace"Bakomai.

Bai mata mgana ba yadai Dauki wayarsa yayi kira har sau biyi ba"a Daauka ba sai ana uku Yadda yake Ladabi da Muryan girma a muryan D.Musa tasan da wani babba ne sai dai Tunaninta ya katse ne sanda taji yana Fadin"Muhibba ce ta dawo aiki yallabai..Ba wata matsala ta cigaba da aikinta..?

Da Sauri ta Dago Tana kallon D.Musa Cikin mamaki nan da nan kwakwalwarta ta hasko mata da wanda yake mgana gabanta ya yanke ya fadi to in yace ya koreta fa.?
bata da ta cewa tunda makarantarsa ce shi ya Dauketa yana da ikon da zai sallamata sai tsoro ya shigeta ta sunkuyar da kanta tana jiran abunda D.Musa zai fadamata tunda har alokacin bai gama wayar ba.
*Janafty*
*SFD0016*
*Ki biya ki karanta cikin salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba, kada ki karanta min littafi sannan kada ki yada'min shi don Allah pay N500 via jamila umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*
*Amnaf_sudanese _collection*
*Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401*
SAIFUDEEN daga chan bangaran da ya ke zaune acikin kayattacen Office dinsa ya matse kansa cikin suit bakake,aiki yake yi sanda Musa yayi ta kiransa dayake basu saba mgana ta waya ba sai dai ya turomin sako shi kuma in ya samu lokaci sai ya bashi amsa ammh ganin kiransa akai akai yasa ya zargi ko ba lafiya ne shiyasa sai ya daga kiran.

Mamaki bai barsa ba sai da ya ambaci Muhibba da farko bai gane ko wacece ba shiyasa cikin muryansa mai Sanyi da Haiba yace"Wata yarinya kenan..?

Sai da ya fadi haka ne sai kuma Idanuwansa da kwakwalwarsa suka Hasko masa ko wacece.

MUHIBBA..!

Da sauri yace"Meyasa zaka tambayeni akan ta cigaba da aiki ko A"a. ?

Ina da matsala da hakan ne..?

D.musa ya rude ya fara mgana cikin rawan baki yana fadin"Sir..".

Katsesa yayi da sauri cikin dan Fusata Lokaci daya yana Fadin"Meye tsakanina da ita da zan koreta Daga aikinta da har zaka kirani kana neman ta bakina..?

D.musa kansa na kasa kamar yana gabansa yace"Naga kamar kun samu Sabani ne."
Saifudden yace"Mun samu sabani kace to ka bar shi a sabanin mana Musa..?Bani da wata alaqa da wannan yarinyar ka barta ta cigaba da aikinta ba ruwana aciki abunda kuma ya faru kamar yadda kace Sabani ne to ka barshi ahakan."
D.Musa cikin Ladabi da girmamawa yake fadin"Sir am sorry..!"
Bai Sauraresa ba ya datse Kiran D.Musa ya dago yana kallon Muhibba da kanta ke kasa tana wasa da gefen Hijabinta Sama sama take jin mganar Saifudeen ta cikin waya,Sai dai yanayin D.Musa kamar fada ake yi mai daga yadda yake faman Ladabi da Sadda kai.
Chapter 45 · 0% Book details