← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 144

Sashe 123

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ido na sakamai ina kallon sa nima shi yake kallo yana nazarin yadda na karbi mganar kamar kar ya ambaci kalmar Tsoro sai jikina ya fara rawa ido na yayi kwal kwal kamar zan yi kuka da Sauri yace"Just Feel Free ki gayamin wani tsoro kike ji..?

Ya yanayin tsoron ki in ya kama ki..?

Fiki fiki na fara da ido kafin nace"Ina jin Tsoro..Bana son a barni ni kadai sai naga kamar zan sake ganinta ne'
Kai tsaye yace"Ita wa..?

Kawai sai hawaye cikin Raunin murya nace"Wata ce..Wata wacce ke son kasheni"
Kansa ya maida yana Rubutu kafin ya Dago yana Fadin"Har yanzu ki na ganinta..?

Na girgizamai kai alamun a"a sai yace"A ina kike Tunanin ganinta?

Sai nayi shuru na kasa mgana bai jira amsa ta ba ya cigaba da Fadin"Zaki iya kwatatamin Suffarta..?

Ido na kwalalo kafin nayi mgana ya Rigani da Fadin"In nace gata nan yanzu a bayanki zaki yarda dani..?

Ai ina jin haka na Zabura na mike sai gani a gabansa jikina ba inda ba ya rawa shima mikewa yayi yana kallo kafin yace"Ki juya bayan ki, ki ganta"
Sai na kasa juyawa na Fashe da kuka ina Fadin"Bazan iya ba..Zata kashe ni"
Kai Tsaye yace"Ki juya babu abunda zata yi miki"
Haka ya rika matsamin akan sai na juya ba inda jikina baya rawa da kayarma ina kuka hawaye share share harda majina Ina juyawa sai ban ga kowa ba sai mu biyu a office din sai na fara waige waige cikin Firgici ina Fadin"Ban gan..ta ba.."
Komawa yayi ya zauna yana fadin"Bayan ita me kike jin tsoro?

Kai tsaye nace mai"Bana son Duhu..Duhu na bani tsoro"
Hannu ya nuna min yana Fadin"Koma ki zauna"
Ina sharan Hawaye na na koma na zauna ina ta faman rawan jiki Ya Dade ya na Rubutu kafin ya Dago yana Fadin"Ki amince abunda kike gani ba zahiri ba ne..?

Da kai na amsa mai sai ya jinjina kai yana fadin"Duk inda kika Samu kanki ki Dauka ba wani abunda zai iya cutar da ke..Wannan matar da kike gani mafarki ne ba Zahiri ba ne"
Da Sauri nace"Ina ganinta fa Likita"
Kai tsayen shima yace"Bazaki kara ganinta ba..Ammh sai kin bari Tunaninki ya Dauki mganata..Bata a Zahiri mafarki ne kina jina ko..?

Na amsa mai da toh ya cigaba da Fadin"Kada ki kara tsorata..Ko da kin ji tsoro ki sani ba zahiri ba ne Mafarki ne shi kuma mafarki ai ba gaskiya ba ne ko..?

Nan ma da toh na amsa mai ina jin Tsoro na yana Raguwa mikewa yayi yana Fadin"Ki hau gado nan zan gwada kanki yanzu"
Ba musu na mike na hau wani karamin gado yazo ya saka kaina cikin wani karfe sai gashi hoton kwakwalwata ya fito cikin Na'urar dake gabansa ya Dade yana Dubani kafin yace na sauka.

Komawa nayi na zauna Tsuru shi kuma yana ta Rubuce rubuce sai chan ya gama ya Rufe Fayel din ya Dago yana kallona kafin yace"Mrs Lere na gama ganinki na yau..Sai nan da Sati Biyu zaki dawo zan saki acikin Dakin Duhu domin na auna yanayin Tsoron ki ammh kafin nan zamu Doraki kan mgauguna da Traatment na wata Shidda In sha Allahu you will be ok kafin Lokacin"
Cikin jin dadi nace"In sha Allahu Dr..Thank you very much"
Jinjina min kai yayi kafin ya Dauki wayarsa ya kira kawai cewa yayi"Dr.Lere u can come in..'"
Ba dadewa sai ga Saifudden ya shigo ni ya fara kallo yana nazarin yanayina Nima shi na ke kallo nufoni yayi yana Fadin"Dr.Me kayi mata naga kamar tayi kuka..?

Dariya kawai yayi bai yi mgana ba bayanin da yayi min yayi masa ya karishe da Fadin"Yanzu zata iya karban Treatment din mu..Zan dora ta kan mgani da ganin Likita after 4weeks,Kwakwalwarta normal ne..kawai dai tsoro ne da Firgici suka Birkitata,kada ka damu she will be ok"
Saifudden ya jinjina kai alamun gansuwa Takardan mganin daya Rubuta ya basa yana fadin"Ta shanye su kafin 2week din da na dibar muku ku dawo ok"
Saifuddeen ya basa hannu suka gaisa yana Fadin"Thank you so much Doctor"
Yana mirmishi yace"Stay blessed Dr."
Hannuna ya rike zamu fice Daga office din Dr.Anandi yace"Mrs Lere Bye see u in d next 2 weeks"
Yake nayi mai har muka fita daga Office din bamu bar asibitim ba sai da ya siyo magungunar guda hudu ne ammh suna da Tsada sosai mun baro Chika mun fara Tafiya na kallesa ina Fadin"Saif mu je gidan Inna don Allah"
Kai Tsaye yace"Kina son zuwa ne..?

Kai tsaye nace mai"Eh nayi kewarta ne."
Dariya yayi kafin yace"Ni wato baki kewata ba ko..?

Ina cunno baki gaba nace"Kai ai kullum muna tare a gida"
Kai ya gyada Hankalinsa na wajen Tuki yace"Daman ina da niyar kai ki ki ga Inna..Shi yasa na so ki bari mu Tahobda wasila kikace mu kaita gidan Adda"
Ina girgiza kai na nace"Sorry kasan ba ni da Hankali sosai"
Daure Fuska yayi kafin yace"in ji wa yace baki da Hankali Muhi..?

Sai ido na ya ciko da Hawaye cikin Raunin Murya nace"Eh mana ni na sanii..In ina da shi meyasan zan rika ganin Likitan shashen masu tabin hankali"
Sai ya kasa bani amsa hankalinsa na wajen Tuki na wani Lokaci zuciyarsa duk ta kuntata duk fa adalilin sa ne na kamu da wannan laluran yana jin girman Gulty din nan acikin ransa.

Ganin yadda yanayin sa ya sauya ne yasa na rike hannunsa guda daya dake saman sitiyari ina Fadin"Saif am sorry"
Mirmishin yake yi yayi min kafin ya kalleni yana rike hannuna Lokaci daya yana fadin"Is ok..Gayamin me kuka Tattauna da Likita?

Kai Tsaye nace"Kawai tambayoyi ya Dinga yimin"
Nan na shiga bashi Labarin irin tambayoyim da ya rika yimin na karishe da fadin"Kaji har yana tambayana ina da aure..?

Ina da ya"ya..?.

Bai san ai ban gama zarewa gabadaya ba"
Dukkammu sai muka kyalkyalce da Dariya cikin Dariyan ne yace"Muhi na bata zare ba tasan abunda take yi"
Daganan muka cigaba da Hira har muka iso gida yana tsayawa da Motar Cikin zumudi na Fice da murnata Tun daga zaure nake kwalama Inna kira bata Tsakar gida tana Dakinta ta idar da Sallar walha kusan cin karo muka yi a bakin kofa tana ganina ta Bude ido Tana fadin"Auta.."
Sai na Fada jikinta ina Fadin"Na"am Inna"
Inna ta rikeni tana Dariya sai gyaran Muryan Saifudden muka ji a kammu Inna tayi Saurin Sakina tana Fadin"Ashe tare kuke shi ne Auta ta shigo tana wannan sangartan tata"
Kansa na kasa yana rike da Jakata yace"Daga asibiti muke Inna"
Inna na Fadin"Toto..To ku shigo mana Saifu ka tsaya daga waje"
Ciki muka shiga Inna ta shimfida mai Darduma ni kuma na Haye gadonta ina Fadin"Ina nayi kewarki nayi kewar gadon ki..Shine baki taba zuwa kin ganni ba"
Na fada kamar zan yi kuka Inna tayi mirmishi kafin tace"Me zan je in yi Auta..?

Ke ai yar Dangi ce Kowa yaje ganinki kuma ai muna mgana ta waya ko?

Baki na tura ban yi mgana ba Inna tayi Dariya suka gaisa da saifudden yace mata daga asibiti muke Inna tace"eh jiya Da daddare da Habibu ya shigo ya fadamin kun yi mgana yau Auta zata fara ganin likita..Uban giji Allah ya Datar damu"
Saifudden yace"Ameen Inna an Dorata kan mgani sannan yace nan da Sati biyu ta shanye mganin mu dawo"
Inna tace"Alhamdulillah Allah yayi jagoranci Allah yasa a dace da abunda ake nema ayi ta Hakuri Saifu Allah ya bada Ladan jinya da zumunci mungode da wahala da ake ta yi da Auta Allah yasa a mizani"
Saifudden kansa na kasa yace"Haba Inna bakomai ni ne ma zan yi godiya Domin duk sanadina ne Muhibba ta gamu da wannan laluran"
Inna tace"Kul kada na kara jin makamanciyar wannan mganar a bakin ka..Ba kai ka Dora mata ba Ciwo ai jarabawa ne ko da Sanadinka ko babu auta sai ta Hadu da Jarabawarta mu zama masu iklasi da Tauhidi"
Saifudden ya jinjina kai yana Fadin"Hakane Inna Allah ya kara girma"
Ta amsa da Ameen aikinsa ta Tambayensa da su Ummi yace kowa Lafiya Sai suka yi shuru ni kuwa na Lafe a gadom Inna barci na neman Daukeni Saifudden ne yace"Ya Habibu baya nan ne Inna..?

Inna tace"aiko tafiya ta kamasa zuwa kano wani abokin su mahaifiyarsa ta rasu jiya da Daddare"
Saifudden yace"Allah ya jikanta da Da Rahma"
Inna ta amsa da Ameen cewar da yayi zai shiga cikin Abu zai bar ni anan sai in ya Dawo sai Inna ta fita ta bamu waje gefena ya kariso ya zauna yana kiran sunana na amsa barci a cikin idona Cikin So da kauna yace"Zan shiga cikin makaranta
Sai na dawo"
Ina Daga kwancen nace"Kada ka Dade kaji Saif dina"
Cikin mirmishi ya sunkuya yayi min kiss a goshi kafin yace"Bazan dade ba Muhi di ta"
Daganan ya fice Daga tsakar gida yayi ma Inna sallama ya fice Mganguna na, suna mota dayake Safe da Dare ne Tunda Safe ya wuce sai Dare kena zan fara sha.

Nasha barci sai azahar na tashi nayi sallah na iske Anty Zeenatu tayi Danwake nan tazo Dakin Inna ina ci muna Taba Hira sama sama Daga ita har Inna dadi kamar ya Kashe su ganin yadda nayi kiba nayi bulbul dani Duk da ban Dawo daidai ba ammh kuma Tabbas Lafiya ta fara samuwa.

Musha Hira da inna duk da rabin Hirar duk itace ni dai sai dai Dariya sai mirmishi wani mganar in nayi kamar mai hankali wata kuma in nayi sai a hankali.

Ina nan Ya Habibu ya Dawo shima yaji Dadin ganina ahaka a fili ya Furta"Masha Allah Auta ta fara samuwa"
Dariya kawai nayi ban yi mgana ba Sai bayan La"asar Saifudden ya Dawo ban jima ba nayi ma su Inna Sallama muka mika Hanya gidan Adda muka fara isa muka Dauki Wasila nan muka yi mangariba da Isha"i sai tara muka koma gida bayan mun take cikin mu da abinci muma komawa gida ya ballamin mgaunguna na sha shi ma yayi min shirin kwanciya domin gabadaya gabbaina sun mutu ko Hannuna bana iya Dagawa.
Chapter 123 · 0% Book details