← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 144

Sashe 13

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sadiya tace"Na cewar da sukayi kila Aljanace ta auresa..Na fara yarda dasu ace Hamma na neman 36 ashekaru ammh bai jiye iyali ba sannan in an aura masa sai ya saki a washegarin bikin anya..?

Mujaheed yayi dariya kafin ya Sagalo Hannunsa saman kafadanta yana Fadin"Ni ai nafi ma Tunanin shine Aljanin..!

Sadiya ta zaro ido kafin tace"Shi wa..?

Mujaheed na Dariyan yanayin ta yace"Shi Hamma din naki..SAIFUDDEEN."
Sadiya ta saki baki tana kallon mijinta shi kuma yana ta mata Dariya Lokaci Daya ya lakace mata hanci yana Fadin"Kanwar Aljani."
Dukan kirjinsa ta farayi cikin Shagwaba tana fadin bataso shi kuma yana mata dariya kafin ya rumgumeta da karfi yana fadin"Sweety..!

Cikin wani yanayin da su kadai suka sani..
******
Washegari Asabar tun wajen Sha daya na Safe Muhibba da Anty Habiba suka gama shirinsu Siyama Saboda alkwarin da Anty Habiba tayi mata yasa bataje Hadda ba su walid kadai suka tafi itama din Muhibba ta kara rokan mata Abban su walid domin da Farko yace sai tatafi makaranta bai ga Dalilin da zai saka tayi fashi ba sai da Muhibba ta saka baki sannan ya barta aje da itan.

Sun gama shiryansu tsab,Dayake tun Safe Maman Arfat din ta aiko aka karban mata Snaks dinta jiya suka yi Dare suna aikinsa ita da Muhibba.

Maman Arfat din kawar Anty Habiba ce Tare sukayi karatunsu a nan Abu zaria,Ita maman Arfat din tana Banzazzau ne da aure kanwar nata kuma tana cikin kongo ne sun gama karatunsu tuni ita Anty Habiba ce bata aiki sai ta maida hankali wajen yin su Snaks din nan da girke girke kuma ba Laifi tana samu sosai dashi.

Abban walid yakai su cikin Kongo gidan sunan sun samu tarba Sosai Saboda Maman Arfat din da Anty Habiba sosai suke kawance.

Muhibba Less ta sanya irin na Siyama saboda kayan Anty Habiba ne daman sun mata kadan sai ta bama Muhibban ta saka sukayi anko da Siyama.

Suna chan har bayan La"asar Su Walid daman Tace in sun dawo akai su Gwarbai gidan su kakaninsu na Bangaran Uba tunda Abban walid din d'an chan kwarbai ne,Domin sai dare zasu dawo.,Anty Habiba kawayensu wadanda sukayo karatu tare duk sun zo sun hade suna ta Fira siyama kuma ta shige cikin yara sa"aninta suna wasa sai Muhibba ita kadai tana zaune tana Faman Danna waya sai Daga baya kanwar su Maman Arfat din Aisha tazo suna dan taba Hira Dayake itama B.Ed dinta take yi a Fce zaria.

Suna cikin Hirar ne taga Sani nata Kiranta tayi mirsisi taki Dauka har Kira Hudu har sai da Aisha tace mata"Muhibba ba kiran ki ake yi ba..

Ta tabe baki kafin tace"Bamai muhimmanci bane..

Dariya tayi ta zata ko Saurayinta ne take ja ma aji suna zaunen sai ga Ya Habiba ta fito daga Dakin maijego tana Fadin"Muhibba ina kika bar wayarki sani yace yana ta kira baki Daga ba.?

Tace "Gata a hannuna ban ga Dama bane..

Anty Habiba tace"Kun fi kusa..yace gashi fa agidana bama nan.

Muhibba batace komai ba Daidai Lokacin Wayar Anty Habiba ta Sake Daukan kara ta Daga tana fadin"Sani gamu nan zuwa.

Dagachan bangaran Sani yace"Yarinyar nan ni ke kiranta tana banza dani..Wlh ki gayamata haduwarmu bazai yi kyau ba sai na mata rashim mutumci.

Anty Habiba na Dariya tace"Kun fi kusa bazan shiga ba sai mun taho..ba nisa nan cikim kongo ne.

Daga haka ta katse wayar tana kallon Muhibba kafin tace"Yace wlh haduwarki baza tayi kyau ba.

Muhibba tace"Ni ai robar wando ce Daidai da kugun kowani mara mutumci."
Wannan karon har Aisha sai da ta Dara kafin tace"Hala yayanta ne..?

Anty Habiba tace"Daga ita sai shi..Fadan sako da sako ne.

Aisha na Dariya tace"Dama yazo nan naga ya wannan haduwar zata kare.

Hararanta Muhibba tayi batayi mgana ba saboda bata da Hayaniya sosai.

Anty Habiba ta shiga tayi ma mai jego sallama har da muhibba ta basu abun Rabo su Snaks din Anty Habiba tace bazata karba ba,Maman Arfat tace bata isa ba,karshe dai Siyama aka bama ledan har Bakin kongo Aisha ta raka su Muhibba bayan sun karbi lambar juna sannanta koma su kuma suka Hau adaidaita zuwa gida.

Suna zuwa kofar Apartment din Su Anty Habiba Muhibba taji ranta ya kara baci ganin Ya Sani da abokinsa Abbati suna jingine jikin mashin Roba roba ta Abbati din ce.

Itace karshen Fitowa Daga adaidaita Anty Habiba ta tsaya basa kudi ita kuma Muhibba ta hade girar sama da kasa bayan ta kara gyara mayafin jikinta.

Ina rike da Hannun Siyama muka zo muka wuce su Sani dake tsaye suna kallona Siyama ce ta fizge hannunta ta Nufi Sani da gudu Tana Fadin"Oyoyo Uncle.

Da Sauri ya Dagata sama ita da ledan Hannunta yana Fadin"Eye yar gidan Uncle me aka samu ne..?

Suna wannan Anty Habiba ta kariso ita kuwa Muhibba daman key na Hannunta har ta Bude gidan ta shige.

Anty Habiba da Fara"arta tace"Sannun ku da zuwa..Sani yan Kano..Abbati barka da zuwa.

Abbati Dogo ne baki,kansa na kasa yace"Yauwa Anty ina yini.

Ta amsa tana kallon Sani wanda yake Biyema siyama bayan ya bata Tsaraban Biskit din daya siyo musu ita dasu Walid.

Tace"Mu shiga ciki sani..Hala Auta ta shige ne..?

Sani yace"Ai yarinyar nan muguwar yar raini ce haka fa ta wuce ko kallo bamu samu ba kamar taga kashi.

Anty Habiba na dariya tace"kun yi Fada ne kila.

Sani na bin bayanta yana Fadin"Wlh ba kowa yajamin ba sai Abbati..Yarinya karama na raina ni.

Abbati yace"Sorry abokina.

Sanda suka shiga Falon gidan ne Sani ya Bude murya yana Fadin"Ka nace ma yarinya sai wulakantaka take yi..Ga manyan bbya chan yan jami"a wlh sai ma ana rubibinka ka tsaya wajen wannan Tsamiyar tana maka yarda ta ga dama..!

Anty Habiba dariya take yi tana Fadin"Sani ka bari Autan inna ce fa.

Sani yayi tsaki yana zama gefen Abbati Dauke da Siyama kafin yace"Ai shiyasa take iskanci Saboda taga kuna ce mata Auta..ni ba Auta ba ko bakwaini ce sai na yanka mata rashin mutumci wlh badai ni zata wulakanta ba.

Anty Habiba yar dariya tayi batace komai ba kitchen ta shiga ta Dauko musu ruwa da Snaks din da sukayi jiya ta kawo musu tana Fadin"Ku fara da wannan kafin mu dora wani abun sunan kanwar kawata mukaje nan kongo.

Sani yace"Ba Case Anty Habiba.

Abbati bismillah.

Abbati dai bai ce komai ba Muhibba yake son gani duk ya takura.

Ganin haka yasa Sani ya kalli Anty Habiba yana fadin"Kira ta saboda ita fa ya matsa sai munzo.

Anty Habiba ta kwalama min kira Murya shake nq amsa mata sai da ta na bata Lokaci sannan na leko daga kofar Dakin na tsaya Dogon Hijabin Anty Duk ya yamutse ajikina yayi Datti Saboda bana so ma ya ganni da kyau yasa na saka.

Dagachan na tsaya ina fadin"Gani Anty.

Anty Habiba tace"Daganan muhibba..?

Ko baki ga Abbaati bane..?

Muhibba ta tabe kafin tace"Waye Abbati kuma..?

Ba Abbati Kadai ba har Sani sai da ya bude baki ransa ya baci ai ba kyau cin ido,kallon Muhibba yayi yana Fadin"Ammh ke kam baki da mitumci..?

In baki son shi ai bai kamata ki wulakantasa ba,Wlh in da Abbati na Daukan mganata da Tuni ya barki Haba..Ni narasa uban me ya gani a wajen ke yarinya ke ba kyau ba yar gidan masu kudi ba sai fadin Ran Tsiya Kada dai ki manta Bello mai Rago dan asalin gaya ne Ubanki Sannan kin ma samu zai taimaka miki ke fa Sauran Aljani ne waya sani ma ko auranki yayi har kun hayayyafa bamu sani ba..?ai shima Abbati wlh Jihadi zai yi in nine ko kafa aka Daura min ke sai na kwance ki na zura aguje."
Ya karishe fada yana hararansa Muhibba ranta ya baci wannan tozarci akan Abbati..?

Sai kawai ta Fashe da kuka ta juya Cikin Dakin Anty Habiba ta kalli Sani Tana fadin"Kaga ka saka Autan Inna kuka ko..?

Sani yace"Tayi na jini ma bazan fasa fada mata gaskiya ba.

Abbati cikin wani yanayi yace"Gaskiya ban ji dadi ba Sani..baka kyautamin ba in bazaka lallasamin ita bai kamata ka sakata kuka ba.

Sani yace"Ai shikenan na barka da ita.

Abbati yace"is better.

Anty Habiba dai Dakin da Muhibba ta ke ta leka Siyama na jikin Sani tana fadin"Uncle Anty kuka take yi..?

Kai Tsaye yace"Ohon mata.

Ita kuwa Anty Habiba daga kofar Dakin ta tsaya tana kallon Muhibba dake kwance kan gado tana kuka kai ta girgiza kafin tace"Auta baki son gaskiya ne..Sannan kinsan Halin Sani sai ya sakaki kuka sau goma arana bai Damu ba..Ni dai ba abunda zan ce sai kiyi hakuri.

Daga haka ta juya ta bar Dakin muhibba ta dago kanta idanuwanta sun yi jajir kamar gauta,Hawaye suka kara zubo mata shikenan sai arika Dangantata da Aljani ya aureta Saboda wata Kaddaranta..?

Kuma ai basu Tabbatar da SAIFUDEEN Ba mutum bane hasashe suke yi bai kamata su rika jifanta da haka ba.
Chapter 13 · 0% Book details