Sashe 21
Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ku yan iska ne..?
Kamar wasu yara kanana suka Hada kai wajen girgizamai kara Tamke Fuska yayi yana Fadin"Ku ba mata bane zaku zauna agida sai dai ku bata bakusan gyara ba...?
Kuna so ku zama kazamai ne bansani ba..?
Nan ma kai suka girgiza cikinsu bamai wani motsi mai karfi yanayin kayansa ya kara kallon kafin yace"Kuma Ummi ce ta koya muku yawo agida Tsirara..?sai suka fara kallon juna cikin mamaki Laala ce tace"Hamma ga Kaya nan ajikinmu..!
Wani uwar Harara ya Maka mata kafin yace"Mara kunya ina mgana kina cewa kuna da kaya..?
Wannan ne kaya don kaniyarki..?
Shashashan yara kawai kada na Fito naganku da wannan shigar in ba haka ba sai yarinya ta raina kanta.
Da Sauri suka hada baki wajen amsa mai har ya juya suna kokarin sakin Numfashin da suka rike,sai kuma ya kara juyowa yana kallonsu da Sauri suka Dauke numfashi kamar za"a yankasu..
Kai tsaye Saudat ya kallah yana Fadin"Ke bakya zuwa makaranta ne kika zo nan kika tare..?
Da Sauri tace"Ai mun gama Jcse sai First Term zamu koma makaranta.
Laala dayake Fadi ce ba"a tambayeta ba tace"Ai tare muke da ita Saudat..Tun Daga lere muka je gaya Dagachan tare muka dawo nan da ita.
Sai da ta fada ya tuna kamar ya ganta a Lere baki ya tabe ya juya yana Fadin"Duk nasan mganinku.Bording School zan kai ku bari Ummi ta dawo..!"
Ai jin haka yasa suka tsure suka Diro kasa suka fara basa Hakuri ko Tsayawa jinsu bai yi ba ya isa kofar Dakinsa ya saka dan makulli ya Bude wanda yana jikin keys dinsa na gidansa na kaduna nada Zaria Saboda gudun bacewa.
Dakin na
nan Tsaf kamar koyaushe Daga gadon har Wardrope din kalan Fari da baki ne Dakin sai tashin kanshin Turaran wuta yake yi mai Dadi,Sai yaji gajiyarsa ta sauka Yasan aiki Ummi ce tasan halinsa baya son Datti ko kadan shiyasa bai taba zuwa Abuja yaga muhallin kwanansa da Datti ba.
Yunwa yake ji Tun fa Tea din daya sha da Safe kafin ya fito ai bazzi rikesa ba,Sannan ga Ummi bata gida yaran nan kuma ba cin girkinsu yake yi ba To ubam me ma suka iya ban da gulma sai iskanci da har zasu Dafa wani abu yaci shi banda Ummi da Mama Zuwaira to sai Addansa yana cin girkinta in yaje gidanta shima ba sosai ba Yana da kyamkyani bakowani abinci yake iya ci ba,Sannan gidan abincin Daya ne ya yarda da ingancinsa da Tsabtarsa yake zuwa yaci abinci wani Lokaci shi ko irin Dinner nan da abokan aiki ke gayyarsu gidajensu ruwa kadai yake iya sha sai yaji kamar bai yarda da abincin ba ko da kuwa gidan na masu da Hannu da Shunu ne haka Halittarsa take bai cika cin abunda baisan cikin wani yanayi aka sarrafasa ba.
Kayan jikinsa ya cire ya Daura Towel babba fari ya shiga Tiolet yayi wanka sannan ya fito ya goge jikinsa ya Shafa mai tunda komai yana dashi anan gidan Wadrope din sa ya Bude ya Dauko Riga da wando acikin Hanger dinsu wandon Baki ne rigar kuma Fara ce Kamar polo shirt sai dai Tana da Rubutun Baki ajikinta an saka Gentle daga kasa cikin Lokaci kadan ya shirya bayan ya kara taje sumar kansa ba Laifi Saifuddeen yana dan Tara suma wacce take karamai kyau da kwarjini.
Takalmi ya saka cikin Saukakkun Budaddun takalmansa Dake Dakin Cikin ma"ajiyarsu ya saka baki na Fatar Damisa mai kyau,Wayarsa karama kawai ya Dauka sauran nan kan gado ya zubesu ya fito Daga Dakin yana Baza kamshin Turaransa na Kamfanin Nivea,Saudat na rike da Moper tana mopping yayin da Zeeha ke bakin kofar kitchen din suna mgana da Laala dake ciki tana wanke wanke Zeeha Fadi take yi"Ammh Laala kin gama damu da kika gansa meyasa baki yi mana sigina ba..?Kin barmu muna ta Zuba zencen kuma ya jimu ko..?
Laala na Dariya tace"Tsab wlh domin nima na daga kaina ne na gansa kuma daga alamu ba Lokacin ya shigo ba..Tun yaushe ina ta muku gyaran murya idon ku ya rufe baku jini ba..
Zeeha tace"Ni dai Allah y..!
Sauran mgana ne ya makale mata jin kamshin Turaransa da kuma bayyanarsa afalon Saudat dai kanta na kssa tana cigaba da aikinta tana kunshe Dariyarta Zeeha kuma da Sauri ta shige kitchen din kamar zata Kifa Laala jin shuru yasa ta harbo jirginsu itama sai tayi gum da bakinta..ko kallo basu ishesa ba ya Taka ya fice Daga Falon aransa yana ayyana Laala a matsayin wacce in Ummi batayi wasa ba sai tayi aure an Dawo da ita Saboda gulma.
Sai da ya fita suka sauke Numfashi Zeeha ta leko daga kitchen kamar munafuka Saudat ta kwashe da Dariya tana Fadin"To ya fita matsoratan banza.
Zeeha ta fito tana sauke Numfashi kafin tace"Allah yaso mu..!
Laala na Kitchen tace"Zeeha tsoro zai ya kasheki watarana.
Zeeha ta harari kitchen din kamar Tana ganinta kafin tace"Eh naji ku in ba Tsoron ba meyasa baki yi wani motsi a gabansa ba..Ai duk shegiyar Darin ce.
Saudat Dariya har tana kokarin Faduwa Zeeha ta Haureta da kafa Tana Fadin"Shegiya ai ke kika kawo gulmar.Allah ya isa indai aka kaiku Makaranta kwana aka hadani da ni"
Me Laala da Saudat zasu yi in ba Dariya ba Sanin yadda Zeeha ta Tsani makaranta kwana Saboda jin Labarin Uban wahalan da ake sha achan.
Yana Fita ya iske Tim da Ibrahim zaune chan gefe suna Hira Bama na cikin mota Tim da Sauri ya taso sai ya Daga mai Hannu alamun ya koma kawai Bama kuma na fitowa yana kokarin budemai gidan baya,Sai shima ya Daga mai Hannu,ya bude bangaran Direba ya zauna Ganin haka yasa Bama ya bashi key din Cikin Girmamawa walet dinsa ya Dauko ya zaro 5k ya bama Bama ko da bai yi mgana yasan na abincin su ne Saramai yayi yana Fadin"Yes sir..!
Kai ya gyada mai kafin ya Tada Motar Ibrahim har ya Bude mai get ya sulala da Motarsa waje.
******
_UNITY HOSPITAL AND MATERNITY,Federal Housing Estate behimg Total Filling station,phase2Lugbe Abuja Fct_
A bakin get din asibitin ya tsaya ya Danna Hon Security suka zo wani bakin mutum sanye da bakaken kaya Saifudden ya Bude glass ta bangaran Direba,mutum yana ganinsa ya washe baki yana fadin"Ranka ya Dade barka da zuwa..!
Hausa abakin Jatau kamar bahaushe sai dai bakatafe ne,Saifuddeen ya murmusa kawai kaf Ma"aikatan asibitin da Ummi ke aiki kama daga Security har masu goge goge da share share da sauran ma"aikata sun sam waye Saifudeen domin sau tari in ya shigo garin In Ummi na wajen aiki nan yake sauka su gaisa sugama mganarsu ya kama Hanyar kaduna shiyasa duk wanda yasan METRO ZALIHA yasan YARO SAIFUDEEEN D'anta ne.
Gaisawa sukayi da Jatau yayi mai alherin Daya saba sannan ya wangale mai get ya shiga ciki saboda Muhimmamcinsa ko pass din da sukan bada bai bama Saifudden ba sosai yake ganin girmamsa kuma ya Tabbatar da Metro Zaliha ta iya Haihuwa Sannan kyakyawan Hallayarta Saifudeen ya Dauko wajen kyautata ma mutane da Dattako.
Haka ya kirga kudin daya basa Dubu Biyar yabi Saifudden da addu"an Fatan gamawa da Duniya lafiya.
A parking space ya faka motar tasa sannan ya fito yana bin Haraban asibitin da kallo dayake yau Lahadi ba Zirga zirgan mutane sosai ba kamar Ranakun Cikin Sati ba.
Cikin Tafiyarsa ta Sarssafa ba jan aji ba,ba kuma wani takama ko iko ba,Haka yake tafiya kamar yana Sauri kamar kuma bazai taka kasa ba.
Hannayensa sanye Cikin Aljihun wandonsa Guda daya,Dayan hannun kuma yana rike da wayarsa sai key din Motarsa.
Tunda ya shiga asibitin yake amsa gaisuwan Nas din da suka sansa wani ya amsa wani kuma yayi mirmishi Office din da yasan Ummi tana Zama ya Nufa gabda zai shiga ya Hadu da Maman Nana wata midwife ce Takai shekarun Ummi anan asibitin itama take aiki tana Dauke da Tarin wasu Fayel a Hannunta tana ganinsa ta washe baki Tana Fadin"Yaro kai ne tafe..?
Rankwafa yayi ya gaisheta ta amsa Cikin Fuska kafin tace wani abu ya rigata da fadin"Allah yasa Ummi tana ciki.?
Yafada yana nuna Office din da suke kallo ta Bude baki zatayi mgana kenan sai ga Ummi ta fito Daga wani Daki tana kokarin Cire Safar hannunta wasu Nas na Biye da ita kusan su goma cikin shigar fararan kaya wasu musulmai wasu kuma yare da Kabilu.
Sanye take da kayan gida Saboda yau Lahadi ta saka doguwar rigar Atamfa da Hijabin nan Three in one Yellow saboda ajikin Atamfarta akwai yellow,Safan Hannunta ta cire ta jefa Cikin Dusbin dake Wajen tana Fadin"Na Dubata saura 10.cm ta Haihu nan da 1hr kenan.."
Tafada Cikin nuna tana musu bayani ne kwata kwata bata Lura da Saifudden ba Sai Maman nana ce ke Mirmishi ganin yadda ya mike yana kallon Ummi ita bata san yana gabanta ba ta juya tana musu mgana kawai taji ta Daki jikin mutum sai da ta kusa Faduwa da azama yasa Hannayensa ya tarota jikinsa yana Fadin"Ummi ki kula fa.
Da muryansa ta fara shaida sa tun kafin ta Dago su hada ido cikin mamaki tace"YARO..!
Daidaita mata Tsayuwarta yayi yana mata Mirmishi gabadaya sai aka Tsaya kallonsu wasu sun san yaronta ne wasu kuma Dayake masu zuwa ne saboda rako ko masu rakon yan Haihuwa baza su iya Dora komai ba.Har da ta saki bakinta Hakoranta sun fito kamar an tuna mata sai ta hade rai batare da tayi mgana ba Ta juya ta cigaba da Tafiya Nurses din kuma suka mara mata baya bai Damu ba Daman yasan za"a rina.
Maman Nana tace"Hala ka tabo Ummin taka ce..?
Kai ya sosa bai yi mgana ba bata Damu tace"Kaje ka sameta..Nasan zata yafe maka,saboda bata Fushi dakai ko dazun nan mganarka ta gamamin..
Yana jin haka bai tsaya ba Har da Gudu ya kara ya sha gaban Ummi Daure Fuska tayi tace"Ina wasa dakai ne..?
Bani hanya na wuce ina aiki ne."
Marairaicewa yayi kafin yace"Ummi..
Ganin zai mata yaudaran daya saba yasa take kokarin rabasa ta wuce ai da Sauri ya rike mata Hannu ya jata kamar wata yarsa ko matarsa Baki ta Saki tana Fadin"Kai..Kai me zan gani haka...?