Sashe 44
Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mujaheed bai ko kara bi ta kansa ba Dayan bedroom din ya shiga yayi wanka sannan ya shigo Dakin da Saifudden yake ya iske yayi wanka ya sauya saukakkun kaya shima wardrope din nasa ya Bude ya Dauki Jallabiya Baka ya saka ya fice Falo ya Sauya tashar Tv ya fara kallon sa Lokaci daya yana Sarrafa wayarsa Saifudden kuma kitchen ya shiga ya Dafa Ruwan zafi ya hada tea ya fito Falo Kujeran da ke fuskartar Mujaheed ya zauna kafa daya kan daya yana shan Tea Lokaci daya yana kallon Abunda mujaheed ke kallo tashar Bollywood suna haska wani India mai suna Dilwale karamin Tsaki yaja shifa baya kallon Fina Finan India bai ma da Lokaci gwara ma Ameriacan yana kallonsu to sai Carton ko labarai ammh bai san meyasa Kallon su haushi yake sakashi ba ko domin bai Taba soyayya bane shi yasa yake Daukan da masu yinta masu shirme.
Kallon Mujaheed yayi a tsume kafin yace"Dazu da mukaje gidan nan..Naji wannan matar tana ta fadin Aljani aljani ban gane mganarta ba.?
Mujaheed yace"Meyasa baka tambayeta tun achan ba..?
Yafada hankalinsa na kan wayarsa,Saifudeen yace"Haba Man..Joke a side don Allah ka Fadamin.."
Ganin yadda ya marairaice ne yasa Mujaheed ya fara Narritive dinsa kan Abunda ya faru da Labarin Muhibba har zuwa sufar shu datake gani kan wanchan Saifudden din Mujaheed ya karishe da Fadin"Shiyasa data ganka ta rika kiran sunan ka tana rike ka ta zata wanchan ne domin ance tun tana yarinya take ganinsa sun shaku da juna."
Har Mujaheed ya gama mgana Saifudden bai Fahimcesa ba kallonsa kawai yake da baki sake kamar wani Wawa,Saboda ma bai gane komai ba Sai ya kara kafa kai kan mug din Tea dinsa ya kurba Daidai Lokacin da Mujaheed yace"Kai fa yanzu haka ita yarinya a matsayin Aljani take ganinka."
Saboda firgita da mganar Mujaheed sai da Tea din da ya Kurba ya Dawo mai ta hanci ya fara Tari Mujaheed ya mike da Sauri yana mai Sannu kitchen ya shiga ya Bude fridge ya Dauko Mai ruwa mai saukakken Sanyi ya samu karamin kofi ya Tsiyayomai ya kawo mai ya sha yana dan Bubbuga bayansa cikin wani yanayi yace"Daga cewa Aljani sai ka fara tari har da kwarewa ko Aljanin ne da gaske bamu sani ba..?
Wani kallo Saifudeen ya jefamai kafin ya Sarara yana Haki yace"Mganar banza ne wannan..Wannan ai labarin ko a hikayoyi bazai taba Faruwa ba ta ina wani Aljani zai bayyana har ta rika ganinsa Kuma ta rayu..?Ku kuma kuka zauna kuka amince da wannan k'are k'are nasu..?
Ya karishe Fada yana maida Numfashi Mujaheed yace"Easy man bafa A sufffarsa take ganinsa ba A taka sufar yake zuwa mata."
Saifudden yayi wata bazawaran Dariya kafin yace"What a stupit Story..?wato anawa sufar take ganinsa yarinyar nan ta ma raina ma mutane wayau ni ina nasanta ma balle ta Dangana da labarinta na karya da ni, ni nafi Tunanin tana da wani kudirinta akaina data ke son cimmawa shi yasa ta Kirkiri banzan labarin da ko a Fina Finai bai taba Faruwa ba."
Mujaheed yace"Yana fa faruwa kai da yake baka san komai ba sai Boko da aikinka shiyasa bazaka san komai ba ammh ko addinin mu munsan akwai Aljanu sannan suna yin kowacce suffa suka ga Dama har ta dabbobi suna komawa ko baka san haka bane..?kuma ta nemi wani abu a wajenka Saboda menene..?.
Da kaga yarinyar zaka san kaddara ce kawai ta Zagaye Rayuwarta baa zata taba' aikata abunda kake zarginta ba."
Saifudden yayi shuru bai yi mgana ba in ana mganar Sanin Addini bazai ce komai ba domin baisan komai ba Shi dai yasan wasu abubuwan Tun lokacin yana gaban Ummi komawarsa Lere shine Tarbarbarewar komai nasa Su iya karatun ba wani Damunsu yayi ba balle su matsa masa sai yayi na bokon ma shi ya Jajirce sannan yazo ya tafi makarantar kwana a kafachan daganan ya shirirince da karatun addinin,Duk da akwai Lokutan karatun addinin bai maida Hankali ba, shi dai bar shi da Dagewa ana Bokon yana ganin kamar shine Tsira in ka same sa shikenan shiyasa bai Damu da sai ya nema ba,Sannan ya koma Abu zaria yana ganin mujaheed na zuwa karatun ka da Muslim association ke yi baya zuwa in ya matsa mai ma sai suyi fada sannan daya bar Nageria sai abubuwan suka jara Tabarbarewa,Saifudden bazai iya tuna yaushe Rabonsa da karanta Qur"ani ba abaya a wajen Ummi yasan bakin karatu ammh Dadewar da yayi baya Bibiyasa yasa ya manta ba lalle in ya Dauki Qur"ani ya iya Hadasa daidai ba a sallah kuwa kananun surorin na kasa ne da ya iya yake karantawa Domin tun suna Jaji barraks yayi saukan Izufi goma ammh gabadaya yanzu basu a kansa rayuwa da kuma yanayin inda ya rayu yasa yake da Rauni Sosai kan addininsa sannan baisan komai ba kan Aljanu ba,ya dai san suma wata Halitta ce irin su ammh baisan wannan mganar da Mujaheed ke fadamai ba,Sannan shi bai Taba yarda da wani Canfe canfe ba Shi abunda ya sani Reality ne ba yadda da abunda bai taba ji ba ko gani a zahiri ba."
Yana cikin wannan Tunanin kamar Daga sama yaji mujaheed na fadin"Hala baka ma san abunda ya faru a kafafan yad'a zumunta bane..?Ko nace yana kan faruwa ma.?
Saifuddeen ya kalllesa a Tsume kafin yace"Mene..?Bansani ba ban bude wayata ba."
Mujaheed ba mgana ya Lalubo Abun ya mikama Saifudden ya karanta sannan ya maida masa wayarsa batare da yayi mgana Mujaheed ya karba yana Fadin"Shiyasa kaga Ummi ta karfafa zuwa su bada Hakuri Saboda abubuwan da suka faru."
Saifudden ya maida kansa jikin Cussion din kujera kafin yace"Ina suka samu wannan Labarin..?
Mujaheed ya tashi ya koma wajen zamansa da farko yana Fadin"Ina zan sani..?abun duniya na boyuwa ne. ?
Saifudden ya tabe baki kafib yace"Sai su bada Himma."
Mujaheed yace"Haka kurum zaka ce..?Saifudden yace"Eh.
A Dakune ganin haka yasa Mujaheed ya sharesa bai kara mai mgana ba, Suna zaune Lokacin sallah yayi Mujaheed yaji kiran salla a masallacin anguwan ya mike ya shiga ya Dauro alwala yazo ya samu Saifudden yadda ya barsa Cikin mamaki yace"Baka tashi kayi alwala ba kada Lokacin sallah ya shige fa.
Saifudden yace"Zan yi..in na tashi."
Mujaheed cikin mamaki yace"An kusa tada sallah fa.
Saifudden yace"Kaje kawai zan yi agida."
Mujaheed yace"Har yanzu baka Daina Sakaci da ibada ba ko Saifudden..?Kana magidanci ga msallaci a kusa dakai baka zuwa Salla cikin jam"i..?Wlh in ka mutu ahaka kana cikin Tabewa ka gyara rayuwarka Tun kafin Lokaci ya Kure maka."
Yafada kai Tsaye kafin ya fice ya bar Saifudden nan,Ya dade da sanin yana da Rauni ta bangaran Ibada,ammh ya Zata ya sauya ashe jiya iyau ce,Har an Tada sallar sai gashi yazo ashe yasan masallaci bai da nisa fa da gidansa wasu ma sai sun yi tafiya mai Nisa ammh Ruwa da iska in ba Lalura ba basa rasa salla cikin jam"i.
Ranar Saboda Mujaheed ya mai Fada yasa har Sallar Issha'i cikin jam"i yayi ta bayan sun dawo ne Mujaheed ya Hada Tea yasha sai faman Tsaki yake yi Saifudden na jinsa bai tankamai ba Tab dinsa ya kunna yana ganin Taron Sakonnin da suke shigowa,Ana ta tambayansa shin gaskiya ne abunda akaji ya taba aure har sau biyu..?.
Amsawa yake da Eh ba ruwansa ko ajikinsa,Har kwimishinoni yan"uwansa wasu basu damu ba sanin Siyasa ta gaji haka bama wanda ya Tambayesa sai sakon D.Musa na ban Hakura kawai is ok ya Turamai Saboda bai da wannan Lokacin.
Tsabar yadda basa mgana Ba Daki daya suka kwana ba Mujaheed falo yayi kwanciyarsa Saifudden kuma ya shige ciki da asuba kuwa sai da ya matsa ma Saifudden ya tashi suka tafi sallar asuba suna Dawowa Suka Fara shiri shima Saifudden yana da shiga office aranar shima Mujaheed haka sun yi waya da Sadiya tace suma sun Shirya itama Ummi yau zata koma Abuja Saboda aikinta.
Dukkansu ba wanda yaci wani abu ko da Takwas na Safe tayi Mujaheed na kofar gidan su Muhibba sun fito tare da Saifudden kawai sai ya Nemi motarsa ya rasa Dariya kawai yayi Daman yasan bazai tsaya ba Kaduna zai wuce,Har cikin gidan ya shiga cikin Shigar Suit kayan Saifudden ya saka Dayake yanayin jikinsu daya shiyasa ba tun yau ba suna saka kayan juna kuma ba"a gane ba Suit din Sabuwa ce Saifudden bai taba sata ba.
Bayan sun gaisa dasu Ummi suke tambayansa Ina yaro..?
Yace yana da Meeting ya riga sa ya wucewa kaduna Daman ya iske su duk sun shirya sun karya Mama zuwaira da Umma Babba Gaya zasu wuce yayinda Ummi zata bi su Mujaheed Zuwa kaduna dagachan ta hau motar Abuja.
Haka akayi sallama kamar kar a rabu,Muhibba dai jikinta duk a Sanyaye kamar ba ita ba,Har kofar gida suka Rakosu ana ta ma juna godiya Muhibba dai tana daga Zaure su Mama zuwaira suka fara Tafiya Isma"il na Tukasu sannan su Ummi,suma suka mika sai fatan Allah yasa su isa lafiya.
Su Inna suka Dawo Cikin gida suna yaba Kirkin su Ummi Muhibba dai Daki ta shige ta kwanta Anty Habiba ma bata jima ba ta kwashe ya'yanta ta koma gidanta yau sun rasa makaranta basu je ba MUhibba bata ma yi wannan Tunanin ba tun ranar da abun nan ya faru ko ta kan wayarta bata bi sai aranar ta Dauka taga kira kirayen su Uncle Hafiz da Anty Jidda duk sai aranar ta Kira su Lafiyarta kadai suka Tambaya basu yi wani bin Daddigi ba,Anty Jidda ce tace yaushe zata Dawo makaranta tace bata sani ba Domin bata san makomar aikin nata ba ajinta Uncle Hafiz ke rike mata yau din da bata zo ba.