← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 144

Sashe 117

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajiyar rai mallam Surajo ya sauke kafin yace"Ta tafi har abada bazata Dawo ba..matan ku koma cikin gida ku yayyafa musu ruwa zasu farfado shi kuma ku bar min shi a wajena shima zai farfado ta Dade ajikinsa ne Shiyasa zai wahala kafin komai ya sake shi ammh zan yi mai wani Turare zai tashi da yardan Allah."
Ba wanda ya iya ko Tarin Ummi ta mike ta koma cikin gida jikinta ba inda baya rawa cikin Matan Mallam wata tazo ta watsa mana ruwa muka Farfado ta jamu Cikin gida,Daga baya ta kawo Kasko da rushi Mallam Surajo ya Dauko
wani garin mgani ya Watsa hayaki ya tashi sama Daman Tuni yace su kawu su fita waje har sai ya gama Dakyar suka kama Baba Surajo suka fita Ya Habibu da Mujaheed basa ko iya motsi Saboda Firgici,Miyau ma rahma ne ya wuce ta makogwaron su sai zare ido suke tsabar yadda suka firgita ba wani mai kwakkwaran motsi acikin su tsabar yadda tsoro da firgici ya kusa ajalinsu acikin dakin nan na Mallam Surajo.
*Janafty*
*SFD0042*
*Amnaf_sudanese _collection*
*Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401*
*Ki biya ki karanta cikin salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba, kada ki karanta min littafi sannan kada ki yada'min shi don Allah pay N500 via jamila umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*
Tsaye suke a kofar gidan mallam Surajo sun yi jigum jigum,kallo daya zakayi musu ka fahimci yadda Firgici ya bayyana atare dasu Baba Surajo dai sai da yakai ga zama a kasa saboda Jikinsa ba karfi Tsabar yadda yake a kidime Kawu ne da Baba Sa"idu ke da sauran karfi da Kuzarinsu Banda su mujaheed Ya Habibu kuwa Makogoran sa ne yaji ya Bushe kamar bai taba shan wani abu wai shi ruwa ba.

Kana kallon su kallo daya Zaka zata kwato su akayi a hannun yan kinafin bayan sun shafe wata da wattani Tsabar yadda Tsoro da firgita ya samu muhallin zama a fuskokinsu.

Kawu ne ya cire hulan kansa ya Share zufa yana fadin"Tab wannan ai shine ana zaton wuta a makera sai aka sameta a masaka waya taba Tunanin duk wannan wahalar da yarinyar nan take sha abun na tare da Saifu ne..?

Yau naji ikon Allah kuma naga Ikonsa da Kudurinsa.."
Baba Sa"idu ya karbe da Fadin"Shiyasa Hajiya ta matsa ma mallam sai da ya amince muka zo wajensa..in dai akwai aljanu tare dakai yana ganin zai gane."
Ya Habibu yace"Shi ko ina ya samu wannan Nasibin..?

Tab ina zan iya Allah ya san yadda ya Hallicemu shiyasa ma bai bamu ikon ganinsu ba Saboda yasan bazamu iya ba'
Ya mujaheed na Sauke Numfashi yace"Tabbas haka ne duk ranar da mutum yaga aljani a sufarsa sai iya mutuwa..Murya ce kawai ajikin Dan adam ammh Firgici da razana kamar su kasheni wlh."
Baba Surajo na sauke numfashi yana Fadin"Ni yaron nan nafi Jin tausayi..Shekara da shekaru yana wahala kai Allah ya shiga Tsakanin nagari da mugu"
Gabadaya suka amsa da Ameen Baba Sa"idu ya gyara tsayuwa yana Fadin"Mu ma bamu san ina ya samo Lakanin ba,Yadai dawo mana da shi..Ammh kamar yadda yace ya same sa ne hannun wani makiyayi ne Fulanin a tashi achan Adamawa wani kauye da ya zauna sannan uwa uba kuma Bafullatanin Malamin addinin musulunci ne babba a Rugarsu yayi karatun Littafai a wajansa da zasu tashi ne ya bashi wannan lakanin na Gane aljani da kuma mgana da shi"
Kawu ya jinjina kai yana Fadin"Ikon Allah.."
Daganan Lamarin suka cigaba da Jajantawa shi ko Mujaheed ya shiga Zurfin Tunani Tabbas ai biri yayi kama da Mutum tun a baya akwai wasu Hallayar Saifudden da ba Daidai ba ne rashin Sakin jiki da mata Kamewa rashin Damuwa da addini da Sauran su ko shi yayi Tunanin akwai matsala ammh ganin ya tambayesa bai gaya masa ba yasa sai ya Hakura ballatana ganin auran su da Muhibba sai ya Fara Tunanin bakomai kamar yadda Saifuddeen din yace.

Suna nan Tsaye sai ga Mallam Surajo ya fito tunda har an fara kiran Sallar La"asar Suna ganinsa suka nufesa kai Tsaye yace Suyi alwala daman akwai wani babban masallaci nan kusa dasu aciki sukayi salla mallam Surajo ne limamin masallacin bayan sun Idar da sallar suka koma Falon nasa suka iske Saifudden kwance yadda suka barsa sai dai na wannan karon yana Sauke Numfashi cikin Salama ne ba kamar Dazu ba..

Kallon su kawu yayi kafin yace"Zai farka nan da lokaci kadan in sha Allahu"
Jinjina kai suka yi gabadayan su cikin Gamsuwa,Baba Sa"idu ne yace zai koma su kawu suna ta godiya Mallam Surajo yace ya bar su kawu anan bai gama da su ba ammh suma komai Dare Tun da ba Nisa sosai gida zasu kwana.

Har cikin gidan Alhaji Sa'idu ya shiga suka yi sallama da su Ummi da Sakon godiya da gai da su Hajiya ya Dauki Hanyar Gumel Daman da Motarsa yazo.

Na farfado sai dai na Farfado cikin natsuwa kamar ba ni ba Tunda kuma na dawo hayyacina Mijina nake tambaya mamaki ya cika su Ummi Anty Habiba tace"Alhamdulillah...Alhamdulillah"
Adda Sadiya sai ciwon ciki ta fara Guduwa saboda Tsoro,duk ta Firgice Ummi sai Fada take mata meyasa bata bi Habiba ta koma cikin gida ba Tunda tasan bazata iya zama ba,Ita dai sai sharan hawaye ga Tausayin Hamma ga Tausayin kanta Hakika Rai ya tsorata kuma ya Jiggata.

Sai bayan da muka yi sallar La'sar wajen Biyar na yammah sannan matar mallam ta leko Dakin da suka sauke mu tace mallam na mgana,Gabadayan mu muka tashi ban da Adda da bata da wani karfin jiki,Muna shiga Dakin ido na sai akan Saifudden dake zaune Dafe da kansa da yaji Tunda ya farka yana dan Damunsa ammh yaji sa sarai Kamar yaro dan karami Duka wani nauyin jiki ko na zuciya sun sakesa.

Tunda na shigo na gansa na nufesa ina fadin"Saiff"
Shima a kasalance ya Dago Cikin wani yanayi yana kallona da Sauri ya mike duk da kansa na saramai ga jikinsa ba Dadi kamar an yi mai duka kowani gabar jikinsa ciwo yake yi ammh haka ya mike jikinsa na rawa yace"Muhi"
Cikin wani irin zumudi da Muradi mai girma da gudu na Nufesa cikin Rauni na fada mai Lokaci daya ina Sakin kukana cikin shesahekan murya nace"Ina ka tafi ka barni..Ina kaje na daina ganinka"
Yana Kamkame da ni kamar wani zai Rabamu yace"Ina nan Muhi ba in da naje..Ina tare dake daga yanzu har zuwa Numfashi na na karshe"Kara shigewa jikinsa nayi ina jin wani kewa na tasomin daga kasan raina.

Gabadaya baki su kawu suka saki suna kallon mu cikin mamaki Ummi kuwa Hamdala take yi a fili tana Dauke kwallar Farinciki.

Mallam Surajo ya kallemu cikin wani yanayi kafin yayi mirmishi yace"Kun yi mamaki ko..?

Ai daman ita shedaniyar ita ke sauya mata mijin nata in ta gansa sai taga kamar zai Cutar da ita ne..Yanzu kuma da ikon Allah mun yi mganinta ta kuma tafi kenan har Abada ma"aurantan zasu Cigaba da Rayuwaarsu har Abada."
Kawu yace"Mallam ka na ganin bazata Kara Dawowa ba..?

Mallam Surajo yace"In sha Allahu nace bazata kara dawowa ba..Sai dai Su rike Addu"a da Azkar da ikon Allah bazata kara Dawowa ba"
Gabadaya aka saka Hamdala Umarni ya bamu da mu zauna agaban sa muka zauna muna rike da juna kamar mun ji Labarin za"a rabamu.

Ya Habibu ne yace"Yanzu mallam shikenan ba wata matsala..?

Mallam Surajo yace"Ko akwai ba mai yawa ba ne..In bata dawo daidai ba ku maidata asibiti in sha Allahu komai zai zama Daidai."
Kawu ya gyara zama yana fadin"Mun gode kwarai mallam ya saka da alheri..Abun sadaka mallam nawa zamu ba da..?

Mallam Surajo ya girgiza kai Lokaci daya yana fadin"bazan karbi komai Daga gare ku ba..Ai alfarman Baba mallam kuka shiga..Na bari fa gabadaya Saboda shi na amince na Karbe ku kada ku Damu duka an zama Daya dukkan ku nan yan"uwana ne don Allah nayi kuma wajen sa nake neman Lada"
Gabadaya suka amsa mai da godiya da Fatan Alheri Saifudden nesa Tunanin sa ya tafi kamar a mafarki yana Tunanin abun da ya faru yana ji kuma alokacin yana gani sai dai abun kamar a mafarki yazo mai Kawu ne ya Zunguresa yana fadin"Saifudden kayi mai godiya"
A yanzu kam ya iya Hada ido dashi Cikin Sanyin sa yace"Mun gode Allah ya saka da alheri"
Mallam Surajo yace"Bakomai sai ku rike addu"a Allah ya kare Tsaremu"
Dakai ya amsa masa cikin Gamsuwa Kawu ya kallemu yana Fadin"Sai me ya Rage..?sai mu haraman Tafiya kenan.

Ko..?

Mallam Surajo yace"bakomai zaku iya tafiya..ammh inn kuka koma gida kada ku rike mai matarsa ku kyale su suje su gina wata Sabuwar Rayuwar"
Ya Mujaheed ya zaro kafin yace"na dauka sai an ga yanayin sa kafin ta koma din.?

Dariya yayi irin ta manya kafin yace"Nace muku ba matsala In sha Allahu bazata Dawo ba..Baku yarda dani ba ne..?na sa Allah acikin Lamarin ina da yakinin zai kara sakata tayi nisa da su in sha Allahu"
Kowa ya gamsu da Jawabin sa an fara Godiya da bankwana ya kalleni ina makale da Hannun mijina cikin barkwanci yace"Ke Saifuddeen din naki guda nawa gare ki..?

Kowa sai ya koma yana kallona ni ma shi nake kallo ammh na kasa mgana Ya Habibu yace"ai dukkanmu
mun zata shi ne ma ke ta bata matsala ashe bashi ba ne"
Mallam Surajo yace"Shi ai Musulmi ne kuma basarake ne..Sannan Bibiyar ta Ahali ce gabadaya..!
Chapter 117 · 0% Book details