← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 144

Sashe 100

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Chan saman kaina naji muryansa yana Fadin"Tashi kije kiyi alwala mu yi shafa'i da wuturi sannan mu dora da Sallar Godiya ga Allah tunda mukayi aure bamu samu daman yin wannan Nafilar mai albarka da ake so kowasu ma'aurata su gabatar da ita ba"
In da zai saurara dakyau da har karan yadda wani miyau mai karfi ya wuce ta makogwaro na zai ji sai dai ina ya riga yayi gaba har ya shimfida abun Sallah juyowa yayi ya sake kallona ganin ina nan a inda ya Sauke ni Cikin mamaki yace"Muhi"
A tsorace na kallesa sai yasha jinin jikinsa da Sauri ya kariso gabana ya durkusa yana Fadin"Muhi me ya faru ne naganki wani iri..?

Ganin yadda ya Rude ne yasa na Kakaro mirmishin da sam bashi acikin zuciya ta na Dora saman Fuskata kafin nace"Bakomai daman zen ce maka ina da alwala ta"
Mikewa yayi Lokaci daya ya mika min Hannunsa in da zai lura da kyau hannun nawa har rawa yake sanda na mika masa ya kama sai yaji gumi ya jika Hannun nawa Cikin wani yanayi yace"Kin tabbatar da kina Lafiya kuwa Muhi..?

Kai na gyada masa cikin son Tabbartawa ba domin ina lafiyan ba Yana rike da Hannuna har gaban alkibla sannan ya sakeni shi yajamu Sallar ni dai gani nan ne kamar na Mutu kamar ina Raye jikina yana min wani yam..yam kamar dai bana cikin Hayyacina bazan iya bada Labarin yadda Sallalolin nan suka Gudana ba sai dai na san daga karshe ya Juyo ya Dafa goshi na yayi addu'a sannan Daga karshe ya roka mana zaman Lafiya da Rayuwa mai inganci da zuru'a Dayyiba har ya gama ban iya cewa Amin ba sai shi ne ya Fahimci haka yasa ka Hannu ya girgizani ganin yana ta mgana bana jinsa a firgice na kallesa idanuwana sun yi Luhu Luhu kamar wacce ta sha wani abu Cikin Nazarina yace"Muhi baki da lafiya ko..?wani abu ya faru ne ban sani ba..?

Shuru nayi kafin nace'Lafiyata kalau me ka gani..?

Cikin dauriyar da na Tattaro ma kaina Domin haka kurum nake kallonsa yau kamar bako a wajena ai nayi islamiya nasan mai wannan sallar tasa take nufi sai bai ja da Nisa ba ya warware kama kafaduna yayi duka da Hannayensa yana Fadin"Muhi ina so mu zama daya..Nagaji da gujema kaddarata na dawo domin na Tunkareta ne"
Cikin mamaki na Kallesa kafin nace"Wata kaddara kenan..?

Kai tsaye yace"Kaddaran da ta sa na kasa mai da ke mace..Kaddaran da ta saka muka kasa zama abu daya'
Sai kaina ya Daure cikin wani nace"Ban ga ne ba..?

Kamar bazai yi mgana ba sai chan yace"Me yasa baki taba tambayanta Dalilin daya har muka kai wadanan wattanin ban taba neman Hakkina na aure a wajen ki ba?

Ban yi kaurin baki ba nace"Na Dauka ba ka ra'ayi yanzu ne duba da yadda auran namu ya kasance"
Mirmishi yayi irin wanda bai kai zucci ba ya mike tsaye yana kokarin Tadani Tsaye na mike ina kallonsa Hancina ya lakata yana Fadin"Kece baki taba nuna min ina da Damar yin hakan ba'"
Sai naji kunyar mganarsa na Sadda kaina kasa ban ce komai ba kara Dago Habata yayi yana fadin"Uhm baki ce komai ba..!?

Dakyar na iya cewa"To me zan ce?ai kasan ni Gonar ce ka in ka nema bazan hana ka ba"
Cikin jin Dadi yace"Da gaske muhi..?to na nema ina fatan za"a bani Dukkan Dama"
Gabana na fadi nace"In sha Allahu"Cikin jin Dadi ya Rumgumeni yana Fadin"Ina sonki Muhi..Zan fada miki komai bayan mun kasance Hakikan miji da mata"
Ni dai daga Lokacin bana ma iya jan Numfashina Dakyau saboda Karatun ne ya sauya,shi ya zaremin hijabin jikina ya Haura dani Saman gadon ya fara Budirinsa jikina ba inda baya rawa shi kan shi yana jin mazarin da jikina yake yi ya Dago yana kallona ai ba yau ya saba tabani ba bai taba jina Cikin wannan yanayin ba ni kuma Tsoro ne ba kuma Tsoron yau zan zama mace ba wani Tssro ne da ban san Daga ina na Same shi ba Daga kasan raina dai yake fitowa har gangar jikina ta Karbi Abun.

Kallona yayi ido cikin ido kafin yace"Are u ok Muhi..?

Kai na gyada mai alamun ina Lafiya sai kawai ya cigaba da Shagalinsa ajikina ina jinsa yau ko Karfin taimakamai bani dashi,Bakina ya kama yana min wani irin sumba da Sai da naji abun tsakiyar kaina Lokaci daya Hannayensa na kara kaina agangar Jikina na Fara jin Dadin yanayin kamar wacce wutar Lantarki taja Haka na fara jin wani Zafi zafi Daga saman kaina,Bakina dake cikin nasa naji Harshensa kamar Dutse Hakoransa naji kamar sun zama Dogaye suna kokarin Samun mafaka a Fatar Bakina Idanuwana suna Runtse ne sai naji Hannayensa da kumbuna suna neman nitsewa cikin Naman jikina Haka nake jin zafin na Ratsani kuma ikon Allah na kasa Bude ido na ballatana na iya yin wani motsi Sai da naji duk in da ya tabani ajikina kamar An Doramin wuta ne Saboda Zafi da azaba sannan farcensa in ya Tabani sai naji sun nutse cikin Naman jikina azaba mai suna azaba haka nake ji na kasa Motsi domin ya damke bakina da naji Harshensa ya koma kamar Dutse ina jin hakoransa da suka koma Dogaye suna Kara kaina cikin bakina suna sukana wani abu ya Tarun min a baki wanda ya kasa wucewa ina so na Ture sa ammh na kasa Saboda ji nayi wani uban nauyi a saman kaina kamar an Doramin Dusen kufaina.

Ina jin yadda jikina ke karban azaba da Radadi ammh bani da mafita sai ta Allah duk iya kokarina na kasa Motsi da Hannuna kamar wacce aka wanchakar haka na jini nayi sama na watsar da Saif dake saman kaina na koma na Buga bayana da Katifa ji kake Jagab na koma na kwanta shi kuma yayi gefe chan.

Ina jin ya sauka akaina kamar wacce na Dawo daga Duniyata na Bude ido na akwai haske tar acikin Dakin Wulgawa nayi na hangesa yana kokarin karisowa gareni sama sama naji muryansa yana fadin"Muhi'
Tashin Hankalin da ba'a saka masa rana sai na hango hannunsa daya ke kokarin kamani Kumbunansa Zaro zaro kamar zai cakamin su ajikina kamar yadda naji Lokacin dayake Tabani ai da wani irin karfin da ban san ina dashi ba sai ganina nayi na Dirko daga saman gadon ina ji yana kiran sunana ban tsaya ba Sai cikin Tiolet,Ina zuwa na Durkusa na Fara Zubar da abunda ya tarun min acikin baki na Cikin Firgita da wani irin Tsoro naja baya har ina Faduwa Saboda Razana...

"Jini"
Na fada da dukkan karfina bakina da Zuciyata da jikina suka Hade suna rawa Lokaci daya Saif daga bakin Kofar Tiolet din naji yana Fadin"Muhi me ya faru ne..?

Jin muryansa yasa na juya ina fadin"Jini...Jiiiiiii...Nniiiii
Mgana ta makale ne sakamakon ganin ban ga Fuskar Saif ba sai jallabiyan jikinsa kawai nake gani sannan kansa Gashin mace ya Rufe tun daga sama har kasa bana iya ko ganin Fuskarsa ammh yana zuromin hannun sa da akaifanan dogaye kuma muryansa na Kiran sunana"Muhi.."
Muhi.

Ban taba shiga irin wannan tashin Hankalin ba na Tsure na Firgice na Fita Daga Hayyacina na Tsandara ihu mai karfi acikin Tiolet din na kamkame jikina waje daya ina wani irin kuka numfashina na Fita Dakyar Na riga na gama sarewa da Rayuwa kawai naji Hannu a saman jikina Muryan Saifudden yana Fadin"Muhi.."
Lokaci daya yana kokarin jawoni Jikinsa idona a runtse na Buge hannunsa da mugun karfi ina Fadin"ka rabu da ni..Ka kyaleniiii"
Lokaci daya na bangaje sa ban gazan da bansan ko ya iya rike kansa ba da mugun gudu na Fita daga Tiolet din ko gani sosai ba nayi garin gudun ceton rai na fita falo na buge goshina da Bango ammh ban tsaya ba Ina jinsa shima ya Biyo ni da gudu yanq Kiran sunana gudun da nake yi kamar na ceton rai ne sai da na dangana da Dayan bedroom dina mai Falo na Rufe kofar sannan na Sulale jikin kofar ina wani irin kuka ina jin sa yazo jikin Kofar yana Bugawa yana Kiran sunana Lokaci daya kuma Wata irin Dariya da sai da Dakin da nake ciki ya amsa da wani irin amsa kuwwa Dariya ce irin mai kyakyatawa din nan sai na rasa ina zan saka kaina na Toshe kunnena ina wani irin kuka kamar zan mutu Saboda yanayin da nake ciki Daga Lokaci ban san kuma in da kaina yake ciki ba Suma nayi da ban Farka ba sai asuba Lokacin ina ji ana ta kiraye kirayen salla amasallatan kusa damu ina Farkawa Cikin wannan yanayin da muryan Saifuddeen na fara cin karo da na Wasila..

Yana fadin"Muhi don Allah ki bude kofar nan ki fadamin me yafaru"
Wasila kuma har da kukan ta tana Fadin"Anty don Allah ki bude Uncle ya Damu nima na damu"
Ina bana ma wanu jinsu domin Kunnena Muryansa kawai yake hangomin da yanayin da na gansa jiya baya na Fara ja ina sakin kuka kunnuwana na Toshe ina Fadin"A"aaaa..."
Da mugin karfi duk sai Hankalimsa ya tashi Daran ranar runtsawa ba wanda yayi ita kanta Wasila yadda yake Bugamin kofa ne ya tada ita ya Birkice Dakinsa kamar yayi hauka bai ga Spare keys din gidan nan ba yana Tunanin suna gidansa na Kaduna.

Yayi magiyar Duniyar nan naki Bude kofa sannan suna jin yadda nake raira wani irin kuka cikin Firgici da Fitan Hayyaci.

Dakyar ya iya yin alwala yayi sallar asuba shi kanshi yayi wani zuru zuru,Wasila ya bari ta zauna kofar Dakina yayi ta neman wayar ya Habibu bai samu ba,Da asuban nan Bama ya Tukasa zuwa gidanmu a Kofar gida suka Hadu da ya Habibu da Sani da jiyan nan ya Shigo gari,Suna ganinsa sai dai gabansu ya Fadi Dawowarsu kenan Daga masallaci Sani na rike da Hannun Yaron wajen Ya Habibu mai sunan baba,Tun kafin su tambayesa Dalili ganin yanayinsa ya isa ya Fassara musu ba Lafiya ba.

Hankalin ya Habibu ya tashi jin Halin da Saifudden yace sun kwana Jiya aciki sani da baisan kwanan zencen ba Hankali tashe yake fadin"Me ya faru da Muhibba din ya habibu.?
Chapter 100 · 0% Book details