← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 144

Sashe 136

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wacce aka kira da Amina ta saketa Lokaci daya tana bangajeta Ta wuce gaban Hajiya tana Fadin"Hajiya kinsan ban sauya Hali ba..Mata tana gayan ba Dadi zan yi mata rashin Mutumci"
Hajiya Nasara tace"to kun dai girma kuna da gab da jikoki da Surukai"
Amina ta yi Dariya ta Buga cinya kafin tace"Wai waya ga Amina da Suruki zai ga Biya uba"
Gabadaya muka yi Dariya kallonta kawai nake yi Hadaddiyar mace ce Doguwa Fatar ta goge kamar yar kasar maroco,Tana sanye da Wata Doguwar riga irin ta larabawa har da yanen su na saman kai,Hakorin makka guda daya a abakinta daya gama Haska bakinta in ta yi Dariya Aminenen dan mallan kenan an girma an zama manya mata She is now 35 ammh kamar yar shekara ashirin tana nan a Yar shillanta.

Hajiya ce ta katseta da gabatar mata damu ta Gaida su Ummi cikin Ladabi Hajiya ta nuna mata ni Lokacin nagaman shan mganina Amina tayi Dariya tana bani Hannu Lokaci daya tace"Assalamu alaiki ya Ukti"
Nima sai na bata Hannu Lokaci daya ina amawa Amina ta rike Hannuna tana kallo kafin tace"Labarin ki ya rigaki zuwa wajenmu..Hajiya ta bamu labarin ki kamar ba gobe..Jinki yafi ganinki wlh gaki mai kyau dake kinsan bana iya barin mgana acikina Haka Amina sa"idu take ina Fatan baxaki damu ba..?

Ina mirmishi nace"Ko kadan kada ki Damu"
Amina na jinjina kai kafin mu saki Hannun juna,Ina ji Hajiya na Fada ma su Ummi Diyarta ne sannan surukarta ce matar Babbar Danta dake Madina Haba shiyasa gabadaya Harshenta ya karye da Larbaci ashe chan suke zaune.

Zuwan Amina sai Hira ta tsinke a tsakaninsu Har da Hamida Hanne dai na ciki tana waya Adda da Anty Habiba an samu nayi sai faman tambayan Amina suke yi labarin Madina kusan Amina da Hira ta karkace baki tana ta zuba Hajiya kuma suna ta Hira da su Ummi ne ni kuma sai dai nayi mirmishi ko Dariya.

Muna cikin wannan Hirar ne sai ga wasu mata Biyu sun shigo daya Gajera ce sosai sai dai Farace sai ta bayanta Farar balarabiya mai kyau da Zati ni kaina kyanta ya shigeni
Har kasa suka duka suna gaida su Hajiya tare da su Ummi.

Hajiya ta kalle su tana fadin"Baku jin mgana bazaku daina Tukin Dare ba ko Sakina..?

Wacce aka kira da Sakina gajerar ciki tayi Dariya kafin tace"Ba nisa fa Hajiya..Kuma tun dazu muka so fitowa baki nayi daga chan gida Dutse"
Hajiya tace"To ai yayi kyau..Kuna Lafiya..?Saratu ya bakunta ai kin zama yar gari yanzu..?

Hajiya Nasara tace"Ta zama Tuni Hajiya Tunda ta fara jin Hausa"
Gabadaya akayi Dariya Hajiya ta kara gabatar da su a matsayin ya"yanta.

Ummi dai ta kasa yin shuru ta kalli Hajiya Nasara tana fadin"Wai kowa sai hajiya tace danta ne..ya'yan gida
duka ya"yanta ne..?kowa sai da yayi Dariya Hajiya tayi dariya batace komai ba Hajiya Nasara ne tace"Hajiya kenan mai maida da'n wani nata..Ya"yanta shidda ne agidan nan ammh ita uwar kowace..sannan yaran Sa"idu duka namu ne ba bambanci Wadanan kuma matan Umar ne Abokan zaman Amina ne Sakina da Saratu"
Ummi da inna nata jinjina kai ni kaina sai da na jinjina karamcin Hajiya,nan aka hadu ana ta Hira abunda na Lura Amina nada kamewa Tsakaninta da abokam zamanta ba gaba da zaman lafiya a tsakaninsu
ammh ba Sakin jiki,Sai dai suna shiga Hirar mu sama sama Musamman ma Sakina ita balarabiyar ba ta wani jin Hausa sosai wani kalmar ma in ta fada sai Hamida ta gyara mata.

Har Hanne ta gama waya ta fito Amina na fadin"Hanne ki rage son miji wlh Bini bini ki shiga Daki kina wani make murya kina fadin Amunullahi na"
Gabadayan muka saka Dariya Hanne ta Rike kugi tana fadin"Eh
din har na kai ki som miji..Da yanzu zai kira ki jikin ki na rawa zaki daga Kina Hubby ki kuma juya yare don kada aji abunda kike fadi"
Amina tayi shewa kafin tace"To baki ji kirarina na ba ne Amina badai ta Mutum ba sai ta Allah..Ni fa NA FITA ZAKKA(Littafin daya kun sa Labarin Amina da Ahalin baba mallam)
Ko agidanmu ko amakota ko makaranta ko agidan mijina a ko"ina ni zakka ce mai ja dani sai dai ya fadi warwarsa"
Dariya su Hamida suka saka Har da Shewa suka bata hannu suka Tafa Hankalin su Hajiya baya kanmu Sakina da Sarood sai dai sukayi mirmishi ko mganarta ta fada sun san gaskiya ta fada gaskiya ne a gidan mijinta ma ita zakka ce hakama a zuciyarsa ma itace zakka.

Nan fa Hira ta kwace afalon nan Hanne na Caccakan Amina tana ramawa Hamida ma nayi Adda Sadiya tace"Amina an yi miki Taron dangi"
Amina tace"Kyale su taron yuyu ne Duk zan iya da su"
Gabadaya sha'awa suke bani Daga gani shakuwar su daga Allah ne.

Muna cikin Hirar sai ga mazan sun shigo gaida su Hajiya kafin su wuce gidan su su kwanta..

Na gane Biyu dai Saboda mun gansu a waje akwai wani mai kwarjinin cikin su kamar Baba mallan sai dai shi ba Tsoho ba ne sannan suna shigowa Dakin ya Dauki shuru yana kuma mgana naji muryansa shine mai zakin muryan da ya bada salla da mangariba.

Naji mamaki Lokacin da Hajiya Nasara tace shine Danmallam Dake Madina babba a ya'yan mallam Ina ji tana bayanin Sauran ban wani ji sosai ba Amina nake kallo yadda take sakarmai kallo kasa kasa har da Dagamai gira shi kuma yana gaban Hajiya a sace yake kallonta yana mata Hararan wasa.

Hajiya ce tayi mai bayanin mu ya kara gaishe da su Ummi su Anty Habiba suka gaishe shi har da ni ya amsa cikin Sakewa yana fadin"Muna tare da su mazan yanzu muka bar su su kwanta muma zamu je gida mu kwanta Hajiya"
Hajiya tace"Dakyau..ammh ka rika yi ma matanka fada suna dai Tukin Dare"
Yana yar dariya yace"In sha Allahu Hajiya mu kwana lafiya"
Hajiya tace"allah yasa..Sakina ku tashi ku bisa Mamah tace min nan yace ta kwana sai su Hanne sun tafi tukunnah"
Ai da Sauri ya kalleta ya balla mata Harara ita kuma tayi Dariya har da Dagamai gira sai ta bani Dariya sai da na Dara Salau salau ya fice sauran suka bi bayansa Su Sakina suka yi mana Sallama suma suka fice Hajiya nasara ma tayi mana Sai da Safe ta fita Su Amina kuma sukajani zuwa Falon kasa Hajiya tace"Bi su Muhibba zaki ji dadin zama da su duk Shakiyaai ne basa ji"
Dariya mukayi gabadaya Ina ta mamaki
n ina sauran yaran ashe wasu suna Shashen Hajiya Nasara wasu kuma suna Gidan Alhaji Sa'idu Anty Hadiza na fama Kusa da Dakin Hajiya muka shiga da yar akwati na tunda nan zamu kwana dukkanmu.

Dukkammu sai da mukayi wanka muka saka kayan barci ni kasa nace zan kwanta Amina tace"Miye haka..?

Baki da matsala fa mu yan gida ne"
Ina ji ina gani suka Turani kan gado na kwanta ni da Hanne Hamida da Amina suka shimfida bargo saman Cafet din Dakin Hanne tayi Tsaki tana Fadin"Kamar ba Dakuna agidan. ?

Amina da gidanki fa wlh ya Danmallam nasan bai ce ki kwana ba kina mugunta ma yayanmu Tun shekaran jiya kike gidan nan kin ki tafiya gidanki"
Hamida tace"Ina gani da Hajiya tace zata kwana sai da ya juyo ya kalleta Cikin mamaki ammh kamar ta Shanyesa ya kasa mgana"
Hanne tace"Daman ai an ce yana Tsoronta kuma wlh na yarda Ya dammallan duk muzuransa na banza ne indai yana gaban Amina ne"
Hamida tace"Ai masu suna Amina sai Allah ga shi nan Nasaka Amina ina Fama..Hanne kema naki Aminar duk Halin mai sunan nata suka kwaso"
Hanne na Dariya tace"Ai shiyasa ya jafar da ya Nasir sukace duk wanda ya sakama yar su suna Amina wlh sai sun Kara yanka rago sun sauya..Sun zan wahalan da suka sha da Shegiyar nan ina zasu kara samun wata Amina jidalin"
Hamida ta kwashe da Dariya tana Fadin"To ai ga Iman nan Ta ci Uban Amina ma a jidali in tazo gidan nan Hajiya tace Addaban yara take yi da Tsiyataku kala kala"
Hanne tace"Wlh Allah yasa ba a kasar nan suke ba da nan garin take da har Hajiya da mallam sai ta gana ma azaba"
Ni dai ina jinsu na kasa yin shuru nace"Iman din yar wajen Amina ne..?

Hanne tace"Ita ce yarta ta Biyu..Shekararta sha uku ammh ta addabi Mutane sunan Hajiya gareta Zainab Dazu fa sai da Jawaad ya yi mata jan ido ta daina dukan su Yusuf'
Cikin Mirmishi nace"Har naji ina sonta tana ina..?

Hanne tace"zaki ganta da Jawaad ya mata tsawa ne ta tafi falon Baba mallam..Aba kuma ya lallashi Amaryansa inaga tana wajen Anty Hadiza basa shiri da Hajiya Saboda Rashin jinta"
Nayi mirmishi nace"Yarinta ne zata Daina in ta girma"
Amina duk na jin mu bata saka mana baki ba wayar ta ke Hannunta tana kira kuma ba"a Dauka ba Hamida Dake gefenta tace"Allah yasa kada ya Dauka"
Amina ta sauke wayar a kunnenta tana Fadin"To sai me in yaki Dauka..?

Amina ce fa ina zamam zamana zai zo yana min yar murya.."
Hamida tace"Daman ai tsoron ki yake ji."
Amina tace"Wlh Hubby baya jin Tsoro na..Nasan dai yana sona..Kuma yana Tsoron jidalina..Ammh baya tsoron nayi ba daidai ba ya tsawa tar min Dalilin daya sa ban bisa ba Tun muna chan na gayamai in kuka zo nam zan sauka,ai bani kadai garesa ba yana da Wasu matan"
Hamida tace"Bai kamata ba Tunda bai baki izini ba"
Amina ta juya baya tana Fadin"Kanki kuma ake ji Hanne"
Ni dai tun ina jin su sama sama Har barci ya kwashe ni sai da asuba na iya tashi Tare muka bi jam"i sallar asuba dukkamu ni dai ban koma ba Saboda da Wuri Ummi tace zamu koma.

Ko kafin takwas na Safe mun yi wanka mun karya in kaga ganni Cikim su Amina kamar mun shekara tare,mun saba cikin kwana Daya ko da mukaje gaida su Ummi suma har sun shirya,Har Daki naje na gaida Hajiya tana ta sakamin albarka bayan Ta Rumgumeni.
Chapter 136 · 0% Book details