← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 144

Sashe 2

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Huhuhu!Huhuhu!
****
DA asuba ma da ta tashi ita ta tashe shi,kin tashi yayi ya koma barci kasala bata sake sa ba,Ganin haka yasa ta janye bargon da ya shige aciki yana juyowa kafin yayi mgana ta rigasa da cewa" A cikin alamomin Munafuki akwai rashin Samun Sallar asuba da isha"i acikin jam"insu"
Tana gama Fadin haka ta sakar mai bargonsa ta juya ta tada sallar.

Ya dade yana kallonta yau ma kalamanta sun gama kashe mai jiki kenan shima Munafuki ne?tunda bazai iya Cewa yaushe da yaushe ne yake samun Sallar asuba acikin jam"i ba.

Tana sallar ya tashi ya shiga Tiolet ya Dauro alwala yazo ya sauya riga ya saka Farar jallabiya ya fice zuwa masallaci duk da lokacin ma an Tada sallah ita kuma tana Idarwa Sai tayi azkar sannan ta mike ta gyara gadon ta kwashe Filon da Blanket din nasa ta ninke ta aza mai bisa gado ta fice Kitchen ta iske Ummi da Zeeha suna aiki bayan sun gaisa taso ta karbi Firan Doyan hannun Ummi ta hanata Cikin Fara"arta take fadin"Kinga Muhibba bar shi maza kije ki shirya Yaro ya ce min da wuri zaku tafi yana da shiga Office da Safanan."
Muhibba bata yi mamaki ba sanin Daman ai ba komai yake fada mata ba Sai kawai ta juya ta koma Dakin Ta Fara Sauri Sauri ta shirya kafin ya Dawo kayan da zatayi amfani Dashi ta Dauko ta zube su kan gado ta Daura babban Towel din Da ta gani acikin Tiolet din ta shiga wanka har ga Allah bata san ya Dawo ba ta saki jiki Sanin sai wajen bakwai na Safe yake shigowa shiyasa ta fito kanta Tsaye har sai da ta kawo tsakiyar Falon Sannan ta gansa Tsaye ya juya baya yana mgana a waya da wani irin Uban Sauri ta juya zata koma Tiolet din kafarta sai ta Bige kujeran madubi sai ta Duke tana Fadin"Wash Innata..!

Sai alokacin yasan ta fito ya juyo a Hankali Lokaci daya yana Sauke wayar daga kunnensa karaf ta Dago kanta suka Hada ido hudu gabadaya Jikinta yana Bude ne Towel din iyakarsa Rabin Cinyarta gashi ta Duka hatta Shatin mamanta ana gani.

Jikinta sai yafara rawa Saboda kaifaffun idanuwansa da ya kasa Dauke su daga kanta kamar mayen karfe haka yaji yana jansa wajen kallonta Kirjinsa na bugawa wani Irin Feeling din da bai taba ji a kan mace a Farke acikin Hayyacinsa ba,yaji yana Tasomai Shiyasa ya kasa Daina kallon kowani kusurwa na jikinta Jikinsa na wani irin Yim..Yam..!

Kamar ana mai susa haka yake ji har Tafin Kafarsa na Motsi.

Ganin haka yasa ta dukar da kanta Jikinta na rawa ta mike duk da Kafanta na mata zafi haka ta juya tana Dingishi gudu gudu ta koma Cikin Tiolet din gabadaya albarkatun bayanta na Hadewa suna kuma Rabe kansu sai da ta shige karar Rufe Kofar Tiolet din yasa ya Sauke wani Gwaron Numfashi"Uhmmmm!"
Kamar irin wanda abu ya sarkeshi haka yaji iskar D'akin tamai kad'an Dakyar yake iya Shakan Numfashi Shiyasa shima ya Fice Daga Dakin da Sauri yana Dafe kansa dayaji ya Saramai
****
Fitowar su kenan Daga Meeting da His Excellency a office dinsa ya bar duka wayoyinsa yana komawa bai bi ta kan wayoyin ba sai ya fara duba Fayel din Daukan malaman da zasu sake yi a Jahar ta kaduna Sai yaga wayarsa na Haske a kasalace ya Dago wayar sunan Ummi daya gani Sai da gabansa ya Fadi Ras haka kurum yaji Tashin Hankalin da bai san Dalilinsa ba.,Da Hanzari ya Daga kiran Da Fadin"Ummi ina kwana."
Dagachan bangaran cikin wani yanayi Ummi tace"Kana Ina ne..?

Kai tsaye yace"Ina kaduna Ummi wani abu ne ya faru..?

Sai da ta sauke ajiyar rai sannan tace"Eh wani abu tabbas ya faru ammh ba"anan ba a chan zaria ne.

Da Hanzari ya mike da wani irin Firgici Sai da ya Ture Takardun Gabansa suka zube bai sani ba acikin ransa ya ambaci sunanta "Muhi"
A fili kuma cikin wani yanayi yace"Muhi Ummi me ya faru da ita..?

Ummi tace"Ka kwantar da Hankalinka nima yanzu Innar Habibu ta kirani
take gayamin jiya basu runtsa Da Daddare Muhibba ta balle ta gudo gida,Sai kuka take da ihu tana Zabura tana Surutai da Sambatu."
Kai ya Dafe cikin mamaki kafin yace"Me kenan Ummi..?

Cikin Natsuwa tace"Abun kamar GAMO tayi yaro."
Gidan nan naku ina Tunanin akwai aljanu ni a Tunanina ita kuma Innar Habibu tace aljanin nan nata mai zuwa mata da Suffarka ne ya ke neman Razanata Saboda ya hanata zaman aure"
Ba wani jin Ummi yake sosai ba Shi ba ya,ce bai aminta da Aljanu bane har yanzu yasan akwai su ammh Siddabarun su ne bai sani ba Cikin Sautin muryansa yace"Yanzu ta na Ina..?

Ummi tace"Tana chan gidansu an kira malamin nan da yasan Laluran ita Muhibban suna
kanta suna mata Rukiya nima gobe ina tafe naga Halin da ake ciki"
Bai gama jin bayani
Ummi ba ya katse kiran saboda Tsabar Rudewa kadan ya Rage ya fadi wajen fita daga Office dinsa.
*****
Gani yake kamar Bama baya Sauri Kafin su iso zaria Bai san adadin Zagin daya riga kunduma su bama ba gani yake kamar basu taka motar dakyau ba Domin bai saba Tukin babban Hanya da sai ya sauke su ya Tuka kansa kila sai ya ma isa a kan Lokaci.

Motar bata gama Tsayawa a kofar gidan su Muhibba ba ya Balle murfin mota ya Daka Tsalle ya fice yau ko neman izini ko sallama haka ya Fado gidan da Bakaken Takalminsa Rufaffu bakake na Fata ya fada Dakin kawai sai dai ganinsa sukayi Tsaye a kansu Wurga ido ya dinga yi ya dai ga Inna da Ya Habibu sai Anty Habiba sai Wani malami da D'alibansa suna zaune wacce suka zagaye ya kai kallonsa sai da yaji kamar zai mutu Muhi dinsa ya gani Gardawan maza Uku su Dannenta wani na mata karatu a kunnenta wani na Uban Fesa mata ruwa kamar mahaukaciya.

Wani irin Sufa yayi sai gashi A gabansu Da mugun Hanzari ya saka Kafa ya shure dayan da ke rike da ita Sauran suna ganin haka suka Saketa Muhibba dake kuka ka shirban ta kyalla ido ta hangosa ai sai ta mike da wani irin gudu da kuka ta Nufesa ta Fada Jikinsa Cikin kyarma abun takaici kanta ba Dankwali ta kusa ma yaye Sikat din jikinta..

Karfaffan riko yayi mata kuka take kamar ranta zai fita cikin Fitan Hayyaci take fadin"Saif zata zata Kashe ni..Ka tafi dani ka boye ni"
Cikin tashin Hankali ya riketa fadi yake"Gani nan muhi..Ba abunda zai faru dake ni SAIFUDDEEN garkuwanki ne"
Mallam Haruna bai dakata ba ya cigaba da karatunsa cikin suratul Jinni Lokaci daya wani al"amajiransa ya watsa wani mgani acikin Rushin wuta dake cikin kasko a gabansu nan da nan Hayaki mara Dadi ya Turnike dakin dukkansu suka Fara Tari Saifudden yaji kansa na juyawa ganin yadda Muhi ke neman sikewa yasa yayi Fatali da Kaskon da takalminsa yaje ya Daki garun dakin ya tarwatse wuta yayi nasa gefen Mutane ma sukayi nasu barayin cikin tashin Hankali.

Inna Dake kuka ka shirban na ganin Halin da Muhibba ke ciki ta kasa mgana Ya Habibu ne ke fadin"Kayi a hankali fa"
Jajayen idanuwansa ya watsa ma mallam Haruna kafin yace"Mahaukaciya kuka mai da min mata..?wannan hayakin ai shi kan shi Cuta ne kada ku kara matsowa kusa da Matata ba in ba haka zan tarwataa komai yanzu nan"
Yadda yake mgana yasa ba wanda ya kulasa har ya Daga Muhibba cak suka fice Daga Dakin da ita Inna zatayi mgana Mallam Haruna ya Daga mata yana fadin"kyale shi..yanzu na Fahimci wani abu koma meke Faruwa yana da karfaffan alaqa da shi mijin nata"
****
Kallo Daya mallam Surajo yayi ma Muhibba bai kara ba sai dai ya D'aga ido ya kalli Saifudden kallo na sosai da sai da ya Tsargu cikin muryansa mai Taushi yace"Bawan Allah ya sunan ka?

Saifuddeen yace"Saifuddeen"
Gabansa na Faduwa Fat!Fat!Mallam Surajo ya murmusa kafin yace"Cikakken sunanka nake so naji"
Saifuddeen ya Runtse ido kafin yace"Dr.Saifuddeen Conel.Salahudden Lere"
Jinjina kai yayi bai kara mgana ba Inna da Ummi suka kalli juna Kawu ya kasa Hakuri ya gyara zama zai yi mgana kenan ya Daga mai Hannu Lokaci daya yana fadin"Ba sai kayi tambaya ba zan amsa muku tarin tambayoyin ku"
Sai da ya kara natsuwa sannan ya Dago kansa yana Fadin"Ba aljanu ajikin wannan yarinyar taku..Sai dai Naga wani al"amari ajikin wannan bawan Allah nan na kusa da ita"
Gabadaya sai kallo ya koma kan Saifuddeen cikin mamaki Ummi tace"Wani al"amari ne Mallam..?

Mirmishi yayi kafin yace"Zata bayyana kanta yanzu nan kun zo inda Aljani bai isa ya boye kansa ba komin karfinsa komin ikonsa..

Zata bayyana.

Zata fallasa komai...

Abubuwa zasu warware kansu.

Duk ita take aikata komai ba"a sani ba muguwa ce sannan bakar Kafura ce ita ta kusa haukata wannan yarinyar ba Domin ita din mai yawan Ibada bace da Tuni ta HAUKATA TA!
****
Waye kai..?

Wata kakkausar murya tayi mgana"Sunana SAIFUDDEEN Kuma ni ba Mutum ba ne ina Daga cikin jinsun Aljanu"
Miye hadin ka da wannan baiwar Allah..?me yasa kake Bibiyarta..?

Ko zaka cutar da ita ne..?

Shuru dakin ya Dauka na wani Lokaci kafin wata iska ta taso ta Tirnike Dakin kamar Hayaki Hatta da Tafin Hannunka baka iya gani Cikin abun da bai fi mintina goma ba sai Dakin ya washe gabadaya su Ummi sun Tsorata Adda Sadiya jikin Mijinta ta makale tana makyarkyata shi kan shi Mujaheed din jikinsa rawa yake yi sai dai ya Daure ne kada Adda Sadiya ta Fahimci ya Tsorata.

Abun da ya bama kowa mamaki Daya sa suka Zabura gabadayan su ban da Saifuddeen dake zaune gaban Mallam Surajo shi da Muhibba Yana kamkame da ita kamar wani zai kwace mishi ita.

Cikin wata irin murya wacce daga jinta sai jikinka ya yi sanyi in ma bai Fara rawa ba yace"Ni ba mai cutarwa bane..Amana ce Sannan Alaqa ce mai Girma Tsakanin Mahaifina Abu Gaddaz da mahaifin Muhibba tun Lokacin yana Raye..Aminci ne da Girman alkawari Tsakanina da wannan Ahalin"
Zabura Muhibba tayi Daga jikin Saifuddeen idanuwanta na kallon sa Ta nuna sa da Hannu cikin Rawar murya tace"SAI..F..DDEE...NN...!
Chapter 2 · 0% Book details