← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 144

Sashe 137

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daganan gabadayan Falon Mallam Hajiya ta rakamu muka gaishe shi Nan muka ga su kawu suma sun shirya har gaban Maallan naje ya Dafa kaina yana ta sakamin albarka Hajiya tace"Mallam sai an zo kawo maka jika zan ce..Ko Umhum Domin Muhibba dai har da Rabo..'"
Kunya duk ta kamani mallam kuma nata saka albarka sai alokacin su Amina suka san ina da ciki.

Har Saifidden sai da suka gaisa da su muka karbi Lambar juna dukkanmu da Saka ran zamu yi zumumci
Har gidan Alhaji Sa'idu min shiga mun gaisa,Baba mallam ya saka aka Bamu kwai kires ashirin Daga gidan gonarsa su kawu nata Godiya.

Mun firfoto sun yo mana Rakiya sai ga Danmallam shi da wani abokinsa da naji sua Hanne na cemai ya Aliyu ina ganin sa sai Hararan Amina ya ke yi ita kuma tana rike kunni alamun neman afuwa.

Hajiya ta bamu Turamen zannuwa da Turaren wuta,Hajiya Nasara kuma ta bamu Humra ni ta hadamin h harda Hijabii guda biyu,Sai godiya nake yi hakika mun ga karamci naga ya"yan su Amina duka barin ma Imam kai yarinyar nan kamar na saceta Fara tas da ita Kamar Diyar larabawa ga gashi Sannan bakinta cau sai larabci Sai dai suna jin Hausa da Turanci ammh Larabcin yafi yawa na Dauketa na Rumgume itama ta rike ni Ta kalleni ta shafa Kumatuma tana Fadin" Anty mai kumatu sunanki"?

Gabadaya sai da mukayi Dariya nace mata"A"a sunana Anty Muhibba"
Tayi dariya tace"a chan madina ina da kawa sunanta Hibbana"
Nayi mata Dariya hausan nata ba"a cika ganewa ba sai ta saka Turanci.

Allah ya Hada jinina da na Imam ganin Farko har da Dagamin hannu da zamu tafi.

Kamar yadda muka zo haka muka koma,Mu daganan sai dai muka bi su ya Habibu zaria,muka Dauki Wasila Muka biya Lere muka sauke Baffa Hashimu Bamu Tsaya ba muka dauki Hanyar kaduna
Su Adda Sadiya sun rigamu isa su Ummi ma sun dauki Hanyar Abuja kawu ma dai sun Dauki Hanyar gaya zuwa Dare dai kowa ya sauka gida Lafiya dagani har Saif akwai gajiya ajikin mu kwana Biyu muna barcin gajiya wasila ita tayi ta gyaran gidan
Mun yi waya da su Hajiya da Amina suna ta godiya Amina tace min Iman ta Dame su da Anty mai kumatu aka bani ita muka gaisa naji ina son na Haifi ya mace nan take na fara addu"an Allah ya bani mai albarka.
*****
Bayan wata Daya.

Mun koma Asibitin gaban Dr.Anandi ya dubani da Sauran gwagwaje ya tabbatar mana da cewa na fita Daga Hadarin ciwon kwakwalwa ya sauke ni kan dukkan wasu Treatment Ma'ana na warke sai dai fatan Allah ya kyauta na gaba.

Cike da Farinciki na Rumgume Saif ina kuka Lokaci daya da Dariya ina Fadim"Am now ok Saif"
Shima cikin jin dadin ya min kiss a saman goshina Lokaci daya yana Fadin"Congratulation My wife"
Cikin natsananin Farinciki nace"Thank you Forever"
Dr.Anandi ya kallemu cikin Farinciki kafin ya mike muma muka mike ya bama Saifudden hannu yana Fadin"Congaratulaton Mrs and Mr Saifudden Lere"
Ya damke hannun sa Yana fadin"Thank you sir..Tanque Very much"
Ya jinjina kai Lokaci daya yana Fadamin"Most wlcm"
Da wannan Farinciki muka sauka gidan Inna kowa yaji Labari sai yayi Hamdala Inna sai da tayi Sadaka saboda Nuna farincikinta Sani na makaranta ya na fama da Final Exam na kirasa na fadamai yayi ta Hamdala afili da Sarari Mutanen gaya da Lere duk sun samu Labari kowa sai fatan alheri haka ma Ummi ita da Inna bansan wanda yafi wani Murna ba.

Shikensn Tunda na samu Lafiya sai Saif ya maida Hankalinsa kan cikin jikina,Domin cikin na da wata Biyar na Fara zuwa awo awani asibtin kudi dake kaduna watarana in Saif na Office ni nake tuka kaina Wasila ta rakani naje wani Lokacin kuma shi yake kaini ya Dawo dani.

Hakika duka zukata sun samu natsuwa Hankula sun kwanta sun kuma natsau waje daya..da Saif yaso Wasila ta fara karatu wannan shekarar ammh ganin ina kara nauyi yasa yace ta cigaba da Lesson din kafin nan gaba sai da ta shiga ni nace mai ya sakata kawai ba matsala..haka kuwa akayi makarantar kudi ya sakata an gwada ta kuma sosai ta bada mamaki Jss2 aka sakata in tata fi Tun Safe sai Hudu na yammah take Dawowa,Bama ko Tim ke kaita su Daukota ni kuma ina aiki kamar su shara da goge goge sai dafa Saukakkan abinci duk da ina da girma ciki ya fito ya faramin nauyi ban zauna ba Saif yayi ta min fada ni kuma sai na nuna mai motsa jiki ne kada ya Damu ina Lafiya sannan hakan zai taimakamin ko don cikin jikina.

Sani ya gama jarabawarsa ya Dawo Gida sai jiran sakamako da Calling bar Sani iyayi fa ya karu sai wanda yaji kuma ya gani yazo ya Dubani muka yini muna Hirar zumunci.

Cikina na da wata Bakwai Adda Sadiya ta Haihu ta kara Samun ya mace aiki akayi mata wato C.S,Mune yan gari da ni akayi ta Hidima Mama Zuwaira tazo ta zauna da ita Ummi tazo barka ta koma,Su Laala suna nan da Zeeha sun zana Gama jarabawar su ta Fita Majeeda ke chan Abuja ita yanzu ta shiga SS3 Din mutanen zaria da lere duk sun zo barka,Suna kuma sai bayan kwana sha hudu sannan akayi Taron Suna yarinya taci sunan Ummi Zaliha suna kiranta Ummin ta.

Anty Habiba ne da Anty Zeenatu suka zo suna suka kwana daya suka koma chan Lere kuwa Inna Talatu ne da goggo Atika suka zo sunan kwanan su Biyu suka koma Daga gaya kuwa Umma karama ce tazo suna ita Umma babba barka tazo.

Ni kaina kwana na Biyu agidan Adda Saboda Zirga zirga yasa Saif yace na zauna sai taro ya watse maijego na nan Lafiya ita da angon karni Mama zuwaira zata zauna sai jikinta yayi kwari Saboda Wasila na zuwa makaranta sai Saif yace mu tafi da Zeeha Laala sai ta zauna ta kama ma Mama zuwaira kuma ma dai Adda na da yar aikin shiyasa aikin bai da yawa.

Majeeda na Abuja tana ta cizon yatsa,an sha Shagali bata nan taso tazo Ummi ta hanata saboda suna Text a makaranta.

Tunda cikina ya shiga wata na takwas,Ummi ta fara yi ma Saif mganar gida zan je gaban Inna na Haihu shi kuma bai ce komai ba.

Ammh ni kaina ina son naje gida na Haihu nayi jegon gata akula dani Sosai sai dai bazan ce komai ba sai abunda Saif ya yankemin Domin shine Duniyata.

Shiyasa ban yi ma Inna mganar ba ammh sun yi da Ummi nima Anty Habiba ta fadamin da muka yi waya wai Inna tace sai dai naje Gaya chan nayi jego wajen Goggo Fa"iza ko Goggo Barira ni ko nace gwara nayi agidan mijina shiyasa ma ban kara jin na damuna ba jin inda Inna ke shirin Turani haba ina Dalili gwara ma su Baffa suna kula damu ammh su goggo Barira kan su kadai suka sani duk abunda ya faru sai dai waya itama sai ta kama bamai jin su ma.

Ban kara jin mganar tatashi ba Sai da jikin Babani ya matsa har an kawota asibitin bakori,Inna ta tafi tana Jinyarta,Saif yamin mganar ina son naje wajen Inna na haihu naki mgana Saboda nasan Halin Inna Tsab zata aikata abunda ta fada ganin naki mgana sai ya kyaleni.

Sai dai gabadaya shirin haihuwata ba wanda bamu yi ba Daga kayan jaririn da zan haifa har Kayan da zan ci Fitar Suna,Mun gama mgana da Saif in na koma Zaria na Haihu wasila zata koma Gidan Adda ta zauna Saboda makarantarta.

Ni dai nayi gum da bakina ban ce ma Saif komai kan mganar zuwa gida Haihuwa ba Tunda Inna har Lokacin bata Dawo ba Duk da an sallami Babanin suna gida a chan Bakorin.
*Janafty*
*SFD0049*
*Amnaf_sudanese _collection*
*Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401*
*Ki biya ki karanta cikin salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba, kada ki karanta min littafi sannan kada ki yada'min shi don Allah pay N500 via jamila umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*
Ban kara tsinkewa da Inna da gaske take yi abunda ta fada ba sai da bayan kwana Biyu Sani ya kirani mu gaisa cikin Hira yake fadamin Ya Habibu ya tafi Bakori ya Dauko Inna da Babani Saboda Inna tace gabanta zata Dawo da ita domin taji Dadin kula da ita Sannan zata rika kaita asibitin Abu zaria,ganin Likita.

Cikin mamaki nace"Topah wai meke damun Babanin ne..?

Bayan hawan jini ta na da wata cutar ne..?

Sani yace"Eh mana an ce Ciwon hanta take fama da shi kuma yaci jikinta har tana Zubar jinin Habo ta baki Ai Inna bazata gane ba ne Gawa kawai zata Dauko ammh Babani kam Lokaci take jira"
Cikin Yar dariya nace"Kai sani ka da dai ka bari Inna taji wannan mganar"
Da Sauri yace"Allah na tuba nima ai ba giyan wake nasha ba Ballatana na fada agabanta Yadda Inna ta Damu da Ciwon Babani ban ga wani abu a gabanta ba bayanshi"
Cikin aminta da mganarsa nace"To wai ina matan ya"yanta..?

Ina su Goggo Shatu suke da sai Inna ta Dauko Babani Daga Bakori zuwa Zaria?

Sani yaji gulma sai ya gyara zama yana Cemin"Kati na fa ya kare kinsan abunka ga Sabon lauya Hajiyar Gwamnati kirani ki sha Labari"
Ina Dariya na kashe wayar sai na kirasa,yana Dauka yace"Ni na zata ma kudin zaki turomin kafin ki kira".
Chapter 137 · 0% Book details