Sashe 111
Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ina cikin wannan barcin na mganin Asibitin muka isa har garin gumel da misalin karfe sha daya na safe da wasu Mintina Dayake sunan babban malamin ba boyayye ba ne kaf garin na Gumel ko yaro ko babba duk wanda ka ambaci sunan Sheik Yunus Abdurrahaman bazanga ya san shi,Shiyasa tambaya daya suka yi duk da daman kawu yace ya Taba zuwa Sau daya,Daurin auran yaran gidan sai ga su a Layin gidan BABA MALLAM.
Tab likafa taci gaba jama"a Domin Layin da ke da kasa yanzu Shimfide yake da Lafiyayyar Kwalta sannan ga Solar mai bada Haske na sama Tunda ga Farkon Layin har karshe wanda ke taimaka wajen kara haska Titin da kawata shi in Dare ya shiga.
Alhaji Sa"idu bai fita gidan Gona ba Ranar Duk da ta kama asabar ne Saboda Zuwan Alhaji sunusi da baki kamar yadda suka yi mgana Lokacin da Moticin suka ci Taya a kofar wani makeken gida wanda kaf anguwan shine Dabam da zubin Tsarin sa yasha Bambam da kowanne.
Eh lalle arziki yaci uban nada kunga yadda gidan Baba Mallam ya koma..?
Gabadaya an sauya tsarinsa kamar ba shi ba ne muka sani Shekaru goma da sha suka gabata yanzu gabadaya ya koma Gidan Bene na zamani mai kyau da Tsari uwa uba masallacin nan ya koma kamar a kasar Madina domin ko"ina gilasai ne sai wanda ya gani kawai.
Alhaji Sa"idu Gusai shi ya fito Tarban su a kofar gida Jama"a kun ga ABA..?
Duk da girma ya kamasa Domin Gemunsa da Kansa furfusa sunfara Lullubesa ammh kuma kallo Daya zakayi mai kasan Likkafa taci gaba yayi kiba ya kara fari da murjewa na alamun Hutu da jin Dadi sun gama Ratsa Rayuwarsa gaba da baya.
Gabadaya suka sauko Daga motan ni kuma cikin mota suka barni Saboda ina Halin barci ammh su kansu yaba Tsarin wannan gidan suke ya mujaheed da ya Habibu masallacin kawai suke kallo sun zama kauyawa.
Sai da Ya Mujaheed yayi mgana cikin mamaki da al'ajabi yace"Kai kun ga wani Masallaci.kamar a Saudiya..?
Ummi da Anty Habiba da Adda Sadiya suma kallon suke yi suna kara yarda da mganar Mujaheed.
Saifuddeen dai baya cikin Natsuwarsa bai Tsaya kare ma ko"ina kallo ba Zuciyarsa da Tunaninsa suna wajen Muhibba fatansa kawai Allah yasa adace Matarsa ta samu Lafiya.
Kawu ne suka Tarbi juna da Alhaji Sa''idu cikin girmamawa da Mutumtata juna na abokan da suka Dade suna kasuwanci shekaru sama da talatin sun Saba Kasuwancin Dabobbi.
Kawu gidajen yabi da kallo cikin mamaki yace"Alhaji Sa'idu ni fa na Rude..Sai naga kamar gidajen nan sun sauyamin da anguwan gabadaya ba haka na san shi ba san da na taba zuwa Daurin auran nan ba"
Alhaji Sa'idu na Dariya yace"Eh gaskiya an samu sauye sauye Dadama..Wanchan Lokaci ba kwalta a saman Layin sannan gidajen ba Gidan sama ba ne aikin bai Dade ba"
Kawu yace"Haba ni dai nace
Kai waje yayi kyau Allah yasa albarka.
Alhaji Sa"idu yace"Ameen ammh cewa zakayi Allah yayi ma yaranmu albarka duka aikin su ne ba namu ba.
Kawu yayi ta saka albarka su Ummi na gefe har nan Alhaji Sa"idu ya kariso aka gaggaisa sannan yayi musu Jagora zuwa cikin gida har sun shiga Haraban gidan ya kalli kawu bayan ya Dakatar da Tafiyarsa Lokaci daya yana Fadin"Alhaji Sunusi ina ita mara Lafiyar kuma..?
Kawu yace"Tana mota barci take yi Alhaji Sa"idu.
Juyowa yayi yana kallon su Ummi kafin yace"Haba ta yaya zaku bar mutum mara Lafiya a mota ita Kadai..?
Maza Don Allah a Daukota a shigo da ita cikin gida'
Kafin ma ya Rufe baki Saifudden a wajen ya juya yaje ya Bude mota ya Daukoni Cak ya Saboni saman Kafadarsa sai da suka gan sa Dauke Dani Alhaji Sa"idu ya kallesa kafin yayi mgana kawu ya rigasa da Fadin"Shi ne Mijin nata Saifudden yaron kanwata gata nan Zaliha"
Ya fada yana nuna Ummi Alhaji Sa"idu ya jinjina kai yana fadin"Masha Allah mu shiga ciki"
Yana gaba suna binsa a baya har Zuwa Kofar Falon da zai sada su da Falon gidan gabadaya gidan ya Sauya Cikin Tsari da zamani.
Suna shiga ya fara kwala kiran sunaa"Hadiza."
"Hadiza"
Da Sauri wata mata ta fara Saukowa Daga saman Step cikin Takun natsuwa Lokaci daya tana fadin"Na"ama Megida gani nan"
Ganinsa da baki yasa ta kariso da Sauri bakinta har Kunne tana yi musu maraba Saifudden ya kallah yana Fadin"Sauketa saman kujera kada ka gaji da Tsayuwa"
Ya fada yana nuna mai Daya Daga cikin Royal chair din dake Falon,Nan take saifudden ya Saukeni bayan ya gyaramin kwanciya Anty Hadiza Daman da mayafinta ta fito sai washe baki take hakorin makka na kyalli Ba domin ace taje makka ta saka ba kawai Saboda Sha'awa ne,Allah na Tuba ai bata san sau nawa taje tayi Umra da Hajji ba.
Sai faman yi ma su Ummi Maraba take yi cikin Sakewa Alhaji Sa"idu ya kalleta yana fadin"Bakin da nayi miki mgana zasu zo ganin Baba mallam.
Ne.Ga mara Lafiyar nan ki kula da matan..Mazan kuma bari na kai su Shashe na su huta a kawo abun karyawa kafin su gama Baba Mallam ya Fito sai mu karisa da su."
Cikin Ladabi ta amsa mai yayi gaba wajen wata kofa bayan yace su kawu su bi bayan sa nan suka bar su Ummi Kwalama wata yarinya kira tayi sai gashi ta amsa ta fito cikin Ladabi da Duka tana gaida su Ummi kafin ta juya tana fadin"Gani Mama."
Cikin Ladabi tace"Kin ji Saukin ciwon cikin..?
Hawa'u da y'a ta ke wajen Alhaji Sa"idu Diyar kanwarsa ce da suka hada iyaye ya Daukota daga gusai Saboda gidan duk babu yara Jawaad na ibadan chan yake jami"arsa.
Cikin Ladabin ta tace"Eh ina shan mganin nan da kika bani naji sauki"
Jinjina kai tayi kafin tace"Dakyau..Muje ki taimakamin mu hada ma baki abun karyawa akwai wasu afalon Aba din ku"
Da Toh ta amsa kafin tatashi tayi gaba itama ce musu tayi bari tazo tabi bayanta Ummi dai tayi Tagumi,Anty Habiba da Adda Sadiya ne ke mgana kasa kasa,Suna kare ma Falon kallo suna kara yabon kyau da Tsari na komai da ke cikin Falon.
Muhibba kuma na kwance har alokacin bata farka ba,Ba Dadewa sai ga yarinyar ta shigo da Farantin kayan karyawa kafin kace me an cika gabansu da duk abun bukata na su Kawu kuma Anty Hadiza ta shigar musu dashi da kanta kafin ta Dawo Wajen su Ummi tana Fadin"Ku sauko ga abun karyawa..Don Allah ku saki jikin ku nan duk gida ne fa"
Ummi ce tayi yake tana fadin"Hakane mungode Allah ya saka da alheri.
Anty Hadiza ta amsa da Ameen tana kallon Muhibba dake kwance tana barci cikin Tausayinta tace"Allah Sarki itace mara Lafiyan ko..?
Ummi ta gyada mata kai a gabanta ta Duka tana Fadin"Ai daga gani barcin ma na wahala take yin sa.Allah ya baki Lafiya gata yarinya ce matashiya"
Ummi tace"Wlh ai barcin ma da Taimakon kwayoyin asibiti ne take yin su ba Domin haka ba,da yanzu ba zaman Lafiya sai ihu da Fizge Fizge"
Anty Hadiza ta yi wani Sukuku cikin wani yanayi kafin tace"Wayyo..Allah ya takaita wahala"
Su Ummi suka amsa da Ameen kafin ta barsu suka sauko nan kasan Cafet suka fara karyawa sama sama ba mai mgana yunwa domin ta zama Dole ne ba babu mai kallon wani abu,Da suka gama Hauwa'u tazo ta kwashe komai ta kai kitchen Ummi na faman mata Sannu.
Anty Hadiza da ta hau sama ta Sake Saukowa suka fara Hira da Ummi Sama sama duk akan Laluran Muhibba har su kawu suka Fito ganin haka yasa su Ummi suka mike Alhaji Sa"idu yace yana kallon Matarsa"Ina fatan sun gama kalacin?
Anty Hadiza tace"Eh sun gama Megida"
Cikin gamsuwa yace"To sai mu karisa gidan Baba mallam din"
Jin haka yasa Saifuddeen ya karisa ya Daga Muhibba cak ya Dorata saman Wuyansa daidai Lokacin da Anty Hadiza tace"Abban Amina in taho muje..?
Yana kokarin fita Daga Falon yace"Taho muje"
Gabadayan su suka rankaya suka fita Daga gidan sai gidan Baba mallam Da kowa yasan yana jikin gidan Alhaji Sa"idu ne,shashen Baba mallam an kara kawata shi ya koma babban Bangare,Daman sun yi mgana ba Dadewa shi yace bakin su kariso duk da Daman tun jiya da ya shigar mai da mai da mganar zuwan su kawu kallonsa yayi lokaci daya yana Fadin"Ban da abun Sa"idu ni ina bada mganin Aljanu ne..?
Alokacin Aba kai ya sosa yana fadin"Baba mallam a dai duba koda da yar shawara ne kila za"a samu mafita"
Bai yi mai gaddama ba Domin Sa"idu yana da wannan girma a wajensa ko kashi ya kawo mai bazai ki karban su ba ballatana Mutane masu kima da Daraja.
Lokacin da suka shiga Falon Baba Mallam sai da suka raina kansu Suka kuma Fahimci wanchan Gidan basu ga komai ba Falo kamar aljannar Duniya,Saboda kyau da Tsaruwa Katon Fali ne mai Dauke da set din kujeru har guda Biyu mabambanta Kalololi.
Kowa natsuwa da Salama ya kamasa Sanda suka zazzauna gaban wannan Farin Dattijon mai kamala da Zati,Wanda Farin gemu gabadaya suka Rufe Gemunsa da Sajensa Hade da gashin kansa zaune yake a saman kujera mai zamam mutum Biyu sanye da Alkyabba da Rawaninsa Da Wata Sanda a hannunsa Domin Tsufa da Ciwon kafa yasa ba ya tafiya sai da Taimakon Sanda gefensa Hajiya Babba ce Cikin shigar kamala da Daraja ita kamar shekaru basu ja ba Sai dai tayi Rama Saboda Hawan jinin da ya sako ta gaba kamar bazatayi Rai ba.
Kallon su kadai ya isa ya sanya maka wani natsuwa uwa uba ga kamala da Hasken addini daya sanya musu wani kwarjini gabadaya kowa cikin Ladabi da Kankantar da kai ya gaida Baba mallam da Hajiya Babba suka amsa cikin Fara"a da Sakewa irin nasu.
Alhaji Sa"idu kusa da kafafun baba mallam ya zauna ya tankwashe kafa Baba mallam ya kallesa kafin ya Dago yana gyara Gilashin da ke karfafamai wajen ganinsa yana fadin"Sai naji kamar muryar D'iyata ko Sa"idu..?
Hajiya Babba Dake gefe tace"Gata nan kusa dani mallam.