← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 144

Sashe 29

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na tabbata Dalibai ma da iyayan yara zasu ji Dadin in har shugaban wannan makaranta yazo kuma ya kalli duka shirye shiryen da zasu gudanar"
Director Musa yayi shuru sai chan yayi mgana cikin Turanci mai kyau da Tsari yace"Tanque for u Advice Uncle Hafiz.!"
Hafiz ya gyada kai kafin ya zauna D.Musa ya gyada kai kafin ya gyara zaman gilashin dake idonsa yace"Nima zan so hakan sai dai nayi mgana dashi har yanzu bai ce min komai ba,ammh zan cigaba da mai mgana nagani ko zai amsa zai samu zuwa..Mutum ne mai sabogigi da yawa ba Lalle ranar mu same ba, sai in bashi da wani Uzuri ammh kamar yadda kace zan Turamai katin gayyata da korafinku Insha Allahu zai ki amsa gayyatar ba.!"
Kowa ya gamsu da jawabinsa Domin gabadaya kowa ya dauka mai makarantar,yan"uwana juna suke da D.Musa Tunda ganin shi ke rike da makaratar Bisa gaskiya da Amana,Abunda basu sani ba shi kanshi D.Musa bai hada komai dashi ba kawai Jajircewansa da iliminsa yasa ya Daukosa ya damka masa Amana shi kuma yayi alkwarin rike masa makarantarsa Bisa Amana duba da Tarin Alherinsa garesa.

Daya bayan malaman ke mikewa suna bada nasu advise din kuma D.Musa baya watsa musu kasa a ido Sakatariyarsa na rubuta jawabin kowa Cikin Mutuntawa Muhibba kamar bazatayi mgana ba ganin ba wanda yayi mganar da ke ranta yasa ta Daga hannu aka bata izinin mgana Tunda ta mike Anty khadija da suke Zaune waje daya da Anty Usaina suka Bita da kallo tana jin Khadija na Fadin"Uwar iyayi."
Ita dai ki ta kansu bata bi tana Rike da Batula har Lokacin mgana ta fara Bayan tayi sallama ta fadi sunanta da ajin datake koyarwa duk da ba kowa ya Damu daya gabatar da kansa ba.

Su Anty Usaina sai tabe baki suke yi suna mgana kasa kasa ita bata ma san sunayi ba ta fara jawabinta mgana tayi kan me zai hana tunda an shirya Dalibai zasu yi Quiz da Games,to me zai hana su yi Debete da Drama shima Sosai yana taimaka ma yara sannan ta tabbata abun zai kayatar.

D.Musa yayi mirmishi sosai yake yaba Natsuwar Muhibba ga Hankali ga Hazaka Cikin jinjina mata ya karbi Mganarta sannan yace ya dorata kan Abunda ya Shafi Debete din da yaran zasu yi shi kuma Uncle Hafiz da wani Uncle James su duba bangaran Drama din,Sai aka fara tafi ana mganganu irin su Anty Usaina yan bakinciki kamar su fashe Uncle James ne ya mike yana fadin shi da ba bahaushe ba ta ina zai shirya drama..?

Uncle Hafiz ya bashi amsa da ai Drama din guda biyu ne In Hausa and In English,Dariya akayi gabadaya kafin acigaba da Tattaunawa sai karfe Hudu saura aka tashi Meeting din Kowa ya Dauki Maltina dinsa da aka raba awajen muhibba ajaka ta saka nata saboda bata cika cin wani abu ba indai ta baro gida ba.

Bata tafi ba saboda Uncle Hafiz yace ta jirasa sai da sukayi mgana Da D.Musa sannan ya fito suka fito alokacin duk malaman sun watse har su Anty Khadija.

Tare suka fito har bakin Titi Tare suka Hau Kekenapep saboda Uncle Hafiz shima yau Dogawara zai je gidan yayar mahaifiyarsa da bataji Dadi zai Dubata,gidanta na farkon Layi ne ita kuma nasu Muhibba sai an shiga Ciki shi aka fara saukewa suka rabu yana jadaddamata ta samo Topic gobe zai tayata Tsara komai kada taji komai,tayi mirmishi ta Dagamai hannu da Fatan ya gaida mai jiki.

Hudu da Rabi ta shigo gida a gajiye Inna ta samu a tsakar gida tana Shanya wake,Dakyar muhibba tama Inna Sannu da gida ta shige Daki...

Inna ta bita da kallo tana Fadin"Auta yau ina kika tsaya ne..?

Lokacin dawowarki ya wuce baki dawo ba nayi ta kiran wayarki baki dauka ba na kira Habiba tace min baki biyo su Siyama ba."
Muhibba Daga cikin Daki tana Kokarin Cire Rigar Jikinta Tace"Inna muna makaranta fa..Meeting mukayi.

Inna tace"Meti kuma..?

Muhibba tace"Taro inna mukayi Akan Taron da makaranta zata gudanar.

Inna tace"Ni dai nace to Allah ya taimaka."
Muhibba data fito ta amsa da Ameen,Inna ta Dago tana kallonta Karamin zani ne ta Daura kafafunta duk a waje buta ta sura tayi makewayi Inna ta bita da kallo tana Fadin"Auta ban hanaki daura wannan Falen zanin ba..?Na fada miki yayi miki karami ki rika Daura wanda na baki din nan shine babba da zai rufe miki har kafunfunki.

Daidai sanda Muhibba ta fito bakin makwarara ta
tsugguna tana fadin"Inna to waye zai shigo...?

Inna tace"Ba domin haka ba sai ka kauce ma idon shedanu ke da yaushe ma kika Rabu da mai bibiyar naki..?

Ammh Taurin kai zai sa ki kara jajibo mana wani bala"in.."
Muhibba
data fara alwala tace"Allah ya tsaremu Inna..

Inna ta amsa tana fadin"Ameen ammh ki rika kiyayewa Auta.

Muhibba tace"To Inna Insha Allahu.

Sai da ta idar da alwalan sannan ta mike tana kallon Inna Dake ta Faman kara baza wake fari a kan Shararren Simitin dake shashen nasu.

Kallon waken tayi kafin tace"Inna An fara ciro amfanin gona ne..?

Inna tace"Eh mana ai kwanakin nan chan Yayanki ke tafiya kwana uku suna aikin wannan ma bai gama Bushewa bane ya kawo Zeenatu ta bazamai,batanan taje gidansu sai ni na karba na baza.

Muhibba tace"Inna ammh gonar Gabari bata gaya ba ko..?

Inna tace"Na gaya ai aikinta ya bada kila sai an gama duka mota zata kwasomai hatsin.

Muhibba ta jinjina kai kafin tace"Allah ya taimaka..Inna bari nayi sallah..

Inna ta amsa mata daganan ta koma Dakinta ta sauya zani ta saka Hijabi ta tada sallah sai da tayi Nafila sannan tayi sallar La"asar tana idarwa Inna ta shigo mata da abinci Taliya Jalop mai kifi Zeenatu ta Dafa kafin ta fita,taci kadan ta Kora da maltinan da ta zo da ita daga makaranta ta sauya kaya zuwa wata Doguwar rigar wani jan yadi Dakin Inna ta koma tana bata Labarin abunda ya wakana a makaranta ta karishe da Fadin"Inna Director musa ni fa ya wakilta wai na bada topic din gasan da yaran zasu yi,ni yaushe zan wani iya..?

Inna na ballan goronta tace'Kul kar na sake jin kince ina zaki iya in bazaki iya ba ai bazai zabeki ba ko ba sauran malaman ne..?.

Muhibba ta daga kai tace"Akwai Inna sannan Uncle Hafiz yace zai tayani.

Inna tace"kin ma ji..Hafizu ai dan albarka ne Dalilin aikin ku tare a makaranta sau nawa in ya shigo anguwannan yake zuwa gaisheni kuma bai zuwa hannu Rabbana ni da Farko ma har nayi Tunanin Sonki yake yi."
Muhibba ta tura baki kafin tace"So kuma Inna..?Tab ni wlh ba sona yake yi ba koma yana sona ni bai min ba.

Inna ta harereta kafin tace"Ai shikenan kin ma kanki ke ai banga wanda zai miki ba kowa kika gani kice baki so.

Muhibba ta mike tana kokarin fita Daga Inna tace"In ma wannan Aljanin kike jira Allah ya rabaku kenan har Abada,Sakarya kawai ina kika taba jin wani soyayya tsakanin mutum da Aljan ban da wannan Saifudden ban taba ganin kince wani ya burgeki ba..

Ita dai har ta fice bata ce komai tasan Halin Inna in ta fara Fadanta bata gajiya.

Dakinta ta shigo alwalan mangariba ce kadai ta fito da ita nan sai ga Anty Zeenatu ta shigo suka gaisa,Sannan ta shigo Dakinta tayi sallar mangariba ta zauna tana azkar bayan ta gama Ta Dauki wayarta ta Bude data ta hau WhaApps sakonnin suna ta shigowa Sakon Sani ne ya bata mamaki yaushe Rabon da yayi mata mgana tana Budewa data ga abunda ya rubuta sai da ta kusa dukawa saboda Dariya ga Abunda yace.

"Lalle ma yarinyar nan..Wai nan gaba kike dani...?

To ni dai ko a musulunci na fita Hakkin ki Assalamu alaikum."
Sai da ta gama Dariyanta sannan ta fita Daga sakon tasan abun sai yafi kudar da shi yaga tagani batayi mgana ba Sauran sakonnin ta dan Duba ta bada amsa sai dai abunda ya bata mamaki tun ranar da Abun nan ya Faru tsakaninta Sani Abbati bai kara kiranta ba,sannan bai kara mata mgana achart ba,baki ta tabe aranta Tana Fatan Allah yasa ya Hakura ne.

Sai da ta yi sallar isha"i ta koma Dakin Inna Lokacin ta wuce ta sameta tana waya da yan Gaya Goggo Naja tana Fadamata an saka Lokacin Bikin Autar ta Inna Firdausi,Ita dai muhibba ficewa tayi ta koma Shashen Anty Zeenatu ta isketa tana Firan doya ta karba tana Tayata tare sukayi girkin Souces din Doya ne za"a ci da Buredi ta Kira Ya Habibu zai zo dashi to bai ma kai ga shigowa ba ya aiko dashi Muhibba tare sukaci da Zeenatu da yara ta zauna suna kallon Gidan badamasi a tashar arewa sai goma ta baro Dakin ta koma Dakin Inna tana shiga Inna na zaune na shafa man Zafi ta Toshe Hanci Tana fadin"Kai Inna basai ki rika shafawa da rana ba kinsan na tsani warin man nan naki.".

Inna ta dago tana fadin"Ga Hanya ficemin daga daki ai ban kiraki ba.!

Muhibba na Dariya tace"Inna nice Auta..Autar taki kike kora ai sai yan Bakin ciki irin su Sani in sunji su rikamana Dariya."
Inna ta tabe baki kafin tace"Ayi mana ina ruwana.

Jin yadda ta amsa ne yasa Muhibba tasan Inna acike take,gadon ta karisa tana Fadin"Allah ya huci zuciyarki Innata...
kai tsaye Inna tace"Ameen.

A kufule ne sai Muhibba ta koma tana Toshe baki ta haye gadon Inna tana sosa bayan ta kafin ta mike ta cire rigar jikinta zani taso Daurawa ta kwanta ganin Inna na Hararanta yasa ta dauki Rigar Barcinta saman Sif din Inna ta zura doguwa mai taushi ta kama kanta ta saka cikin hula domin Inna fada take mata in ta kwanta ba Dankwali..

Zuwa washegari Inna ta Huce Tare ma suka fita Inna ta wuce gidan su Zeenatu zata
biyama Hajiya karima zasu Dubiyar wata makociyarsu ne aka kwantar a asibiti.
Chapter 29 · 0% Book details