← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 144

Sashe 92

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya Dawo da Kwalin Degree na hudu akan Na"ura mai kwalkwala wannan wani Fanni ne na Nasara acikin rayuwarsa,Yana Dawowa ya kwasheta suka tafi kaduna sai da tayi sati uku sannan ta Dawo shima Saboda makaranta na ranta ne da ace baya Ranta da Tuni ta bar wannan aikin koyarwa ko wata nawa zatayi bata je ba tana zuwa Cikin girmamawa kowa zai karbeta su Anty Usaina sun ga ba Riba sun kama kan su sai dai agaisa a sama sama.
******
*MUHIBBA..!*
Tun jiya da Saif ya koma Kaduna na Ke ji na sukuku kamar ban da Lafiya sai na Dauka ina kewarsa ne kawai Jiyan ma ban je makaranta ba sai yau din Tun da na dawo nayi salla na kwanta Ina barci sai bayan La"asar na tashi Duka gabbaina suna min ciwo ga wani kasala da Ciwon kai da naji yana Damuna Dakyar na iya yin alwala nayi sallah na Dade a wajen ban iya tashi ba,Wayata na jawo na Kira Saif bai dauka ba,sai na maida ta gefen gado na ijiyeta da Tunanin baya kusa da wayar in yazo kusa zai kirani.

Cikina na shafa Rabona da abinci Tun Doyar da na soya da Safe na ci kuma ta kare daman kadan na Soya sauran kuma Junaidu na kwashe mawa,Kuma bana jin shan Tea haka kurum naji ina sha"awar naci Danwake mikewa nayi na zare hijabin jikina da nayi salla da shi,Na fice zuwa kitchen yana nan Tsaf da shi,Domin kafin na fita sai da na wanke komai na goge shi sannan na Fita zuwa makaranta.

Ina da garin Fulawa ta sai na Saka kuka Kadan na jika kanwa na kwaba dashi,daman na kunna gas na Dora tukunya yana Tafasa na Fara saka Danwake na Daman shekaran jiya muka tafi ni dashi muka yi Cefane da Salat da kwai nake so naci sa bakina da Miyau na har tsinkewa suke yi kamar wata mai ciki.

Kafin mangariba na gama komai har Salat din na Hada na yanka kwai aciki Dafaffe da na Dafa,Ban bar kitchen din ba sai da na goge ko"ina na wanke kayan da na bata,Sannan na fita na koma Dakin mijina chan nake Rayuwata daman in baya nan in naji kewarsa t
a Dameni ko ban furta ba ni kaina na san Ina matukar kaunar Saif komai nasa mai kyau me classis da Unique,Wanka nayi na Dauko Rigar sa mai Dogon hannu na saka Fara ta kawo min har gwiwa sai na hadata da wani wando na Baki na jeans.

Sai da nayi sallah sannan na Saka Bakar Hulata mai Love a samanta na Fito Falo na kunna kallo Tashar arewa na saka duk da kallo ni bai cika Damuna ba,Na damu saboda har yanzu na kara kiran Saif bai Dauka ba na Fara Tunanin ina ya shiga ne haka..?

In dai yana Lafiya zai kira ni da Safe da yammah yaji Lafiyata haka kafin Barci ya Daukeni tare muke addu"am barci Sannam mu kwanta tare Dalibar da har ya zame mana jiki gabadaya.

Ruwa na Fara Daukowa da Maltina Daman ina da yaji na Anty Habiba ta aikomin dashi duk nazo na gama jera su,Daki na koma na Dauko mayafi na Mikama Junaidu nashi ya karba yana min godiya,Sannan ta koma cikin gida afalon farko na yada Hijabin jikina na koma Kitchen na niyyar na Dauko cooler da na saka Danwake na da Voul din da na Saka Salat dina.

Sai dai me..?

Gaba na ne ya fadi Ras!

Ras!

Ganin Danwaken da na gama wahaalar yi da Zakwadin naci ne watse a kasa An yi Daya daya dashi a Tsakar Kitchen din Salat din magashi nan a kasan Tayels kacha kacha,kamar irin an ci ma an Rage har saman cabinet din sai da ya baci da Danwaken da Salat din.

Kamar an dasa ni haka na Coge a bakin kitchen na kasa gaba ballatana baya mamaki da al"ajabi duk ya Rufeni ga Haushi da Takaici abunda yasa ban Firgita ba ganin Gabadaya Coloor din Danwaken ta rikota a kasa sai nayi Tunanin ta fado ne komai ya watse.

Kitchen din na shigo Allah yasa da Takalmi a Kafata Kugu na rike cikin jin Haushi nace"Garin sauri ne ban Ijiye cooler din da kyau ba kenan..?

Na fada kamar ina Tambayan kaina ammh abun mamaki shi karamin Voul din da na saka salat din yana saman Cabinet din kitchen kuma shima ya zube to in haka ne kenan ba Faduwa sukayi ba wani ne ya fado dasu..?

Tuna haka da nayi sai da gaba na ya fadi,Ras to in mutum ne ya fado da shi to waye ya yi min wannan barnan..?

Ita Kadai ne agidan nan Daga ni sai Megadi shi kuma aikinsa iya Bakin get ne,Ganin zan firgita kai na yasa na watsar da wannan Tunanin ta Duka ta fara kokarin Tsabtace kitchen din abun hau shi ma ko kadan babu duka ya Bare a kasa duk son ta da Danwake ranar bataji ba Duka ta share ta kai Bola Kwai ta soya tea din da bata son ta hada shi ta hada dai ta sha,tana bata rai Saboda takaici ma tana gama Sallar Isha"i ta shige Daki ta kwanta ta Nutse cikin blanket din Mijinta ta na Shakan Daddan Kamshin Turaransa mai Dadin kamshi,Sai chan ta fara barci ya kirata yana bata Hakuri sun je Dinner gidan kwamishinan Ruwa ne ya kara aure sai ya hada walima agidansa dake Kaduna.

Washegari ma kafin ta bar gidan sai da tayi Miya da niyar in ta Dawo makaranta,sai kawai tayi Farar shinkafa,Sai dai me..?Tana dawowa taga abun mamaki kamar na jiya haka ma haka na yau ya faru,Anyi Dama dama da Miya akitchen din da miyar ga Namar Rago din datayi miyar dashi nan kaca kaca a kitchen din mamaki ya kara kamata Ko tsayawa ma tayi wani Tunani ba ta yi ba Tsabtace kitchen din ta fara yi Taliya da kifi ta Dafa sukaci Miyace mai yawa zata iya kai mata Sati daya kafin ta kare.

Abun bai fara bata tsoro ba sai da aka yi mata irin haka sau hudu ana Biyar din ne ta Tsorata Domin cousscouss tayi Ranar jallop dinta da Kifi Daki kawai taje tayi sallar mangariba kafin ta Dawo ta nemi Cooler abinci ta rasa ta Duba ko"ina bata Har cikin Store Tana fitowa Falo taga Cooler a kofar Falo murfi yayi barayinsa bata kara Jin faduwar gaba ba sai da taga yadda aka rika Bin kujerun falon aka rika Sauke abinci abinci an yi Dama dama dashi har kan center table din dake Falon ta Daga kafa kenan taji ta Taka abu da sai da ya kwasheta zata Fadi Allah ya taimaketa ta rike bango ta kai kallonta taga abun mamaki abinci ne aka Bi layi dashi Har zuwa Cikin Falon Muhibba sai taji jikinta ya fara rawa Bata ko tsaya neman mayafi daga ita sai riga da sikat na atamfa da Dankwali ta kwashi gudu zuwa Haraban gida Lokacin Junaidu ya Zagaya,jin yadda ta kwalamai kira ne yasa ya fito a Firgice domin bai taba jin ta Kirasa haka ba yadda ya ganta ne yasa ya rude kasa ya Duke a gabanta yana Fadin"Hajiya allah yasa ba wani laifi nayi ba..?

Muhibba tana Haki tace"Don Allah wani ya shigo gidan nan ne yanzu..?

Junaidu ya Dago yana kallonta cikin mamaki kafin yace"Anya..?

Ai hajiya ba wanda ya shigo gidan nan bayan ke wani abu ne ya faru.?

Kanta ta Dafe da ya fara sara mata kawai sai ta juya ta koma cikin gida Junaidu ya bita da kallo shima sai hankalinsa ya tashi Bai taba ganin Hajiya ta fito haka ba kenan akwai matsala shima sai ya kasa zaune ya kasa Tsaye baya fata ace sakacinsa ne yasa wani abu ya faru.

A tsorace Muhibba ta Tsabtace Falon Wannan karon ta Firgita matuka,Ranar barcin ta Cikin Tsoro tayi shi,Abu kadan in taji sai ta Firgita in da Allah ya taimake ta Washegari Friday Saifudden ya zo mata Weekend,Kuma cikin ikon Allah har yazo ya tafi abun bai kara faruwa ba shiyasa ma bata gayamai ba ammh da Farko tayi niyar fadamai sai dai ganin bata da Hujja yasa bata ce mai komai ba Har yazo ya tafi sai dai yana Tafiya Abun sai ya Tsananta duk abunda zata ijiye shi in dai naci ne akitchen kafin ta Dawo ya Haramta gareta Zata zo ta iske a barna ta sa.

Abun ya isheta Ranar da taje gidan ya Habiba gaida Amir dinta Yayi zazzabin Hakori take fadamata abunda ke faruwa kai Tsaye Anty Habiba tace"Ni fa ina ganin baraye ne ko Burgaye ne suka shigo muku gida suma yan iska ne sun saba barna.

Sai taji mganar Anty Habiba ta zauna mata ranar kafin ta koma gida ta biya shago ta siya Gam din nan na kama Beraye na Littafi guda hudu ta tafi dashi gida ta saka Biyu a Store biyu a cikin kitchen Duk da ta Duba ko"ina bata ga ta inda Berayen da Anty Habiba take zargin su ne ba Domin ko"ina a toshe suke babu ta inda kwaro ma zai shigo ballatana beraye.

Sai dai bata sauya Tunaninta ba Bata so Abun kuma yazo ya wuce yadda take zato.

Sai dai abun nan har yayi kwanaki Hudu ko Kwaro bai sauka akai ba Sai kawai ta Dauke su ta zuba a Dusbin Ganin kuma bata kara ganin haka ba sai tayi Tunanin berayen ne da gaske kila sun gudu ne.

A wannan Satin ma Saif yazo mata Weekend Ranar asabar da yammah ya shigo garin daman Tun yana Hanya ya Kirata ya fadamata sai ta kasa zaune ta kasa Tsaye tana kokarin yi mai abun Tarba ta gyara gidan ko"ina da Sauran Dakunan suna tashin kamshin Turaran wuta ta shiga kitchen Tuwon Shinkafa tayi miyar agushi da Ganyen Ogun,wanda yaji Naman Sa da man shanu sai da ta gama komai Ta kwashe ta kai Falo ta Jera saman wani Faranti bata yarda ta bar shi a kitchen ba.
Chapter 92 · 0% Book details