← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 144

Sashe 71

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Data koma cikin gida ba Domin shawaran Anty Habiba na tayi mai girki ba sai domin cikinta Domin tasan in ma tayi baci zai yi ba illai kuwa Tea ya sha adaran daman itama kadan ta Dafa macaroni mai Kifi ita da su Bama,sai ranar yasan tana basu abinci Saboda ya fito Daga kitchen ya ganta ta shigo Falon da Lullubinta kaloonta yayi cikin mamaki ita kuma ganin haka sai tayi saurin cewa"Su na kai ma abinci Tunda ina Dafawa."
Bai ko kara kallonta ba da Mug din Tea a Hannunsa ya koma saman kujera ya zauna yana kokarin kunna Tv dake falon ita kuma Dakinta ta Shige aranta tana ajiyar rai kamar wacce taga abun tsoro.

Cikin ikon Allah washegari ma Lafiya lau tatashi,ita bata ma san baya gidan ba sai da ta fita mikama Junaidu abun karyawansu yace su Bama sun fita da Oga shi kuma cikin ABU suka shiga suna da Taro na Laccarorin B.A english,Dayake course dinsa yana son abun da ya shafi karatu shiyasa ya Samu zuwa bai dawo ba ssi bayan La"asar a restaurant ya tsaya yaci abinci kafin ya Dawo gidan ya iske Su Asma"u da Aisha sun kawo mata Ziyara suka gaisa sama sama ya shige Ciki Shi da bai ma san su ba.

Suma yana Dawowa suka yi shirin Tafiya,tayi tayi su zauna suka ki zama su kam bai ma san Tafiyar nasu ba ballatana yace a kaisu itace ta basu 1k tace su yi na Mota suka karba suna Godiya.

Washegari Monday Tun karfe bakwai ya bar gidan bayan ya bar mata kudi kamar wanchan karon bai mata mganar Direban dayace ba itama bata kara mai mgana ba,Kamar kar Ya koma Kaduna shikenan Mafarkinta ya Dawo yanzu ma Kuri kuri take jin abun shiyasa ta fara Tamtaman anya mafarki ne..?

Haka zataji komai na Dakinta na Girgiza ana bara baran kayan ammh kuma data tashi sai taga komai na Dakin yana nan a inda yake,A satin kaf a makare take zuwa makaranta tasani Ana Daga mata kafa ne Saboda Matsayinta in da a baya ne da Tuni ta amsa Kiran D.Musa
Damuwa ta kara yi mata yawa Bata da aiki sai kuka gabadaya ta fara gajiya da al"amarin Shiyasa ranar Jumma"a da Safe data farka Lokaci ya tafi kafin ta shirya goma tayi yasa ta fasa zuwa makaranta ta Turama D.Musa sakon bazata samu zuwa ba ya Turo mata da amsar"Take ur time Madam..!"
Sai da taci kukan ta ko Girki ta kasayi Saboda Hannunta da kafafunta yau tatashi da yakushi kamar na Kafafun mage duk an karceta har a kumatunta.

Inna ta yanke shawaran kiran sai da ta kirata bayan sun gaisa Inna tace"Auta lafiya naji muryan ki wani iri kamar kin yi kuka..?

Muhibba taja majina tana Fadin"Inna na tashi da ciwon kai ne."
Inna ta mata sannu cikin Tsausayawa tace"Kin sha mgani..?

Muhibba ta daga mata sai kuma ta Fashe da kuka Inna tace"To ban da abun Auta Daga ciwon kai sai kuka..?.

Ki samu ki kwanta zai sauka Insha Allahu."
Daga haka sukayi sallama ta kasa Fadama Inna matsalarta.barcin kuma tayi sai bayan azahar tatashi ta iya yin wanka tayi sallah sannan ta shiga Kitchen tayi girki taliya da Nama ta Dafa ko ci batayi ba na Junaidu ma ta kasa fita ta mikamai.

Dakinta ta koma ta zauna kan gado tana auna abubuwan dake Faruwa da ita sai kuka sai ga Kiran inna ta share hawayenta ta Dauka Inna ta tambayeta ya jikin tace ta samu Sauki har sun yi sallama Muhibba tace"Inna menene ke kawo yawan mafarke mafarke marasa kyau..?

Inna tayi shuru kafin tace"Ke kike yin mafarki mara kyau muhibba..?

Sai ta samu kanta da ce ma Inna"Bani bace Inna wata malamar makarantarmu ce ke tambayata."
Tana jin sauke ajiyar zuciyar Inna na Salama da tace ba ita bace sai taji kwalla ta kawo idonta ya Inna zatayi in tace mata itace?

Meke shirin Faruwa da ita..?Ko dai Saifudden ba Mutum bane zai Dawo mata Domin ta fara rasa Tunanin ta kan abunda ke Faruwa da ita tun zuwanta gidan nan.
*Janafty*
*SFD0026*
*Amnaf_sudanese _collection*
*Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401*
*Ki biya ki karanta cikin salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba, kada ki karanta min littafi sannan kada ki yada'min shi don Allah pay N500 via jamila umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*
Tana ji sanda Inna ta kara sauke Numfashi kafin tace"Kinsan duka addu'o'in Auta ko kin manta su ne..?

Muhibba sai da ta share hawayenta sannan tace"Na sani Inna ina so ki kara Tunamin ne ko da na manta fa wasu"
Inna ta gyara zama tana fadin"To ki Fadamata kada ta rika kwanciya batare da alwala ajikinta ba sannan azkar din kwanciya barci da Annabi ya koya mana Falaqi da Nasi da iklas kafa uku uku sai Ayatul kursiya kafa uku shima ta tofe kanta tunda ga sama har zuwa tafin kafarta,Allah yayi alkwarin turo mala'ikun da zasu kare ta har zuwa wayewan gari sannan ta rika kwanciya ta hannun Damanta mun san malamai sun gayamana cewa mummunan mafarki daga Shed'an ne kyakyawan mafarki daga Allah nr In tayi mafarki mara kyau sai ta sauya wajen kwanciya bayan ta tashi tayi addu"a ta Tofa a Hannunta na Dama da Hagu in ta tashi da Safe kada ta sanar ma kowa ta yi Sadaka."
Muhibba na ta gyada kai kafin tace"In sha Allahu inna zan fada mata."
Inna tace"Ki kara mata da kada bakinta ya daina Fadin Hailala salatin Annabi da Istigifari sannan kada ta karatun Qur'ani ya zame mata nauyi shi Alqur"ani waraka ne ga dukkan wata cuta Auta ko kema ki dage safe da Rana da yammah azkar kada ya bar bakin ki sannan karatu Qur"ani ya zama abun yin ki ko da wani Lokaci ko da mun shiga Jin dadin Rayuwa in muka manta da Allah sai shima ya manta damu."
Muhibba ta jinjina kai kafin tace"Allah ya kara girma Inna duk zan sanar da ita.."
Inna taji dadin haka kafin su katse kiran sai da ta kara Tunasar da Muhibba,kamar tasan da ita ne abubuwan ke faruwa bayan sun gama waya Muhibba ta samu salama domin tunda tazo gidan, in ba a waya ta saka Karatu tana bi ba jikinta na mata nauyi wajen Daukan Qur'ani ta karanta har azkar din Safe da yammah ba ko da yaushe take samun Damar yi ba ammh mganganun Inna sun saka ta gane kuskuranta acikin Ranta kuma ta kuduri niyar insha Allahu zata dage kada sanadin haka yasa ta haukace acikin gida ba wanda ya sani.

Tun daga Ranar Muhibba ta maida bakinta wajen ambaton Allah Sannan karatun Qur"ani ta tsara shi kullum Izu Biyu take karantawa da Safe,Bata da Hadda ma ammh tasan ba inda bazata karanta a Qur"ani ba,kuma Alhamdulillah taga chanji Domin Tunda ga Ranar kamar an yi ruwa an Dauke Lafiya lau take kwanciya kuma tatashi Lafiyanta kalau..

Saifudeen ma wannan satin bata gansa ba ya dai turo mata sakon ta kula da kanta Ranta ya baci da wannan Halin nasa aranta tace ai tasan yana mgana kiranta ne bazai iya yi ba ita fa matarsa ce ba ita tace tana son ba shi yace yana sonta ammh abunda yake nuna mata kamar Dole akayi mai aiko akuya ce ya ijiye bai kamata yayi mata wannan rikon sakainar kashin ba uwa uba ya barta agida ita kadai abubuwa na neman su gagareta shi yana chan bai ma san an yi ba.

Saboda yadda Ranta ya baci ko kallo sakon ma bai isheta ba ta saman waya taga Notification din ko Budeshi batayi ba daman sakon sa in yayi yawa ne Layi biyu na ranar ma Layi Daya ne.

Ranar monday tun 7 tana makaranta da wuri taje,saboda ita kanta bata jin Dadin Uban lattin datake yi sannan ga fashi a sati bai fi taje sau uku ba,D.Musa na sane da komai sai dai bai isa yace wani abu ba,Tunda su ke da makaranta ammh Saboda Students sannan kuma Uncle Hafiz nada ajinsa Nauyi ne suka karamai ya zama Dole suka bada Vacancy malami ko guda Daya da zai rike ajin in Muhibban bata zo ba tun wanchan Satin ya Turama Yallabai mganar ta Massages ammh bai bashi amsa ba,sai ya kara Turamai ta Chart kuma ya gani bai ce komai ba aransa yana ta tunanin Allah yasa ba Laifi yayi ba.

Shi kuma Saifudden ya gani basu samu zama bane suna ta zuwa inda Gwamna ya bada aikin gyaran makarantu suna zuwa har da gwamnan suna gani da idon su yadda aikin ke tafiya saboda kuma shi abu in ba ya shafi aikinsa bane bai cika Damuwa ya maida kansa ba...

Ya shigo zaria Ranar Laraba yayi karatu da Safe bata ma sani ba kuma yana gama abunda zai yi ya koma kaduna yasan da Safe ne tana makaranta shi yasa bai damu da ya koma gidan ba,da kansa ya nemi yaron dake mai share share yaje gida ya share Dakinsa sannan ya kira mai mai wanki da guga shima yace yaje ya kwashe kayan sa,mai mai wanki suna da karamin kamfani wajen da suke yin wanki na manyan mutane mata da maza sai dai a kawo maka agoge acikin leda.
Chapter 71 · 0% Book details