← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 144

Sashe 5

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muhibba ce ta katse kallon da Inna ke jifanta dashi da cewa"Inna na fito.."
Inna ta kara binta da kallo Daga sama har kasa Tana sanye da Riga da Zani na wata jan Atamfa sai Hijabinta Baki Dake jikinta yakai mata gwiwan kafafunta sai Takalminta baki mai Saukakken Tudu sai jakarta dake Rataye a Kafadanta da Dogon Littafi nan na 80pages a hannunta..

Muhibba ba fara bace baka ce kamar Innarta Sannan bata da kyau na azo agani sai dai fasali irin ta y'a mace.

Dogon Fuska gareta Da Hancinta Daidai bata da wani kyan da za"a zuzuta kamar yadda kowa ya sani ne.

Muhibba Shuru shuru ce sannan kuma bata da Hayaniya ballatana Fada tana da kawaici da Hakuri da kuma kauda kai kan wasu al"amurran.

Matashiyace yar kimanin shekaru Ashirin da Biyar a Duniya,Malamar makarantace kamar yadda Burinta yake tayi karatunta Tun daga matakin primary har matakin B.Ed dinta a kwalejin Horas da Malamai Dake Zaria da Taimakon Yan"uwanta guda Biyu ya Habibu da Anty Habiba da kuma Jajircewan Uwa Irin Innar Habibu.
tura baki nayi cikin yar Shagwaba na katse Dogon kallon da Innar ke bina dashi da cewa"Inna nafa makara..?

Bakwai da Rabi har ta gota fa..?

Inna ta daga Labulen Dakin Muhibban din tana kallon Kwanon koko da kosai din data Shigar mata dashi kafin ta Dawo da kallonta kan Muhibba tana Fadin"Auta ina fatan kin Shanye kunun chan duka ko..?

Muhibba tace"Ina zan iya shanyewa duka ban da abunki Inna..?

Inna tace"Ai baki fi karfin ki shanye din ba..Sangarcewa kika yi da kuma Kulafucin wannan koyarwa taki da kika saka kanki.."
Muhibba tace"Inna to ai yafi nayi ta zaman gida kuma ko..?

Ko kara mgana batayi ba ta wuce madafi dake cikin Karamin Tsakar gidan Tana Fadin"A dawo lafiya..!

Muhibba tayi yar Dariya kafin tace"Inna tawa..Sai na Dawo kila in Biya gidan Anty Habiba in mun tashi..

Inna na zama kan Kujera yar Tsugguno tana Fadin"Allah yasa ba Hirar SAIFUDDEEN din da kika saba zaki je ki isheta dashi ba..?

Muhibba ta tura baki tana buga Kafa Cikin alamun Shagwaba kafin tace"Kai Inna ni ba na bari ba..Tunda ke da su ya Sani kuka ce wai BA MUTUM bane na daina mganarsa"
Inna tace"Au mukace wai ma ne ko..?

Don mai garin ku in Mutum din ne ina yake..!?

Yarinya kin hadu da gamo tun kina karmarki kin girma ma baki daina Damun mu da zencen wanda bamu taba ganinsa ba."
shuru nayi ban kara mgana ba kawai sai na juya zan fice Daga gidan Inna na Dariya tace"Yau haka zaki tafi baki yi sallama da yayan naki ba..?

Ban waigo ba tace"Ai mun gaisa da asuba. !

Daga haka na fice Daga gidan Inna ta Rakani da Dariya Lokaci Daya tana fadin"Allah ya Tsaremin ke Auta..!

Wake ta Dibo tana Tsincewa so take ta Ragema Zeenatu aiki kafin ta fito baka bar Mutum yayi ta aiki shi kad'ai ba kana zaune da sunan Suruki alhalin Kuma kana da Lafiya da kwarin jikin da zaka iya taimakawa da wani abun.

Ina Fita da kafata ta taka har Bakin Titi Dayake gidan namu ba Nisa da Titi Adaidaita na tare ta Sabon gari na shiga ina ta Faman Duba agogon Fatan Dake Hannuna,Bana so na makara sannan makarantar da nake koyarwa ba kamar sauran makarantau bace suna da Doka da oda duk da ta kasance makaranta ce ta kudi mai zaman kanta.

Makarantar tana cikin Sabon gari ne,Kofar wani Tamgamemen gini na Zamani mai hawa biyu mai adaidaitan ya tsaya Daga ganin ginin wanda ya zanasa ya kware a aikinsa matuka Makarantar mai Fentin green white green Tutar Nageria,Makarantar ta Tsaru matuka gaya tundaga get dinta zaka Fahimci makarantar ta Tara komai na cigaban Dalibai.

Ana saukeni nq bama mai Nepep din kudinsa na Nufi get din makarantar da Get man na fara gaisawa kafin na shiga cikin makarantar inda aka ributa sunan makarantar kamar da Dutsen Zinare.
*SAIFUDDEEN ACADEMY..*
Makarantar tana da Shashe uku ne shahen farko primary section ne sai shashe na biyu Junoir Section ne sai Shashe na karshe Senior Section.

Muhibba primary section take aiki Tana matsayin Class Room Teacher na primary 4a.

Kafin na wuce aji na sai da ta shiga Staff Room smuka gaisa Head Teacher na Primary section din mu sannan na gaisa da Sauran malamai maza da matan da nagani acikin Office din na karbi attendence book na saka sunana Hannu sannan na mikama Head Teacher din mu Lesson plan dina ta karba Tana Fadin"Yanzu nake musu korafin kin fi su himma..Baki taba shigowa Cike Attendence bakiyi Submmiting din Lesson note dinki ba.."
Muhibba tayi mirmishi batare da tace komai ba Anty Khadija ta primary 3a ke ta faman Harara ta shi ko Uncle Hafiz na primary 6b cewa yayi"Sannu da aiki Anty Muhibba."
Na amsa mai cikin Fara"a da Fadin"Uncle Hafiz ya Student..?

Yana Mirmishi yace"Gasu nan muna ta Fama.."
Cikin Yanayi na nace"Allah ya taimake mu.

Gabadaya"
Ya amsa mata da Ameen Kafin HeadTeacher ta kalle mu tana Fadin"Uncle Hafiz ring d bell Lokacin Assembley yayi fa..

Antys get Ready.."
Tafada tana kokarin Daga wayarta Dake hannunta.

Tare Muhibba suka fito da Uncle Hafiz shi ya Kada bell din Dalibai Dake cikin ajijiwansu suka rika fitowa Daman Dokar makarantar ce yara basa wasan banza a waje kafin Assembley.

Kowani section Tsarin su Dabam ne kamar yadda komai nasu Dabam dabam suke gudarwa kamar irin su Assambely da Sauransu tunda kowani Shashe yana da girma da Fadi Saboda makarantar akwai girma sosai kamar wani karamin gari.
*Littafin Saifuddeen na kudi ne pay N500 via 0552179550 Jamila umar Gt bank,sai a turo evidence of payment ta wannan Lambar 09069067488 ko kuma katin waya na Mtn sai adauki Hoton katin a tura ta wannan Layin kai Tsaye 09069067488 mutanen mu na Niger kuma zasu tuntubi Kausar aglan Nissa ta wannan lambar domin karin bayani +22796562223 Ina maraba da masoya na a duk inda suke*
*Janafty*
*26/01/2023*
*Janafty*
*20/01/2023*
*SAIFUDDEEN*
_(Ba mutum ba ne)_
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty
*GRA:Zaria*
8:50am.

Misalin karfe takwas da Mintina hamsin na wannan ranar ta litini monday tushen aiki,awani katafaran gida ginin zamani Dake GRA cikin Rantsatsiyar anguwanan Dake cikin zaria.

Kai tsaye daga cikin gidan Cikin wani Katafaran babban Bedroom wanda ya kunshi Kalan baki da Fari Kama Daga gadon har Wardrope din Dake D'akin,Labulayan duka Farare ne tas har ta Cafet din Daya malale Dakin mai kalan Baki da Fari ne gwanin ban sha"awa Domin harta Blanket din Dake kan gadon fari ne tare da Zanin gadon da Filolinka duka Masu kalan Farare ne tas suna kyali suna tashin wani Sanyayyan kamshi mai shiga Jiki da zuciya gabadaya.

Kofar Tiolet din Dake cikin bedroom din ta Bude wani kakkarfa Namiji ya bayyana yana sanye da Rigar wanka Fara tas sai karamin towel Dayake Tsane kansa dashi domin akwai alamun Digan ruwa ajikinsa.

Gaban Katon Dressing mirror din dake D'akin ya karisa yana cigaba da Tsane kansa Kyakyawan kafafunsa masu cike da garsasa suna tsinewa Cikin Italiyan Cafet din Dake shimfide abakin madubin karami da shi kalan Fari shima da baki baki ajikinsa.

Kansa na Duke ne yana Goge kansa sai da ya gama sannan ya Dago bayan ya Cire karamin Towel din dake kansa,kyakyawan Doguwar Fuskarsa ta bayyana wanda kallo daya zakayi mai kaga kammaninsa da diban jini da yake yi da larabawan Sanjaha da suka fara samun matsugguni agarin na Lere dake Jahar kaduna.

Dogo ne sannan kakkarfa ne Daya samu Inganci Ruwa biyu na Fulani acikin jikinsa shi ya bashi Daman zama murjajjan jiki kamar wani Bakin Bature,Ba fari bane sannan kuma ba baki ba ne, yana Tsaka tsaki ne Doguwar Fuska garesa mai Dauke da Hanci har baka sai Faffadan Tattausan Lebunansa wadanda suke a cure Daga gashin giransa dana idonsa zaka gasgastan ya Hada jini da fulani ko labarawa Saboda yadda yake mai Santsi da kuma murdewa kamar yana Relezzer.
_*DR.SAIFUDDEEN CONEL.SALAHUDEEN LERE*_ kenan,D'a ga marigayi Conel.

Salahuddeen Inuwa Lere da Metron Zaliha Bungudu asalinsu Fulanin Bunkuri ce dake Jahar zamfara,rashin zaman lafiya da tashe tashen hankulan na yan Bindiga da yan Boko Haram yasa suka baro garinsu ita da kanwarta Zuwaira da yayansu Sunusi suka yada Zango a Gayan kano Nageria.

Ba Dr.

Bane a bangaran Likitanci Dr ne a bangaran karatu,Saifuddeen mutum ne mai kwakwalwa,da Tarin ilimin boko da na addini,Yana da Tarin Degree a bangarori da Dama har guda shidda Inda dai yafi kwarewa shi ne yana da shaidar Degree biyu kan Karatun B.A English,sannan Akan Letriture yayi phd dinsa a standford University,Sannan ahalin yanzu haka Shekaru biyar da suka gabata ya fara Laccaring a Abu samaru a bangaran Department din B.A English,Sannan Shekarun biyun da suka gabata da Sauya sabon gwamnati gwamna mai ci a yanzu Abdulhadi Shitu ya zana sunansa a matsayin Kwamishinan ilimi na Jahar kaduna Saifuddeen bai taba Siyasa ba ballatana mafarkinsa sai kuma rana Tsaka yaji sunansa a matsayin kwamishinan ilimi ta Jaharsa,sai dai yasan Nasaran sa daga Allah ne,sannan shima akwai Jajircewan sa da kokarinsa Tunda tun yana Secondary sochool dinsa na federal Science and Tecnical Collage(FSTC)KAFANCHAN,An san sa wajen Hazaka zai ya iya cewa da Taimakon gwamnatin Jahar kaduna ya samu Shedar Degree dinsa na biyu bayan ya gama karatun Degree din sa na farko a BUK KANO, kafin ya tafi Stanford Universty yayi Master dinsa duk da Tallafin gwamnatin Jahar kaduna a wanchan Lokacin Datake bama Hazikan yaran da suke da kokari Socholarship.

Shiri yake a gaggauce saboda yasan Lokaci ya tafi barcin daya kwashe shi ne mai bai mai adalci ba,Yasan za"a rina Saboda jiya sai D'aya na Dare ya iso Zaria wannan gidan nashi da ba wanda yasan inda yake sai Mujaheed da Ummi sun san ya mallaki gida a zaria ammh acikin su ba wanda yasan inda gidan yake ballatana har su taba Takowa yaji Dadin haka ko bakomai yaji Dadin haka Saboda a wannan gabar wannan gidan ya zame masa mafaka Daga Laifin da su Ummi suke ganin ya aikata musu wanda a wurinsa ba laifi bane saboda riko da wannan kalmar tasa na ba biyayyah ga abokin Halitta wajen sabama mahallaci.
Chapter 5 · 0% Book details