← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 144

Sashe 116

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ya fada cikin wata giggitaciyar kara da yasa Saifudden ya kara kwanciya gaban Mallam Surajo Cikin muryanta da Karfi tace"Saboda SAIFUDDEN nawa ne ni kada'i nawa ne ni kadai Daga ni sai YA'AYA NA nayi alkawarin Duk macen data Rabe sa sai Na KASHETA.."
Ba Wanda yaga sanda ya Dauko wani Ruwa a kwalba sai dai karan Watsa ma Saifudden din akaji Daga saman Fuskarsa har kirjinsa wani kara da ihu mara Dadi ya Karade Dakin Cikin Tsawa yace"Naki ne ke kadai uwarsa ce ke ko Ubansa..?

Ina ruwan ki dashi kina jinsun aljanu shi kuma Bil'adama..?

A ina kika Taba jin inda Mutum da Aljanu suka zama abu daya ko Allah ai ya bambata mu daku ya baku karfin damu bai bamu ba ammh sai ya karrama mu bil"adama..

Me ya sa kike Tare da shi..?

Miye sa kike Bibiyan Rayuwarsa?

Kuka kawai take yi muryan ba Dadi kara watsa mata ruwan yayi ta kara Sakin kuka Tana fadin"Kana kona ni..Daman jinya nake yi..Sun sa na rasa idona guda daya..Ka daina zan yi maka bayani"
Ko Sauraranta bai yi ba ya cigaba da Watsa mata wannan Ruwan ta Firgice ta rasa ina zata shi kuma Fadi yake"In baki yi mgana ba,ba iya Idon ki D'aya zaki rasa bq har ta Rayuwar naki zaki iya rasawa gabadaya"
Haka take Gyada kai kamar kadangaruwa Cikin Galabaita da Ihu tace"Nace KA BARI..ka bari zan yi mgana..Zan yiiii mganaaaa.."
Jin haka yasa ya Dakata yana Fadin"Muna jinki bamu da Lokaci..!

Kanta na kasa tana wani irin gunjin kuka ta fara fadin"Ni sunana RAZINA ni kuma Ina daga jinsun Aljanu..
shekarata dari Hudu da goma a Duniya"
Gabadaya sai kowa ya Rikice Mujaheed kamar ya suma Saboda Tsori Adda Sadiya kuwa kamar mutum Mutum.

Kawu ne kadai da Baba Sa"idu masu karfin hali.

Mallam Surajo yace"Ashe ma ke Tsohuwace kika hana Rayuwar yaran nan zaman Lafiya tunda ke kin ga jiya kin ga yau kina shirin ganin gobe ma in baki yi min taurin kai ba cigaba da bayani ina jinki"
Cikin Tsiwa tace"TO ai MIJINA NE..!

Mun yi aure dashi Shekaru Talatin da wani abu kenan har mun Haifayyafa ya"yan mu goma ni da shi"
Ummi jikinta na rawa tace"innalillahi wa"inna ilairraju'un"
Mallam Surajo kuma sai yace"Mijinki Ta ina..?

Wasu ya'yan kenan..?

A ina kika taba ganinsa har kika aure sa mu bamu sani ba..?

Sai ga bayani Tiryan Tiryan.

"A barikin Jaji muka Hadu wata rana ya fito yana kwallo da Safe ni kuma ina ganinsa sai naji duk Duniya bana son kowa sai shi Tun daga Ranar na Aure shi ina kuma Tare dashi na kuma yi alwashin Nesanta shi da kowacce mace na cire masa Sha'awar mace a zahiri sai acikin mafarkinsa Nake zuwa mai muna Saduwa da juna Sannan nake Haukatashi Duk sanda wata mace ta Rabesa,Ni nake sakamai kasala ya daina yawan ibada da Sallah akan Lokaci Saboda zai iya raba ni dashi yamin Nisa ni ba musulma bane na kuma san yadda Addu"a da Ibada ke Ruguzamu shi yasa na samu Dama daya koma Hannunsa kakarsa ba wanda ke matsamai ba kamar Lokacin yana wajen Mahaifiyarsa ba ita kan taso ta shiga Tsakanina da abunda nake so saboda ita mai yawan sallah ne da Karatun Qur'ani sannan shima Tana Tursasamai yanayi..na samu galabar zama dashi Tsawon wadanan Shekaru ne bayan na Mishi Dabaibaiyi baya iya yin komai na Ibadarku,Ni naake sakamar kasalar da sai tayi ta sakashi barci na awanni masu Tsawo,Ni nake saka shi yana sakan Duka matan daya aura kuma na samu Nasara har sau biyu sai dai na samu Gardama da Turjiya ta bangaran wannan yarinyar tana neman ta shiga Duniya ta bayan kuma mun riga mun Hayayyafa da Saifudden mijina ne ni kadai..Ita Kadai ce naga soyayyarta a kwayar idon sa,Sannan ita Kadai ce ta Gagari Dabaibayi na ita Kadai ce macen da azahiri yake jin sha'awarta nayi kokarin shiga Rayuwarta Tun Farko sai na kasa Saboda akwai wasu Sarakan Darakun aljanun da suke Tsare da Ahalinsu ganin haka yasa nayi ta Bata tsoro tun ranar da aka Dauran auran su da Saifudeen har shigowarta gidan nan nayi ta mata azabobi Saboda ta bar min Duniyata ban yi nasara ba shi kuma ko nayi kokarin ya Saketa sai na kasa aiwatar da Kudurina ana haka tazo ta fara Lalatamin shirina Saboda itama mai Ibada ce tayi ta kunna Karatun Qur'ani acikin gida tana Sallah tana addu"a tana neman illatani Sai kuma ta koma bangaransa shima ta rika sakashi yana sallah Shikenan sai ta kuncemin Dabaibayin da nayi masa tayi nasaran raba Tsakanina da Duniyata nayi jinya sosai Dalilin haka shiyasa da na dawo na rika Firgitata ina Tsoratar da ita da Niyar in bataji ba sai na Kasheta.

An yi zargin wani abu dabam ni kuma ina Labewa da haka ina kara Birkita Tunaninta,Ni ce na ke fito mata a sufoffi Dabam Dabam ina Lalata Tunaninta ita Dangin ta suka ja mata azabata ta fiye taurin kai ne na yi kokarin
da tabar min shi da Lalama taki jin gargadi na da taji tun farko da ban mata illah ba,sai dai tana da Taurin kai ita da iyayenta suna da Addu"a da Allah bakin su shiyasa na kai wani Lokacin ina Wahala akanta nayi alkwarin Saifuddeen bazai Taba kusantar mace ba sai ni kad'ai acikin mafarkinsa sai naga yana so ya rusamin wannan alkwarin Shi yasa na bayyana ajikinsa adaran da zai isa gareta na Firgitata na saka tsoronsa aranta sannan nayi mata Dukan mutuwa so nayi na Kasheta ammh ban samu Dama ba Ni ban yi niyar kasheta ba Taurin kanta ya ja mata Na fada mata ta kyalemu Duniya ta ce ta shigo ammh taki jina Shiyasa nayi mata haka"
Dakin sai ya Dau shuru bamai mgana Ummi haka take hawaye wani na koran wani Mallam Surajo yace"Shin adalci ne kina Jinsin Aljanu kice zaki auresa..?

Kin manta shi Bil"adama ne.?

Kin rabasa da komai nasa ciki har da yaji Dadi da matarsa kin Tabbata Muguwa bakar azzaluma"
Da Sauri tace"Kayi hakuri don Allah kada ka cutar dani"
Tsawa ya Daka mata yana Fadin"Kar ki kara Hada ni da Ubangijina Domin baki sam shi ba sai nayi alkwarin na miki illar da ko gobe kika ga wani bil"adama bazai kara Baki sha"awa ba"
Kuka ta fara tana fadin"Zan tafi..Daman ina da mijina in da mijina Sunansa ZAHMUJI"
CIKIn Dariyan keta yace"au daman kina da miji kika zo shi kika shiga rayuwarsa kika hanasa zaman Lafiya..?

Kin tabbata muguwa..Bazan barki ba sai nayi miki Tabo Tabon da arniya irin ki bazata kara kusatar Musulmi Bil'adama ba"
Bai Saurari magiyanta ba ya Dauko wani karamin kwalba a kasan Dardumansa mganin ciki wani kala ne aciki yana Bude mganin warin ya mamaye Dakin ba Dadin shaka Jan jiki take yi tana kuka tana Fadin A"a ammh sai da ya watsa mata shi ta Fara Ihu tana Birgima tana Fadin"Ka...ka...kaa..!

Sai kakarin Amai ta rike wuyanta tana Shure shure kan mallam Surajo na kasa yana ta motsi da bakinsa ba wanda yasan me yake fadi.

Sai da yaji Ta daina motsi ta koma tana kakarin mutuwa sannan ya Dakata yana Fadin"Ki yi nisa da wannan Ahalin
Kiyi nisa da Bil"adama
In ba haka ba in muka sake cin karo..Sai na KaShe sai na kasheki DA ayoyin Allah RAZINA"
Dakin ne ya fara jijjiga sai kuma aka koma Buga abu gaf gaf gaf
Kamar Kwanon Dakin zai Dauke Mallam Surajo fadi yake yi"Ki tafi..Tafiya na har Abada ki barsu su Zauna cikin salama in kika Sake Dawowa zan kona ki da ayoyin Allah..Tafi..Ki tafi..Tafiya ta har Abada"
Sai kawai komai yayi tsit kamar kiftawan ido Adda Sadiya sai da ta suma ni da ita mujaheed kuma jinsa na wani Lokaci sai da ya tafi Ummi ce bakinta na rawa tana addu"a ita da su kawu Baba Surajo dai sai fitsari a zaune Saifudden kuma nan ya fadi yashe a kasa kamar baya Numfaahi.
Chapter 116 · 0% Book details