← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 144

Sashe 104

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na razana na fita Daga Hayyacina ban san ina kaina yake ba nadai san na Fita Daga Dakin aguje har haraban gidan ina gudu ina jin sautin ta a kaina tana fadin"Ki tafi..Ki bar nan nan din DUNIYA TA CE...!
ban samu kowa a bakin get ba na Bude na fita ina tafe ina Faduwa ammh ban Sare ba Gudu nake yi kamar mahaukaciya Lokacin Safe ne ba Mutane gudu ne na ceton rai da Zuciyata da gangar jikina nake gudu,Gudu ne na ceton rai daga Mutuwa gudun Tsira gudun Tsoro da Firgita gudu ne da nayi shi cikin Fitan Hayyaci da gangar jiki ban zan iya Tuna wani yanayi ba ne ko wani Lokaci ko wata hanya nabi ba Nadai san nayi ta gudu har sai da Numfashina ya fara barazanar kwacemin abu daya na sani shine nayi Gudu ne Tunda ga Gra har Dogarawa da Kafafuwa ban san ya'akayi na gane gidan mu nadai san na shiga gidan mu a tsakar gida na Hangi Inna da Buta ta fito Daga makewaye nasan na mika mata hannu sai dai bansan ko ta kamani ba naji Duniyata tayi sama cikin Fitaar Hayyaci nace"INNA TA..!!
*****
*Kaduna*
Yau tun Safe da ya tashi bai jin Dadi jikinsa duk yayi sanyi kasalar da ta Dade bata shige sa ba ita ta shigesa sai 7 am ya tashi yayi sallar asuba ya makara sannan yayi ta kiran wayar Muhi bata shiga ya kira na Junaidu In ya Dauka kuma bayajin Jinsa hakanan yake jinsa ba Daidai ba Domin suna Meeting da Gwamna ba da bazai Fita ba Zaria zai tafi sai dai ganawar na da Muhimmancin da Dole sai ya Hallata shiyasa ya shirya ya tafi.

Taron ne na
Kwamishinonin da His Excllency ya bukaci ganinsu dukkansu Taron da ya Dauke su adadin Sa'o'i Hudu kafin su gama shi dai gashi nan kawai kamar yana wajen ammh Tunaninsa da Zuciyarsa suna wani waje daman tsikar jikinsa kawai yaji tana tashi wani abu na Faruwa,kuma yana kyautata zaton muhi ce domin itace kadai ta shiga Duniyarsa ta mamayeta gabadaya.

Fitowar su kenan Daga Meeting da His Excellency a office dinsa ya bar duka wayoyinsa yana komawa bai bi ta kan wayoyin ba sai ya fara duba Fayel din Daukan malaman da zasu sake yi a Jahar ta kaduna Sai yaga wayarsa na Haske a kasalace ya Dago wayar sunan Ummi daya gani Sai da gabansa ya Fadi Ras haka kurum yaji Tashin Hankalin da bai san Dalilinsa ba.,Da Hanzari ya Daga kiran Da Fadin"Ummi ina kwana."
Dagachan bangaran cikin wani yanayi Ummi tace"Kana Ina ne..?

Kai tsaye yace"Ina kaduna Ummi wani abu ne ya faru..?

Sai da ta sauke ajiyar rai sannan tace"Eh wani abu tabbas ya faru ammh ba'anan ba a chan zaria ne."
Da Hanzari ya mike da wani irin Firgici Sai da ya Ture Takardun Gabansa suka zube bai sani ba acikin ransa ya ambaci sunanta "Muhi"
A fili kuma cikin wani yanayi yace"Muhi Ummi me ya faru da ita..?

Ummi tace"Ka kwantar da Hankalinka nima yanzu Innar Habibu ta kirani
take gayamin tun safe basu runtsa ba, Muhibba ta balle ta gudo gida,Sai kuka take da ihu tana Zabura tana Surutai da Sambatu."
Kai ya Dafe cikin mamaki kafin yace"Me kenan Ummi..?

Cikin Natsuwa tace"Abun kamar GAMO tayi yaro."
Gidan nan naku ina Tunanin akwai aljanu ni a Tunanina ita kuma Innar Habibu tace aljanin nan nata mai zuwa mata da Suffarka ne ya ke neman Razanata Saboda ya hanata zaman aure kamar yadda ya faru kwanaki"
Ba wani jin Ummi yake sosai ba, Shi ba yace bai aminta da Aljanu bane har yanzu yasan akwai su ammh Siddabarun su ne bai sani ba,yagaji da jin wannan bayanin shikenen komai sai ace aljanu aljanu matar sa na shirin haukacewa baza ayi Tunanin kaita asibiti ba.

Cikin Sautin muryansa yace"Yanzu ta na Ina..?

Ummi tace"Tana chan gidansu an kira malamin nan da yasan Laluran ita Muhibban din suna
kanta suna mata Rukiya nima gobe ina tafe naga Halin da ake ciki"
Bai gama jin bayani
Ummi ba ya katse kiran saboda Tsabar Rudewa kadan ya Rage ya fadi wajen fita daga Office dinsa.

A haraban wajen yaga su bama suna Tsaye suna gadinsa yadda suka ga ya fito a firgice ne yasa da Sauri Tim ya bude mai mota ya shiga jikinsa har wani rawa yake yi Bama ya shiga bangaran Direba da Sauri suka bar wajen sai da suka Dau hanya ne ya sanar da su zaria zasu.

Gani yake kamar Bama baya Sauri Kafin su iso zaria Bai san adadin Zagin daya riga kunduma ma su bama ba,abunda ba Halinsa ba ne, gani yake kamar basu taka motar dakyau ba Domin bai saba Tukin babban Hanya da sai ya sauke su ya Tuka kansa kila sai ya ma isa a kan Lokaci.

Motar bata gama Tsayawa a kofar gidan su Muhibba ba ya Balle murfin mota ya Daka Tsalle ya fice yau ko neman izini ko sallama haka ya Fado gidan da Bakaken Takalminsa Rufaffu bakake na Fata ya fada Dakin Inna kawai sai dai ganinsa sukayi Tsaye a kansu Wurga ido ya dinga yi ya dai ga Inna da Ya Habibu sai Anty Habiba sai Mallam Haruna da D'alibansa su Gaddafi,suna zaune wacce suka zagaye ya kai kallonsa sai da yaji kamar zai mutu Muhi dinsa ya gani Gardawan maza Uku su Dannenta wani na mata karatu a kunnenta wani na Uban Fesa mata wani ruwa kamar mahaukaciya.

Wani irin Sufa yayi sai gashi A gabansu Da mugun Hanzari ya saka Kafa ya shure dayan da ke rike da ita Sauran suna ganin haka suka Sakeni Muhibba dake kuka ka shirban ina
kyalla ido na hangosa ai sai na mike da wani irin gudu da kuka na Nufesa na Fada Jikinsa Cikin kyarma abun takaici kanta ba Dankwali ta kusa ma yaye Sikat din jikinta..

Karfaffan riko yayi min kamar zai maida ni cikinsa
kuka nake yi kamar raina zai fita cikin Fitan Hayyaci nake fadin"Saif zata zata Kashe ni..Ka tafi dani ka boye ni"
Cikin tashin Hankali ya riketa fadi yake"Gani nan muhi..Ba abunda zai faru dake ni SAIFUDDEEN garkuwanki ne"
Mallam Haruna bai dakata ba ya cigaba da karatunsa cikin suratul Jinni Lokaci daya wani al"amajiransa ya watsa wani mgani acikin Rushin wuta dake cikin kasko a gabansu nan da nan Hayaki mara Dadi ya Turnike dakin dukkansu suka Fara Tari Saifudden yaji kansa na juyawa ganin yadda Muhi ke neman sikewa yasa yayi Fatali da Kaskon da takalminsa yaje ya Daki garun dakin ya tarwatse wuta yayi nasa gefen Mutane ma sukayi nasu barayin cikin tashin Hankali.

Inna Dake kuka ka shirban na ganin Halin da Muhibba ke ciki ta kasa mgana Ya Habibu ne ke fadin"Kayi a hankali fa Saifudden"
Jajayen idanuwansa ya watsa ma mallam Haruna kafin yace"Mahaukaciya kuka mai da min mata..?wannan hayakin ai shi kan shi Cuta ne kada ku kara matsowa kusa da Matata ba in ba haka zan tarwataa komai yanzu nan"
Yadda yake mgana yasa ba wanda ya kulasa har ya Daga Muhibba cak suka fice Daga Dakin da ita Inna zatayi mgana Mallam Haruna ya Daga mata yana fadin"kyale shi..yanzu na Fahimci wani abu koma meke Faruwa yana da karfaffan alaqa da shi mijin nata"
Ya Habibu ya kallesa kafin yace"Ban gane ba..?kasan a yanayin da Auta ta Dawo gida kuwa..? ina shashena Naji Inna na kirana da kuka ina Fitowa na ganta kwance bata Numfashi muka Ciccibeta zuwa daki muka fara yayyafa mata ruwa Tana farfadowa ta fara Zabura tana fadin gata nan zata kasheta zata kasheta ana cikin wannan Halin sai ga yarinyar dake zaune da ita tazo tana kuka tana Fadamana Halin da yarinyar nan ta kwana aciki tace tana ganinta ta fito da gudu megadi kuma ya shiga makewayi shiyasa ta samu Damar kwacewa ta fito mallam munsan kasan matsalan Auta don Allah ka Dakatar da Dauketa kada komai kuma ya koma baya"
Ya fada cikin wani yanayin Sarewa da kasawa Inna sai sharan hawaye take yi tana jan Jarbi Anty Habiba tace"Kada ma yace zai maida ta wannan gidan ni wlh na fara tsorata Haukata Auta ake son ayi"
Duk mallam Haruna na jin su bai ce komai ba kansa na kasa yana ta Karatunsa sai chan ya Dago yana Fadin"Habibu duba min su suna ina yanzu..'
Da Sauri ya mike ya fita Tsohon Dakin Muhibba ya leka suna ciki suna kamkame da juna kamar zasu koma Daya Muhibba tayi shuru ki tarinta bakaji shi kuma yana faman Shafa bayanta zuwa kanta yanayin su kadai ya isa ya saka ka kuka Cikin matukar tausayinsu ya Dawo ciki ya zauna yana fadin"Suna tare acikin wannan Dakin..Auta kuma ta Daina kuka da wannam zabura zaburan"
Mirmishi yayi kafin ya mike yana Fadin"Lokacin sallah ya gabato zamu tafi"
Inna tace"Mallam haka zamu bar Muhibba cikin wannan Halin.?

Kai tsaye yace mata"Abun yafi karfina Inna..Koma wani aljani ne kafiri ne arne ne sannan mugu ne,kuma azzalumi ne Ku godema Allah addu"a da kariyan Ubangiji na tare da Muhibba da Fitan da tayi ta Haukace tabi Duniya"
Salati suka saka sai kuka Inna da Anty Habiba cikin Lallashi yace"Akwai abunda na Fahimta ammh bazan Fada muku ba sai na Dawo"
Daga Haka ya fice Dauke da Qur'aninsa suma su gaddafi suka maramai baya,suka bar su Inna na ta kuka Ya Habibu na Lallashin su shima Hankalinsa duk ya tashi Sani ya koma makaranta jiya ba Rabon yaga wannan Tashin Hankalin.
Chapter 104 · 0% Book details