← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 144

Sashe 24

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Awannan kwanakin Ummi ta gasgata Iya bata kaunarta hankalinta ya tashi alokacin an samu shigowar Waya hannu ta wayar Conel ta ara ta Kira Yaya Sunusu ta labartamai Halin Datake Ciki shi ya wanko kafa yazo har Gaya ya duka gaban iya yana rokonta sannan ya gayamata Ummi basu da kowa uwa da uba duk basu sannan ba wasu cikakken Dangi shi ne nan uwa da ubansu tayi hakuri ta sanya ma wannan auran albarka,Iya saboda kwarjin ya sunusi da kuma Baiwar iya Sarrafa Harshe yasa ta aminta har ta saka ma auransu albarka Shi kuma wannan karamcin na Iya yake dubawa da har yau duk abunda take yi bata taba bashi Haushi ba.

Ummi ta fara zama abarikin Sojoji na Zaria a basawa,cikin Aminci ita da Mijinta mai sonta,sati Uku sukayi ya shiryata ya maidata makaranta,in ya samu Lokaci yana zuwa ya ganta suna Jarabawar gamawa,ta samu Cikinta na Fari Dakyar da Sodin goshi ta karisa Jarabawan,Daga Tsafe Gaya ta koma gidan Yaya Sunusi domin bata Fadama Conel ramar zasu gama Jarabawa tana ko zuwa gaya kamar Ciwo na Jira ta fara amai Da Zazzabi Har da su kwanciya asibiti,Achan ne aka Tabbatar tana da shigar Ciki Wata Uku murna wajen Conel baki yaki Rufuwa Saboda farimciki yasa da Ummi tace zata zauna agida bai Hanata ba sai da yaje Lere ya sanar da su Iya Atika ta zugata tace Ummi ta Dawo gaban Iya ta kula da ita aiko Ya na Dawowa Iya ta Murje ido tace ga yadda za"ayi bai da yarda zai yi Daya Fadama yaya sunusi bai nuna wata Damuwa ba sai ma Ummin ce ta Damu ganin haka yasa Matar Ya sunusu da suke kira Umma tace Su tafi Zuwaira Wacce tayi Candy tana Gida,Sai ya sunusi ya amince ammh bayan Conel ya tabbatar mai da ba matsala,Ko da Ummi ta koma gaban Iya da Renon Cikinta Iya batayi murna ba ganin harda Zuwaira tun awannan Lokacin Iya da Zuwaira basa Shiri Saboda Zuwaira tafi Ummi baki sannan tun tana budurwanta bata Cika Daukan Reni ba in Iya ta Fadi Daya ita zata maida mata ashirin ne sannan ko Atika in tazo gidan suna Gogawa da Iya ta gaji ne tace Conel ya Tattarasu ta gaji Cikin Ummi na Wata Biyar ta koma gidanta dake Zaria ita da Zuwaira tana tayata wasu ayyukan.

Haihuwar SAIFUDDEEN yazo da wani Budi da Tarin Alherai,ya kuma ga Soyayya da Kauna wajen iyayansa Sannan Hatta da Iya haihuwan Saifuddeen ya Saussauta kiyayyarta ga Ummi Gida gaya ta koma Umma ta mata wankan Jego duk da ba Haka Iya taso ba sai dai wannan karon har Lelenta bai goyi bayan Ummi tazo Lere tayi jego ba wato Hashimu.

Shiyasa tayi shuru da bakinta sai dai kafin sugama wanka Iya bata san adadim zuwanta gaya ba Saboda Saifuddeen da Conel ke matukar so Shiyasa ya sakamai irin sunansa Wato Saifudeen Salahudden kenan..

Ummi dai agaban mutane ta na ma Saif alkunya bata iya Daukansa sai in ba kowa saboda kunya sannan Tun Watarana da sukaje Lere yana kuka ta Rikesa tana jijjgasa tana kiran sunansa Iya ta mata tas tace bata da kunya tana ma yaron fari wasa har tana Kiran sunansa,Wannan shine mafarin da Ummi bata kiran sunan Saifuddeen sai dai YARO.

Mafarin zaman Zuwaira a Hannun su kenan Conel ya riketa ya sakata makaranta ita kuma Ummi jarabawarta ta fito kuma tayi kyau Conel yayi mata alkawarin nema mata aiki acikin asibitin barikinsu duk da ita ba Soja bace ammh ai matar Soja ce.

Saifuddeen na da wata goma sha Daya yana Tafiyarsa ko"ina Conel ya samu karin girma da Sauyin wajen aiki an maidasa barrak din Jaji chan suka koma ita kuma Zuwaira tana Kano chan tayi aure har ta fara karatunta a Sa"adatu Rimi collage kano.

Sun koma Jaji ba Dadewa Conel ya shiga ya fita Ummi ta fara aiki da asibitin Barrak din a matsayin ta na matar soja sannan kuma da albashinta mai tsoka duk Dalilin Jajircewan mijinta da har gobe bata Daina kukan mutuwarsa ba.

Wani karin baiwa ta Ubangiji Saifudden nada shekara uku a Duniya ta samu cikin Sadiya,Cikin bai bata Wahalan kamar na Yaro ba har cikinta na wata tara tana zuwa aikinta Ranar ma data haihu a wajen aikinta ne ta haihu achan sai dai aka Kira Conel aka fadamai Matarsa ta Haihu
A barkin Jaji aka sha sunan Halimatu Sadiya wannan karon sannan Iyami dake matsayin kakarsu ya sunusi ya Daukota Daga chan bungudu tana zaune dasu ita tazo ta zauna da Ummi har ta gama wankanta sannan ta koma Gaya alokacin Zuwaira sun samu Hutu tazo,Sai wahalan bata yi ma Ummi yawa ba,Saifudden nursing School din cikin
Barikin ya Fara karatunsa,Sadiya ma data tasa sai aka sakata suna zuwa Tare alokacin har Ummi kuma na cigaba da kula da ya"yanta da mijinta da aikinta Tana kuma samun kwarewa alokacin ne Conel ya barta ta koma Makaranta ta Dora Hnd dinta akan Midwife,sai dai tun kafin ta fara Iya dataji Labari tace bata amince ba Taya ya zata tafi gantalin karatun ta bar ma yaranta da wa..?Ya sunusi shima Dayaji shima bai goyi baya ba Shiyasa sai Ummi ta Hakura ta Cigaba da aikinta kawai ba yadda Conel zai yi shima sai ya Hakura.

Saifuddeen nada shekara Shidda Sadiya kuma uku da wani abu Conel ya samu karin girma da mikaminsa na Conel alokacin Cikin Barrak din I Division na Kaduna suka koma da zama Sun bar Jaji,Lokacin Rayuwa tayi kyau sosai kudi da jin Dadi sun zauna Conel kusan duka shine Hidiman yan"uwansa har da na yan"uwan Ummi.Saboda da suka bar Jaji sai ta hakura da aikin ta zauna tana kula da ya"yanta da basu Tarbiya Mutuwa ita ta yanke wannan zaman jin dadin Conel ya Rasu Saifuddeen yana da shekara goma aduniya Sadiya kuma Bakwai,Sakamakon Hadarin Mota,Daga kaduna zuwa zaria sai gawansa aka kawo Ummi tayi kuka kamar ranta zai fita a Lere aka yi Jana"izarsa Sojoji suka rakasa makabarta Dakyar aka bari Iya ta gansa ita da Ummi sukamai addu"a Saif yasan babansa ya rasu alokacin Sadiya ce sai dai bim mutane da kallo Zuwaira tazo da D'anta Mujaheed wanda Tsakaninsa da Saifudden Shekara ne da wattani.

Tun bayan bakwai Ummi tasan tayi Rashi Domin zama na musamman iya ta shirya akan Ummi zata basu su Saifudden in Conel yayi Arba"in da Rasuwa da wannan bakincikin ta koma Gaya da zama tana Takabarta Ya sunusi da Umma na faman bata baki ganin yadda ta damu yasa yaje Lere da kansa ya roki Iya ta barma Ummi Sadiya sai su Dauki Saif ganin girmansa yasa ta amince haka kuwa akayi Tana fita Takaba Iya ta karbe Saifudden Sannan an raba gadon Conel,Hukunar Soja ta kasa ta kawo kudade masu yawa ga iyalan Mamacin sannan ga Gonakin conel da Shanayensa Daya gada su aka bar ma Sadiya da Saifudden kudi kuma aka Raba da Iya da Ummi sauran kuma nasu Sadiya ne da Saif.

Saifuddeem a garin Lere ya Rayu yayi kukan rabasa da Ummi da Adda Sadiyarsa kanwarsa abokiyarsa sai dai ba yadda zai yi Dole ya saki Jiki ko mutuwa zai yi, iya bazata barsa ya koma Gaya ba sai ya maida hankali a karatunsa inda ya tafi makarantar kwana dake kafachan
Federal Science Tecnical Collage(FCTE) KAFANCHAN Ya cigaba da makarantarsa Dayake yana aji Biyar ne Conel ya rasu.

Saifudden tun fara karatunsa mai kwazo ne kuma gifted ne gasan duniya in makaranta zata saka shi zai ce sun sha zuwa Quiz da makarantu Saifudeen Salahudden lere ke daga musu martabansu tun a wadannan shekarun nasa malamai da Dalibai suka Shaida kokari da Hazakarsa uwa uba ga Uban naci irim na babansa Daya yi gado in ya Dukufa kan Littafi kamar Computer in ji Iya alfahari take dashi matuka tana kallonsa kamar Mahaifinsa sau dadama a wajen Iya Saifudeeen ya samu Labarin kuruciyar mahaifinsa da gwagwarmayansa Duk in da akayi hutu yana zuwa Gaya,wajen Ummi wacce ta koma tana Dora Hnd dinta a Tsafe inda tayi Diploma dinta,Sai ta samu Hutu take zuwa gida Sadiya kuma tana Tare da ya"yan Sunusu an saka ta makaranta Umma na kula da ita bata da wata damuwa.

Rayuwar ta gangara Ummi ta zo ta gama karatunta ta zama Cikakkiyar Midwife alokacin aiki baya wahala sai ta samu aiki a aaibitin dake garin Gaya Allah ya taimaketa ba"ayi nisa da ita ba ta fara aikinta cikin kwanciyar Hankali alokacin ne Manema suka mata cha ita kuma tace bazata kara aure ba Har Abada Tun Ya sunusi baya mgana har ya fara mata mganar aure domin yace tana da kuruciyarta bai dace ta zauna haka ba.

Ummi dai ta dinga Zillewa sai da Conel ya shekara bakwai a kasa sannan tayi aure shima saboda ya sunusi ne kada yace taki jin mganarsa wani Lauya ta aura dake aiki a Supreme Court na garin Abuja Shi Haifaffan Sulaja ne Banufe ne sai dai yana da Tarin Nagarta yazo gaida matar wani makocinsu da a ka kaahe mijinta to Matar yar gaya ce bincike ya kawosa yaga Ummi asibitin datake aiki yako makalemata ya taba aure matar ta rasu wajen Haihuwa ita da abunda ke Cikinta.

Lokacin da Labarin Auran Ummi yaje lere Iya kuka ta saka tana Fadin Ummi taci Amanar Salahudeen duka duka yaushe ya rasu har tayi aure.?

Iri wadanan mganganun na Iya sun sakama Saifudeen jin Haushin Ummi Tunda Lokacin suna shiryen shiryen Zana jarabawar gama secondary School ne,har Ummi ta tare agidan mijinta Dake Abuja Saifuddeen bai je ba sai da ga baya da Mama zuwaira taje har lere ta samu Saif din sukayi mgana ya gayamata abunda Iya ta dinga Fadi ita ta lallashesa sannan ta Daukesa bada Izimin Iya ba sai Abuja yaje yaga Ummi da Addansa da Barrister yace ta Daukota zai riketa Cikin Amana sai Hankalin Saif ya kwanta nan Mama zuwaira ta barsu shi da Mujaheed ta koma kano zasu yi ma Ummi Hutu taji Dadi shi kanshi Barrister yaji Dadin haka zai kwashesu su fita parks park ya siya musu wannan ya siya musu wannan nan da nan suka saki Jiki dashi har gobe Saif na jinjina karamcin wannan bawan Allah.
Chapter 24 · 0% Book details