Sashe 55
Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Muhibba ta tabe baki kafin tace"Wasu kawaye..?Daman ina da kawaye ne..?Ni ai yana chan kallo bai isheni ba inda ma kika ijiyesa ban jirga sa daga wajen ba."
Anty Habiba ta kama baki Tana fadin"Au Allah..?Ina jamilar nan ta islamiyan ku din nan da Nusaiba..?
Muhibba tace"Ni fa ba kawa ye na bane kawai muna gaisawa ne saboda muna anguwa daya ammh ke kan ki kinsan bani da wata kawa Shakikiya."
Anty Habiba tace"Haka za"ayi Bikin ba kawaye masu mgana da abokan ango..?
Muhibba ta yamutsa fuska batayi mgana ba Anty Habiba bata Damu ba ta cigaba da fadin"To yan makarantar da kike koyarwa fa..?Ko Yaron nan Hafizu ai kya kai ma ya shaida ko..?
Muhibba tace"Kai Anty Habiba Ni bani da wata kawa a makarantar nan kinsan kuma abunda ya faru kuma yanzu suji zan auresa a Tunaninki wani kallo zasu min..?
Anty Habiba tace"To ke ina ruwan ki da mutane ke dai ki fita Hakkin zaman tare."
Muhibba tace"Ba ruwana bar ni na zauna Lafiya chan in sunji agari ba dai a bakina ba domun har gobe akwai wadanda ke min kallon Hadarin kaji a makarantar nan."
Anty Habiba tace"Ai shikenan ammh ni kan na bama Abban Walid ya kai ma Asma"u dana bashi nasu Hajiyarsu sannan zan aika ma Maman Arfat ita da Aisha Kanwarta."
Tabe baki Muhibba tayi bata kara mgana sai da Anty Habiba ta kalleta kafin tace"Sani ya sa ni..?
Muhibba tace"Bana ji domin da ya sani zai kirani karatu fa yayi zafi ya rage amfani da waya ko Chart sai yayi Sati bai hau ba."
Anty Habiba tace"Gaskiya nima mun jima bamu mgana ba ammh zan kirasa na Fadamai kilama Innar tasa ta Kirasa ta shaidamai bata same shi bane."
Muhibba tace"Sosai kinsan Maraya ne."
Ita da Anty Habiba suka saka Dariya Tuna Inna ko abu akayi sai ta ce Allah Sarki dan marayan Allah bashi da kowa sai ni ko kuma in ya kawo wata Bukata Ya Habibu ya fara mai Fadan me yake yi da kudi sai Inna ta shigarmai Tana fadin"Haba Habibu Maraya ne fa bashi da kowa sai mu in bai kawo mana kukan sa ba Sata zai yi?.,shi kuma da yaji haka sai yayi kadan Tsausayi yana Fadin"Wlh Inna Marayu na shan wahaala a wannan Rayuwar."
Sani kenan Inna na matukar ji dashi Gani take yi wahala kawai yake sha achan makarantar.
Ranar Litini da Safe sai ga Kiran Sani a wayar Muhibba tana Dauka ya fara mata Kirarin "Amarya..Amaryan kwamishina Firstlady sai kin yi..!"
Maimakon taji dadi kawai sai ta Fashe masa da kuka sai jikinsa yayi sanyi Cikin Lallashi yace"Haba Auta..Me ye na kuka daga abun Farinciki..?
Muhibba na jan majina tace"Amaryan da ko Lambar angon bata dashi Sani..Ita za"a kira Amarya..?Meyasa baza ku fahimci wani abu ba auran fa ba kamar sauran auran da kuke gani bane, baya sona nima bana son shi Haduwar mu sabani ne ba wani abu ba."
Sani sai da ya gama Sauraranta sannan yayi gyaran murya yana Fadin"Saurareni Muhibba..Kinsan nima da naji Labarin nan ba da ga gida naji ba a waje naji mganar nan"
Cikin mamaki Muhibba tace"Daman ba Inna ko Anty Habiba suka Fada maka ba..?
Da sauri yace"Ba su kirani ba Saboda tun friday na kashe wayata..Da Safan nan na kunnata na hau WhatApps sai naga sakon Abbati na Fatan Alheri shine na Kira Inna na tambayeta sai take Fadamin yadda abubuwan suka Faru Nima da farko sai da nayi mata wannan mganar da kika gama yi min ita Auta ammh kalaman da Inna ta Fadamin sai suka warware Lamarina Jiki na yayi sanyi na sallama komai kinsan me ta fadamin..?.
Kamar Tana ganinsa sai ta girgiza mai kai Cikin sigar lallashi yace"Muhibba ban ga Inna alokacin da muke mgana ba ammh Naji muryanta cikin Tsananin Farinciki kuma yana da Nasaba da wannan auran naki ne muhibba..Ta Fadamin Tun haihuwarki take miki addu"a da Sadakan samun miji Nagari da ingatacciyar Rayuwa,Ta na kuma da yakinin Allah ya Dade da amsa addu"arta ta kuma fadamin har yau bata Daina ba kuma bazata Daina ba Har Abada Ta kuma Tabbatar in babu Alheri aciki Allah zai watsar da mganar in kuma da Alherinsa to za"ayi Kalamanta sun sanyayamin jiki Muhibba kema shi zan maimaita miki kiyi Hakuri ki gayama Allah muna namu ne shi ya riga ya gama nashi Sannan ki sani kowani aure yana da Sabani da Sanadinsa ki yi hakuri ki barma Allah komai abunda ya Kaddara mu dauka Alherin mu ne."
Sai ga Muhibba na share hawayenta Cikin karsasashi tace"Madallah da Uwa bada Mama irin Inna..Madallah da Dan'uwa irin Sani."
Sani yayi wata Dariyan jin Dadi jin ta Saki ranta kafin yace"A kallah dai yarinya tunda bazaki kirani da Ya sanin ba ina Laifi ki rika sakaya sunana Kina Cemin Barrister Sani."
Yadda ya fadi Barrister sanin ne yasa Muhibba ta fara Dariya har sai Da Anty Habiba dake gyaran Falo ta leko Tana Fadin"Wannan dariyan fa ke da waye haka..?
Muhibba na Dariya tace"Ni da Barrister Sani ne."
Yana jinta yace"Yauwa ko ke fa..!
Anty Habiba tace"yaji Labari kenan..?Ai na kirasa ban same shi ba."
Muhibba tace"Abbati ya fadamai ya kira Inna..Kinsan Inna har gidan su sai da ta aika da alewa."
Anty Habiba na barin Dakin tace"Ta kyauta hakkin makotaka kenan..".
Muhibba ta tura baki sai daga baya ta Fahinci sani ya katse wayarsa daman Tana da kudi sai tabi bayansa yana Daga Kiran yace"Ranki ya D'ade Matar kwamishina."
Muhibba tace"Nabi kwamishina da gudu..!
Sani yace"Kai kai kul dinki kada ki yi Zunubi ki zagi mijinki ba ruwana."
Muhibba na Dariya tace"Su miji manya..
Sani yace"Ni dai duk ba wannan ba ki samu ki fara shigar mai da sunana nan gaba kadan sai kiji an zana sunana a matsayin Lauyan gwamnati Tunda nasan ai suna zama da gwamna."
Muhibba ta kwashe da Dariya tana Fadin"Ai sai ka bari ka gama karatun ayi muku calling of bar tukunna Barrister."
Sani ya hade rai kafin yace"Bana son Wulakanci..Aji uku nake malama na Tsallake matakai ni fa daga yanzu in mutum bai kirani Barrister Sani ba Allah ya gani bazan amsa ba.."
Muhibba tace"Har da su Inna da Ya Habibu kenan..?
Sani ya sausauta murya kafin yace"To su dai zan daga musu kafa in sukace Barrister din ma ya wadatar."
Muhibba Dariya hadda rike ciki Sani yaji ransa yayi fari kanwarsa tayi Dariya Cikin Nishadi yake fadin"Yi
a hankali Ranki ya Dade kada ki kware daga sama muji sammaci.
Muhibba tace"Ina da Lauya..Barrister Sani bello mairago."
Sani yace"Kuma fa hakane..Ammh kibi a sannu kada haka ya Rudeki ba mai iya ja da gwamnati."
Muhibba tace"Gaskiya ne Barrister Allah ya ida nufi."
Ya amsa mata da Ameen kafin yace"Ya ake ciki ne me zan samu ne..?
Muhibba tace"Me zakayi da kudi Sani ko fa Ranar naji ya Habibu na gayama Inna ya Tura maka kudi."
Sani ya bata rai kamar yana ganinsa kafin yace"Shi ya Habibu ya Rayuwarsa da haka ne..?Sai yayi ta tallata ni abakin duniya."
Muhibba ta rike baki tana Fadin"Innar ce bakin Duniya.?
Cikin kunkuni yace"Daman ita kikace..?Sai naji kamar kin ce matarsa.?
Muhibba ta kasa Daina dariya Fadi take"Allah ya shiryeka Barrister."
Ya amsa mata da Ameen in da gaske kike yi yarinya ya Daura da Fadin"Don Allah me zan samu ne.?
Yanzu fa kune gwamnati."
Muhibba tace"bani da ko asi..Ina dubi biyar dina dana ara maka baka Biyani ba wajen wata Biyar kenan."
Sani ya ciji yatsa kafin yace"Kash..Haba Ranki ya Dade ba girman ki bane tuna kananan kudi haka kuda kuke Kyauta da dubu Dari kamar baku yi ba..Haba dai gaskiya ki bari in kwamishina yaji saibyace kina kokarin batamai suna."
Muhibba na Dariya tace"ya dade bai ce..Sai ka Biyani kudina."
Sani yace"Y'ar na
harkar arziki fa bada tsiya ake yinta ba..Kamata yayi in anyi gaba asan anyi gaba adaina kokarin ci baya Ranki ya Dade..!"
Muhibba nata Dariya sai da Ya samu ya Lallbeta da Dadin bakinsa tace zata Turamai 3k sannan yace ta kai ma Anty Habiba waya suyi mgana ta mike ta fita a kitchen ta ganta tana goge ta mika mata wayar ta fice yunwa take ji Tashinta kenan Ya Habiba sun Dade suna mgana da Sani sai da kudin Muhibba ya kare sannan ta fito ta iske Muhibba ta Hada Tea tana sha wayarta ta mika mata tana Fadin"Sai Bikin ki sani yace zai dawo."
Muhibba tace"Barrister Sani dai Anty Habiba..!
Tana Dariya tace"Shakiyin banza yanzu ya gama fadamin naci kaniyarsa da Barrister din nan"
Muhibba ta kwashe da Dariya tana Fadin"Kin ci zarafin Barrister sai mun ci ki tara."
Anty Habiba sai Dariya take yi taji Dadin ganin Auta ta warware bayan ta gama karyawa ta gyara falon ta share su siyams suna gidan kakaninsu tun shekaranjiya.
An kawo ma Anty Habiba aikin Cake shi suka yini suna yi washegari sai ga Asma"u tazo sai tsokanar Muhibba take da Amarya ita kuma ta mata bakan tobina wata Amarya wacce ko Lambar ango bata dashi.
Tare suka yini da Asma"u da zata tafi Muhibba tace ta kwana sai da ta Kira Hajiyarsu sai tace ta kwana mana bakomaj Tunda itama tana da yan Hutu bayan su Siyama akwai yaran kanwarsa Anty Mama dake aure a kaduna suma duk suna nan sun zo Hutu.
Zaman Asma"u sai ya kara Debema Muhibba kewa Inna kuma sai dai su gaisa a waya bata Damu da tadawo ba Saboda ta ga tana jin dadin zaman gidan Habiba fiye da nan ita kadai,ammh a daga a inna ta fara Korafin Auta ta Dawo hakanan.