← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 144

Sashe 49

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mujaheed na zama gefensa yace"Kai dai bari bayan mun koma a ka kai mu wani gida muka kwashi gara Man abinci sai wanda ka zaba Bayan mun Natsa bayan sallar mangariba yayan Amarya yazo ya kai mu cikin gidan muka yi gaisuwar surukai bayan mun Fito ne Datti yace yana son Amarya sai gata ta fito ita da kawayenta sai mu ka koma wanchan gidan ashe gidan yayanta ne daya gina muna ta Hira dasu Har bamu san Lokaci ya tafi ba."
Saifudden ya saki Siririn Tsaki Kwata kwata Labarin bai Burgesa ba,Cikin Tura Haushi yace"Da kun sani chan kuka kwana.."
Mujaheed yace"Kaima kasan bazai yuyu bane da chan din zamu kwana"
Saifudden bai kara mgana ba shima Mujaheed din sai ma ya mike yana Fadin"Ka shirya da wuri zamu dauki Hanya."
Daga haka ya fice Saifudden ya rakasa da Harara daman garin duk ya ishesa,Yana gama abunda yake yi ya tashi ya shiga wanka bai wani jima ba ya fito ya Shafa mai ya shirya kansa Cikin wani yadi mai ruwan kasa shara shara ne har ana ganin Shatin Farar Vest dinsa,Yadin da ka gansa mai Tsada ne domin ya bama wasu kudade masu kauri baya.

Bai sanya Hula ba,saboda bata Dameshi ba,bai ma zo da ita ba duk wahala ce,koda karfe goma na Safe tayi duk suna shirye abunsu saboda tafiya da Amare su mujaheed sun tsara komai Mujaheed shi zai Dauki Amarya da iyayanta Salmanu kuma ya Dauki Kawayenta,Ta Mudansir kuma sai ya Dauki su Ummi da sauran mutane ta Saifudden kuma Tsarin da suka zo Saboda sun san ko giwan wake suka shiga Saifudden bazai shiga mota daya da wasu ba,na gida ma ya aka cika da Halinsa.

Karfe 11 na safe da wani abu suna kofar gidan su Sa"adatu ana ta shiryen Shiryen tafiya,Saifudeen na Tsaye bakin motarsa Bama da Tim na gefensa sun sha kuni da bakaken gilasai shi kuma ya Harde kafarsa daya ya jingina da Motarsa.

Hannayensa Sarkafe a kan kirjinsa yana Bin kowa da kallo kafarsa cikin wani ubansu bakin Takalmi,hakama bakin agogon Hannunsa baki na kanfanin Rado ne.

Mujaheed da su mudansir suna cikin gida abun ma har mamaki yake bashi,su rika shiga cikin gidan mata ko ajikinsu Tsakani ga Allah sun bala"in batama mutane Lokaci sai da Sha Biyu ta wuce sannan suka Fito da Amarya da wadanda za"a tafi dasu Saifudden ya Kira Mujaheed yana Masifa sai ce mai yace"Cool Down kasan bazamu dauko yarinya iyayanta basu mata Nasiha ba ko..?

Saifudeen yace"aikin banza nasihan ne duk zamanta dasu basu yi mata ba sai yau..?aikin banza kawai"
Daga haka ya datse kiransa yana tsaki har zai koma Mota suka Firfirto,Har da su Ummi,Amarya ita da iyayenta guda biyu sai kawayenta guda uku,sai su Ummi,Mujaheed ne kan gaba wajen tsara komai Saifudden yayi Tsaki aransa ya Bude bayan mota ya shige kawar sa"adatu dake gefenta ta duka tana mata rada"Kawata waye wanchan gayen da ke tsaye bakin Mota da wasu Askarawa..?

Sa"adatu na cikin Mayafinta Lullube tana kuka tana ta kanta tace"A ina?

Sai ta nuna mata Motar Saifudden daya riga ya shige ciki sai dai su bama Dake ta faman mazurai,Girgiza kai tayi kafin tace"Ban gan shi ba.

Salamatu Bashir azare tace"Ya shiga mota.."
Sa'adatu na jan majina ta kara kallon Motar ta cikin mayafinta daidai sanda Datti yaje ta glass ya sunkunya suna mgana cikin sanyin mganarta tace'Ina jin tare suke da su mine."
Salamatu tace"Ba tare suke ba jiya ai bamu ganshi ba."
Sa"adatu tace"Ba dole sai kin gansa ba na Tuna jiya Mine ya fadamin da Cousin Brother dinsa suka zo yana bani Labarinsa kamar shi ne kwamishinar kudi ne ko na ilimi na kaduna nadai manta.."
Salamatu ta zaro ido kafin tace"Wannan din..?

He is too young fa..?

Sa"adatu bata kara mgana ba,tana ji da kanta,Salamatu kuma sai Faman kallon motar take tana so ta kara ganinsa sai dai bai kara fitowa ba mamakin matsayinsa ne ya kamata ganinsa ba wani babba ba, sai dai zata iya yarda da mganar Sa"adatu ganin su Bama sai zare ido suke yi bakin mota,Tana tare da Sa"adatu kanwar babanta tazo ta riketa sai babbar yayar mahaifiyarta,Suka shiga da ita motar Mujaheed sauran kawayen kuma dama su Hudu ne suka shiga ta Salmanu daman yace uku zai dauka ta Mudansir Ummi suka shiga ita da Hajiya Gaje sai yayar Amarya Hajiya Marliya da yarta Samira shikenan mota ta cika Salamatu bata samu wuri ba da har tace ta Hakura Sa"adatu na Hawaye tayi ma Mujaheed mgana yace baza ayi haka ba ya bude mota ya fita Motar Saifudeen ya nufa yana Kishigide cikin mota ya wani Hade rai Datti kuma bai ma shigo ba Tukunna..

Shiga cikin motar Mujaheed ya yi yamai mganar Salamatu zata dan Raba a Motarsu wani banzan kallo yabi shi dashi kafin ya jinjina kai yana Fadin"U are not serious..Serious Mujaheed.."
Yana fadin haka ya kauda kai Mujaheed yace"Kusa da Datti zata dan zauna motocin ba waje kuma kawar Amaryan ce tace tare sukayi karatu a ATBU Bauchi bazata ji dadi ba in bata samu zuwa ba."
Saifudden yayi mai banza sai da ya kara mai mgana sannan a Fusace yace"Sai dai ko na sauka a motar sai ka sata domin bazan hada Numfashi da wata ba kaima ka sani."
Mujahed yace"Me yayi zafi..?

Saifudeen yaja wani uban tsaki kafin yace"Bansani ba."
Afusace ya bude daya gefen ya fito yana Huci Mujaheed bai yi mamakinsa ba Saboda yasan Halinsa Tunda Datti yaga yanayin Saif yasan bai amince ba cikin Rashin Damuwa ya kalli Mujaheed yana Fadin"Kuje kawai dan"uwa ni da ita salamatu sai mu bi yo ku a motar haya ce daga baya."
Mujaheed yace"Haba don Allah bar wannan mganar dole ma zata shiga motar nan ko wani yaso ko bai so ba".

Saifudeen bai kara kallonsa ransa ne kawai yake na tafasa jin zai hada Zaman Numfashi da wata macen macen da bai sani ba,ba kanwarsa bace ba kuma kowa ba Tashin Hankalinsa Daya Tafiyar bata awa daya ko Biyu ne bace ta awanni ne masu yawa abunda bai Taba Faruwa dashi ba, bayan Ummi da Sadiya da su Laala bai taba Daukan wata mace a motarsa ba Zufa sai keto mai yake yi ji yake kamar wani abu ne zai Faru dashi in ya hada zama da wata macen da bai sani ba.

Yana nan tsaye yana Tunanin mafita sai ga Unmi sun dawo da Mujaheed yana ganinta yasan abunda ya aikata kafin yayi mgana ta rigasa Hannu kawai ta nuna mai tana fadin"Shiga mota mu wuce."
Sai ya tsaya ya kasa mgana balle shiga Motar juyawa tayi tana fadin"Ina wacce zasu tafin tare.

Mujaheed ya yafito Salamatu da Hannu Daman hankalinta na kansu sun Fitowar mai kyau din chan Daga Mota Cikin Takunta na gayu da yauki ta karoso ta gaida Ummi ta amsa Cikin Sakewa sai dai mamakin kamar Ummi da gayen nan mai kyau yake kama sai dai Tunaninta ya Tsaya daidai sanda Ummi ta kara kallonsa tana Fadin"Wai bazaka shiga bane sai na Duma maka Dundu..?

Tafada cikin bacin rai baki ya Bude yana Fadin"Haba mana Ummi..!

Dundun kuwa ta Dirkamai a kafadansa Tana fadin"zan maka rashin mutumci yaro ka shiga nace."
Mujaheed na kunshe dariya yake yi bai yi mgana ba Datti ne yace"Ummi gaban Excort dinsa kike dukansa.

Ummi tace"Ai sun san wajen uwarsa bai wuce duka ba..Shige muje.!"
Sai da ta fada sannan Salamatu ta kara kallon Ummi mamaki ya kara kamata yanzu wannan matar ne mamar Gayen nan mai kyau kamar ba ita ta Haifesa ba yar Caras da ita.

Agabansu ta Bude mota ta shigar dashi Saura kadan ya saka kuka Sannan tace Datti ya shiga sannan Salamatu Bama zai yi Tukin wannan karon Tim na gefe ya kame.

Ta Window ta leke tana kallon yanayin Fuskarsa yadda ya Hade kamar bai Taba Dariya ba ta Daure Fuska itama kafin tace"Yaro ka kula."
Haka kaawai tace mai kansa ya jinjina Cikin wani yanayi kafin yace"Ok Ummi."
Motar su ta koma ta shiga bayan sun gama sallama da sauran Dangin Sa"adatu mutanen arziki sun ga karamcin Motar salmanu ne ta fara yin gaba sai ta Mujaheed sai ta Mudansir ta su Saifudeen ne a baya Tunda suka shiga Motar nan Saifudeen ya juyar da kansa bai ko kara Motsi ba yana ji Datti na Fadin"am sorry Saif..!

Ko juyowa bai yi ba Tsabar yadda Rayuwarsa ke cikin wani Hali Aransa ya gama tsara yadda zai Tatama Mujaheed Rashin mutumcin da bazai taba mantawa ba duk shi ya jamai wannan bala'in suna Fara tafiya Datti ya koma suna Hira sama sama da Salamatu da sai wani karya harshe take yi tana iyayi Lokaci bayan Lokaci Tana Satan kallon Saifuddeen da ko da gigin wasa bai kalli barayinsu ba..

Datti na ankare da ita aransa yayi Dariya kawai in dai Saifudeen ne baya Fatan tayi *Sabo da kaza* (Surayya Dee) ballanta Saifudeen ya yanka mata kazar Wahalarta
Shi kuwa basu san Halin dayake ciki bane gabadaya Tunda suka Fara Tafiya Kunci da Duhu suka lullube zuciyarss,sai kuma zafi dayaji yana Huda Jikinsa kamar ana watsa mai wuta sai zufa sai zufa yake yi tun yana Daukan Lamarin wasa sai yaji kamar ana hura ma Fatar jikinsa ruwa Cikin Bude murya yace"Tim d A.C.."
da Sauri Tim ya kure karfin gudun A.C din Motar,Saifudden har alokacin bai ji ya daina jin zafin dayake ji ba Cikin Tsawa yace"I said.." bai gama mgana ba
Jikin Tim na rawa ya kure A.C din gabadaya Saifudeen bai daina jin yanayin dayake ji ba Salamatu da Datti suka kalli juna Cikin wani yanayi Datti ya kallesa yana Fadin"Lafiya kuwa saif..?.

Ko kallonsa bai yi ba Gabadaya ya Birkice wani irin zafi yake ji yana Buso sa tun daga kasan kafarsa har zuwa Kwakwalwar kansa Cikin Birkicewar yanayi ya kara Daga Murya yana fadin"I said...

Mganar sa ta katse sanda Tim yace"Sir ..
Chapter 49 · 0% Book details