Sashe 34
Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Muhibba ta cije yatsa kamar tayi kuka ta koma ta na Fadama Inna,hakuri kawai ta bata itama Auta ta manta Sani ne ita daman ta sani ya mata wayau ne kawai.
*Littafin Saifuddeen na kudi ne pay N500 via 0552179550 Jamila umar Gt bank,sai a turo evidence of payment ta wannan Lambar 09069067488 ko kuma katin waya na Mtn sai adauki Hoton katin a tura ta wannan Layin kai Tsaye 09069067488 mutanen mu na Niger kuma zasu tuntubi Kausar aglan Nissa ta wannan lambar domin karin bayani +22796562223 Ina maraba da masoya na a duk inda suke*
*Janafty*
*SAIFUDDEEN*
_(Ba mutum ba ne)_
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty*
*Amnaf_sudanese _collection*
*Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401*
Sani bai dawo gidan ba sai bayan sallar isha,'i tara saura sai gashi ya shigo Dakin Inna inda ya tarar da Ya Habibu na zaune yana cin Tuwo Inna na chan gefe saman sallayanta Yayinda Muhibba ke saman gado tana Latsa wayarta Sani nayin sallama Ya Habibu da Inna suka amsa cikin Kallonsa Ya Habibu yace"Yauwa daman kai nake jira..Matso nan ka fadamin mai Auta tayi maka daga dawowarka ka tabata."
Sani ya kalli Muhibba ita kuma ta ballamai Harara rai ya bata kafin ya kariso gefen Ya Habibu ya zauna Lokaci daya yana fadin"Tsakani ga Allah bantaba ganin munafuka irin Muhibba ba..kwata kwata bata da buri sai na ganin ta hadani da Ya Habibu."
Inna na Dariya batace komai ba,Ya Habibu ne yace"Ba wani munafunci ai ka aikata ne nafa san halinka sani.yanzu dai ina alkawarin da kayi mata tunda ta cika maka naka meyasa ita baka cika mata nata ba. ?
Ya fada yana ture kololin gabansa Sani ya marairaice Kafin yace"Yaya to sai ita baza taba aikin Allah ba sai domin abun duniya..?
Ina Laifin najata ga aikin Lada ni fa daman bani da wata gurasa banda ma wulakanci irin na yarinyar nan ina yayanta har sai na Biyata zata min aiki..?
Yaya ka duba fa wannan mganar..?
Ya Habibu ya mike yana fadin"To wa ya ce ka mata alkwarin..?
Sani ya Sosa kai yana Fadin"Tsabar son abun duniya ne ya jamata haka."
Muhibba ta zaburo tana Fadin"Har na kai ka..?
Sani na dariya yace"baki da adalci Mubibba,ni da nake dan makaranta awata ba kudin dake shigomin sai wanda yaga Allah irin su Ya Habibu da Anty Habiba su tuna dani..Yarinyar nan tsabar son abun duniyan ki har ya baci ga ki da uban kudi duk wata kina D'aukan albashi ammh bazaki godema Allah idon ki da komai yana kan d'an marayan Allah..Muhibba ina jiye miki Tsoron wannan son abun duniya kada watarana ya zama ajalinki."
Ba Inna kadai ba hatta Ya Habibu daya daka wanke hannu sai da yayi Dariya Muhibba ta tafa hannu kafin tace"Aiko sai dai kayi ta cewa ina da son abun duniya..bashi ne na daina baka Saboda baka biyani in ka ranta kamar ka samu na Baitil Mali,aje abi wani sarkin ni kam bada kudina za"a kashe ma yan matan titi ba."
Jin abunda tace ne yasa yayi gum bai kara mgana ba Inna tace"Ashe bashi kake lallabawa nema dole ko kayi hakuri mai so ai baya fushi.
Sani na Hararan Muhibba yace"Inna sau daya ne fa..!"
Ya Habibu yace"Ai koo sau nawa ne kadai lallaba sai ka daina damun mu da kumfar baki."
Sani bai kara mgana ba Muhibba kuma sai faman mai Dariya take yi Sani ai ta kiyayi bashi kudinta rence Wlh ita da kudinta sai ta raina kanta kuma in zai biyata biyan wulakanci a rabe rabe kamar ta roka,wani lokacin sai dai ta gaji ta barmai Shiyasa ta yanke shawaran daina basa bashi ko yazo tambaya sai tace ba ta kudi a hannunta ta tura ma Anty Habiba daman ita take turama kudin kadan take amfani dashi bata da wata Lalura gabadaya Ya Habibu shi ke Dauke da Nauyinsu dukkansu bai gaza ta kowani bangare ba.
Washegari sai ga Sani yazo ya na masifa da Muhibba akan sai ta fitomai da Turaransa data Dauka Muhibba ta kekashe ido tace ita bata Dauki wani Turare ba ya kalleta ya kara kallon ta takaici ya kamasa kamar yayi Bindiga yasan ita ta Dauka domin ba wanda zai mai wannan aikin sai ita Turare ne na mata mai Tsada 3k ya siye shi Wata Sabuwar Budurwan da yayi a Tudun wada zai kaimawa tsaraba shine yarinyar nan ta Dauke zata raina mai wayau.
Muhibba na kallon yadda yake huci kamar Dariya ta subuce mata sai da ta kanne Toyan kosai take yi a acikin Kitchen yau kunu da kosai zasu karya Dashi Inna na Daki ita ta taya Autar tata suka wanke waken.
Sani ya kariso kofar kitchen din yayi Tsaye hannunsa rike da kugu yace"Muhibba tun muna shaida juna ki fitomin da Turare na da kika Dauka acikin Jakata."
Muhibba ta kankance ido kafin tace"Sau nawa zan fada maka bani na Dauka ba..?
Sani yace"Wlh ke kika Dauka munafuka waye zai shiga dakina har cikin Jakata ya daukan min abu in bake ba..?
Muhibba tace"Kana da Hujja ne..?
Kawai ka kullamin sharrin sata wlh in na kai ka kotu sai ka biyani tara."
Sani yayi kasake ya kasa mgana sai chan yayi kwafa kafin yace"Zaki sani ne.
Ya juya fuu zai tafi muhibba har zatayi dariya sai taga kuma ya sake dawowa sai ta kanne gabanta ya Durkusa ta kallesa yadda yayi Laushi kafin tace"Miye kuma..?
Sani yace"Don Allah muhibba in kin gani ki bani..Wlh ba nawa bane na Sako ne fa."
Muhibba tace"A ina zan gani .?ni fa tunda ka dawo ko Kofar Dakin ka ban leka ba nace maka Allah bani na Dauka ba.."
Sani yayi shuru yana kallonta ta juya tana Fadin"Tunda an dauke sai ka bama mai sakon hakuri haka Allah ya kaddara.
Tafada tana kokarin Danne Dariyanta Sani ya Mike yana kallon Muhibba kafin yace"Nasan ke kika Dauke sa..bakomai ki je don kanki..Sannan ki sani ba Hali bane daukan abunda ba"a baka ba sata ne karara."
Muhibba in tayi mgana Dariya zai fasallata,Sani ya juya ya fita daga kitchen din yana fadin"Wlh in ma mugunta kika shirya kin ma kanki ne..Domin cikin abunda zan bada na gudumuwar auranki zan cire kudin wannan Turaren kinga kin ma kanki ne bani ba.!"
Daga haka ya wuce Dakin Inna Sai alokacin Muhibba ta saki Dariyanta har da Buga Cinya,Tana jinsa ya leka yana cema Inna"Kina dai jinta ko Inna..?Autar ki dai ta koma halin dan bera sai ku rika kafa kafa da kayanku..tana jin Sanda Inna tayi Tsaki Tana Fadin"Ni rabani da sabgarku.
Daganan ta jisa ya koma Dakinsa kamar zai tashi sama muhibba tayi Dariya har cikinta na ciwo har da Hawaye,Jiya nan daya bata haushi yana guduwa ta shiga Dakinsa daya manta bai rufe ba jakar daya dawo da ita ta bude nan taga Turaren ta kuma san na mace ne tunda an saka For Women,kuma tana da tabbacin wata ya siyamawa Sani ko Cikinsa sai yayi ma kwange saboda yima yanmata Hidima tako Daukesa ta kai Dakinta ta Boye Cikin kayanta,ko da ta gama suyan kosai suna karyawa adakin Inna sai da Innar ta kara tambayanta in ta Dauki abun sa ta basa Muhibba ta karkace tace ita bata Dauka ba sai Inna ta kyaleta Sani Saboda Takaici bai ko sha kokon da kosan ba Ya Habibu kuma yau Lahadi bazai fito da wuri ba..
Sani dole ya hakura da Turaren nan daman a ranar yake so yaje gidan su yarinyar yakai mata Tsaraba yanzu kuma Muhibba ta bata komai,shi kuma bayason yaje hannun Rabbana a matsayinsa na Babban yaro kuma yace Inna ta aramai dubu uku tace bata dashi kuma yasan tana dashi ta hanashi ne kuka ne kawai sani bai yi ba Muhibba kuma shawaran yadda zai Rama abunda tayi mai kawai yake yi shi Fatansa ma Allah yasa watarana Atm dinta ya shigo Hannunsa ya Rantse ga Allah ko nawa ne aciki sai dai taji asalansa sai dai daga baya ayi wacce za"ayi.
Mubibba bata fito da Turare ba sai Ranar Talata da Daddare ta dauko ta bama Inna tace ta rika fesawa Inna ta kalleta kafin tace"Ke daman yanzu ke kika Dauke shi turaren nan..?
Muhibba tace"Inna da wata chan ta fesa ai gwara ke ki fesa."
Shiyasa na daukeshi.
Inna ta girgiza kai tana fadin"Allah ya shiryamin ke Auta.
Muhibba tace"Ameen Innata..Don Allah kada ki maida masa har zai iya siyan ma budurwa turare Inna ya manta Dake..?
Ai bai ko kyauta ba.."
Inna tace"Allah ya baki miji nagari Auta fatana kenan saboda ke macece mai jin kan iyayenki.
Muhibba ta amsa da Ameen suka cigaba da Hirarsu aiko Inna bata gayama sani mganar Turare ba,Duk da ba fesa turaren take ba tadai adana shi Cikin kayanta zatayi kyauta dashi in taje gaya ko Bakori.
Ranar Laraba bayan Muhibba ta dawo daga makaranta ta shirya zata tafi gidan Anty Habiba tana shirin Tafiyar ne Sani ya shigo gidan ganinta da Jaka yasa ya kalleta Lokacin datake Daura dankwalin Atamfar dake jikinta yace"Inna ina wannan yarinyar kuma zataje..?
Inna na gefe kan Tabarma tana bare gyada tace"gidan yar'uwarku Habiba.
Sani yace"Chan zata koma ne hala naga ta Dauki rabin kayanta ne tana Fama da wata uwar jaka.
Muhibba tace"Yau dai zan tafi sai kaji kanka agidan..."
Sani yace"Ai ni ba wannan tafiyar nake bukata ba..Malama ki bar mana Filin Daki ki tafi gidan mijin ki, ki barni dagani sai uwata..
Muhibba tace"aiko nayi aure inna tawa ce sorry guy.
Sani ya karkace kai kafin yace"Wai don Allah ina zaki ne..?