← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 144

Sashe 138

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai Tsaye nace"Zan saka maka ni dai bani Labarin"
Sani yace"Shegiya Auta"
Bata rai nayi kamar yana ganina nace"Au nice ma Shegiyar da Mijina har da Tsohon ciki..?

Da Sauri Sani yace"Kaina Bisa wuya Hajiya Muhibba mai ciki"
Dariya nayi ban ce komai ba shi kuma sai ya cigaba da fadin"Ni ma yadda Anty Habiba ta dan gayamin kinsan ai taje duba Babanin chan bakorin tace Inna kadai ke wahala da ita..Su goggo Shatu suna zaune ba abunda suke taimakama Inna,Babanin kuma ta fadama Innar su basu yi ba sai surukanta..?ai naka sai naka Dadin zama kuma sai bare gani inna tayi Babani na cikin wani Hali Shiyasa ma ta yanke shawaran Daukota bayan ta Tuntubi ya Habibu"
Kai na jinjina ban iya cewa komai ba sai Allah ya kyauta mun Dade muna mgana da Sani yace min suna saka ran nan da Lokaci kadan Za"a su shiga Bar nace mai ina ya nema da Sauri yace min"Abuja na saka"
Ina Dariya nace"Kai sani ina Laifin Kadunan mu..?.

Sani yace"Tab Ai nagaji da ganin kaduna na gwara na sauya sheka kin ji"
Ina Dariya nace"Sai kun fito kenan zaku je Service..?

Sani yace"In sha Allahu"
Kai tsaye nace"Allah ya taimaka ya nuna mana da rai da lafiya.

Mun cigaba da Hirarmu acikin Hirar ne,ma nake fadamai mganar zuwa Gida na Haihu da kuma abunda Inna tace Sani yayi dariya ya buga kafa kafin yace"Tab..Kice zaki jegon Kauye..Ko bakomai zaki sha kunu da Tuwon dawa"
Bata rai nayi kamar yana kallona nace"Wlh ba inda zani"
Sani yace"Ahto gwara ki kama Mutunciki ki zauna gidan mijinki ki Haihu asirin ki a rufe saboda Inna yanzu ba ta kanki take yi ba..Dake zataji ko da Babani..?.

Mganar Sani gaskiya ne shiyasa ban kara ma wata mgana ba mukayi sallama,Muna gama wayar na Turamai dubu biyu katin waya sai gashi ya kirani yana fadamin meyasa ban Turamai ta banki ba kai Sani akwai son abun duniya.

Tunda naji haka sai na Shafama kaina Lafiya da mganar zuwa gida nayi jego na Saifudden kuma bai kara min mganar ba Domin yaga yayi min ban ce mai komai ba duk da shima ba son Tafiyar tawa yake yi ba.

Mganar Sani ta tabbata Domin na kira Inna washegari na gaisheta ta Sanar dani ta dawo gida tare da Babani,Ban tsawaita ba nayi fatan Allah ya bata Lafiya na kashe wayata da Daddare da Saifudden ya Dawo na Fadamai Inna ta Dawo tare da Babani sai yace gobe zai shiga Zaria sai muje mu dubata Tun da ga Zeeha sai ta zauna kafin Wasila ta Dawo daga makaranta..

Haka kuwa akayi duk da Nauyin Cikina da yayi kasa alamun ya kai watan haihuwansa haka na shirya na Bisa muna Hanya naga Saif nata kallona yana kunshe Dariya a Fusace nace"Bangane ba kana kallo na kana Dariya ba..?

Domin Tunda cikina ya Tsufa nazama Masifaffiya.

Cikin Daga Hannu yace min"Ni kika ga ina yi miki Dariya..?

Kaina na kauda ban kara mgana ba na Bude Jakata na Dauko wayata na shiga Camera ina Duba kaina nan na Gano Munin da cikin ya sani yake ma Dariya komai na Fuskarta ya kara Girma Kumatuna sun kara girma sannan duk nayi Duhu Ba ma kamar Hancina da na ga yau kamar ya kara zama wani sunduki na taba shi da Hannuna na dago Lokaci daya Ina kallon Saif da yake kallona Muna Hada ido ya kauda kai yana Dariya kawai sai na yi wurgi da wayar Hannu na Dauki jakata iya karfina ina Bugamai Lokaci daya na Fashe da kuka sai ya Rude ya fara kokarin kare kansa yana fadin"Muhi...muhi...Muhi"
Ban sauraresa ba sai makansa nake yi Cikin kukan shagwaba nake fadin"har ka samun abun dariya..?

Waye ya maidani haka in ba kai ba..?

Ko Damuwa da su Bama dake gaban Mota ban yi ba,kuma suna jin mu sai dai basu juyo ba Dakyar ya samu ya Rikeni bayan ya kwace jakan Hannuna ya Rumgumeni ina ta mutsu mutsun kwace kaina na kasa sai na koma nayi lakwas ina jan majina..

Cikin Tattausan murya ya min rada"Haba Muhi daga wasa...?

Kirjinsa na Daka ina Fadin"Bana son wannan wasan ka bari"
Da Sauri yace"Angama ranki ya Da'ade"
Yafada Lokaci daya yana Saramin Dariya nayi ina Tura baki na Dago kaina ban ankara ba naji yaja Hancina yana Dariya a fusace na Juyo na make hannunsa na bisa na Turmushe da Sauri yace"Muhi.."
Da dan karfi ya nuna min su Bama sai na kom chan gefe na zauna na Hade rai ina Hararansa kunnuwansa ya kama Duka Biyu ya wani marairaice min ni kuwa na kara Hura Hanci na Kauda kai har muka iso Zaria yana ta shan Uban Hararanta.

Shi kuma bai daina bani Hakuri ta Sigar yaren Kurame ba.

Mun iske Anty Habiba agidan Saboda haka bayan Saifudden ya shiga sun gaisa da Inna ya Duba Babani da ke ta barci ya shiga cikin makaranta ya barni.

Anty zeenatu sai tsiya take min da Fadin"Auta kada fa ki haihun mana anan"
Ina jinta ban yi mgana ba Anty Habiba ce tace"Shikenan ma kinga ai Gida ta dawo".

Ina jin su ban tanka ba ganin Inna ma batace komai ba Dakin Inna daman aka Sauki Babani shiyasa bayan mun Idar da Sallar azaahar a Tsohon Dakina ni da Anty Habiba taga ina ta bata rai ta kalleni tana fadin"waya ta mana Autar gidanmu..?

Na tura baki ina fadin"Wai don Allah kin ga abun dariya a fuskata ne Anty Habiba..?

Ta kalleni ta kara kallona tana fadin"A"a ni ban ga komai ba sai Sauyawar Hallitar dake jikin ki..Rai ne a tare dake kike Dauke dashi Dole komai naki ya sauya Auta"
Kallonta nayi kafin nayi kwafa ban ce komai ba ta kara ce wa"Me ya faru ne Hala..?

Cikin Takaici nace"Ba Saif ne yake ta min Dariya ba..Tun fa ban gane ba har na gane yau muna hanya sai ya kalleni yayi Dariya sannan kwanakin nan bai da aiki sai na ya jamin Hanci yana Dariya"
Me Anty Habiba zatayi in ba Dariya ba,na kalleta raina ya kara baci Cikin gatsali nace"Ko kema zaki ja Hancin ne sai ki yi Dariyan ki me Dalili..?

Da Sauri tace"Ayyah yi hakuri Auta..Rabu dashi bari ki haihu ki Dawo Sisin ki sai kin yi mai yanga"
Kai na girgiza kafin nayi mgana Sani ya Fado Dakin na dago ina kallonsa wani Uban zabura yayi yana kallona Har da wani kasa da glass din da ya sanya a idonsa irin kallon nan na Sama da kasa.

Anty Habiba na kallon mu Dariya na cinta tace"Baka gane ta ba ne..?.Auta ce fa..?

Sai Sani ya Dafe kai da kirji kafin ya zare glass din idonsa yana fadin"What Auta ce ta koma Haka..?

Bura uba waya ga Bulunbuto sunan wani Abun yara ba"
Anty Habiba sai da ta kwanta Saboda Dariya ni kuwa raina ya kara baci na nuna kaina ina kallon Sani nace"Ni ce ma mai kama da Bulunbuton..?

Sani yace"Gaskiya sunan ta gaskiya Auta..Kuma tana da Daci kin ga Hancin ki..?

Ya fada yana yar Dariya yunkurowa nayi na mike na warci wani Jug dake gefe na ruwa na wurga ma Sani yayi Tsalle ya fice Daga Dakin yana Fadin"Bafa ni na kai zomon ba Rataya aka bani balle ki Huce a kaina"
Tab daman wai haka masu cike suke komawa.?.akwai babbar masala in dai hakane".

Daya tabbatar da na Harzuka bai Dawo Dakin ba ya shiga Dakin Inna muna jin su suna mgana Dagachan kuma ya kara gaba.

Ganin yadda na ke ta Sakin Huci kamar wata mesa yasa Anty Habiba Bata tankani ba sai da ta ga na Sauka har ina Daukon Anmir dinta,ina mai wasa ganin haka yasa tace min"Ya mganar da muka yi kwanaki zaki Dawo ki yi jegon ne agida..?

Ina Tura baki nace"Ina fa Kinajin abunda Inna tace..Sannan ga shi ta Dauko Babani,da ni zataji ko Da ita..?

Anty Habiba tace"Da wannan don wannan..kuma kinga Haihuwar Fari ce duk ba dole ba ne ki dawo gida sai a samu wacce zata zauna dake kawai ki yi zaman ki agidanki"
Na yamutsa fuska kafin nace"Ni fa da naje Gaya nayi jego gwara naje Lere gaban iya ko kuma Naje Abuja wajen Ummi na zauna nasan zata Kula dani"
Anty Habiba ta gyara zama tana Fadin"Kul kar na kara jin wannan mganar a bakin ki Auta..Komai Lalacewar naka sune naka..Gayan da kike gudu nan ne tushen mu duk in da mukaje muka Dawo wlh bamu da kamar su suma basu da kamar mu..Sannan in aka tsaga jininmu aka Tsaga nasu duka abu daya ne..ammh inda kike Tunanin zuwa chan din ba naki ba ne Auta kara ne kawai da zumunci,Saboda haka ko da wasa kada ma ki kara fadin wannan mganar wani yaji ko da Mijinki ne sai ya raina ki sannan ya Raina ahalin ki komai Lalacewar Naka Dangin to ka Kimanta su a gaban mijinka da Danginsa"
Tabbas mganar Anty Habiba Gaskiya ne sai naji jikina ya mutu ta cigaba da Fadin"Kowani zuru'a kika gani suna da nasu nakasu..Ko chan lere da kike Tunani yaushe ne Ummin ta samu Saken su ba sai kwaanan ba..Itama ai babu abunda bata gani ba ammh kuma Ai shi Saifuddeen din bai gushe su ba Duk da Cin kashin da suke yi ma Mahaifiyarsa kinga kenan ya nuna miki Suma nashin ne kuma ba'a sauya ma Tuwo suna Auta komai lalacewar su Goggo Barira bazaki je Gaya kiyi Jego su barki haka baki kula da ke ba..Ko banza ai sun san Dan'uwan su Bello ya Haifeki akwai wannan Darajan jinin da bazai bari su wulakanki ba suma ai sun san nasu ko Mahaukaci ne kuwa yasan nashi da wanda ba nashi ba"
Cikin gamsuwa da kalamanta nace"Hakane na bar mganar daman mun fadama kowa ba sai ke"
Anty Habiba tace"Yauwa ko kefa..?
Chapter 138 · 0% Book details