← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 144

Sashe 98

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ban kawo komai ba nace"Eh Inna tun jiya"
Kai Tsaye tayi mirmishin su na manya kafin tace"Allah ya zaunar daku lafiya Duk wani sharri Allah ya Tsare ku.

A kunyace na amsa mata Tunda da na Dawo gida ko da yaushe Inna sai ta Kirani taji Lafiyata ta kuma kara Tunasar dani amfani da abunda mallam Haruna ya jadaddamin haka ma Ummi da su Adda Sadiya har da Mujaheed ba abunda zan ce ma Dangin mijina sai godiya sun Tsaya kai da Fata wajen Lalura ta.

Wekeend
din nan mun yi shi cikin Farimciki matuka,har yawo ya Dauke muka tafi ni da wasila ya shako mana Siyayya har da ita,Kaya na saka ya siya mata domin tana Bukata Gida muka wuce ya gaida Inna sun ji Dadin ganina Lafiya,wasila muna zuwa ta Ruga gida tana bama Babarta labarin Dadin da take ci,Sai da zamu koma muka je gidan Saif ya gaishe da Lami yayi mata alheri tana ta godiya fadi take"Bayan kudin hakkin ta kuma Alhaji har da wani Dawainiya..?

Kai Tsaye yace mata"Ba kudin aikin wasila na baki ba Mama nayi miki kyauta ne a matsayina na yayan Wasila"
Daga haka ya fice tayi godiya da addu"an kamar zata kwanta mana ni kaina sai da ta bani Tsausayi muna Hanyar komawa gida duk abunda muke Tattaunawa kenan cikin Harshen Turanci Tunda muna Tare da Wasila a bayan mota.

Bai koma ba sai Ranar Litini da Safe,yaso ya tafi dani to ba Dama Saboda mallam Haruna yace na zauna waje daya na gama amfani da mgangunar daya bani ammh bai tafi ba sai da na batamai rai da mganar komawata makaranta kallo na yayi cikin mamaki kafin yace"Muhi na dauka kin hakura da wannan aikin..?

Ina tayasa Daura Tek Tie dinsa nace"Ina son aikina Saif don Allah kada kace zaka hanani."
Bai kara min mgana ba sai da muka rakosa ni da Wasila yake ce mata"Wasilar Uncle ki kula da Anty kin ji ko..?

Da kai ta basa amsa ya sake fadin"In bata cin abinci ki Dauki wayarta ki kirani ai kin iya ko..?

Da Sauri tace"Uncle ban iya ba"
Dariya nayi ina musu gwalo kaina ya Rankwsa na wasa Lokaci daya yana Fadin"Zan kamaki ne"
Ina rike da wayoyinsa ya karba ya bama Bama shi kuma Tim har ya Bude mai mazaunin baya,Hannuwana ya rike bayan Wasila ta koma cikin gida,Cikin wani yanayi yace"Ki kular min da kanki don Allah Muhi"
Cikin Daga kai nace"In sha Allahu.Sai dai ina so na koma makaranta Student suna Debemin kewa"
Rai ya bata kafin ya sakeni sai da ya shiga Motar sannan yace"Muhi ba domin mganin da kike amfani dashi ba bazan barki anan ba..Take Care sai mun yi waya"
Haka ya tafi ina Dagamai hannu kuma naki barin mganar har da mukayi waya sai da na kara Tunamai ganin haka yasa ya shareni daya kira mun gaisa zai ce na bama Wasila da na bata sai ya fara tambayanta naci abinci..?kamar loma nawa..?

Dame dame naci..?

Ita ko ta zauna tana Famam zayyamai Tun yana bani mamaki har yazo yana bani Tausayi so na yake yi yana son ya Kula dani Saboda mganar aikin nan yasa yaki zuwa Satin nan sai cemin yayi yana da Taro sannan an gayyace sa Confrence kan abunda ya shafi ilimin jahar Kaduna bazai samu zuwa ba nan kuwa Rigimata yake gudu.

Aiko bai Tsira ba Domin yana Dawowa na kara tadamai da mganar Saboda malaman makarantar mu sun kara zuwa gaisheni,Har da su Anty Usaina,sai bayan La'asar suka tafi sai tambayata suke ko na bar koyarwa ne sai dai nayi shuru nace zan dawo.

Daya ga na tada mai da rigima sai ya kalleni yana fadin"Muhi nace miki bazaki koma aikin nan ba meyasa bakya jin mgana ne..?

Me kika nema kika rasa..?

Kina fama da kanki da wannan Lalurar zaki koma cikin mutane ne a kara samin matsala..?

Tun da naji ya fadi haka nasan ya kashemin wannan Burin nawa ai sai na kwanta na fara kuka da Birgima ina Fadin"Wato ga mahaukaciya
kada naje cikin jama"a na fara hauka dole kace haka..kuma bani na sakama kaina Lalurar ba Allah ne kuma bar Izgilanci kaima baka fi karfin Allah ya Jarrabce ka ba"
Har ga Allah ba da wata manufa na fada abunda na fada ba ammh sai naga ya kara Daukan zafi Cikin wani irin kallo ya kalleni kafin yace"yanzu ni kike jefa ma da wad'anan mganun muhi saboda ina neman kare lafiyarki..?

Je ki yi abunda kika ga Dama rayuwarki ce"
Daga haka bai kara kulani ba Da na Fahimci na bata komai sai na Shiga Taitayina ammh har ya koma bai Shiga Harkata sai dai zai Tsaya na shiga mganina naci abinci ammh baya sakarmin Fuska sai dai yayi ta jan Wasila da Hira abunsa.
da zai tafi bayan ya barnin kudi da wasila kadai yayi mgana sai duk naji ba Dadi Anty Habiba na kira na Fadamata abunda ya faru ta hau ni da Fada tana fadin"Auta kin yi sakarci mijinki me sonki mai kula da Lalurarki shine zaki gayamai mganar banza..?

Ina kuka nace"Wlh ba da gangan bane"
Tsaki taja kafin tace"Ban da wawanci Albashinki fa kin ce bai yanke ba Aikin ne yace ki daina zuwa Saboda Lafiyarki ammh kike wani iya Shege..?mata nawa ne ke bukatar irin Damarki Allah bai basu ba..?

Ina sharan Hawaye nace"To ya zan yi yanzu yana ta Fushi dani ko kira na yayi sai dai yace na bama Wasila"
Anty Habiba tayi Tsaki kafin tace"Ban sani ba.kada ki kirasa ki basa Hakuri ki zauna shi ya baki..Kuma wlh na karajin mganar aikin nan da Inna ko ya Habibu zan hadaki su yi mganinki"
Da sauri nace"A"a bazan ma kara ba Don Allah kada ki fada musu.

Bata Saurareni ba ta kashe wayarta,Da Daddare da ya kirani ina Dauka yace min"Ba ma wasila wayar"
Kawai sai na sakamai kuka ina yi har da Jiniya samin baya son kukana.

Sai da yaji kukan ya fara kassarashi sannan yace"Me kike so nayi miki Muhi..?kince ban kyauta miki ba ina Izgilanci da Laluranki na baki Dama kiyi yadda kike so menene Laifina anan..?

Cikin kuka nace"Eh mana da Laifinka ka shareni ka daina kulani sai dai ka kira kace na bama wasila.

Mirmishi yayi kafin yace"Ai tayani kula dake take yi muhi duk motsinki ita take fadamin komai kawai na kyaleki ne ki yi yadda kika ga Dama har ga Allah bazan takura miki ba.

Ki koma aikin ki in ma kikace na kori kowa a makarantar zan koresu sai ki zauna ki yi ta koyar da Student din Tunda haka kike so"
Baki na Tura kafin nace"Ni bana so..Bazan koma ba Tunda baka so.!

Da Sauri yace"Are u sure..?

Kai na gyada mai kafin nace"Am sorry"
Mirmshi yayi kafin yace"Na yafe miki Muhi nima am sorry kin ji ko..?

Cikin shagwaba nace"Sai kace i Love u Muhibba.."
Yana Dariya yace"Muhi muhi..Ina sonki..Zaki kasheni watarana Lokaci na bai yi ba..Zan fada ma Ummi kin kusa kashe mata yaronta'
Ina Dariya nace"Yaro..?

Yarooo..?

Kamar yana ganina yace"Ke..Ina wasa dake..?

Sunan nan fa Ummi kadai take kirana ina Shuru"
Cikin son na ZOlaya shi nace"Yaro na.."
Yana jinjina kai yace"In na kamaki Sai kin fadamin waye yaro."
Bakina na Danne ina Fadin"Meyasa Ummi bata iya kiran sunan ka..?

Kai Tsaye yace"An ce Iya ce tajamin in Ummi na min wasa ina jariri sai tace tayi rashin kunya ni ai na Fari ne..Mama zuwaira tace duk Iya ce tajamin wannan kunyar farin wajen Ummi"
Ina dariya nace"Iya bata kyauta ba"
Shima Dariyan yake yi kafin yace"Ina rabaki da iya..Nima nan ta sha Hadamin gadar zare ina Tsallakewa dakyar"
Nan ya shiga bani Labarin abunda ya faru lokacin da iya ta Dake sai an yi koman Majeeda da sanda ya Zurmasu iya har da zuwa wajen mai mgani sai gashi ina Dariya har da rike ciki ina Fadin"Laaa Saif.."
Yana mirmishi yace"Na"am Muhi di'na"
Saboda Dadin Hira sai wajen sha biyu muka gama wayar shima shi yace naje na shafa mganina na kwanta kada na manta nayi addu'ar barci kafin na kwanta bamu rabu ba sai da yaji na fara barci sannan ya katse kiransa.

Haka Rayuwarmu ta cigaba da gangarawa lafiya kam ta samu a wajena mganar aikina kuma Saifudden ya soke shi kowa yaji sai yace hakan yayi daidai Saboda Im kula da Lafiyata,Ina jin Dadin zama da Wasila matuka saboda tana Debemin kewa sannan anyi Hutun makaranta siyama da Walid sun zo min Hutu sai gidan ya cika sai kuma ga bakin Abuja Laala da Zeeha da Majeeda,sati daya suka min kamar kada su tafi sai dai ba Dama Ummi tace zasu je Lere chan majeeda zata karishe Hutun ta su koma su laala in suka Dawo zasu tafi suleja wajen dangin babansu.

Weekend din da zasu tafi Saif ya Dawo muka fita dasu shopping yayi musu siyayya duk abunda suke so sai da ya siya musu Wasila taje ganin gida,Muna Hanyar Dawowa Ina gidan gaba Ni da Siyama su Laala na baya har da Walid yana ta Buga game a wayata na kalleshi hankalinsa na wajen Tuki ta madubi na kalli Laala ta min Signa cikin sanin kan mganar na jinjina mata kai kafin nayi gyaran murya nace"Hamma ka siya ma su Laala komai ka manta da abu daya?

Bai kalleni ba yace"What is dis...?

Kai Tsaye nace"Wayoyi mana"
Sai da yayi kamar bazai tanka ba yana gani suna min Signa ta baya yasan kwanan zence kai tsaye yace"Ba wacce zata rike waya yanzu sai nan gaba"
Laala ta subuce baki tace"Sai yaushe Hamma..?

Juyowa yayi yana Hararanta Lokaci Daya yana fadin"I know..Ko tarin ki na karaji sai na tattakaki marasa kunya kada kuyi facing karatinku ku zauna kuna zencen banza"
Laala ta kama bakinta kanta na kasa Majeeda ne da Zeeha suka hada baki suna Fadin"Ba ruwan mu Hamma!

Kai Tsaye yace"I don"t care ko da ruwan ku ko ba bu..Na riga na yanke Hukunci"
Jin sun yi Tsit ne yasa na kallesa nace"Haba mana Hamma"
Mirmishi gefen baki yayi kafin yace"Ai nace na gama mgana ko Adda Muhi..?
Chapter 98 · 0% Book details