← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 144

Sashe 91

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saboda cikin Anty Habiba ya Tsufa yasa ta roketa ta bata Siyama ta rika kwana a wajenta zaman ita kadai ba Dadi da ta tambayi babanta sai ya amince shima Saifudden din yaji Dadin haka yana son Siyama sosai tare suke zuwa makaranta su kuma Dawo tare sai yarinyar ta rika Debe mata kewa matuka.

Ana Haka Anty Habiba ta Haihu Sai suka fara zirga zirga da Hidima ta samu namiji yaci sunan Baba Bello an yi ma Anty Habiba Kara.

An sha suna sosai Muhibba kwananta uku sannan ta koma gida ita da Siyama Saifudden ma ba"a barsa a baya ba yayi bajinta matuka a sunan kawayen Anty Habiba nata Santin yadda Muhibba ta koma tayi kiba ta kara Fari ta murje,Siyama dai bayan suna taga jariri ta gudu gidansu Muhibba ta koma sai ita kadai gashi yanzu sai yafi sati biyu bai zo Zaria ba ko ma ya shigo kwana Daya ne,Wani Lokacin ma sai ya shigo cikin Abu bata sani ba sai ya koma sai ya kirata ya fadamata.

Cikin wannan Halin da Tsukin da suke wanda yayi daidai da Wata goma Cif da auran su komai ya Sauya..Guguwar Kaddara ta Fara Walagigi da Rayuwar Muhibba"
*Janafty*
*SFD0033*
*Amnaf_sudanese _collection*
*Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401*
*Ki biya ki karanta cikin salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba, kada ki karanta min littafi sannan kada ki yada'min shi don Allah pay N500 via jamila umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*
Wannan satin ba su da wani aiki sannan bai da shiga office shiyasa tun ranar alhamis ya shigo zaria wannan kwanaki ukun da suka yi tare da Muhibba sun sa ka shi cikin Ranakun Tarihin su na auren su domin sun bama junansu dama fiye da Tunanin kowannen su,Saifudden bai fita ko'ina sai ko masallaci da yanzu ya zame mai jiki daganan kuwa yana gida Tare da Muhibba,har ya koma ba tayi girki ko sau daya ba duka fita suke yi su ci abinci,ya hanata girki har sai ya koma zaman da suka kara yi Muhi ta kara Fahintar waye mijinta yana da barkwanci da zolaya sannan yana da Kirki matuka fiye da yadda tayi Tsammaninshi ta Dauka mutum ne mai Tauri da Rashin Sakewa ashe ba Haka bane yana mgana sannan yana barkwanci da wasa da Dariya sai da zama yayi zama Tsakaninsu sannan ta kara Fahimtarsa.

Ranar Lahadi har goman Dare suna Rufaida yoghourt na Pizzet,suka sha Fura da yoghourt,Sannan suka riko Bread din su suna mota suna Hira cikin Farinciki da Annushuwa Restaurant ya biya da su suka yo Oder Ferfesun kayan ciki da Chips suka tafi dashi,Kamar kada gobe tayi yace zai tafi kaduna daya ga ta Damu sai yace ta shirya su tafi kaduna wani Satin Sai su dawo tare sai tace ya bari sai ya kara Dawowa.

Ranar Litini da Safe ya tafi ammh sai da ya fara shiga cikin makaranta yayi ma Dalibai karatu sannan ya wuce Kaduna tare suka fita ita tana Motar ta shima yana cikin tashi Bama na Tuka sa Tim na Hakimce a gefe har Kofar makaranta suka rakata sai da yaga Shigarta sannan ya sa suka juya kan Mota zuwa Samaru.

Zaman Kadaici ne duk ya isheta mun yi mgana da Anty Habiba tace na Fadama Mijinta in ya amince sai a neme mata yarinyar da zata taya ta zama to bata samu damar mai mganar ba Satin da ya ce zai shigo bai Samu shigowa ba,bai fada mata ba ne bai jin Dadi yana ta Zazzabi Mujaheed ne da Adda Sadiya suka rika kula dashi kuma ya Rokesu kada su fadama Muhi kada Hankalinta ya tashi.

A waya ta fadamai mganar mai taya ta zama shi kuma ya amince tayi ma Inna mgana Daman kwanaki Ummi ta fara mai mganar shima yaga Dacewar haka shiyasa yace a samo ko nawa zai biyata In sha Allahu jin dadin haka yasa ta Kira Inna suka yi mgana,Inna tace zata je wajen Hajiya karima ta mata mgana a bincika a mokota in da aka san baza'a samu wata matsala ba.

To an ta bincikawa ba'a samu ba Inna tace kada ayi gaggawa a bari a samu a inda ya Dace shiyasa sai mganar ta dan Tsaigaita.

Sani ya diro garin Washegari daga makaranta Muhibba gidan Inna ta Sauka,Yana kyalla ido yaga Motar nan ya karbi key ya shiga gari ai Muhibba gajiya tayi da jiransa ta hau Mashin ta koma gida washegari ma Keke napep ta hau zuwa makaranta Motar nan sai da ta kwana uku ya kawo mata gida Shima Inna ce ta fara Fadan bata san rashin hankali ta saka Ya Habibu yayi mai mgana Dole ya maido ma da Muhibba motar ta ita bata wani damu ba,Dadi ma take ji ta na da wani abun da Dan"uwanta zai iya Karba a wajenta har ya Mora hakan ma arziki ne.

Ana cikin haka akayi rasuwa a lere mace ce ta rasu babar Diyar Baffa Hayatu ce tayi aure da yaranta Hudu ban santa ba ammh naji mutuwarta matuka Tare da Inna muka tafi Da Sani achan muka kwana Daya muka Hadu da Ummi da su Majeeda,Iya tana ta ina zata saka damu Har Ummi na mamakin yadda Iya ke Nuna min kauna inna Talatu ma haka kamar ta Goya Ummi ganin yadda Rayuwar Majeeda ya kara inganta,Sai a ranar da zamu dawo Saif ya shigo garin shi da Mujaheed da Sadiya da take fama da Laulayin ciki Ummi na ganin haka ta ce Maza su kai ma Mama zuwaira Nihad ta yayeta Kawu ma yazo shi da Isma'il sai dai Mama Zuwaira ba ta zo ba Daman tace ma Kawu Ummi ta Dauke mata ba sai tazo ba.

Dole Muhibba ta bar su Inna suka koma Washegari ita kuma sai da ta kara kwana Daga Umarnin mijinta,Sai da akayi uku gidan ya watse Ummi ma aranar ta koma har da Majeeda Saboda makaranta Adda Sadiya kuma Gaya suka wuce saboda kai Nihad wajen Mama zuwaira kamar yadda Ummi tace.

Satin bai koma har sai Lahadi sai gidan yayi mata Dadin zama har ta girki tare suke yi yana tayata da Hira da Yanka albasa ko juya abu akan wuta ,Sallah kuwa wani Lokacin shi yake jan su jam"i acikin gida Dukkansu sun yi kiba sun chanza kamar ba su Hankalulan iyaye da yam"uwa sai ya koma ya kwanta Ganin ya"yan nasu cikin kwanciyar Hankali musamman Ummi da Inna da suka fi uban kowa zullimi.

Cikin Tsukin akayi bikin Asma"u naje akaci Biki da ni,Saif ya Bani dubu Ashirin na bata gudummuwa,sannan washegari ni na tuka su Anty Habiba zuwa gidan Amarya a samaru zata zauna duk inda nabi sai bi na ake da kallo ni kaina na san na sauya nayi Kiba ina cin mai kyau ina shan mai kyau sannan ina Dora mai kyau ba iya ni ba Kaf Dangina suna yabon Halin miji alheri bana sanin yayi musu sai dai a Kirani ace nayi mai Godiya musamman Sani da suka zama so close da juna sai dai ya Kira ta yana Fadamata yallabai ya tura mai kudi yayi mai kaza yayi mai kaza Rashin Kulatan da bai taba yi a Shimfida ba bai fara Damunta ba sai a wannan Lokacin da ta kara sanin ciwon kanta Anty Habiba sai tsiya take mata taga tayi Kiba ko ciki gareta ita dai ta kasa Fitowa ta fadi wani abu Dangane da auranta Sirrin nan ta rike shi bata Fatan wani ko wata su ji wannan al"amarin.

Abunda ke bata mamaki shi ne ko Hannunta ya rike a bisa kuskure da Sauri yake sakinta kamar wanda wani Shooking ya ja sa ko ya taba wani abu mai cuta itama ko da kuskure ta tabasa haka yake mata tun bata Daukan abun wani abu har ta fara Damuwa zasu yi hira da wasa da Dariya ammh ko kadan ta rabe sa sai yanayin sa ya sauya yanzu nan Annurinsa zai Dauke daganan ma sai dai ya shige Daki ya kwanta sannan Tun bayan zuwan su Abuja suka kwana Daki daya bai kara yarda sun kara kebewa Daki daya da Niyar kwana ba,ita ko Muhibba shirye take in dai zai gayyaceta ba zata ki amsa gayyatan nasa ba.

Acikin watan aka kira su daga Unites States Universtiy(USU) dake San_Diego,california domin karban Cerficate din na Shedar Degree din su akan abunda ya shafi Na"ura mai kwalkwala wato computer da suka yi Duka Karatin su ta Online.

Yaso ya tafi da Muhibba domin har ya fara nema mata Visa sai kuma aka yi rashin Sa"a ta fara rashin Lafiya Zazzabin Dare mai zafi da ciwon kai ba Domin tafiyar Dole ba ce da bai yi ta ba,ammh Gida ya maida ta gaban Inna kafin ya tafi,Sati daya yayi ya Dawo abun mamaki yana barin kasar Muhibba ta mike garas Daman Inna nata bata mgangunar gargajiya tana Fadin maleria ce ke saka Zazzabin Dare Da farko tayi Tunanin ko Ciki ne sai da taga Muhi din na Fashin Sallah Sannan ta Sare ba ciki bane.
Chapter 91 · 0% Book details