← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 144

Sashe 59

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mirmishi tayi kafin ta juya tana Fadin"Nagode Allah ya kiyaye hanya."
Bata jira komai ta shige gida shima Mujaheed ya sa sakon bayan mota kafin ya shiga mazaunin Direba su bar anguwan sun Dauki hanya Mujaheed ya kaleesa yana kara Tempreture din A.C din motar kafin yace"Amaryanka tana da kunya.."
Ko kallonsa bai yi ba ballatana ya tankasa Hankalinsa ya fara kwanciya jin zafin jikinsa na Raguwa.

Muhibba kuma data koma cikin gida Inna ta nuna mata kudin da suka Zube mata tana su zo su dauka suka ki Dawowa itama sai taje ta Dauko na wajen nata ta bama Inna,Inna ta rike Baki kafin tace"Allah ya saka da alheri."
Muhibba ta Zazzage ledan Sadiya kayan kwalliya na kamfanin makari Zube acikin ledan kama daga Turaruka da mayuka Inna ta Bude baki kafin tace"Duk naki ne wannan..?

Muhibba tace"Adda sadiya ta aiko min dashi."
Sai inna ta fara sharan kwallah Tana Fadin"Dangin sa suna kaunarki Auta..Allah yasa gidan zamanki ne sai ki kirata ki yi mata godiya."
Muhibba aranta ta amsa da Ameen kafin ta kwashe kayan ta maida leda Kudin hannun Inna ta bari shashen Anty Zeenatu ta koma ta kwashe komai ta maida kitchen ganin basu ci da yawa ba ta gyara mata Dakin ta kulle mata ta koma Dakinta.

Ta kira Adda bata Dauka ba sai daga baya ta Kirata Lokacin tana gidan su Anty zeenatu suna suka gaisa ta mata Godiya Sadiya tace ba komai an zama Daya ta tambayi ya suka isa Sadiya tace tun dazu suka iso gida Lafiya Hamma na gidansa Mujajeed kuma na ciki yana Hutawa Muhibba tace in ya tashi ta gaishesa.
*******
Ummi hankalinta ya kwanta dataji Labarin zuwan yaro zaria bakin Sadiya sannan sun yi waya da Muhibba sai dai da ta tambayeta kunya yasa ta kasa bata amsa Abun da ke Burge Umma kenan gata Ta taso Cikin Birmi tayi ilimin zamani bata da Karamniya na yan matan zamani nan kunyarta da natsuwarsa yasa take Fatan ta zamo Haske ga Rayuwar yaro.

Ummi taje lere ta kwana Daya suka Tattauna da Iya,Iya ta bata Daman tayi sha"anin ta in da taga dama su dai anan zasu yi nasu Bikin,Ummi tace Tana Tunanin chan gaya zata koma suyi Bikinsu Tunda basu da kowa achan Abuja yan"uwa duk suna nan Iya tace hakan yayi nan ne ma Iya ke Fadamata mganar Saifudden na Daukan Majeeda ya kai mata Ummi batayi mamaki ba sanin Halin yaro bata nuna ma Iya bata san da mganar ba sai ta nuna mata ita ta Bukaci hakan in Talatuwa da Hashimu zasu bata Majeeda zata tafi da ita Abuja ta hada ta dasu Laala iya taji Dadin haka nan take tasa aka kira Baffa Hashimu da matarsa daman ta sanar dasu zencen Baffa Hashimu ya aminta Talatuwa ne taki amincewa da cewarta aure ya kamaci Majeeda ba zaman bariki ba.

Ammh yadda taga Ummi ta nuna tana son Daukam Majeedan sannan Tun farko suma dasawa da Ummi bata da matsala ko kadan daman tayi shawaran da yan"uwanta suka nuna mata ba komai cigaban su ne,Domin Majeeda zata samu ilimi da chajin Rayuwa nan take ta amince Ummi taji Dadi tana ta godiya ta amsa da cewa zata rike Majeeda kamar ya"yanta Laala da Zeeha ammh saboda Hidimar dake tasowa sai bayan Biki zata tafi da ita su iya suka amince Goggo Atika ce tayi ta fushi Saboda ba Majeeda taso a Dauka ba taso a Dauki Daga cikin ya"yanta ne Sanin Halin ta yasa ba wanda yabi ta kanta kafin Ummi ta bar garin sai da ta ce ma majeeda ta shirya ta kusa zuwa ta Dauke su koma Abuja Majeeda Murna da Farinciki kamar zai kasheta Mutanen gidan sai taya Talatuwa Murna suke yi domin wannan babban Cigaba ne.
daga Lere Ummi gaya ta sauka Daman bata da aiki kwana uku a Satin su Laala suna da makaranta wajen matar Barrister Mu"az ta bar su Dr Laila likita ce,Nan ma kwana Daya tayi ta juya bayan sun yi mgama da Kawu kan nan zata dawo ayi Bikin Kawu yace suma su Baba Surajon sun ce nan Habibu yace za"a Daura auran.

Shikenan ma ta kwana gidan Sauki Mama zuwaira tayi mganar Hada Lefe Ummi tace ta kira D'anta suyi mgana.

Haka kuwa akayi Mama zuwaira ta kirasa da Farko yaso ya fara mata mganar baisan lefe ba data Fara Fadanta bai san Lokacin daya amsa mata ba Miliyan biyar tace ya Tura mata in ma da Ragowa zata Dawo mai dashi.

Bashi da Mafita Hakan nan ya Tura mata Saboda yasan ko giwan wake yasha bazai yi wasa da Mama zuwaira ba, Tsab sai ya ganta a kaduna ba wani abun Damuwa bane.

Ita da Umma Babba suka ziyarci kwantin kwari na Kano suka hado akwatina da kayan lefe akwati goma Shake da kayan arziki wajem miliyan hudu da rabi suka batar suka yi tasha Mota da kayansu suka Dauko hanya chan suka kwana a kanon Saboda sun yi Dare gidan yayan mijinta in da ake Rikon Saudat washegari da wuri suka iso Mama zuwaira ta kira Ummi ta Fadamata sai tace su bar kayan nan kafin tazo sai a shirya kaiwa in sun Fadi in da za"a kai musu kayan.

Chan zaria ma sai faman shirin su suke yi ita dai muhibba nata ido ne Sadakin ta,Ya Habibu ya hada ya bada aikin Gado da kujeru ta Hannun mijin Anty Habiba kaninsa nayi dayake na gida ne kaya mai kyau masu inganci,Kayan kitchen kuma Daman Kudin albashin Muhibba in ta Turama Anty Habiba kayan kitchen take siya Daya bayan daya tana yarwa da aka Duba kaya cike sai kadan da za"a kara,Ya Habibu yace ba matsala waken suyarsa ya saida Anty Habiba da Zeematu ke siyayar har katifu sun siya dayake gado Biyu Inna tace ayi mata itace Auta.

Ita Muhibba bata ma ta kansu sun koma makaranta Hankalinta yayi gaba Ango ko waya bai taba mata ba Tunda suka tafi gwara su Mujaheed ma sun yi waya sau biyu bayan Tafiyarsu da Sadiya ne suke waya ita ma ta tambayeta Size din takalmanta da Iners dinta kuma ta tambayeta menene blood group dinta Tace Da Ita B POSITIVE ne,sannan Gegontype di'na AA ce Sadiya na dariya tace shima Hamma AA ne ammh Blood group dinsa O POSTIVE ne.

Tace itama AA ce ummi ta fada musu Abbansu ne A.A.

Biki ya rage saura Sati Biyu Ummi ta Kira Inna kan inda zasu kai Kayan Lefe Inna tace su kai su gidan su Mihibba na Gaya iyayenta su karba Sosai Ummi ta ke yaba ma Inna wajen karamci,Nan kuwa aka kai kayan Ummi bata ma samu zuwa ba ta waya taga kayan Saifudeen kuma ko ta kan al"amarim ma bai bi ba.

Su goggo Naja dasu Inna Firdausi da su Goggo Fa"iza da Goggo Barira da makota suka hadu suka karbi kayan arziki masha Allah sai wanda ya gani sun kawo kudin dinki 50k aka basu tukwaici suka ki karba Baba Surajo ya basu Buhun masara da Wake Tukwaici suka karba suna Godiya Mama zuwaira ce da Umma babba da karama sai Sadiya data zo aka kawo kayan da ita.

Kwana Biyu Tsakani Inna Firdausi da Goggo Naja suka Dauko kayan lefe da Fati suka kawo zaria su Anty Habiba da Makota suka karbi kayan arziki ana Budewa mata nata saka albarka Muhibba sai da suka watse ta iya ganin kayan Daga nesa,su Anty Habiba sun Tsara hatta su Goggo Naja zaria zasu taho ayi Biki su bar mazan chan tunda su iya nasu Daurin aure ne nan akayi mganar jere Anty Habiba ta tambayi muhibba ko tasan inda zata zauna tace bata sani ba.

Sadiya Anty Habiba ta kira ta mata mgana ita kuma ta kira Ummi ta Fadamata,ita da kanta ta kiraasa ta tambayesa gidansa na Zaria Muhibba zata zauna ko na kaduna.?

Saifudden ya kasa cewa komai Ummi kuma ta yanke mgana tace Zaria zan zauna Saboda aikinna yace shikenan zai Turama Sadiya address din gidan akwai megadi basu da matsala Ummi tace Ya turama Muhibba din bai iya gayamata bai da lambarta ba, yayi gum da bakinsa.

Shi fa bai yi komai ba duk abunda ke Faruwa Mujaheed ke gudanar da komai,har ta katunan Biki shi ya Bugashi Hardcopy da Softy Copy gayya fa Mujaheed ya ke yi ba d'an kad'an ba domin yace sai Labarin Bikin ya fita Duniya kowa yaji.
*Janafty*
*SFD022*
*Amnaf_sudanese _collection*
*Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401*
*Ki biya ki karanta cikin salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba, kada ki karanta min littafi sannan kada ki yada'min shi don Allah pay N500 via jamila umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*
Kaf mutanen sa sai da Mujaheed ya Turama Michel sakataransa ya turama musu harda commissiors din su na kaduna gabadaya sai dai waya kawai yake samu na Fatan Alheri da Tambayan ashe aure zaka yi Lere..?

Dayake haka wasu ke kiransa shi dai sai dai yake bai da bakin Mgana kuma yana da Tabbacin har gwanna Sakon gayyatar ya iske sa tunda shi mutum ne mai Kula da kuma amfani da Social media sosai domin sanin abunda ke faruwa a Jaharsa da kuma sharhin mutane akan mulkinsa duk da yana da masu take masa wannan bangaran ammh shi a karan kansa baya wasa da duk abunda ya shafi al"ummar daya ke jagoranta.
Chapter 59 · 0% Book details