← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 144

Sashe 7

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Koda Sadiya ta fito Falon karaf Daidai Lokacin da Inna Atika ke nuna Ummi Tana fadin"Karya take yi iya..Wlh ko Rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba Tasan inda D'an iskan yaron nan yake..Tasani ai itace uwarsa sannan in akwai wacce ke zuga Saifuddeen wajen Bijiremana ai itace.

Kada ku yarda da Magiyarta da wannan kukan munafuncin data saba Rudar ku dashi"
Tafada tana jin kamar ta kai ma Ummi Duka wacce ke duke a kasan Saman Cafet din Dake falon inda Iya ke zaune ranta bace tana Faman jijjiga Jiki Baffa Hashimu na gefe ya kasa mgana Baffa Hayatu na zaune kan Hannun Kujeran da Iya ke Zaunee goggo Atika da Daman bata bar komai na Tijaram iya ba, tsaye take ta kasa zama tana Faman auna ma Ummi Dake duke tana sharan kwallah gaban Iya harara.

Kafin Sadiya tace wani abu Laala Dasuke leke a Dakin da suke tayi Zaraf ta fito Tana Fadin"Iya mganar gaskiya Ummi fa batasan ina Hamma yake ba..Muma nemansa muke yi.."
Tafada idonta kar domin bata da Tsoro.

Ran Iya ya baci ta Dago tana kallonta kafin tayi kyaci Lokaci Daya tana Fadin"Su cin Danko har da su kaza..?

Ke kuma miye naki aciki..?

Da zaki sakomin baki ina mgana..

Kaji min ja"irar yarinya mara kunya.?

Tafada tana kumfar baki ko Tsufanta bata Duba ba,Domin ta tsufa kawai jin Dadi me ya lullubeta Ammh zata bama Saba"in baya sai dai ganin yanayinta zakasan tun tana matashiyarta ta iya tijara da bala"i.

Goggo Atika ce ta rike Haba kafin tace"Iya abunda aka kitsa mata ta Fada mana fa.

Ke yarinya ki kama bakin ki kafin yanzu ki shiga hannuna ki raina kanki.."
Laala ta juya ido zatayi mgana Ummi ta Dago Cikin kwallah kafin tace"Shema"u koma ciki nace.."
Kin tafiya tayi ganin Ummi na Hawaye ta kasa mgana sai Zeeha ta fito kamar tayi kuka tana Fadin"Ummi..!

Kafin Ummi Tayi mgana Adda Sadiya ta shigo Tsakiyar Falon tana Fadin"baku ji me Ummi tace bane..?

Ku wuce ku koma Daki kada wacce ta Sake fitowa."
Ba su isa suyi musu ba yasa Zeeha ta kama Hannun Laala suka koma dakin da suka fito suka Hada kai suka Fashe da kuka aduniya basu da kamar Ummi Shiyasa basa son zuwa lere saboda babu Alheri kwata kwata a zuwansu kowani Lokaci Ummi tazo da kuka take komawa..

Bayan fitan su Laala Falon Sadiya ta kalli Iya tana fadin"Ina kwanaku iya..?

Dukkansu ba wanda ya amsa sai Baffa Hayatu,kadai ya amsa sai jikinta yayi sanyi Bayan Ummi tabi ta Duka Tana Fadin"Dom Allah kuyi hakuri..Ba Laifin Ummi banee..Wlh batasan Hamma..!

"Ke rufe ma mutane baki..ai kema munafukar ce.."
Baffa Hashimu ya tareta tun kafin ta karisa kawai sai ta saka musu kuka Tana Fadin"Wlh gaskiya na ke fada muku..Bamu san me yasa Hamma yayi haka ba kuma bamu da masaniya.."
Iya tayi wani Dariyar rainin Hankali kafin tace"Ai ko jikina duka kunne ne bazan yarda ba Sanin Zaliha yaron nan ya Tozartamu ba..Komai yake Faruwa tana sane ita ke saka shi..Haka yayi ma Amira kuma ita ta sakashi Saboda ba Dangin ki ya Dauko ba ko Zaliha..?

Shiyasa kika saka shi Daki jiya kika basa Umarnin Sakin Majeeda,yarinya karama da batasan komai ba,an maida ita bazawara Gida nachan ya koma kamar gidan makoki uwarta da Danginta sai koke koke suke yi Hashimu sai kiran yaron nan ya ke yi bai same sa ke kika ce wayar ma ya kashe ko Zaliha..?

To gamu acikin gidan nan ko mu ko ke Zaliha"
Goggo Atika ta karbe da Fadin"Sai Saifu yazo gabammu ya Fada mana Dalilinsa na Tozartamu muji ko ya Sauya wasu Dangin ne damu.."
Ummi na kuka ta kasa mgana Sadiya ma Nayi iya ta gaji da jin kukan su ta Daka ma Sadiya Tsawa tana Fadin"Ki rufemin baki munafuka kema ai duk Daya kuke ba, man ta saka kika yi d'an uwanki Shitu ba..?

Ta aura miki D'an kanwarta ko..?Danginta sune Dangi mu kuma duk yan iska ta saka kuka Daukemu..?

Rufemin baki Kafin na saka Atika ta Nada miki Dukan tsiya.."
Sadiya tayi tsit sanin Halin Iya ada suna shiri ammh tun mganar auranta suka samu matsala Saboda taki Shitu yaron wajen Baffa Hayatu ne shine harda shi Haushin da suke ji na Ummi Iya ita adole sai sun dawo gida sun Auri Dangi Kada Ummi ta Karbesu Gabadaya duk da kuwa Hamma a wajensu ya tashi bayan rasuwar mahaifinsu kwace su sukayi Hannun Ummi ita kadai suka bar mata ta koma gaya inda yayansu yake da zama da iyalansa Kafin ta sake yin wani aure ta koma Abuja da zama.

Baffa Hashimu ne yana Huci yace"Mufa ba kuka muka ce ki Tsamu kina mana ba Zaliha baki zaki Bude ki Fadama ina yaron nan Saifu yake..?

Nayi rantsuwa bazan yi kaffara bai isa ya maida min y'a karamar bazawara ba karyansa tasha karya wannan karon.."
Ummi na kuka tace"Wlh bansani ba sau nawa zan rantse muku..bansan inda yake ba.."
Atika tace"To ke baki san ina yake ba wa kike so ya sani..?

"Ku zaku san inda yake mana..Tunda kuka makala masa auran da baya so.."
Atare dukkansu suka waigo suna kallon Mama Zuwaira tsaye kikam da Hijabinta Data gama sallah Fuskarta ahade suna ganinta suka kara Hade rai sanin Halinta mai zafi ce bata Daukan raini ba kamar Ummi bace
Atika ce tace"To ta ya ya kuma mu zamu san inda yake..?

Kudai kukasan inda kuka Boyesa Tunda abun naku rashin mutumci ne."
Ko kallonta Mama Zuwaira batayi ba,Ta isa ga Ummi tana Fadin"Yaya zulai ki daina wannan kukan don Allah..Taya ya zaki zo su tasaki suna Fada miki mganganu haka kiyi shuru..?

Ko baki yi musu bayanin kema baki san me ya aikata ba ballatana ya gayamiki inda yake ba..?

Ummi na kuka tace"Zuwaira na Fada musu basu yarda bane..Tayani kara Fada musu wlh bansan ina yaro yake ba."
Mama Zuwaira tace"To ba kin gaya musu ba..?

Zaman me kike yi taso muje Daki kiyi wanka na kira yaya sunusi yace yana Hanya yau zai Taho.."
Ummi ta Dago tana Fadin"Jiya fa ya koma Zuwaira..?

Mama zuwaira na Hararan su iya tace"To ai ta kama ne..Gani nayi zasu yi miki Taron Dangi gwara yazo su san kema kina da gata.."
Atika ta tsoma baki da Fadin"Ina gatan yake..?

Nace ina gatan yake yar kanzagi..?

Mama Zuwaira ta Daga mata Hannu Tana Fadin"Ke Atika ki iya bakin ki Domin ban saka Dake ba.."
Tafada cikin Kaushinta sanin Halin Zuwaira yasa bata kara mgana ta koma tana wani zare ido.

Baffa Hashimu ne ya kalleta sanda ta tada Ummi Tsaye tana rike da Hannunta ya kada kai kafin yace"Ke zuwaira har yanzu bazaki Daina Rashin Da"arki ba.

Ko..?

Iya ce ke mata mgana kika D'agata me kike nufi..?

Ta kallesa wani Shekeke batayi mgana ba illah Hannun Ummi data Damke tama Fadin"Muje kiyi wanka Yaya zulai don Allah.."
Ummi bataso tafiya ba Mama Zuwaira ta jata tana Fadin"Sadiya saka su Laala su Dafa mana ko Ruwan zafi ne mu sha Tea in yaya sunusi ya iso yau gaya zamu wuce domin banga amfanin zaman mu anan ba.."
Sadiya murya dishe ta amsa mata su Iya suka bi Mama Zuwaira da kallo har ta Shige da Ummi Ciki Atika tace"Kan bala"i Iya..!

Iya ta Daga mata Hannu Tana Fadin"Kada kice komai Atika..Ai zuwaira daman bata da mutumci ko na Miskala zarratin..ki bar su muna nan sai dan"uwan nasu yazo ayi ta kare..Wlh Tallahi wannan karo ko ni ko Zaliha..Kuma Auran Majeeda kamar Saifu ya maidashi ya gama zai gane ni nayi Nagudar Ubansa yazo Duniya Tunda ya zama d'an jakar Uba.."
Atika sai kara zuga iya take Baffa Hashimi kuma sai Huci yake saki ga waya a Hannunsa yana ta kara kiran lambar Saifu bata shiga Baffa Hayatu dai na zaune shi dan cewa abi komai a Sannu ne.

Sadiya kuma sai da tayi aikin Lallashin kannen nata kana suka shiga Kitchen suka Dafa ruwan zafi suka soya Dankali Saboda sha"anin nan da kayan abincin su suka zo Duk da daga Babbar gidan su Ad
da Sadiya din ake aiki musu da abinci n suka zo garin, gidan da suka sauka Gidan da Hamma da Sadiya suka gada ne nq mahaifinsu suka Bugesa suka falala ya koma na zamani nan suke sauka indai suka shigo Lere kamar koda yaushe.

Su Iya kuwa basu jirga ba sun yi Rantsuwa sai an yita ta kare duk suna zaune su Laala suka gama Hada Breakfast,Sadiya ta kawo musu goggo Atika ta mata tsawa tace ta kwashesu hakanan ta kwashe jikinta a sanyaye.

Ummi kuwa tana ciki tayi wanka Mama zuwaira ta lallabata tasha Tea ta bata panadol Mganinta na Hawan jini ya mata karfi tasha shi yanzu sai zuwa Dare.

Banza da su iya Sukayi Mama zuwaira ko kara lekosu batayi ba itama ta gaji kan Damuwar yar"uwanta itama ta amince yau ko so ko dangim Saifuddeen
Har ta su Laala sun yi wanka itama Adda Sadiya tayi wanka ita da yarta Nihad sannan tana jiran kiran Mujaheed ne ya sanar mata agidan gwamnati Su Saifudeen suka Shiga meeting din ammh zai jira ya gani in sun fito ko Shi Saifun din ya Hallacin Taron..?
Chapter 7 · 0% Book details